Showing 27001 words to 28227 words out of 28227 words
Chapter 10 - Matar Bahaushe by Mrs.Basakkwace.txt
mene HANEEFA da girmanki da shekarunki ƙaramar yarinya ta fiki iya riƙe miji?,tou tun wuri ki gyara".
"Tou ya zanyi ƙawata",HANEEFA ce ke magana duk tayi ƙozai ƙozai ta faɗa,yanzun tashiga hankalinta don ko kulata SALEEM yadena yi in yafita tun safe bai dawo wa sai dare shine take ba ma ƙawarta labari,ƙawar ta ringa mata faɗa da nasiha,kuma tace da yadawo ta nemi gafarar shi ai yanzun zama ake da kishiya lafiya,kishin mai aji ake bana hauka ba kuma taji ta ɗauka nasihar ƙawar tata tayi nadaman abinda tayi tun baya da tayi biyayya da baai mata kishiya ba da ta zauna ita kaɗai da taji nasihar MOMYNTA daba haka ba.
Washagarin da suka dawo tafiya HANEEFA tazo gidan MOM da farin ciki MAIMUNATU ta tarbeta itama haka aka gaisa faram-faram,har ƙasa ta duƙa ta gaida MOM da DAD,MOM sai mamaki take abinda HANEEFA bata taɓa yiba kenan a tsaitsaye take mata magana yau itace guywa har ƙasa.
Itako zama tay ta shantake sai jan MAIMUNA take da hira,koda SALEEM ya dawo yaganta sai mamaki yake tare sukai dinner awajen ne tanemi gafarar kowa SALEEM ba ƙaramin daɗi yajiba haka maimuna da mom,anan ne MAIMUNA tace,YAYA, AUNTY yakamata MOM ta aura DAD ɗinmu koh?.
Kallon-kallo kowa keyi awajen.
MUNAYYA koh tace,"eh wallahi aunty kaima ka amince koh MAHFUZta faɗa tana mai kallon MAHFUZ da ba hankali, sosai gyaɗa kai yayi yana wasan shi HANEEFA ma tace, wallahi ko sun dace",MOM ko kunya SALEEM yace, na ɗau nauyin komi ran jumaa za'ai,DAD murmushi kawai yakeyi ,MOM kunya kamar ta nitse ƙasa,suko ƴaƴan sai hiran yanda zasu sha biki sukeyi daga bisani SALEEM da HANEEFA sukai musu sallama suka wuce,MAIMUNA da taga zasu wuce shida HANEEFA wani ƙululun kishi ya taso mata dannewa tayi tai masu yaƙe harda rakiya a motor shi suka koma aka bar motor HANEEFA,MAIMUNA da ƙyar taja ƙafar ta ta shiga ciki wani nauyi takeji aranta mijinta shida wata.
_🤔 kaji min mata iyayen kishi kiga mata da mijinta ki aura kice zaki kishi baa aure aka aure ki🙄😏_
SALEEM da HANEEFA sun raya daran nan cikin farin ciki da ƙaunar juna suka dirje juna,yayinda MAIMUNATU da ƙyar bacci ɓarawo ya saceta sabida tsananin kishin dake cin zuciyar ta.
Washagari da HANEEFA yazo ya aje ta kafin ya wuce aiki anan tai break fast tana ta nan nan da ƴan biyu MAIMUNATU ko haushinta takeji kamar ta maketa gani take anci amanar ta.
_WAI ALLAH SU MAIMUZ IYAYEN KISHI SUKAYI DE SUNNA_
AGURGUJE
Ranan jumaah aka ɗaura auran MOM ND DAD akan sadaki 150k SALEEM ya biya sadakin shine waliyin MOM yayinda BAFFAN shi ne waliyin DAD duk da ƴan uwanshi suzo abin ya ma dangin MOM ɗadi sosai dana DAD ɗin SALEEM dama sunjima suna mata maganan aure tai ta musu hanya-hanya,anci ansha anyi ƴar walima dan ginsu ne kawai sai ƙawayen MOM da MOMYN HANEEFA aranan MAIMUNATU ta ta koma ɗakinta HANEEFA sai murna take ,adaran ranan SALEEM kaman jira yake saida ya ɗebi gara abin sa,HANEEfA kwashe su BASAM tayi ta tafi dasu ɓangareta acewar ta karsu damesu yau akwai harka.
Zaman gidan SALEEM gwanin ban shaawa kowa burinta ta ga tafi ƴar uwanta iya kula da miji inkungan shi baku iya gane shi yayi ɓulɓul dashi harda ɗan tumbi abinsa hankalin sa yayi matuƙar kwantawa ga matan sa sun haɗa kan su kamar ba kishiyoyin juna ba abin gwanin ban shaawa.
DAD ya dawo da ƙiban shi yayi kyau MOM tattalin abinta take sosai kamar ƙwai,su MAIMUNATU insunzo gidan abin har mamaki suke tsohuwa da iya kula da miji,wani abu in tayi suke jin kunya ba MOM ɗin ba.
_🙄🙄🙄🙄 kaji ƴaƴan zamani ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mata ƙafa salon ai mata kishiya_
Ɓangaren MAMA bayan taji sauƙi ta nemi gafarar ƴaƴanta da mijinta nan suka yafe mata,yanzun tayi sanyi tagane Allah ɗayane komi ta samu ƴaƴanta mujinta dabbobin ma ta kwashe ankai kasuwa ta saida tazo tai ma ƴaƴanta hidima da kuɗaɗe,adduan ta yanzun Allah ya fiddo masu da miji suyi aure.
_SU MAMA ANJI JIKI_
Ɓangaren HAJIYA HINDATU kuwa ta haɗu da wasu ƴan damfara sun damfare ta sun tafi da duk kuɗaɗenta hatta gidan da take bai tsira ba saisa suka sa ta saida suka amshe kuɗi ,akan zasuyi wani kasuwanci da zata samu kuɗi sosai dole badon tanso ba ta koma ƙauye,a ƙauye ko ɗan raɓa ta akayi a ɗakin hatsi nan take kwana ƴan uwanta da suka tambayeta ina mijinta cewa tayi dasu ya mutu,koda labari yaje kunne ƴan uwan DAD sukace ƙarya ne yanan da ranshi da matar shi ƴaƴanshi da jikokin sa.
Ataƙaice de HINDATU tazama kamar mujiya abinci sai an tsammata shima kamar ta roƙa matan ƙannenata da yayyunta siyita zagi da hantara duk ta yaƙune ta zama abin tausayi.
DAD da labari yaje mai yai dariya shiryawa yayi suka tafi da MOM a ƙofar gidan su HINDATU ya tsaya ya aika aka kirata tana fitowa ta ganshi buɗe idanuwa tayi gani yanda ya zama wannan ce matar tashi kenan kallonta yayi a wulaƙance yace HINDATU kenan kinga yanda rayuwa yake soya lokaci lokaci ko ni kikaso ki gani a wulaƙance albarkacin haihuwa ban wulaƙanta va gaki ke a wulaƙance Allah ya kyauta ciro takadda yayi a aljihu ya wurga mata,itako sai zubar hawaye take baibi ta kanta ba ya faɗa motor driver yaja shi sai gidan su inda ƴanuwa ke ta murna aranan suka dawo kaduna.
BAYAN SHEKARA GOMA
abubuwa masu daɗi da marasa daɗi sun faru nasara da rashin sa sunfaru inda MAIMUNATU ta ƙara haihuwan ƴan uku duk maza yayinda taba HANEEFA su BASAM kyauta tunda ita haryanzun haihuwa shiru,tunda ta haifa ƴan uku ta sa kuka ita de saita huta dole badon SALEEM naso ba sabida farin cikinta ya yarda sukai tsarin iyali su BASAM an girma ana primary four yayinda ƴan uku AƘIL maisunan mahaifin MAIMUNA ,ARIF mai sunan maihaifin HANEEFA ,AFIF mai sunan BAFFAN SALEEM,SALEEM an girma anzama magidanci yazama babban mutum sosai haka HANEEFA da MAIMUNATU girama yazo musu amma inka kalla su BASMA zakace ba MAIMUNATU ta haife suba ƙannan ta ne sabida yanayin jikinta mai kyau su AƘEEL suna da shekara biyar shiryawa sukai suka nufi gidan MOM da ta zaɓa dattijuwa yanzun sosai da ita da DAD har furfura suka aje hango wasu kyawawan yara nayi da saida nayi da gaske nagane MUNAYYA ne da MAHAFUZ suka girma haka cike da murna suka tare au BASAM inda MOM ke kwance jikin DAD shiko sai shafa gashin kanta yake suna hira,su MAIMUNATU sun saba gani saide suyi dariya,HANEEFA tace," kai MOM kude baku tsufa",dariya suka sa nan suka zauna akai ta hira cike da nishaɗi, saidare suka bar gidan.
Ɓangaren su MAMA duk ta aura da ƴaƴan ta inda ta bugi ƙirji tai musu kaya naji da faɗa batare da kosisi ALHAJI ba yanzun zamanta lafiya take da ƴaƴnta da mijinta.
HAJIYA HINDATU tayi aure inda ta aura wani ɗan giya y ɓa dake ta kuma dole ta fita tayo aikin wanke wanke da shara ta kawo masa kuɗin giya sannan taciyar dashi,yanzun tana danasanin abinda tayi a baya tana tunain yanda zata ga su MAIMUNATU ta nema gafarar su duk sanda zata ji labarin sunzo kafin taje zata iske sun wuce duk ta rame tayi baƙi zanin ɗaurawa ya gagareta duk mijinta ya kwashe ya sayar yasha giya,kuma bata isa tayi magana ba tasha duka.
_KAƊAN KIKA GANI_
ƘARSHE
SUBUHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIK'ASHADU ALLAH'ILAH HAILLALLAH'WA'ASH HADU'ANNA MUHAMMADAN ABDUHU'WA'RASULUHU