Showing 3001 words to 6000 words out of 28227 words
Chapter 2 - Matar Bahaushe by Mrs.Basakkwace.txt
fahimce ni","ni yanzun abinda nafi ji matarka da ƴan uwanta karsu zargeni akan ƙarin auran nan","MOM karki damu nasan yanda zan shawo kan matsalar nan dan duk wanda ya matsa min akan auran nan nima zan matsa ma","a'a baza ai haka ba ko kaɗan"," MOM alfarma ɗaya","faɗi nama",MOM banson kowa yasani tukunan sai nan gaba",kabari zami magana zuwa gobe","ok MOM",miƙewa yayi itama ta miƙe suka jera atare suka fito.
MAIMUNAH ƙare ma falon kallo tayi duk haɗuwan falon gidansu wannan yafishi nesa ba kusa ba zuba masu MUNAYYAH abincin tayi ta tasa mata yayinda ta ɗau MAHAFUZ ta ɗaura kan shi kan cinyar ta tafara bashi saida ta tabbatar ra ciyar da ƙannanta ta basu ruwa sun ƙoshi kafin taci itama bata jima da gamawa ba suka sakko,tanajin takun tahowan su ta ƙara ƙasa dakai gabanta na bugun onefive kar nan ma awulaƙanta su a kore su tou in ankore su ina zasu a wannan daran .
ƙarasowa sukai MOM tazauna kan kushim zama yayi a gefenta ya kwanta akan cinyarta,MOM ƙare musu kallo take cike da tausayawa kayan jikin su kaɗai zai shaida suna yanayin babu,amma daga gani sukaji wanka kwana biyu zasu goge.
Cikin sanyin muryanta tace,"ina wuni HAJIYA barka da dare".
Murmusawa tayi cike da fara'a yanayin yarinyar ya burgete tana da matuƙar sanyi tace,"lafiya ƙalau,alhamdulillah,barkan ku dashigowa sabuwan rayuwa,Allah yabamu haƙuri zama da juna,duk wani abu da zanfaɗa sai Allah yakaimu gobe sabida yanzun dare yayi yanzun ciro min key ɗakin ka agyara musu kafin safe a gyara musu",miƙa mata makullin dake hannun shi yayi,dubawa tayi ta cire ta maida masa saura tana faɗin,"tashi katafi gidan ka dare nayi","uhmmm MOM kingaji dani koh?,cike da shagwaɓa yake maganan.
Riƙe baki tayi tace,"tou cigaba da zama ni ɗaga min ƙafa karka karya ni",turo baki yayi tare da miƙew shafa kan MAHAFUZ da MUNNAYYA yayi yace,"zan wuce saida safe mi zan kawo muku?,MUNAYYAH tace,UNCLE sweet",murmshi yayi yace,"sai kuma mi?,MAHAFUZ yace,"UNCLE bobo",acikin muryanshi da bai ƙwarai da magana ba.,dariya yayi yace,"tou angama","MOM good night","ok ka kula da kanka"ficewa yayi yana murmushi.
MOM muƙewa tayi tace, ina zuwa,bari insa a gyara ɗakin",miƙewa MAIMUNA cikin sanyin murya tace,MOMY kibari in gyara","aa baza ai haka ba ki huta lokacin hutunki ne yazo",a'a MOMY ba hutu nazo ba dan Allah ki bari inyi", "tou muje",miƙewa tayi tace,"MUNAYYA kujira.
MOM murmushi tayi tare da kama baki tace,ohhhh ni LAILAH nayi abinkunya bansan sunan ƴaƴan nawa ba ɗan neman nama bai faɗa min ba kuyi haƙuri dan Allah".
Murmushi tayi tace,"MOMY ba komi sunana MAIMUNA ƙannaina MUNAYYAH DA MAHAFUZ", nyc name Allah ya rayamin ku",ameen MOMY muma Allah yabamu ikon miki biyayya",ameen MEENAH buɗe ɗakin MOM tayi suka shiga ɗakin ba wani ƙura yayi ba komi gashi jere gwanin ban sha'awa an aje shi a muhallin sa,buɗe wadurob ɗin tayi taciro wani pink bedshirt tace,"cire wannan kisa wani don ya kwana biyu baa canja ba",tou MOMY,saida ta duƙa ta amshe zani,abu ba ƙaramin daɗi yayi ma MOM ba daga ganin yariyar zatai biyayya da ladabi.............!
MORE COMMENTS
MORE TYPING🖌️
SAMBANJIN DAƊIN ABINDA KUKE MIN KASHE MIN GUYWA KUKE😔😢�
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
*INAYINKI OVER MY MASOYIYA SIS AISHA GOHE MAI MURYAN......😷🏃♀️*
*SHAFI NA TAKWAS DANA TARA 8&9*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
__________📖Yaye zanin gadon tayi ta musanya wani gadon koh tsaf ya gyaru kamar a zuba loman tuwo aci MOM batai mamaki ba yanda taga tayi aiki shape-shape ba daga gani inda aka rene ta ta horu da aiki sosai harda wanke bayi acikin ƙan ƙanin lokaci kafin ta ta feshe ko ina da room freshner MOM na zaune kan kujera tana kallon ta tana aiki cike da ƙwarewa.
Saida ta ɗan duƙa tace,"MOMY na gama",cike da ladabi take maganan,MOM murmushi tayi tace,Allah ya miki albarka,muje ki ɗauko su ki musu wanka sai ku kwanta in Allah yakai mu gobe zaa samo muku kayan canjawa","a kunyace tace,"tou MOMY mungode Allah ya saka da alkhairi","amin" cewar MOM kafin taci gaba da faɗin tou bansan kuma kakmar godiya a tsakanin mu komi nayi muku yima kaine,ku ɗauke ni a matsayin mahaifiyar ku inshaAllahu zan maye gurbin ta,nauyi ne ku akan mu Allah ya ɗaura mana in muka cuce ku Allah bazai taɓa barin muba saiya saka muku dan haka kisaki jiki komi kirinƙa yinsa kai tsaye a halin yanzun baki da inda yafi nan gidan kune kuma gidan iyayen mijinki ne kinji MEENATU", ƙara ƙasa da kai tayi tace,eh MOMY nag......,saurin rufe baki tayi da ta tuna MOM tace bata son godiya,murmushi MOM tayi da taga ta fara magana ta datse,miƙewa tayi tai gaba tana yayinda MAIMUNAH tabi bayanta,koda suka isa falonMAHAFUZ kwance yake kan cinyar MUNAYYA yayi baccin sa hankalinshi kwance itako sai shafa gashin kansa take,MOM ta kalle ƴar yariyar da batafi 8years ba har ta iya ɗaukan ƙanin ta a cinya yana bacci buɗe baki tayi tace,"baby baki tsoron ya karya miki ƙafa?,murmushi tayi tace,"MOMY na iya ai",murmushi MOM tayi tace,"tou naji daga yau baki ƙara ɗaukan shi zan ɗauke shi mu rinƙa kwana tare",da sigar wasa tai maganan,dariya tayi tace,"MOMY ai ƙani nane ko AUNTY? ta ƙareshe maganan tana kallon MAIMUNA,dariya duk suka sa MOMY tace MUNA ɗauke shi kimai wanka yanda zaiji daɗin baccin mukwana lafiya karku manta da addua",tou MOMY",gaba MOM tayi yayinda ita kuma ta ɗauke MAHAFUZ,MUNAYYA kuma tabi bayanta har ɗakin su,direct toilet tai dashi ta cire mai kaya tai masa wanka kafin ta mayar masa don babu wa ƴanda zata canja musu basu taho da komi ba koda sun taho dasu ba ma mora duk sunyi datti kuɗin sabulun wanki ya gagare su,zuwa tayi ta kwantar dashi tace,MUNAYYA ma tacire kaya,cire kaya tayi suka shiga bayin tayi mata tace ta maida kayanta ta hau gado ta kwanta itama,kafin itama ta cire kaya ta watsa ruwa ta maida tufafin ta ta fito MAHAFUZ tuni yakoma baccin sa MUNAYYA ma ta fara lumshe hawa gadon itama tayi azkar ta karanta ta shafa musu kafin rufe ido tunan rayuwar baya ya faɗo mata tai saurin kaudashi don sam bata son tina baya.
Kai tsaye da SALEEM ya fita yashiga motor sa mai gadi ya buɗe masa get ya fice a gidan,gidan sa ya nufa,yanda ya bar gidan haka ya ƙara zuwa ya iske shi saide kuma yanzun falon wani ƙarnin kifi ke tashi da alaman taci kifi ta bar dattin a wajen girgiza kai kawai yayi ya nufi ɗakin sa ya buɗe ya kulle ya shiga wanka yayi tare da ɗauro alwala ya gabatar da shafai da wutiri ya juma yana adduoi akan auran shi dq MAIMUNA da HANEEFA kafin ya shafa ya kwanta,tunanin halin HANEEFA ba ƙaramin damun sa yayi ba bacci ɓarawo ne ya ɗauke shi.
*********
ALHAJI-ALHJI-ALHAHJI,cewar TALATU, uhum ba kunne keji ba wai kina ta kwaɗa min kira ha",tou kuɗin ice zaka bada ko kuma ka bada kuɗin koko",tou TALATU ina na gansu ki ranta kiyi",akan mi zan ranta ma kuɗi ALHAJI baka biyan bashi,ni kuma kuɗin da ke jikina dabbobi na zan sai ma abinci wallahi",dabbobin ki sunfi ƴaƴanki kenan?"aa amma da incida ku gwamma nacida su kai tausayina kake koh ƴaƴanka na tausayina,in sun samo cinye abinsu suke saide inga sun kawo ma", "keko TALATU sam baki da godiyan ubangiji,tou shin aike ce baki tausayin su shiyasa suma basa tausayinki amma miye basa miki yawan cin MATAN BAHAUSHE baku da godiya Allah wallahi","wallahi ƙaryanka ALHAJI kace bani da godiyan Allah in bani mai haƙuri ba wazata zauna da MUGUN MIJI irinka kafita kanemo ka kasa zuciya duk ya mutu","tou ya isa basai kinci mutunci naba yi gaba",aiko baka ceba auran ƙaddara kawai",fita tayi tana bambami,bai kuma ce mata uffan ba,don yana biyeta zaai ɓatatta,fita tayi tasa hijjab ta ɗau bokitin dusan awaki tafice don siyowa.
Bayan fitanta babban ƴarta AMEENAH ta haɗo ma mahaifita tea mai kauri da ƙwai ta kawo masa farin ciki yayi ya rinƙa sa mata albarka dama haka jiya ya kwana cikin shi na kuka,tambayan shi tayi halan baida kuɗi shiyasa tajiyo shi da mahaifiyar su yace,eh"girgiza kai tayi cike da takaici halin mahaifiyar su bata iya temakon ƴaƴanta da mijinta kuma lalitanta cike yake da kuɗi da tasaya musu abinci gwamma tasai ma awakin ta,kiran ƙannan ta tayi ta basu tea ba bread saida ta tabbatar tacika musu ciki kafin tace suje suyi wasan su.
Dawowa tayi ta ba ma awakin ta abinci ta koma ƙofar ɗaki ta zauna sai zare ido take tana yin dogo da baki tana jiran wani ɗa ya taɓota ta sauke haushin ubansu akan sa.
***********
Tunda ya tashi da asubah ya je sallah bai shigo ba sa shidda da rabi ko da yadawo ya kwanta kasan cewar weekend ne bashi ya farka ba sai shaɗaya wanka yayi yafito ya shirya a gurguje sabida ya tina dasu MAIMUNA basu da kaya ko ɗaya a gidan da bazai fitaba sai da la'asar
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
*INAYINKI OVER MY MASOYIYA SIS AISHA GOHE MAI MURYAN......😷🏃♀️*
*SHAFI NA GOMA DANA SHA ƊAYA 10&11*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
__________📖Da bazai fitaba sai sallah la'asar kai tsaye kasuwa ya nufa ya jijjido musu kaya da takalma da mayafi komi na budurwa saida ya sayo ma MAIMUNATU aka loda masa a motor,saida ya biya ya sayo mata waya mai kyau mai tsada kafin ya nufi gidan mahaifiyar shi.
Afarfajiyan gidan yai packing ɗin motor sa yayinda yasa masu aiki su shigo masa da kayan kai tsaye falon MOM ya nufa MUNAYYA da MAHAFUZ ne kaɗai zaune kan kushim suna kallon tasaha MBC 2 duk sun ƙura ma tv ido kamar zasu cinye shi saida yazo ya tsaya a gaban su kafin sukasan ya shigo da murnan su suka rungume shi suna faɗin oyoyo uncle,shima da murnan shi ya ɗaga MAHAFUZ ya sauke kafin ya ɗaga MUNAYYA ya sauke yace,"ina MOM da aunty?,MUNAYYA tace," suna madafa(kitchen),UNCLE ina sweet ɗin mu tun jiya baka dawo ba",murmushi yayi tare da sosa ƙeya yace,"na manta sister luv,"UNCLE menene sister luv kuma?,ohh baki makaranta bane bakisan mai sister yake nufi ba kenan?,"eh UNCLE DAD yace,"bai dace asamu makaranta ba haka MOMY babba ma tace ta ƙarashe magana kamar zatai kuka,"cike da tausayawa yake kallonta da ace yanzun tana kusan primary two amma batasan komi ba,shafa kanta yayi yace,"karki damu kinji MUNAYATA zansaki dake da AUNTY da MAHAFUZ tsalle tayi ta rungume shi tace,"yauwa UNCLE shiyasa nike sonka",murumshi yayi yanda yarinyar yaji tashiga ransa lokaci ɗaya MAHAFUZ ma dariya yayi yana masa gwarancin sa kalan maganan yaran da basu ƙware wajen magana ba,labari suka rinƙa yi suna dariya kamar abokan sa MAHAFUZ akan cinyar sa yayinda MUNAYYA take ta bayan sa ta sargafe wiyan shi da hannun ta har masu aiki suka gama shigo da kayayyakin da ya siyo.
MAIMUNA na kitchen ta ɗaura abincin rana da ƙyar MOM ta batta zatayi da tace ta bari akwai masu girki tana nace ita zatayi yau abarta haka MOM ta faɗa mata mai sukeso suci yau( CARROT JUICE ND SPAGHETTI MAI VEGGIES) dage dantse tayi wajen girkin tunda ba mai wuya bane kuma akwai komi na buƙata a kitchen ɗin abubuwan da ta fara tanada sune kamar haka,
albasa,attaruhu,koren tattasai,chilli, jan tattasai,vegetable oil,maggi,food seasoning,green beans,thyme,masoro naman rago, yanda ta haɗa
da farko ta dafa taliyar
ta tai half done wato ta dafa kaɗan bata dahu sosai ba, kafin ta dafa naman ragonta ya dahu tuɓus wanda yasha su thyme da maggi da masoro,
sai ta samu tukunyan ta mai kyau ta yanka albasa, chili, attaruhu, tattasai, Koren tattasai se ta soya da mai,sai ta zuba maggi da seasonings ɗinta sai ta zuba masoro,sai tasa ruwa kaɗan wanda zai ƙarasa dafa taliyar da shi,sai tasa zuma rabin ƙaramin cokali ko se tai grating kwa-kwa kaɗan ta zuba batai minti talatin ba ta dahu sai ta kashe gas ɗin ta ɗauko kula ta juye ta rufe.
JUICE ɗin ta haɗa shima kamar haka,carrot,cittah,Sugar,flavour,da farko ta wanke carrot ɗinta ya wanku sosai sai ta yanka ƙanana ta zuba a blender,
tai ta wanke cittah itama tayanka ƙanana ta zuba a blender tasa ruwa ta markaɗa da carrot ɗinta, yayi laushi,
sannan sai ta-tace tasa sugar da flavour,ta juya sosai sai ta sa a fridge yayi sanyi.
*NOTE: Shi carrot yanada kyau sosai wajen kara lafiyar ido👌🏼*
buɗe kitchen ɗin tayi ta zata fito wani ƙamshin girki ya biyota kallon kallo sukai ma juna tai saurin sadda kai ƙasa,shiko lumshe idanuwan shi yayi ƙamshin abincin nan ya shige shi sosai har miyau ɗinshi ya tsinke,haɗiye miyau ƙutt muryanta yaji ya kuma sauka adodon kunan sa tace," barka da yini YAYA cikin sanyin muryanta mai daɗi,ƙara lumshe idanuwan shi yayi don take yaji tsigan jikin shi ya motsa da ƙyar ya iya buɗe baki yace,"lafiya ƙalau",daga haka yai shiru ya cigaba da wasa da su MUNAYYA amma zuciyar shi na wajenta yanaso yace ta tashi tazo ta zauna amma bakin shi yamasa nauyi ita kuma tana duƙe daga nesa ,sakkowan MOM ne cikin shigar dogon riga na rantsa-ts-tsar leshi leshe ta kashe ɗaurin Aisha Babangida in kunganta ba zakuce ita ta haife kamar SALEEM ba sai ƙamshi yake tashi tace,"aa MY BOY yaushe kashigo?,murmushi yayi yace,"najima MY LUV,yaci gaba a faɗin muna wasa ne da yarana",murmushi tayi tace," san.....maganan ta maƙalewa yayi sanda tai ido biyu da MAIMUNATU dake duƙe kanta ƙasa tai saurin ƙarasawa tana faɗin,"MY MUNAH lafiya mai SALEEM ya miki?,ɗago kyawawan idanuwan ta tana girgiza kai tace",MOMY wallahi baimin komi ba",taɓa baki yayi yace,"ohhhh MOM da sharri zakimin?,"gidanku da sharri ta faɗa tana galla masa hararan wasa taci gaba da faɗin ai nasan hali kamar yuwan cikina",dariya duk sukasa harda su MAHAFUZ kamar yasan mi ake faɗa,itako MAIMUNATU murmushi tayi da yasa kumatunta lotsawa.
MOM cike da kulawa ta miƙar da ita tace," fita batu nai ki saki jikin ki kidena kunyar shi kinji ƴata",gyaɗa kai kawai tayi MOM tace,"harkin kamala?," cike da ladabi tace,"eh MOMY", "ok bari insa IYYA ta jera a dining", zaunar da ita tayi akan kujera tana kallon kayan da ke jibge a falon batai magana ba ta illa zuwa da tayi ta fara buɗewa kayan MUNAYYA ne ta buɗe farko tace,"babyta zo in gwada miki aiko da sauri tabar bayan SALEEM tazo inda MOM tafara gwada mata aiko cif ita haka ta gwada ma MAHAFUZ suma cif duk sun masu kyau duba na MAIMUNATU tayi suma duk sunyi kyau MOM cike da farin ciki tace," gaskiya MY BOY ka iya zaɓe Allah yayi albarka Allah yasa kafi haka", yace,"ameen my lovly MOM", duban MAIMUNAH tayi tace tashi muje ɗakina inason magana dake,miƙewa tayi tabi bayanta suka haura sama ɗakin MOM tazauna a ƙasa MOM ta zauna gefen gado tace,MAIMUNATU ki sake jikin ki SALEEM mijinki ne na sunnah,yake ƴata kijanyo hankalinshi ta hanyan kissa da kisi-sina bawai ki nuna masa kina buƙatar wani abu daga gareshiba a'a ki dinga yimai shagwaɓa kina dan kwanciya akan jikinshi kina shagwaɓe masa misali kice masa baby kinuna masa ƙirjinki kice masa baby ƙai-ƙaiyi yakemun ka sosa min amma fa ciki shagwaɓa kamar zakiyi kuka hmmm daga susa lbr zai canza,nasan zakice MOM bata kunya ko?,ba rashin kunya bane kina da kishiya MUNAH dolebna gyaraki ki zamto mai masa godiya ko da yaushe komi ƙanƙanta abu in ya miki ki gode masa baki da wanda zata faɗa miki abinda nake faɗa miki nice madadin mahaifiya a gareki,karki zama cikin mata cewa miji wai me ka ta ɓai mun? Toh wallahi manzan Allah yace irin wannan matan ba zasu ji ƙanshin aljanna ba ma,haram ne kuma mace tace miji ya sake ta ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba babu wani dalili ko hujja da Allah zai karɓa daga wurinki duk randa kika tsaya a gabansa da laifin cin mutuncin miji,rashin biyayya,cin amanarsa da wulaƙanta shi
Miji yana da girman da sai da manzan Allah s.a.w yace da za’a umarci wani yayi wa wani sujjada toh da an umarci mace da tayi wa mijinta,kar ki yi gan-gancin cin zarafin mijinki ko yi masa maganganu marasa daɗi dan wai shima yana yi miki,shi da yayi miki shi da Allah,ke kuma ladan haƙurinkina wurin Allah (me neman aljanna ina ruwansa da wani)ki cire a ranki cewa wai mutum kike wa biyayya,kisa a ranki Allah ɗaya halicce ki shi kike yiwa,dan Allah ne yace kiyi aure kuma kibi mijinki shine hanyar aljannarki
da yawa mata na mistake wai suce su zasu ƙwatarwa kansu ƴanci da cin zarafin miji,da bijere masa da ƙin yi masa biyayya,to kin samu ‘ƴanci kin rasa aljanna me kika yi kenan?,kinyi ɓatan ɓakatan-tan kenan ,ki kalli fa,sujjadar da Allah kaɗai ake yiwa amma ace wai da za'a yi wa ,ba'ace annabi ba,ba'a ce iyayenki ba,ba'a ce malaminki ba sai aka ce miji,kinga kuwa lallai ana so a nuna miki ne bayan Allah da manzonsa babu wanda ya chan-chanci biyayyaa da total devotion irin mijinki,
Mijinki yafi iyayenki,haka addinin musulunci yace,amma da an faɗa nasan zaki ga wasu suna kunfar baki,to ba haka mata masu ilimi suke ba
kar ki ga ana ta zancen maza kullum basu da kirki basu da kaza basu da kaza,sunyi kaza sunyi kaza
Allah yana sane ya yi su a haka!
Ko an faɗa miki zamu samu aljanna a banza ne?
Haƙurinmu,da juriyarmu Allah yake gwadawa,yana so yaga zamu yi masa biyayya akan abinda ya umarce mu,mma mata basa ganewa,wata in ance tayiwa miji biyayya sai tace ai bashi da mutunci,yayi kaza yayi kaza,dan Allah karki zamo cikin mata masu wanan mugun ɗab'ian kizamo mace da mijinki zai rinƙa alfahari dake sai tsafta tsafta cikon addini daga jiya zuwa yau na miki shaidan tsafta amma ki ɗaura