Showing 21001 words to 24000 words out of 28227 words
Chapter 8 - Matar Bahaushe by Mrs.Basakkwace.txt
da MOM don kar naƙuda ya tashi cikin dare .
Yayinda SALEEM har yacire rai da ƙara ganinta amma yana yawan mafarkinta tana cikinjin daɗi da kwanciyar hankali inde yana cikin damuwa musamman in HANEEFA ta ɓata masa rai takan zuwa ta faranta masa rai,inko ya tashi da safe ya rinƙa sadaka kenan.
Haneefa ko wulaƙanci da gori atunanin ta MAIMUNATU tabar gidan har abada ita kaɗai ne yanzun zataci gaba da murza zaranta yanda takeso.
Wayewar safiya asabar ta tashi da ciwon baya da na mara kaɗan kaɗan haka ta ringa daurewa don kar MOM ta gane ,MOM ko taao ta gano wani abu jin inta tambaye ta tanacewa ba komi yasa ta ƙyaleta ,adaddafe tai sallah magariba muƙewar da zatayi ta kasa bayanta da mararta ya amsa ta yanka uban ihu.
Daidai lokacin yaturo ƙofa wazai gani ihun wa zai ji inalillahi'wainna'ilaihiraji'un kawai yake nanatawa yana murza idanuwa a tuanin shi gizau ɗin da tasaba masa yau ma tai masa ,MOM da tajiyo ihunta fitowarta daga kitchen taje ta sa ai mata faten tsakin da tace yau shi take sha'awa,bangaje shi tayi ta shiga ɗakin tana faɗin sannu tare da ɗagota.
Cizan leɓen ta tayi tare da addu'a,SALEEM ƙara buɗe baki yayi ganin MAIMUNATU da tulelen ciki tou cikin waye waya mata yaushe tai ciki yaushe tazo gidan nan kuma.
MOM cikin ɗaga murya tace,"katemaka mana muje asbiti haihuwa ce tazo".
Yanayin da MOM tai magana yasa ya riƙe tambayoyin sa da ya ƙunso zai watso ya cincime ta yai waje da ita, MOM akwatin kayan haihuwar ta ɗauko tabi bayan su.
MORE COMMENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
*SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU DANA ARBA'IN DA UKU 42&43*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
__________📖Yanayin yanda MOM tai magana yasa ya riƙe tambayoyin sa daya ƙunso zai watso ya cincime ta yayi wa ita ta tana ta salati tana gantsarewa,MOM akwatin kayan haihuwar da ta haɗa ta ɗauko tabi bayan su.
Agidan baya ya kwantar da ita MOM da ko mayafi babu tashiga gidan gaba shima shiga mazaunin driver yayi ya ma motor key maigadi ya wangale get yafice amintina ƙalilan ya isa asbitin sabida gudun da yayi da sauri aka amsheta aka shiga da ita labour room ,shida MOM na tsaye bakin labour room MOM na ta adduan saukanta lafiya yayin da shi kuma tunani yake ya akai MAIMUNA take da ciki dama MOM tasan inda take toh cikin waye ne baride ya jira ta haihu yaga ɗan dawa yake kama kafin ya samu daman yi ma MOM tambayoyin nan,a zuciyar shiko farin ciki kamar anbashi kyautar wani abu amma ya rasa farincikin minene?
MAIMUNATU ko ana labour room anacin kwa-kwa ɗanya inciwon ya taso mata addu'o'i ,kala-kala ke fita abakin ta da ya lafa mata taji wani mugun yunwa ya taso mata hanjin ta kamar zasu tsinke daƙyar ta buɗe baki tagaya ma nurse ɗaya yunwa takeji.
Nurse da sauri taje ta iske MOM na zaune ta rafka tagumi azuciyarta koh addua take Allah ya sauke MAIMUNATU lafiya ,MOM na ganin NURSE ɗin ta miƙe tana tambayan tahaihu ne,nurse ɗin tai murmushi tace a'a abinci takeso taci dai inda hali asamo mata,MOM ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya tace tou ,kallon SALEEM tayi dayake ta sintiri tace,"MY BOI abinci take so taci kaje ka sayo mata kafin ka koma gida ka dawo zakajima","ok MOM",kawai ya iya faɗa ya nufi motor sa yashiga yabar haraban asbitin aiko baijima ba yadawo MOM yaba ma abincin ta shiga dashi,aiko MAIMUNA na ganin ta ta ƙanƙame ta tana kuka tana faɗin MOM kiyafe min MOM kice SALEEM ya yafe min MOM mutuwa zanyi wallahi,MOM dan Allah kafin in mutu kice SALEEM yaje ya ɗauko min DADY mu in yaganshi gida baije aikiba in ganshi in roƙe shi gafara shi.......!,MOM toshe mata baki tayi tana girgiza kai itama tana hawaye ahankali tafurta bazaki mutuba inshaAllahu haka dama zafin naƙuda yake bari in sa SALEEM yaje gidan ku ga abincin kici kinji kita addua kidena kuka",cikin muryan lallashi MOM ke mata magana,"toh MOM yayi sauri",sake MOM tayi MOM ta fice ta iske shi tsaye inda ta barshi yana ganin ta ya tambaya ta haihu ne ,MOM ta bashi ansa ta hanyar girgiza kai kafin ta faɗa masa saƙon MAIMUNATU,jimmm kaɗan yayi can kuma yace,"tou MOMY bari de naje",baijira abinda zatace ba yajuya a sanyaye karde da gaske mutuwan zatayi inta mutu ya zaiyi da ƙyar ya jure rashinta a zahiri a baɗini koh tana manne cikin zuciyar shi,dole yaje ga mahaifinta duk da ba lallai ya saurare shiba amma zai roƙesa yazo ko so gudane yaga ƴar tasa,da tinani kala-kala ya ƙarasa ƙofar gidan su MAIMUNATU ya fito ya tsaya jimmmmmm kamar bazai je bakin get ɗin ba de ya ƙarasa yafara nocking.
DAD ɗinsu lokacin yana madafa yanata fama da ice ga hayaƙi don yanzun HAJIYA HINDATU tadena siyan gas saide tabashi kuɗin ice yaje unguwa mai nisa ya sayo kafin ya ɗaura sanwa yanzun ma tana ɗaki ita da ƙawayenta yana nan yana fama da wuta ga hayaƙi gashi taƙi ci gashi tabashi lokaci inbai gama ba zaisha zagi,nocking ɗin gwt da yajiyo ne yasa shi miƙewa atinanin shi mutanan tane ,don shi ba mI zuwa neman sa kowa ya guje shi yazama kamar mujiya acikin jama'a .
Zuwa yayi ya buɗe ƙofar get ɗin yana ƙare ma SALEEM kallo yana tunanin ina yataɓa ganin wannan fuskar.
SALEEM ko cewa yayi sannu baba don sam baigane shiba don lokacin da yagansa bai cikin natsuwar sa shiyasa bai ƙare masa kallo ba.
Banbaraƙwai DAD yaji kalman SALEEM wai BABA daganin yaron nan ɗan mutunci ne tunda har ya giramama sa amma duk wa ƴanda suke zuwa wajen HAJIYA bamai kallon sa da mutunci balle yace masa BABA,bissimillah yaro HAJIYAR na ciki".
SALEEM ya girgiza kai tare da cewa," BABA mai gidan nazo nema BABAN su MAIMUNATU da MUNAYYA da MAHFUZ,tana asbitine dan Allah in yana nan kamin sallama dashi in roƙeshi yaje ya ganta nine mijinta".
Yai maganan cikin sanyin murya kamar zaiyi kuka.
DAD ko jin yace,"shine mijin ƴarsa dama shi yaba ƴarsa yawani gwalalo idanuwa yanabin sa da kallo.
Ganin kallon da yake masa yasa jinkin SALEEM ƙara sanyi yace,"Baba bade mai gidan ya mutuba?,ta tambaya da alaman tsoro ƙarara afuskar shi.
DAD yai ƙasa da kai tana sharan hawayen da suka zubo masa da bayan hannu,SALEEM koh ganin yana hawaye tsoro ya ƙara kamashi tabbas BABAN MAIMUNATU ya rasu.
"Nine mahaifinsu ba kowa ba dan Allah kakaini garesu na roƙe gafarar su na cutar dasu da mahaifiyar su nima rayuwa gashi ta juya min baya lokaci kaɗan na gode ma Allah da ya ƙara sada ni da ƴaƴana kafin na mutu a wulaƙance".
Yana magana yana matsan hawaye.
SALEEM ko a tsorace yake kallon sa tabbas yanzun da ya ƙaremai kallo yaga tsantsar kaman shi da MAHAFUZ saide MAHAFUZ yafishi farine tou miya faru dashi haka yakoma kamar almajiri ya rame duk da alokacin bai wani ƙare masa kallo ba amma tabbas yasan yana da ƙiba.
"Dan Allah muje kakaini nayi kuskure inma bazaka jera dani ba ko da ƙafa kamin kwatanci zanje inda take".
Maganan sa yadawo da SALEEM duniyar tunanin da ya lula,yace,"BABA muje ga motor ma awaje".
"Naga jikina yayi ƙazanta da yawa nashiga motor ka na ɓata ma duk warin hayaƙi nake sai inyi sati banyi wanka da sabulu ba saide innayi ma HAJIYA wanki yan gutsatsarin sabulu in ɗauka inyi wanka dashi".
Cike da tausayi SALEEM ke kallon sa azahiri yace," muje BABA", DAD ko da yamanta HAJIYA tasa shi sanwa haka yabi SALEEM ,shiya buɗe mai ƙofar motor saida yashiga ya kulle kafi ya zagaya yashiga mazaunin sa.
Ɓangare MAIMUNATU kuwa..............!
_UHMMMMM NA MANTA BAKU COMMENT_
MORE COMMENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
*SHAFI NA ARBA'IN DA HUƊU DANA ARBA'IN DA BIYAR 44&45*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
__________📖Ɓangaren MAIMUNATU kuwa in naƙuda ya tashi taci wiya da ya lafa taji yunwa sai taci abinci jin bayan gida tayi tace ma nurse ɗin takaita banɗaki,nurse ɗin tace tayi anan yunƙurin da tayi sai kan baby nurse ɗin ta temaka mata baby yafito ta ƙara wani uban nishi saiga na biyu allura akai mata mahaifa tafito nurse ɗaya na gyara yaran ɗaya na gyarata tasss aka gyarata bata ƙaru sosai ba yanda zaa ce dole sai an ɗinketa kasan cewan yaran ƙananu ba kalan manya-manyan ƴaƴan ba.
Bayan an gama gyarata aka kaita ɗakin hutu yaran kuma aka fita dasu wajen MOM,MOM jikina rawa ta miƙe tana tambayan ta haihu mi aka samu?,nurse ɗin tace,"sai anbani goron albishir gasu har biyu daga gani kama suke da mahaifinsu don mahaifiyar su tafisu kyau".
"Ƴan biyu fa kika ce nurse?,MOM ta tambaya cike da mamaki.
'Ƙwarai kuwa",nurse ɗin ta faɗa a taƙaice tana murmushi miƙa ma MOM ɗaya tayi ta riƙe ɗaya taci gaba da faɗin ,"mace,da na miji amma mace tafara haihuwa".
MOM duban fuskar babyn take tabbas kama take da SALEEM wannan ƴa kamar an tsaga kara,wani daɗi da farin ciki ya mamayeta bakin ta yaƙi rufuwa sai addu'a take musu.
"Ina mahaifiyar tana lafiya dai ko?,MOM ta tambaya tana mai kallon nurse ɗin.
"Tana cikin ƙoshin lafiya tana ɗakin hutu zaki iya shiga muje in aje babyn guda".
"Toh mashaAllah,lafiyar uwar yafi mahimmanci ba lafiyar ƴa-ƴan ba ,awaje na".
"Tabbas kuwa ,cewar nurse ɗin,in uwa ba lafiya tayaya zata kula da ƴaƴanta".
Daidai lokacin SALEEM suka ƙaraso haraban asbitin bayan yai packing suka fito tare da DAD suka nufo inda MOM suke tsaye.
Suna ƙarasowa yace,"MOM ta sauka lafiya ne ya take ya babyn mi aka samu?,lokaci ɗaya ya jero wa ƴannan tambayoyin.
MOM cike da farin ciki tace,"ƴan biyu kyautan Allah mace da namiji kaga yanda suke kama dakai kamar an tsaga kara,tana maganan tana miƙa masa na hannunta".
Gaban shi ya yanke ƙirjinshi na tsanan ta bugu,jikina rawa ya ansheta yana duban fuskanta tabbbbas wannan jinin shi ce suna tsana nin kama lokacin yana yaro miƙa ma MOM ita yayi ya amsa na hannun nurse yana kallon shi tabbas ƴaƴan duk shi suka biyo ashe MAIMUNATU nada ciki tabar gidan sa kansa har yanzun ɗaurewa yayi,duk da farin ciki na mamaye zuciyar shi baisan sanda yake washe hauru ba duban DAD yayi da yake tsaye tsuru-tsuru yana bin su da kallo yace.
"DAD kagani ko kaddaran aure na tafito da MAIMUNATU randa muka haɗu ,kaƙi fahimta cewa ba yawan banza take zuwa ba ka aura min ita a wulaƙance ashe rabon ƴan biyu mace da na miji ne a tsakanin mu na tabbata basu kenan ba wani haihuwar sai ƴan uku".
DAD ƙasa yayi da kansa yana matsan ƙwalla cike da dana sanin abinda yayi,MOM ko kallon shi take yanda SALEEM yabata labari ai mahaifin su MAIMUNATU mai kuɗi ne ba almajira kalan wannan ba gashi kuma suna kama da MAHAFUZ ƙila shine inko shine Allah ya gwada masa iyakan sa.
"Wanan shine mahaifin su ?,MOM ta tambaya cike da mamaki.
"Eh MOM" cewar SALEEM yanayi yanakallon newborn baby sa da hankalinsa nakan babyn.
Nufa ɗakin da MAIMUNATU take sukayi tana kwance tayi shiru kamar mai tunanin wani abu bacci takeso tayi amma yaƙi zuwa mata jin anshigo yasata juyawa ganin waƴanda suka shigo yasa ta yin murmushi tana mai ƙoƙarin miƙewa tace,"YAYA ina DAD ɗin bakaje ka kira min shiba koh",ta faɗa magana kamar zatayi kuka.
Matsowa yayi yazauna agefenta yana ma babyn kiss a baki yana murmushi yace,"ga DAD nan tsaye".
Ɗaga idanuwan ta tayi ta zuba ma mutumin da yake bayan MOM idanuwa ƙare masa kallo tayi gabanta na tsanan ta bugu tabbas wanga DAD ɗinta buɗe idanuwa da baki tayi maƙogaranta ya bushe.
DAD ƙasa yayi da kai ahankali yace,.........!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
*MATAR BAHAUSHE*
NA *MRS BASAKKWACE*
SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*
DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*
*SHAFI NA 46&47*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
DAD ƙasa yayi da kai ahankali ya buɗe baki yace,"MAIMUNATU dan Allah kiyi haƙuri keda ƴan uwanki ku yafe min haƙƙin ku bazai taɓa barina ba kinga yanda rayuwa yayi dani".
Dake zuciyarta tayi kukan dake niyan ƙwace mata ta haɗiye shi binsa da kallo kawai take maganan bakinta ya maƙale abin da yafaru can baya ya ringa dawo mata a ƙwa-ƙwalwa 'da take face girgiza kai,dafe kan ta tayi da hannuwan ta biyu.
MOM ƙarasowa tayi ta dafa kafaɗar ta,yayinda SALEEM ya kafe ta ido shima DAD haka.
MOM tace,"MY MUNAT mahaifinkine tunda har ya nuna har ya nuna yayi kuskure dama shi rayuwa in mutane basu hore kaba duniya zata hore ka tou yanzun duniya ta hore mahaifinki kiyafe masa ki masa afuwa".
"MOM na yafe masa shima ya yafe mana",ataƙaice tai maganan don yanda takejin zuciyar ta cunkushe mata.
"Nagode Allah ya albarkace ku ya albarkace rayuwarku MAIMUNATU na nema gafarar ku Allah bai bani ikon na naime na mahaifiyar kuba".
"DAD karka damu UMMIE mu bamai riƙo bane ta yafe ma bata taɓa riƙon ka aranta ba abinda ta ɗauka rayuwar auran ta ƙaddara ce".
"Hmmmmm kide bari MAIMUNATU na cutar da BILKISU sosai haƙƙin ta bazai taɓa barina ba",ya ƙarashe maganan yana mai zubar hawaye.
"DAD dan Allah kadena karkai mana kuka,babu kyau zuban hawayen mahaifi ga ɗa abinda ya kamata kaita ma UMMIE mu addua".
MAIMUNA taya zanbar zubar hawaye tun sanda nai miki auren wulaƙanci na wulaƙanta ku da ƙannan ki nabada ku a inda bansani ba,nashiga halin ƙunci da damuwa,nan ya kwashe abinda ya faru tun bayan barin su gida har zuwa yanzun ya ƙarashe maganan yana mai fashewa da kuka.
MAIMUNATU saida ta masa kuka taringa tunowa yanda lokacin UMMIE su itama ta sha wahala.
Ba ƙaramin tausayin sa su MOM sukaji ba duk jikin su yayi sanyi.
"DAD kabar kuka haka katashi dan Allah".
SALEEM ya tashi ya aje babyn dake hannun shi ya ƙarasa inda DAD ya miƙar dashi yana share masa hawaye da hannun sa.
Nan aka zauna anata jajanta alamarin da yafaru da labarin bayan rabuwa,da yamma aka sallame ta bayan likita ya duba ta ya tabbatar babu matsala,gidan MOM aka wuce da ita SALEEM na liƙe da da ƴan yaran shi duk hararan da MOM kemasa amma yayi kamar bai gani ba,DAD ko yaso ya koma amma SALEEM ya hanashi.
"MUKHTAR-MUKHTAR-MUKHTAR,wai har yanzun girkin don iskanci yau zan maka rashin mutunci tunda kanaji ina ƙwala maka kira kana jina wiyanka ya isa yanka".
"Dan Allah HAJIYA HINDU ki rinƙa rage masa icen damuna kinsan sai ahankali inkina son sauri kisai gas mana".
Wani mugun kallo ta wurga ma ƙawar tata da suke zaune suna fira tare da jan tsaki tace.
"Miye amfanin namijin da bazai fita ya kawo ba kawai ka maida shi boyi boyi yarinƙa ma aiki nide bazan fita ba in nemo ba sannan inzo inbiya ma'aikata,bari inga uwar mi yakeyi tun ɗazun".
Tafaɗa tana mai miƙewa tana ta ƙorafi da masifa harda zagi,koda ta isa wajen madafar amma babu shi,buɗe baki tayi tare da harzuƙa BQ ta nufa da sassarfa tana ƙwala masa kira ganin ba kowa yasa ta tabbatar ya fice bada izinin taba duba tunkunyar tayi taga ruwa ne kaɗai da jajjagen kayan miya ranta ɓaci yayi ta rufe tukunyar tana ƙwafa tana ta zage-zage harta koma ɓangaren ta,ƙawar ta najinta bata ce komi ba,shiru shiru ba DAD ba labarin sa tana zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai girgije-girgije take kamar bishiyar kanya.
DAD ko yana can ansa an gyara masa ɗaki musamman koda su MUNAYYAH suka ganshi sai murna suke su haye kan jikin sa suna wasa ,SALEEM baibar gidan ba sai goma ya wuce shima MOM ta kore shi koda yaje gida HAJIYAR gidan nashi tayi bacci abinta ba ruwanta da jiran miji taga ya dawo ko bai dawo ba.
_LALLAI HANEEFA UWAR BALAGAZAZZU😆_
Washagari bayan ya tashi yayi sallah asuba ya kira MOM bata ɗaga ba bacci ya koma bacci bai farka ba sai tara ya tashi yai wanka ya shirya ya fito .
Tana zaune ta kalmashe ƙafa tanacin indomie tana latsa waya dubanta yayi har zai kauda kai kuma yatina wani abu yace.
"Ina kwana HAJIYA HANEEFA kin tashi lafiya".
Wani daɗi ya baibayeta SALEEM yadawo SALEEM ɗin da saida taɗancin magani kamar bazatai magana ba kafin tace ,"lafiya ",a taƙaice.
Mamakin ta yake yaushe zata gane ita ba kowa bace ta dena wannan uban girman kan amma sai ya basar yace," masha Allah nafa samu ƙaruwa HAJIYA HANIFA".
Ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi akaikaice kafin taci gaba da danna waya,tace.
"Maika samu nide nasan ban haihuba kuma nice kaɗai matar ka kuma baka da tunkiya ko kaji agidanan hala kafara kiwon kifine ban sani ba".
Murmushi yayi jin kalan rainin wayo HANEEFA wai ita kaɗaice matar sa.
Yace,"ko ɗaya kishiyar kice ta haihu MAIMUNATU ta haifa ƴan biyu mace dana miji,suna gidan MOM ".
Jin maganan da ya faɗa loman da takai ya zubo wayar hannunta ya suɓuce cike da mamaki take kallon sa.
Murmushi ya sake tare da cewa,"kishirya anjima kije kiga ƴaƴan naki".
"Ƴaƴana kuma ko ƴaƴan shegu kadena haɗa kanka da wannan shegun ƴaƴan yaushe tai cikin a ina ta same su da kana iya ciki ma mace aini yakamata in fara samu ba ita ba,wallahi bazamu ɗau ƴaƴan shegu ba a gidanan salon in haihu ƴaƴana suƙi auruwa a gurɓata musu tar biya".
Cike da masifa da ɗaga murya take magana.
Dariya ya sheƙe da ita saida yayi mai isar sa sosai kafin ya dubeta da take tsaye ta riƙe ƙugu yace.
"Dadina dake HANEEFA aikin jahilci ya