Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 40195 words

Chapter 6 - ZAMAN AURE Book Complete Document .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

538

Ads at the middle of Article

da wulakancin da kakemin ,nifa nafara zargin.....


kan takarasa ya katseta cikin karaji idonsa yakada yai ja borin kunya duk ya kamashi ya ce






"Areefa!,dakata kar kiyi gigin cewa kina zargina dan mutukar kika furta hakan ,wlh sai na dau mummunan mataki akanki ,kinfara daukar zugar kawaye ko ,to kiyi bazan hanaki ba amma kisani bazatai miki kyau ba"






"Hmm,Hafeez kenan ai banason dama taimin kyau kawai de kana borin kunya ne ,kuma wlh bazan yarda ba"




dagowa yayi ya zuba mata daradaran idanunsa masu mutukar kyau kan yayi magana wayarsa tashiga ruri hannu yasa a aljihunsa ya zaro wayar kan yadaga ta fizge wayar ta nufi daki da sari.








*NASEEBAGAWO*
✍🏻
[3/19, 10:29] β€ͺ+234 814 620 5819‬: οΌ»6:19Am,2017οΌ½








*@πŸ’¦πŸ’¦NASEEBA GAWO*πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦








*ZAMAN AURE*
πŸ’¦πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™‚πŸ’¦








*NA*


NASEEBA I UBAπŸ’










*Subahhhanallahi wabihamdihi subahanallahi azim,tawakallatu ala hayyu lazi la yamutu,Alhmdulillah ,ala kul halin*










*sakon gaisuwa gareki ummy aisha dafatan kina lpy,Naseeba nata cigiyarki,ina gaidaki kyauta bada ko sisi ba*πŸ˜ƒ
















*16*










~~~cikin dakewa sakna ta dago da idonta ta dubi kamal,shiru tayi batare data ce masa kalaba,cikin daurewar fuska ya dubeta yace,




"wace magana kika fadawa lubna,da har zata tareni wai tanason magana dani"?




yafada yana zare mata idanu kamar wani ubanta,ahankali tadago da kanta ta zubawa fuskar sa ido tace,




"Banfahimceka ba kamal,kana tunanin zan zaunar da lubna infada mata sirrin *zaman auren mmu* ne,to bahaka nakeba,saboda haka kadena zargina akan abinda bani da masaniya akai,duk me yayi zafi,kawai dan naki biye maka wajen sabawa ubangijinmmu,bisa ga kyautar da ba kowa yakewa ba,sai ga wanda yaso,asanda yaso,shine kullum burinka ka daga min hankali,wlh kamal ka ji tsoran Allah"




tana kaiwa nan taja bakinta tayi shiru shikuwa dada harzuka yayi yacigaba da surfa mata masifa ,cikin daga murya yadakatar daita tare da daga mata hannu ya dora da


"malama yaisa haka ki adana kalaman bakinki dan karshenta zasu amfaneki nan gaba,amma bayanzuba,dan kunnuwa na basa,kaunar jinsu"




kuka ne ya kwacemata cikin fushi ta dubeshi tace




"wlh kamal kaji tsoran Allah ,kasani Allah yana iya jarabar ka ta inda yaso asanda yaso wace irin rayuwa ce wannan kakeyi inajiye maka fadawa tarkon abokai domin *sandin aboki* babu halin da bazaka fada ba,wlh nasan su suke zuga ka"




wata razananniyar tsawa yadaka mata ya zubawa fuskar ta ido kana ya dora da


"sannu,yar masana ko ince alhuda huda,sarkin sani ,meyashafeki dacsbokaina dahar zaki sako su cikin lafazin bakinki,to kibude kunanki da kyau kiji abinda zanfada miki,








*Jameel*




cikin kankanin lokaci jameel ya kammala hada break fast,juyewa yayi a kula yanufi dakin labiba yai saa ta bude tana tsaye jikin mudubi daga ita sai towel juyowa tayi ta kalleshi ta dauke ido,ajiye kayan hannunsa yayi, yakaraso kusa da ita ya tsaya ta bayanta ahankali ya kira sunan ta da kasalalliyar murya




"Everlasting,pls kiyi hakuri da abinda naimiki jiya wlh nakasa control din kaina ne,nakai makura,baason raina hakan tafaru ba,but innshaallahu ,i will never do it again"






banza tayi masa tacigaba da shafa mai a fatar jikinta,tare da yaye towel din jikinta ,take tsigar jikin jameel ta tashi saboda yanayin da yaga labiba ,dama tarko ta dana masa ya kuma kamashi ,shiru yayi yacigaba da kallonta ,ahaka ta shirya tsaf,hannuta yakama ya nufi inda yaajiye kayan abinci yazuba mata ,tare da bata abaki ,cikin kissa da shagwaba,tadubeshi,tace




"jameel,wlh mutukar kanason= zaman lpy,a gidannan sai ka biyani wahalar da kabani jiya kuma
bakai ba fita ko nan da can sai bayan kwana uku,haba ka dinga abu ba tausayi ba imani aciki"
ido ya tsuramata saboda yadda
kalamanta suke mutukar sosa masa rai,amma ba shi da yadda zaiyi haka ya hakura ya biye mata ,yarasa dalilin da yasa baya iya yiwa labiba musu,ahaka rayuwa tai tafiyarwa da jameel shi yake komai na aikin gida ,yau tun safe,yatashi da wankin kayan labiba ,dan taki,yarda adinga kaiwa gurin wanki,tana kwance a parlor tanacin apple kawai sai ji tayi ,








*Abdulmalik*






sanda Abdulmalik ya shiga parlon Ruhaima tana toilet da sauri tafito tasameshi tsaye kallonsa tayi tace






"Malik,lafiyarka meyafaru haka,wlh ka daga min hankali "




cikin kankancewar ido ya dubeta ya dora da ,




"yazaki ki bawa inna abinci,kan wane dalili,hakan tafaru,Ruhaima inna fa uwa tace,bazanyarda ki wulakanta min ita ba,gsky "




shiru Ruhaima tayi tarasa ma mezatacewa Abulmalik ,inna kuwa tana labe tanajinsu ,kuka ne ya kwace mata cikin shasheka tace




"Haba Malik,tayaya zanhana inna abinci ,wlh nadafa mata couse couse,tace bataci ,kuma gas ne yakare da sai nadafa mata wani abun,gaskiya nagaji wlh ya kakeso nayi "






jikinsa ne yai sanyi ganin ta tana kuka rarrashinta yashiga yi tare da kwantar mata da hankali ,hakan da inna tajine yadada bata mata rai aranta take tunanin Ruhaima ta asircemata da ,kwafa tayi tajuya zuwa dakinta ,haka rayuwa tai ta tafiya yau da dadi gobe ba dadi kamar kullum Abdulmalik ne zaune a parlorn inna misalin 9. 30 na dare ta tsare shi da hira tun yana fahimtar ta har yagaza ganewa ,Ruhaima kuwa tana daki tana jiransa shuru be shigoba,sai wajen 11 sannan tabarshi ya koma parlornsu kai tsaye daki ya nufa yai wanka yashirya cikin kayan baccinsa masu kyau da taushi ya haye gadon jikinsa yajata ya shiga yana shakar kamshin turaranta ,dada shigewa tayi jikinsa ,tare da aikawa junansu sakonnni kamar daga sama sukaji muryar inna tana buga musu kofa shiru sukayi can yataso yana tambayar ta lpy,cikin rawar baki tace,








*Hafeez*








cikin zafin nama Hafeez ya riko Areefa tare da murde hannunta ya kwace wayarsa,nan tashiga surfa masa rashin kunya ,banza yaimata yai shigewar sa,dakinsa hade da sawa kofar key,gajiya tayi ta nufi dakinta wanka tayi ta haye gadonta tashiga neman layin Alhj Namidi kamar jira,yake ta,kirashi bygu biyu ya daga nan suka shiga hirar su kamar ba matar aure ba,


washegari Hafeez be fitoba ,sai wajen 8,lokacin tana zaune kan dining tana break fast,ko kallonsa batayiba ,zama yayi yaja cup yashiga hada tea yanayi yana danna wayar sa can tanisa tace


"zanje gida anjima,dan haka ina bukatar kudi ,saboda zanbiya saloon"


shiru yaimata kamar bejita ba ,sajen da yakewaye fuskar sa yashafa yace.


"ya da saurin sakkowa haka,kenan kin tabbatar min nike da iko da ke ,da kuma gidana ko,kwana biyu kina da damuwa Areefa,ko meye dalilin hakan?"




shiru taimasa ta hau karkada kafa tare da lumshe idanunta ,murmushi yayi sannan ya dora da




"mutukar naisa dake ,to bainda zakije dan banbarki ba"




yana gama fadar haka ya kwshi wayoyinsa tare da ajiyemata kudin cefane ya fita,harara tabi bayansa da ita ,sai kuma ta mike tanufi daki.








_Lallai wannan shine zaman aure ko wanne da irin nasa_πŸ€¦πŸ»β€β™€








*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:29] β€ͺ+234 814 620 5819‬: [6:19Am,2017]






*@πŸ’¦πŸ’¦NASEEBA GAWO*πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

*πŸ’¦N I G*πŸ’¦










*ZAMAN AURE*
πŸ’¦πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»πŸ’¦






*NA*


NASEEBA I UBAπŸ’










*Alhumma anta amartana biduaika,wa wa,addana biijabattika,fakadi daaunaka kama amartana yazul jalalu walikiram,wahasbunallahu,waniimal wakil*πŸ‘πŸ»πŸ˜°










*Hakika wannan shafiin nakine kawata ta kaina BILLY LADAN,marubuciyar prince sadeeq,Naseeba na mika sakon gaisuwa gareki,bazan boye miki ana mugun tare* 🀝🀣












*17*










~~~shiru sakna tayi tana sauraron kalaman kamal masu kama da zubar garwashi,shikuwa cikin isa,da irin salon masifar sa yake fadin,




" sakeena,nafiskanci yadda wuyanki yai kwari ko tunda har kinkai matsayin da ina fada kina mayar min yayi kyau, lubna kike gani shiyasa kike dada narkewa bakya hassala komai a gidannan saboda kina ikirarin wai kina da ciki ko ,to yau ba sai gobe ba zata koma gida sai naga yadda zakiyi ,kuma ban dauke miki komai ba game da kula dani ,haka kazalika ni kamaludeen na dau alkkawarin raba ki da cikin jikinki dan banga dalilin haihuwarki yanzu ba ,dafatan kalaman bakina sun shiga kunnuwan ki ,masu kama da kashi"




da sauri ta dago da kanta ta zuba masa idanunta masu ambaliya da ruwan hawaye murya adashe tace




"kamal kayi min duk abinda kaga dama ,kuma ina nan akan bakata wlh tallahi baka isa karabani da kyautar da Allah yaimin ba ,dangane da tafiyar lubna kuwa ,ai ba wani abun bane Allah zai taimake ni wajen kula da aiyukana ni kullum mai nema maka shiriya ce gurin Allah ,kuma ina rokon Allah ya darsa maka tsoransa "




tsawa yadaka mata hade da nuna ta da dan yatsa ,yana huci yabar dakin cikin daga murya ya shiga kiran lubna,da sauri ta fito,daga kitchen din


"yaya kamal gani"




"oya,kije ki hado kayanki kizo na saukeki a gida ,zamuyi tafiya ne"


dagowa tayi ta kalleshi ,dauke kansa yayi batare da ya kuma kallon ta ba ,tashi tayi ta nufi dakin sakna a kwance ta tarar da ita ,gaban gadon ta karasa,ta zauna ahankali ta kira sunanta,




"Aunty sakna,yaya yace zakuyi tafiya yau ,saboda haka inshirya ya kaini gida amma aunty,sai nake ganin kamar yaya,akwai abinda yake nufi"




murmushin karfin hali sakna tayi ta dubi lubna kan tayi magana sai ganin ,shigowar sa sukayi shiru sukayi dada hade rai yayi








*jameel*




~~~cikinta ne ya murde hade da tashin zuciya ,jameel na toilet sai jin zubar amai yayi ,da sauri yabar aikin da yake ya nufo dakin tozali yayi da labiba tana ta amai ,hankalinsa ne yatashi nan ya rungumeta ,har sai da ta gama tsaf sannan ya taimaka mata tayi wanka parlorn yadawo ya gyara wajen tsaf ,dakin ya koma ya tarar da ita tafito tana kwance a gado,daga ita sai towel ,kan gadon ya karasa hade da janta jikinsa yace




"sannu Everlasting,meke damunki?me kikaci yasa ki amai"




shiru tayi tadada lafewa a jikinsa jiyayi shaawar ta na fisgar shi amma bazai sami biyan bukata ba dole ya hadiye shaawarsa can ta nisa tace




"jameel,kadafa min danwake kaji ,shinakeson ci "


da sauri ya dubeta ,"Everlasting dan wake kuma ? ai bansan yadda akeyi ba ,yanxu yazaai keenan ?




"haba jameel,tambayata ma kake yazaai,kafini sanin yadda zaai ai ,nide abinda nasani kawai shine, danwake zanci"


"ok yi hakuri mrs jameel bari asamo miki danwake aduk inda yake"




cikin rawar jiki ya janyeta daga jikinsa ya dora da ,


"karki damu,bari inje ,sai dai bankarasa wankin ba"


banza taimasa hade da gyara kwanciyar ta ta kwanta,shiryawa yayi tsaf,yakarasa gabanta yahada fuskar ta da tasa ya sakar mata kiss ,sannan ya fita,kai tsaye gidansu ya wuce ,gurin hajiyarsa tana ganinsa tasaki faraa nan ya zube ya gaidata taamsa da walwala,dubansa tayi tsaf take tagano dan nata kamar bashi da nutsuwa a hankali ta kira sunan sa ,da sanyin murya yaamsa nan ta dora da ,








*Abdulmalik*






~~~cikin hanzari Abdulmalik yabude kofar dakinsu inna kuwa sai raba idanu take da sauri ya tambayeta ,




"inna lafiya meyafaru a tsohon daren nan"?




"kai dannan aljanune adakina kaji yadda suke hira ,kai akwai lauje cikin nadi ,nafiskanci de kawai baason na zauna a gidan dana ne kawai"




shiru yayi can ya numfasa yace ,




"haba,inna wane irin aljanu kuma,gsky gidannan ba komai,muje inrakaki dakin mugani "


da sauri tace,"Aa,basai munje ba tunda zuwan bashi da amfani bari intafi inkwanta da safe mayi maganar"


kan yaankare ta tafi ,Ruhaima tana bakin kofa tana jinsu ,mamaki lamarin inna yabata ciki ta koma tai kwanciyar ta ,bashi da zabi ,shima binta yayi suka kwanta ,


Dasafe sunje gaida ta ta dubi Ruhaima tace




"to,uwar kinibibi daga yau nasa doka agidannan kai Abdulmalik inzaka bada kudin cefane ,to ni zaka dinga kawowa inyaso tazo ta karba a guna "




da sauri suka dago da kansu suka kalleta Abdulmalik ne yai karfin halin cewa,












*Hafeez*










~~~cikin kankanin lokaci Areefa tashirya tsaf,ta fito gidan ta rufe tai tafiyarta kai tsaye gidansu kawar ta tanufa ,nan sukai ta hira ,wayar tace ta hau ruri tana dubawa taga sunan Alhj namadi dariya tasaki suka tafa da kawartata dada gyara fuskar ta tayi suka fita a cikin mota suka sameshi




hafeez kuwa yana fita kai tsaye gidansu fauza ya wuce ,yana isa,yakirata awaya tafito,daukar ta yayi a mota suka fita,kai tsaye,wani babban hotel suka nufa ,isar su keda wuya ,suka ci karo da ,










*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:29] β€ͺ+234 814 620 5819‬: οΌ»5:57Am,2017οΌ½








*@πŸ’¦πŸ’¦NASEEBA GAWO*πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦


πŸ’¦N I GπŸ’¦








*ZAMAN AURE*
πŸ’¦πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™‚πŸ’¦






*NA*




NASEEBA I UBAπŸ’










*Alhmdulillahi lazi ahayana baada ma amatana wailehir nushur,Rabbi yasir wala taasir allahumma yasir alaina*πŸ‘πŸ»










*Wannan shafinπŸ† nakine kawata JIDDATULLAH TIJJANI ,mai littafin ALMAJIRA,ina godiya bisa kwarin gwaiwar da nasamu daga gareki nagode sosai,hakan shi ya tabbatarwa da Naseeba ana tare ,dan haka kiyi komai da wanga page ba komai domin kuwa nakine ke kadai*πŸ†πŸ€£πŸ€£










πŸ’¦
*Tsokaci game da littafin ZAMAN AURE, anya kuwa abinda naseeba ke rubutawa yana faruwa a gidajan auranmmu ko de shaci fadi ne kawai irin namu na marubuta ?fadi raayinki game da hakan*πŸ™…πŸ»














*18*








~~~cikin daurewar fuska kamal ya ke dubansu sunkuyar da kai lubna tayi sakna kuwa kallon mamaki take masa cikin ranta take fadin




_"wai dama haka rayuwar aure take ,miji yacanja kamar bashine wanda ada kafin auran ku baya son duk wani abinda zai bata miki rai ,kullum burinsa ya faranta miki rai ba,amma gashi yau anwayi gari yazama kamar bakin kumurci ,wane irin ZAMAN AURE ,kenan sukeyi_


*Nasseeba kuwa cewa tayi da sakna,haka rayuwar auran take ,gaba dayanta hakuri ce domin kuwa ankirata da ibada,kenan ibada sai anyi hakuri*








maganarsa da yakewa lubna ne yadawo daita daga zancan zucin datake ,cikin dakewa yake fadin




"malama,tashi kishirya,minti 10,kawai nabaki zaki zo ki wani zauna,uban me kike cewa ,wlh lubna ki shiga ki maida hankalinki,kinji de nafada miki"




yana gama fada ya koma parlor ya zauna ,lubna kam baki ta turo tana kunkuni ahaka ta shiga toilet ta yi wanka,cikin kankanin lokaci tagama shirinta tsaf ,sakna na kwance tana kallonta kusa da ita tadawo ta zauna ahankali takira sunanta




"Aunty sakeena zantafi,nasan bainda zakuje ,kuma nafiskanci akwai matsala a *zaman auranku* saboda haka wlh sai nafadawa Hajiya da na koma kiyi hakuri"




saurin katse ta sakna tayi ta cikin raunin murya tace




"Haba lubna ,meakayi da har zakije kifadawa hajiya,to gaskiya banyardaba,kuma maganar tafiya da zamuyi tunda yafadi hakan,may be tafiyar zamuyi ,dan haka ni ban aikeki ba kuma kar ki soma "




dariya kawai lubna tayi,ta dau jakar kayanta ta mike dan tafiya,yunkurawa sakna tayi ta tashi tahadomata wasu materials sababbi da kayan kwalliya hade da kudi tabata ,godiya taimata ta nufi parlor ,yana zaune ya dora kafa daya kan daya ,yana ganin ta fito yaja dogon tsaki ya mike ,yafita binsa tayi a cikin mota tasameshi ,baya ta bude ta zauna, afusace ya juyo ya kalleta yace




"ke waye driver direbanki dazaki wani kame abaya ,dalla dawo gaba "




dariya ce taso kubcemata tayi kokari ta gumtseta gaban tadawo tazauna da sauri ya figi motar wani gigitaccan horn yashiga yi da gudu mai gadin yazo ya bude masa gate din ya fita,cikin kankanin lokaci suka isa gidan nasu ,begama yin parking ba lubna tafito daga motar kai tsaye dakin Hajiyar su tanufa tana zaune akan sallaya sai ganin lubna tayi ta zube ajikinta nan ta shiga tambayarta






"Auta wane irin sammako ne wannan kamar wata korarriya,ina sakeena ,da kamal din"?






baki ta turo gaba hade da narkewa ajikinta nan ta kwashe komai ta fada mata game da *zaman auran* kamal da sakna ranta ne yai masifar baci ,ana haka sai gashi ya shigo da kayan lubna da bata tsaya ta dauka ba wani kallo Hajiyar ta watsa masa take jikinsa yai sanyi jikinsa ne yabashi lubna tafadawa Hajiya tabbas yasan bazasu kwashe ta dadi ba,












*jameel*






~~"Dan marayan zaki anyawa kuwa babu abinda ke damun zuciyar ka nifa tunda ka auri yarinyar nan gaba daya kasanja ,meke faruwa da *zaman auranku*"?




murmushin karfin halin yayi ,dan bazai iya furta,mata komai ba yasha zuwa takanas dan yafada mata amma dayazo gabanta sai yakasa hoton labiba ne kawai a zuciyarsa ahankali ya dago da kansa yace






"Hajiyata,kar ki damu danki bashi da wata damuwa ,yanzumma dai labiba ce bata da lpy shine tace danwake zataci ,zuwa nayi kiyi mata kinji Hajiyata"




murmushi tayi dan ta fuskanci inda zancan nasa ya dosa tashi tayi ta shiga kitchen cikin kankanin lokaci sai gata da danwake a kula mai kyau,ta kawo masa yana kwance idonsa alumshe kamar me bacci ahankali takira sunan sa,




"Danmaraya,tashi ka kaimata kar tai ta jira,har yafitar mata a rai"




"to,Hajiyata sannu angode ,Allah yaja mun da ranki"




dariya tayi taamsa da "Ameen"




yatashi ya tafi,sanda ya karasa gidan tana parlor a zaune ,cikin rawar jiki yakarasa gabanta yaajiye mata kular agabanta kallonsa tayi awani yatsine tace




"jameel,sai yanzu ,to kadauke abinka banaci ,tun yaushe kafita"




cikin sauri yadago ya dubeta yarasa ma mezaice mata kawai sai ya ,






*Abdulmalik*




~~shiru inna tayi tana sauraran abinda Abdulmaliki zaice




"inna dan Allah kiyi hakuri,da abinda zance ,ni sai nake ganin kamar Ruhaima ita yakamata ana bawa kudin cefane ,amatsayinta na,mai girki......






batabari ya gama fada ba ta daka masa wata uwar tsawa tadaka masa tadora da




"yayi kyau,Abdulmalik,
yau ka tabbatar min da cewa matar ka gaba take da mahaifiyarka to nagode da irin wannan sakayyar to amma kasani ,kan takarasa tasaki kuka


hankalinsu ne yatashi Ruhaima ce ta dubi Abdulmalik tace




"Malik,ayi yadda inna keso ai ba wani abu duk daya ne ,dan Allah inna kiyi hakuri "




"Dallacan rufemin baki munafuka ,juya kawai baki da aiki sai lashewa dana kudi ki haihu ,kinki ki haihu saboda tsabar mugunta "




shiru sukayi karshe suka bata hakuri hade da bata kudin cefanan yafita daki Ruhaima ta koma tasaki kuka mai tsuma rai ,




da yamma tana kitchen ta kusa kammala girki kawai sai ga inna taja ta tsaya a kofar kitchen din ,cikin daga murya ta kira sunanta




"ke Ruhaima uban me kike dafawa ,ko san ranki kike dafawa "




"inna sannu da fitowa,amm dama tuwan shinkafa nake miki "






"to,sauke bashi zanci ba,alkubus nakeso"




shiru Ruhaima tayi tarasa ma mezatace can ta sauke girkin ta koma daki ,binta innar tayi har dakin ,






*Hafeez*






~~cikin kissa Areefa ta kalli Alhj namadi shi dinmma ita yake bi da asirtaccan kallonsa irin na yan duniya hade da kiran sunanta






"my love,daga nan sai ina muka nufa,?






dariya tayi hade da kashe masa ido sanan tace,


"Duk inda ranka yaimaka zabi,domin kuwa zabinka shine nawa"


jinjina kai yayi hade da lakacemata hanci yaja motar suka tafi kai tsaye guest house dinsa suka wuce,nan suka hole abinsu ,dazata tafi yadakko kudi masu tarin yawa yabata ta bude kofar gidanta ta shige






Abdulmalik kuwa karo sukai da tsohuwar budurwar sa mai suna Anisa,murmushi yasakar mata ya karasa gurinta nan suka gaisa tambayarta yashiga

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads