Showing 24001 words to 27000 words out of 28227 words
Chapter 9 - Matar Bahaushe by Mrs.Basakkwace.txt
miki yawa ance miki MAIMUNATU koda ta bar gidan nan da ƙafarta tafita MOM tazo ta ɗauketa ta tafi da ita ta ɓoyeta sannan ai ni yanzun nagane ina haihuwa yaushe nema mukai auran wai shekara nabiyu ne fa muke kuma tsakanin auranta da naki inbaki manta ba wata ɗaya da kwanaki ne matata dallll na buɗeta aleda in faɗa miki sannan ko ƴaƴan nan shegune basu da uban da yawuce ni tunda na aure uwar su kuma sun halatta gare ni sannan jan kunne na ƙarshe karki ƙara cema ƴaƴana shegu",ya ƙarashe maganan yana nunata da yatsa yana murza su waje ɗaya,baijira mai zatace ba ya sa kai ya fice ya barta baki buɗe,wato ita SALEEM ke faɗa ma maganganu akan wata banza wai kishiya.
SALEEM ko gidan MOM ya wuce gida cike yake da ƴan barka ƴan uwan su SALEEM da duk sun ɗauka HANEEFA ce ta haihu basu san da ƙarin auran da yayi ba sai sunzo suga wata ce daban MOM take faɗa musu yayi aure ne kawai a ɓoye BAFFAN shi ƙanin babansa sai faɗa yake saida MOM tamasa bayanin yanda yayi auran ya haƙura.
Maijego tana shan tattali a dangin miji wasu basuyi niyan zuwa ba atinanin su HANEEFA ce amma da sukaji ya ƙara aure tururuwa ake yara da yamma kowa yasan HANEEFA bata da mutunci.
SALEEM kullum kafin yaje aiki sai ya biyo in ya dawo sai ya biya baibarin gidan sai goma ko shaɗaya.
Mahaifiyar HANEEFA tazo barka harso biyu amma HANEEFA ko zuwa batayi ba sabida baƙin cikin dake cin zuciyar ta ace har wata tazo ta haihu ita ko ko ɓatan wata batayi ba ,bata jeba sai ana gobe suna shima MOMYNTA ta kirata ta zazzageta kafin ta shirya taje shima a tsaye tai barkan ko ɗaukan ƴaƴan batayiba ta ta taunan cingam tasa kai ta fice,ƴan uwan SALEEM ko ba wanda yabi ta kanta MOM ce kaɗai ta kulata sai MAIMUNATU duk da tana ta wani shan ƙamshi tana hura hanci kamar na *MY SURUKA FATEEMA ZAHRA😆 KUNSAN HANCIN NAN GUNGUMEME NE MUSAMMAN INTANA DA CIKI WAI BOTORAMI😜🤣*.
DAD ko yana ɓangaren da aka ware mai SALEEM ya masa sabbin ɗunkuna akwanaki kaɗan ya murje yafara maida ƙiban shi,kullum yana liƙe dasu MUNAYYA da MAHAFUZ tare dashi ake kaisu makaranta aje ɗauko su,harya manta da HAJIYA HINDATU,sai lokaci-lokaci yake tunata yasan koda ta duba bata ganshi ba bazata ji komi ba ko ajikin ta zataci gaba da alamuranta taci gaba da cin karanta ba babbaka.
Ranan suna yara sunkaci sunan Mahaifiyar MAIMUNATU da mahaifin SALEEM gidan suna ya cika ya tumbatsa sosai maijego taci ado kamar baza'a mutu ba,duk inda ka waiga zaka hango kowa nakai loma juyawan da zanyi na hango PRINCESS naciro cokali acikin jaka waro ido😳 nayi da buɗe baki😯 ban gama mamaki ba na hango LEEMERT PINKY itama taciro nata harta yaji don in ban manta ba akwai wani gidan biki da mukaje shima harta yaji taje😉 wai SAKEENA GUSAU irin wannan cin shinkafa haka hannu baka hannu ƙwarya kamar zaa ɗauke plate ɗin🤔,hango FATEEMAH ZAHRA nayi tana tura drinks acikin jaka,wai mutane da dama ashe sun san da sunanan harda su LIPTON GIRL naman kaji kawai akeci kunsab bataci sai sallah-sallah,zugar ƴan MATAR BAHAUSHE FANS na hango suna ta salfie agefe SIS NAJAART FANS suna gefe suna hira AISHA BAGUDU FANS ba abinda suke sai rawa,su AISHA JB yanzun aka shigo anci uba adon kyau na zuba a ƙasa wai mashaAllah HAFSAT GARKUWA kuwa fansa duk sun buga anko kunsan mayun biki ne ZAFAFA FANS wai manyan mata maganin ƙananan yara ba abinda suke sai tashin ƙamshi,MAA'ULLE UWAR TSOKANA FANS ba abinda suke sai kallon ƙasar atamfan kowa,biki yayi biki dai gida yacika yai fal harda su LEEMAT ƳARFILLO ,duk anzo aci arage atafi da na dare gida anci ansha anyi hotuna maijego sai canja kaya take kala-kala ana hotuna bakin MOM yaƙi rufuwa haka bakin angon ƙarni baban ƴan biyu ALHAJI SALEEM gidan mutane basu dana shigowa ba har dare haihuwar nan antara abin arziki anyi suna lafiya kowa ya watse amma banda LEEMART PINKY da MRS BASAKKWACE da suka ce sai angama suyan nama sunci iya cin su anbasu tsaraba.
_WAI YAU NAGA KWAƊAYAYYU🤔😆_
Musamman MRS BASAKKWACE hanjin da akasoya tafi kowa ci harda maijego kamar ita ta haihu😯
_BARI INYI SHIRU DON ANCE WAI MASIFAFFA CE MATAR BASAKKWACE ƊINA HAKA NAKE JI AGUN ƘAWAR TA PINKY LEEMAH😜_
KUYI COMMENTS KUGA TYPING😚
Ɓangaren HAJIYA HINDATU kuwa bata damu da rashin ganin DAD ba cewar ta gwamma da ya nemar ma kanshi madafa don ita dama ta gaji da cidashi,cigaba tayi da al'amuran gaban ta bata kuma damuwa da rashin ganin sa ba balle ta neme shi.
******
MAMA fa an rafke anji jiki ciwo na ta cinta tana kwance sai an kwantar an tayar komi sai anmata kamar ƙaramar yarinya yayinda yaran duk suka gujeta in sunyo ƙofar ɗakinta kuwa banɗaki zasu je,MARYAM ce kaɗai mai ƙoƙarin kulawa da ita sai ALHAJI ,sauran ko ko oho ba ruwansu da ita sunce taje awakin da ta fiffita fiye dasu suyi jinyar ta.
Maryam ko tace,sabida albarkacin haihuwa zata kula da ita ,duk da itama ta wulaƙanta-ta ,bata kula da ita ba sanda take neman temako.
_ALLAH YA KYAUTA JINƘAN ƊA MA WANI ABUNE ALLAH YA KYAUTA NA GABA,WALLAHI AKWAI IYAYE MATA DA YAWA MASU KALAN HALIN MAMA BASU JIN ƘAN ƳAƳAN SU BASU IYA TEMAKON SU DA KO SISI BA,ABINDA SUKA SANI KAWAI ƳAƳA SU NEMO SU KAWO MUSU KUMA DOLE SIYI MASU ABINDA SUKESO TUNDA ANCE ABI UWA TOH DA ALLAH YACE ABIKI A GWAGWA CE KE TOH KO AGWAGWA NAJIN ƘAN ƳAƳANTA KO KAZA KI TAƁA MATA ƳAƳA KIGA YANDA ZASUYI DAKE,MATA MUNA DA ƘWAƘWALE KIFI🙄_
MAMAkoh ba abinda take faɗa a kullum sai ku yafe min,abinda na muku shi kaɗai take faɗa sabida zafin ciwo,baccin duk sun watse sun barta.
Akwana atashi ba wuya su MAIMUNATU anyi kwana arbain da haihuwa,da ita da ƴaƴanta sinyi ɓulɓul sabida kulawan MOM sai sheƙi suke yi abin su yayinda SALEEM kullum yana liƙe dasu,DAD ma an murmure anyi kyau yakan shigo falo suyi ta hira da MOM wani lokaci kuma su fita da SALEEM duk da har yanzun bai sakin jiki sosai dasu.
Bayan arbain da kwana biyu suka shiryawa da DAD da MOM da SALEEM da MAIMUNATU,MUNAYYA,MAHAFUZ,da ƴan biyu da ake kira BASMAH DA BASAM sai kura,da sukaje kowa mamaki yake ganin ALHAJI MUKTHAR ya rame gashi ba HAJIYA HINDATU toh ina take kowa tambayan dake ƙunshe abakin sa kenan,wa ƴannan kuma da sukazo dashi waye su,basu wani samu tarban arziki ba wajan ƴan uwan shi,hakan yasa jikin sa ƙara yin sanyi,MOM ta kwantar masa da hankali,ita taje ta same su tai musu bayani komi ta kuma faɗa musu ita surukar shi ce dan Allah tunda ya gane kuskuren shi su yafe mai,girmanta da kwarjinin ta kuma sabida Allah suka yafe masa sukai ta masa faɗa da nasiha akan biye mace da yayi tashiga tsakanin sa da ƴan uwan shi ,neman gafaran su yayi suka yafe masa yanata farin ciki da murna.
Haka suka shirya sukaje ƙauyen ƴan uwan mahaifiyar su MAIMUNATU bai taɓa xuwa ba sai yau suko sai murna suke suga ƴaƴan BILKISU da jikokinta sai nan nan suke dasu kwanan su biyu suka shirya suka taho cike da tsarabobi kala-kala.
Kwana ɗaya sukai agarin kura suka dawo kaduna cike da murna da farin ciki.
"Kike cewa mene HANEEFA da girmanki da shekarunki ƙaramar yarinya ta fiki iya riƙe miji?,tou tun wuri ki gyara".
"Tou ya zanyi ƙawata",HANEEFA ce ke magana duk tayi ƙozai ƙozai ta faɗa,yanzun tashiga hankalinta don ko kulata SALEEM yadena yi in yafita tun safe bai dawo wa sai dare shine take ba ma ƙawarta labari,ƙawar ta ringa mata faɗa da nasiha,kuma tace da yadawo ta nemi gafarar shi ai yanzun zama ake da kishiya lafiya,kishin mai aji ake bana hauka ba kuma taji ta ɗauka nasihar ƙawar tata tayi nadaman abinda tayi tun baya da tayi biyayya da baai mata kishiya ba da ta zauna ita kaɗai da taji nasihar MOMYNTA daba haka ba.
Washagarin da suka dawo tafiya HANEEFA tazo gidan MOM da farin ciki MAIMUNATU ta tarbeta itama haka aka gaisa faram-faram,har ƙasa ta duƙa ta gaida MOM da DAD,MOM sai mamaki take abinda HANEEFA bata taɓa yiba kenan a tsaitsaye take mata magana yau itace guywa har ƙasa.
Itako zama tay ta shantake sai jan MAIMUNA take da hira,koda SALEEM ya dawo yaganta sai mamaki yake tare sukai dinner awajen ne tanemi gafarar kowa SALEEM ba ƙaramin daɗi yajiba haka maimuna da mom,anan ne MAIMUNA tace,YAYA, AUNTY yakamata MOM ta aura DAD ɗinmu koh?.
Kallon-kallo kowa keyi awajen.
MUNAYYA koh tace,"eh wallahi aunty kaima ka amince koh MAHFUZta faɗa tana mai kallon MAHFUZ da ba hankali, sosai gyaɗa kai yayi yana wasan shi HANEEFA ma tace, wallahi ko sun dace",MOM ko kunya SALEEM yace, na ɗau nauyin komi ran jumaa za'ai,DAD murmushi kawai yakeyi ,MOM kunya kamar ta nitse ƙasa,suko ƴaƴan sai hiran yanda zasu sha biki sukeyi daga bisani SALEEM da HANEEFA sukai musu sallama suka wuce,MAIMUNA da taga zasu wuce shida HANEEFA wani ƙululun kishi ya taso mata dannewa tayi tai masu yaƙe harda rakiya a motor shi suka koma aka bar motor HANEEFA,MAIMUNA da ƙyar taja ƙafar ta ta shiga ciki wani nauyi takeji aranta mijinta shida wata.
_🤔 kaji min mata iyayen kishi kiga mata da mijinta ki aura kice zaki kishi baa aure aka aure ki🙄😏_
SALEEM da HANEEFA sun raya daran nan cikin farin ciki da ƙaunar juna suka dirje juna,yayinda MAIMUNATU da ƙyar bacci ɓarawo ya saceta sabida tsananin kishin dake cin zuciyar ta.
Washagari da HANEEFA yazo ya aje ta kafin ya wuce aiki anan tai break fast tana ta nan nan da ƴan biyu MAIMUNATU ko haushinta takeji kamar ta maketa gani take anci amanar ta.
_WAI ALLAH SU MAIMUZ IYAYEN KISHI SUKAYI DE SUNNA_
AGURGUJE
Ranan jumaah aka ɗaura auran MOM ND DAD akan sadaki 150k SALEEM ya biya sadakin shine waliyin MOM yayinda BAFFAN shi ne waliyin DAD duk da ƴan uwanshi suzo abin ya ma dangin MOM ɗadi sosai dana DAD ɗin SALEEM dama sunjima suna mata maganan aure tai ta musu hanya-hanya,anci ansha anyi ƴar walima dan ginsu ne kawai sai ƙawayen MOM da MOMYN HANEEFA aranan MAIMUNATU ta ta koma ɗakinta HANEEFA sai murna take ,adaran ranan SALEEM kaman jira yake saida ya ɗebi gara abin sa,HANEEfA kwashe su BASAM tayi ta tafi dasu ɓangareta acewar ta karsu damesu yau akwai harka.
Zaman gidan SALEEM gwanin ban shaawa kowa burinta ta ga tafi ƴar uwanta iya kula da miji inkungan shi baku iya gane shi yayi ɓulɓul dashi harda ɗan tumbi abinsa hankalin sa yayi matuƙar kwantawa ga matan sa sun haɗa kan su kamar ba kishiyoyin juna ba abin gwanin ban shaawa.
DAD ya dawo da ƙiban shi yayi kyau MOM tattalin abinta take sosai kamar ƙwai,su MAIMUNATU insunzo gidan abin har mamaki suke tsohuwa da iya kula da miji,wani abu in tayi suke jin kunya ba MOM ɗin ba.
_🙄🙄🙄🙄 kaji ƴaƴan zamani ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mata ƙafa salon ai mata kishiya_
Ɓangaren MAMA bayan taji sauƙi ta nemi gafarar ƴaƴanta da mijinta nan suka yafe mata,yanzun tayi sanyi tagane Allah ɗayane komi ta samu ƴaƴanta mujinta dabbobin ma ta kwashe ankai kasuwa ta saida tazo tai ma ƴaƴanta hidima da kuɗaɗe,adduan ta yanzun Allah ya fiddo masu da miji suyi aure.
_SU MAMA ANJI JIKI_
Ɓangaren HAJIYA HINDATU kuwa ta haɗu da wasu ƴan damfara sun damfare ta sun tafi da duk kuɗaɗenta hatta gidan da take bai tsira ba saisa suka sa ta saida suka amshe kuɗi ,akan zasuyi wani kasuwanci da zata samu kuɗi sosai dole badon tanso ba ta koma ƙauye,a ƙauye ko ɗan raɓa ta akayi a ɗakin hatsi nan take kwana ƴan uwanta da suka tambayeta ina mijinta cewa tayi dasu ya mutu,koda labari yaje kunne ƴan uwan DAD sukace ƙarya ne yanan da ranshi da matar shi ƴaƴanshi da jikokin sa.
Ataƙaice de HINDATU tazama kamar mujiya abinci sai an tsammata shima kamar ta roƙa matan ƙannenata da yayyunta siyita zagi da hantara duk ta yaƙune ta zama abin tausayi.
DAD da labari yaje mai yai dariya shiryawa yayi suka tafi da MOM a ƙofar gidan su HINDATU ya tsaya ya aika aka kirata tana fitowa ta ganshi buɗe idanuwa tayi gani yanda ya zama wannan ce matar tashi kenan kallonta yayi a wulaƙance yace HINDATU kenan kinga yanda rayuwa yake soya lokaci lokaci ko ni kikaso ki gani a wulaƙance albarkacin haihuwa ban wulaƙanta va gaki ke a wulaƙance Allah ya kyauta ciro takadda yayi a aljihu ya wurga mata,itako sai zubar hawaye take baibi ta kanta ba ya faɗa motor driver yaja shi sai gidan su inda ƴanuwa ke ta murna aranan suka dawo kaduna.
BAYAN SHEKARA GOMA
abubuwa masu daɗi da marasa daɗi sun faru nasara da rashin sa sunfaru inda MAIMUNATU ta ƙara haihuwan ƴan uku duk maza yayinda taba HANEEFA su BASAM kyauta tunda ita haryanzun haihuwa shiru,tunda ta haifa ƴan uku ta sa kuka ita de saita huta dole badon SALEEM naso ba sabida farin cikinta ya yarda sukai tsarin iyali su BASAM an girma ana primary four yayinda ƴan uku AƘIL maisunan mahaifin MAIMUNA ,ARIF mai sunan maihaifin HANEEFA ,AFIF mai sunan BAFFAN SALEEM,SALEEM an girma anzama magidanci yazama babban mutum sosai haka HANEEFA da MAIMUNATU girama yazo musu amma inka kalla su BASMA zakace ba MAIMUNATU ta haife suba ƙannan ta ne sabida yanayin jikinta mai kyau su AƘEEL suna da shekara biyar shiryawa sukai suka nufi gidan MOM da ta zaɓa dattijuwa yanzun sosai da ita da DAD har furfura suka aje hango wasu kyawawan yara nayi da saida nayi da gaske nagane MUNAYYA ne da MAHAFUZ suka girma haka cike da murna suka tare au BASAM inda MOM ke kwance jikin DAD shiko sai shafa gashin kanta yake suna hira,su MAIMUNATU sun saba gani saide suyi dariya,HANEEFA tace," kai MOM kude baku tsufa",dariya suka sa nan suka zauna akai ta hira cike da nishaɗi, saidare suka bar gidan.
Ɓangaren su MAMA duk ta aura da ƴaƴan ta inda ta bugi ƙirji tai musu kaya naji da faɗa batare da kosisi ALHAJI ba yanzun zamanta lafiya take da ƴaƴnta da mijinta.
HAJIYA HINDATU tayi aure inda ta aura wani ɗan giya y ɓa dake ta kuma dole ta fita tayo aikin wanke wanke da shara ta kawo masa kuɗin giya sannan taciyar dashi,yanzun tana danasanin abinda tayi a baya tana tunain yanda zata ga su MAIMUNATU ta nema gafarar su duk sanda zata ji labarin sunzo kafin taje zata iske sun wuce duk ta rame tayi baƙi zanin ɗaurawa ya gagareta duk mijinta ya kwashe ya sayar yasha giya,kuma bata isa tayi magana ba tasha duka.
_KAƊAN KIKA GANI_
ƘARSHE
SUBUHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIK'ASHADU ALLAH'ILAH HAILLALLAH'WA'ASH HADU'ANNA MUHAMMADAN ABDUHU'WA'RASULUHU
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*SHAFI NA 48&50*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*

"Kike cewa