Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 40195 words

Chapter 2 - ZAMAN AURE Book Complete Document .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

531

Ads at the middle of Article

stupid zancan naki, kinji dai na fada miki "






Yanagama fada ya figi rigar sa yasa ya shiriya tsaf tana tsaye tana kallonsa a hankali ta karasa gaban sa ta dau turare zata fesa masa kamar yadda ta saba hannu ya daga mata alamar ta dakata karba yayi ya fesa ya mayar ya ajiye ya kafa hular sa yayi kyau sosai duk inda ake son namiji yakai kamal yakai mukulin motar sa ya dauka yai hanyar parlor cikin sauri sakna tasha gabansa tai nare nare tace




"honey bee, pls kayi hakuri bazan kuma ba kazo muje kayi break fast kar ka fita baka ci komai ba kaji "




" meye damuwar ki da rashin yin break fast dina,malama matsa ki bani hanya in wuce "


Matsawa tayi ya wuce ko kallon ta be kuma yi ba guri tasami ta zauna take taji kanta ya sara hawaye ne ya shiga ambaliya a fuskar ta sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi tayi alwala tayi sallar walaha ta dau alkuranin ta tafara karantawa take tasami nutsuwa taji zuciya tayi wasai parlor ta fito zuba ruwan tea tasha hugun daakewa kofar parlorn ne yasa ta tashi dan ganin me hugun tana budewa tasaki faraa dan ganin bakuwar tata










labiba kuwa tana karbar wayar jameel ta kashe bata ma duba waye ba duban sa tayi tace




"jameel yazaai ne yunwa nake ji wlh "




" to mezakici everlasting ko in karbo mana abinci gurin hajiya ta "




" a wane lokacin kenan kawai ka shiga kitchen dan sauri nake nafada ma saloon nake son zuwa "




Kin tsefe Kan naki ne"?






" kafiya jan magana wlh jameel taya zan iya tsefe kai na kai zaka tsafan to, kagama girkin sai muyi tsifar "
























" yes, ma"


Yanagama fada ya nufi hanyar dakin sa sai gashi ya fito daga shi sai vest da gajeran wando tana kwance murmushi ya sakar mata ya shiga kitchen indomie ya dora cikin kankanin lokaci ya kammala ya zubo musu a plate ya kawo da kyar ta sakko ta fara ci sai shagwaba take wai tagaji kwantar da murya yafara yi yace




"haba everlasting ki daure kici sai ayi tsifar sai muyi wanka in gasa miki jikinki da ruwan dumi "




" jameel, dawa zakai wankan kar kace dani cab Allah ya sawake to wa zai min wankin undies dina ko salon mu tsaya wanka na batawa kaina lokaci"


"Hmmm shikenan everlasting badamuwa sai in zauna kije ki dawo "


" better"


Tsefemata Kan yayi tashiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya mukulin motar yabata ta fita guri yasamu ya zauna ya dafe kansa yashiga tunanin irin bakar rayuwar da ya tsinci kansa ciki








Abangaran abdulmik kuwa gaba daya hankalin sa ya bawa inna dan jin wane irin sharadi zata furta duban sa tayi tace




"Abdulmik so nake a dinga kawo min amincin gidan ka tun daga na safe har na dare "




" inna abincin gidana kuma?


"baze samu bane, a hakura "




" aa inna, ina ganin de kamar dan aike ne zai zama matsala "




" oh! meye amfanin kudinka malik, ai tunda kana kana da kudi dan aike zaa samo, sai kasai masa babur kana biyan sa duk wata"






Shiru yayi yana jin jina kalaman innar tasa can ya nisa yace


"shikenan inna badamuwa inshaallah zaai yadda kika ce"








"yauwa saura kuma yar mulkin tayi son ranta dan bazata so hakan ba tafiso daga ita sai yanuwanta Hmmm naso ace kana da kanne, wlh da taga yadda *kannan miji* zasuyi ko da yake ai ko basu akwai *uwar miji* "




Shiru yayi mata takaraci surutun ta kudi ya ajiye mata a gabanta karshe yaimata sallama yatafi tana ta sama sa albarka wani shuumin murmushi inna tayi




Kai tsaye abdulmik gidan su ruhaima ya wuce lokacin tana tare da ummanta da kannan ta dasuka zagaye ta sai wasa da dariya suke ummanta ce ta dube ta tace




"ruhaima dafatan kuna nan lpy ko "?






























" lpy kalau umma sai dai matsalar innar sa kawai"




"bakomai ruhaima ke de kicigaba da yaimata biyayya kamar yadda zaki min ban yarda ki saba mata "




" shikenan umma inshaallah zan kula "






Sallamar abdulmik ce ta katse musu zancan da suke yi da faraa umma ta tari abdulmik suka gaisa cikin mutun tawa sukai mata sallama suka tafi tun a hanya abdulmik yarasa yadda zaiyi ya fada mata bukatar inna ahaka har suka isa gida sai da suka zo bacci sun kwanta yajata jikin sa sannan yafada mata Shiru ruhaima tayi can ta janye daga jikin ta daga nasa tace






Abangaran hafeez kuwa sai da ya bari kiran areefa ya katse sannan ya tashi ya fita cikin motar sa ya shiga sannan ya kira ta bugu 2 ta dauka cikin shagwaba tafara magana




"Hello yallabai, katafi kabarni da kewa ni de gsky kadawo "




" sarka mai rikicin gan gan, to indawo me zan miki, me kike so daga gurin hafeez, fadan inji "




Dariya tayi sannan tace," sai kace ka manta areefa ko, to bari in tuna maka areefa bazata iya rayuwa batare da hafeez ba ayanzu haka ina kwance sai juyi nake nakasa bacci wlh "




" ayya muyi daya sweet hert nima nakasa baccin, amma abinda zaai yanzu ki rufe idon ki zan ta fada miki kalamai masu dadin sauraro da kwantar da hankali har kiyi bacci "




Dariya tayi, tayi yadda yace nan ya shiga jero mata kalamai masu dadi akarshe ya juya zancan zuwa na tada hankali da shaawa areefa rasa yadda zatayi tayi saboda yadda taji kewar mijin nata ta dawo mata sabuwa karshe yai mata sallama ya kashe wayar Shiru tayi karshe ta yanke shawarar kiran saurayin data yi a school














*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[3/19, 10:27] ‪+234 814 620 5819‬: [5:54Am,2017]




*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦




*💦T F*💦










*ZAMAN AURE*
💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦










*NA*


NASEEBA I UBA 💐










*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿👏🏻






💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦








💦💦
*Wannan shafin nakine kawata fayeex usman hakika kin cancanci yabo bisa namijin kokarin da kikai wajen kawo mana novel dinki mai suna hanyar yaman mun waazantu kuma munnishadantu Allah ya kara basira kina yi munjin dadi sai munji ki a sabon novel dinki naseeba tace ana ana tare*🤝💦💦













*5*












~~~ganin maman su kamal ne ita da lubna kanwar sa ne ya sa sakna sakin murmushi ta karasa gurin su hade da rungume lubna dubansu tayi tai musu sannu da zuwa mama ce ta amsa da




"yauwa sakeena sannu kinji dafatan kuna nan lpy ko "




Tsuguna wa sakna tayi ta gaida mama cikin girma ma wa ta amsa da kulawa duban lubna sakna tayi tace




" gsky lubna nayi fushi sai yau ko kullum cikin zuba idon ganin ki nake sai yau kika biyo mama "


Dariya lubna tayi sannan ta dubi mama tace






" mama dan Allah ai kullum ina son zuwa ko wlh aunty sakna makaranta, amma kisha kuruminki kwana 2 zanmiki "




Cikin jin dadi sakna ta dubi lubna tace


" kai amma naji dadi sosai kice yau ina da babbar bakuwa, mama yasu aunty da su suhaif "




" kowa lpy kalau sakeena ya kamal din dafatan dai kuna lpy ba wata matsala ko "






Cikin ran sakna matsala ce fal hade da damuwa amma bazata iya bayyana sirrin su ga wani ba dan *mijin ta sirrin tane* afili ko sai tace wa mama




" Aa, mama ba wata matsala muna zaune lpy "




" To Alhmdulillah ayi ta hakuri kinji ita rayuwar auri da kike ganin ta hakuri ake yi da juna, amma hakan bazai sa in daya ya cutar da daya akasa daukan mataki ba duk abinda kamal yai miki ba dai dai ba nabaki dama ki fadamin kinji yata "




" Hmmm to, mama nagode Allah yakara girma "




Tashi tayi ta je ta kawo musu danbun nama da ruwa da lemo da kyar mama ta dan ci kadan tai musu sallama ta tafi sabulai sakna ta dakko ta bawa inna nan suka zauna ita da lubna sukai ta hira




Da yamma sukai girkin su tare har bayan magariba lubna bata ga kamal ya dawo ba duban sakna tayi tace






"Aunty wai yaya fa, dama baya dawo wa da wuri ne?




Shiru tayi saboda bata san amsar da zata bata ba can ta nisa tace




"eh to, yadanganta da yanayin uzurin sa a ranar lubna "




" Au wlh nazaci baya dawo wa da wuri ne infadawa Mama "




Dariya kawai tayi nan suka ci abinci suka taba hirar su hamma lubna tafara yi duban ta sakna tayi tace






" Bacci ko,? taso muje ki kwanta "




Tashi lubna tayi suka nufi bedroom ta kwanta duban ta sakna tayi tace




" Haba, lubna yazaki kwanta ba tare da kinyi alwala ba "




" kai Aunty wlh bacci nake ji dan Allah ki barni "




Da kyar sakna ta lallaba ta ta yi alwala sannan ta zo ta kwanta parlor ta koma ta sa plate din Quraani tanaji wayar ta ta dauka ta shiga neman layin kamal tana ta ringing be dauka ba ahaka bacci baro yai gaba da ita


Kamar kullum kamal be dawo ba sai wajen 12:30 na dare abige ya shigo yana ta surutai tozali yayi da sakna tana kwance a Kan kujera tana bacci kawai sai jin mutum tayi ya fado kanta wata kara tasaki wacce ta gigita lubna da ke kwance a daki hannu yasa ya toshe mata baki sai kuma ya shiga kwarara amai ba kakkautawa ahaka lubna ta.






Abangaran labiba kuwa tana fita kai tsaye gidan su ashanty ta nufa tana shiga tayi tozali da kawar tata suka rungume juna cikin so da kauna duban ta ashanty ta dubi labiba tace




"kai kawata kingan ki kuwa gsky kina balai jameel ya tsaya miki wlh "




" cab jameel ya tsaya min ko na tsaya wa kaina sai kace kin manta halin jameel Hmmm yanzu dai kawata aikin malam yayi kyau ko ince yana kyau dan sai yadda nayi dashi dan yanzu haka yana gida nabar shi da wanki da girki "




" kai kawata baki da kyau wlh mijin ki ne fa "




" ashanty kenan sai kace baki san halin
maza ba, ko mai mace tai musu su suka janyo saboda in suka sami dama sai su maida mace tamkartamkar baiwar da suka sa kudi suka siyo, to wlh ni labiba ban yarda wani da namiji ya dan dana min bacin rai ba "




" Da kyau kawata, to yanzu ki shiryo akwai wani sabon malami daaka bani labari zan raka ki wajen sa "




" Allah, Ashanty to zamuje gobe gobe nan "




Nan dai sukai ta kulla mugun nufin su akan bawan Allah karshe sukai sallama labiba ta tafi kai tsaye gurin salon ta wuce








Jameel kuwa tun bayan fitar labiba ya hada under wears dinsu ya wanke tas ya wanke toilet din bayan yagama tsaf ya nufi kitchen girki ya dora musu yana yi yana share gumi ahaka ya kammala ya zuba a kuloli, wanka yayi ya dora alwala har zai fita masallaci labiba ta shigo da mota tsayawa yayi ta shigo ya mai da gate din ya rufe ahannu yasa ya bude mata murfin motar ta fito jakar ta ta mika masa yadanyi jum kafe shi tayi da ido take jikin sa yafara rawa a hankali ya ce.








Abangaran gidan Abdul malik kuwa jan ruhaima yayi jikin sa yashafi fuskar ta yace




"my dear dan allah kiyi hakuri da abinda zance "




" ina jinka malik fadi abinda kake son fada ruhaima me biyayya ce agareka"






"to godiya nake dear, ammm, dan Allah zaa dinga kai wa inna abinci tun daga na safe har na dare dafatan zaki bani goyon baya wajen kyauta ta mata "




Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta nisa tace






" Badamuwa malik inshaallah zaayi kamar yadda inna take so "


" yauwa my dear nagode sosai Allah ya bamu zuria ta gari, dan haka ki shirya a wannan daren mai tarin albarka zan baki baby kinji "






"Allah yasa sweet malik"




Tana gama fada ta shige jikin sa tare da sakarwa kirjinsa kiss bargo yaja ya rufe su


Washegari tun da safe ruhaima ta tashi ta dora girki kunun gyada tayi da doya da kwai ta kammala ta zuba a kula tasa a kwando ta dau nasu ta kai dining area ta ajiye daki ta koma ta shiga tashin abdulmalik a hankali ya bude idonsa janyo ta yayi jikin sa ya rungume ta cikin shagwaba ta dube shi tace


"sweet malik dan Allah katashi angama amincin inna ka kaimata kaji "


Ido ya lumshe ya shafi fuskar ta sannan ya mike ya zura jallabiyar sa ya fito bin bayan sa tayi tasa masa kwandon amincin a bayan motar sa taskar masa murmushi mayar mata yayi yaja motar sa ya tafi




Sanda ya isa gidan inna tana parlor ta rafka uban tagumi yayi sallama ya shiga ko kallon sa batayi ba sai da ya tsuguna a gabanta yace




"inna sannu da gida dafatan kin tashi lpy


"Bansaniba Abdulmalik sai yanzu kuka ga damar kawo min karin kumallo duba fa kaga agogo karfe nawa to ka dau abincin ku bana ci "




Tana gama fada tasa kuka ruhaima ta mallake mata da rasa ma me zaice mata yayi can yanisa yace.










Abangaran areefa kuwa kiran hydar
tayi awaya sukai ta hira cikin hirar tasu ne take fada masa tana gyayatar sa gidan ta, Shiru yayi can kuma ya amsa da




"shikenan baby badamuwa to amma iyan yanki fa in suka tambaye ki waye ni mezaki ce?




"ka kwantar ma da hankalin ka basa kasar nan sunyi tafiya "




" ok badamuwa Baby sai goban zan shigo "






Nan sukayi sallama ta kashe wayar ta kwanta


Hafeez kam suna gama waya da areefa ya koma ciki a parlor yasami khady daga ita sai vest da gajeran wando ta bazo da gashin ta sai taunar cingam take har zai wuce sai kuma ya dawo ya zuba dara daran idanunsa tasowa tayi tana rangaji kamar bishiyar da iska ke kadawa




















*NASEEBA GAWO*.


✍🏻
[3/19, 10:28] ‪+234 814 620 5819‬: [5:44Am,2017]




*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦




*💦T F*💦










*ZAMAN AURE*
💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦










*NA*




NASEEBA I UBA 💐












*Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina*👏🏻










💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦














*Sakon gaisuwa gareki Hafsat Hamza hakika naji dadin shawarar warinki gareni hakan shi ya tabbatar min da cewar ana tare to, naseeba ma tace ana mugun tare Nagode kawata*🤝
















*6*










~~~Dada tsorata lubna tayi taja bargo tarufe kanta tana ta zare ido ga uban gumi da yake ta keto mata da kyar tasamu bacci ya dauke ta


Sakna kuwa kuka tasaki mai ban tausayi yana gama aman yai bacci kamar wani karamin yaro ga dakin ya dumame da wari hade da tasamin giya da kyar ta zame jikinta tashiga toilet ta dauro towel parlorn ta dawo ta gyara gurin tas to goge sannan ta fesa air freeshner hade da kunna turaran wuta take dakin ya kauraye da Qamshi wanka tayi hade da dauro alwala tazo ta tayar da sallar nafila da rokawa mijin nata shiriya gurin sarki Allah




Be farka ba sai misalin hudu saura kansa ne ya sara take yafara kwallawa sakna kira cikin bacci taji kamar muryar kamal da sauri ta fito ganin sa ta yi dafe da kai da sauri ta karaso gurin sa idonsa arufe yace




"Hada min ruwan dumi zanyi wanka "




Batare da taamsa ba ta tashi ta nufi bedroom dinsa ta hada masa ruwan dawo wa tayi tafada masa cikin layi ya dubeta yace




Oya, kama ni intashi"


"Honey bee, bazan iya daga ka ba "






Wata razanan niyar tsawa yadaka mata ba shiri ta kama shi ya mike suka nufi daki tai maka masa tayi ya tube kayan sa ya shiga toilet din zama tayi bakin gado tana share hawaye kwalla mata kira yayi ta tashi da sauri ta nufi toilet din






Gidan jameel kuwa labiba ce ta dubi jameel tace






"ya de, ka tsaya kana kallo na lpy "


" wai labiba meyasa kike min haka ne kin manta matsayina a gurin ki ko "




" NA manta Jameel sai ka tuna min "




Tana gama fada tai gaba cikin fushi jikin sa yai sanyi ya bi bayan ta a daki ya sameta tana cire kayan jikin ta da sauri ya karasa gurin ta da niyar tai maka mata hannu ta daga masa a hankali ta ce




" kar ka tabani Jameel bana so kabarni kawai "




Janye hanunsa yayi ya ja gefe ya tsaya ya ma manta salla zaiyi dauke kanta tayi ta nufi toilet dan watsa ruwa sai lokacin ya tuna da salla, sallaya ya shimfida ya tayar da salla har ya idar bata fito ba addua yayi ya shafa ya tashi ya bude wardrobe ya dakko wa labiba wata riga mara nauyi yaajiye mata akan gado hade da rafar kudi ta 500 ya fita parlor ya rafka uban tagumi tana fitowa taga kudi akan gado murmushi tasaki wata rigar ta dauka tasa tadanyi kwalliya ta fito zuwa parlorn yana zaune yasa abinci agaba yana jiranta guri tasamu nesa da shi ta zauna cikin rawar jiki yataso ya zauna kusa da ita a hankali ya kira sunan ta




"Everlasting, dan Allah kiyi hakuri da abinda na fada miki inshaallah i will never do it again "




" Jameel inka gaji da ni ai basai ka wahalar da kanka ba just tell me "




Toshe mata baki yayi da nasa ya shiga tsotsa cikin rawar jiki kamar zakin da yasami abinci sai da ta bari yayi nisa gaba daya yagama fita hayyacinsa sannan ta zame jikinta ta yunkura zata tashi riko hannun ta yayi ya mare rece fuska a hankali yace




" pls Everlasting ki taimaka min yau daya insami nutsuwa wlh nakai karshe zan iya mutuwa fa "




" Hmmm I am sorry 2 say *kasa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads