Showing 1 words to 3000 words out of 29178 words
Chapter 1 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt
WATA RAYUWA
by Fatima S Umar Jajira
Na
Fatima S Umar Jajira
Pree book
Episode 1
Murya a sanyaye ta ke magana
"Haba dan Allah malam ka taimaka ka saida mun yadi É—aya É—ari uku da hamsin."
"Haba hajiya a wannan tsadar rayuwar kike zaton zaki samu yadin hijabi me kyau irin wannan a É—ari uku, ai yanzu komai na rayuwa ya tashi hakuri zakiyi ki siya kan haka."
Girgiza kai ta yi ta zaro kuÉ—in sa ta bashi, ya yanko mata yadin hijabin ta baro gurin.
Saida ta yi tafiyar ƙasa mai nisan gaske sannan ta tari kafu babur ta ce ragowar canjinta ashirin ya ƙarasar da ita kan layin su, saida mai kafu babur ɗin ya gama mita sannan ya ce ta hau su huce.
Daƙarfi ta ban kaɗe labulan ɗakin ta fito ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki, a sanyaye ya fito daga ɗakin ya zo gaban ta murya atau shashe ya ce
"Haba Hauwa'u ya ina miki magana zaki fito ki rabu dani, hakan da kikayi kin kyauta kenan?"
Cikin tsawa ta ce
"Dakata Yusuf har wata maganar kyautawa kakeyi? Kai kyauta mun kake? Yaza'ayi na ringa ci da kaina da yaranka har dakai katon banza katon hofi sannan kace na maka rashin kyautawa."
Yaji ciwan maganar ta amma bai nunaba ya ce
"Naji duk abuda kikace, na yarda laifi nane, amma na roƙeƙi da ki koma ciki muyi magana."
"Wallahi ba inda zan É—ara naje daga nan duk abunda zaka faÉ—a ka faÉ—a a nan."
Nunfashi ya sauke ya ce
"A'a Hauwa ki daure mu shiga daga ciki kinga duk mutan gidan sunajin abuda muke faÉ—a."
Kansa tayo da faÉ—a.
"Saime dan sunji adalci ka kemun da zaka ce mushiga ciki, ai gara kowa yaji rashin adalcin da kake mun a cikin gidan nan."
"Haba Hauwa'u bafa ke kaÉ—aice a cikin irin wannan yana yin ba mata da yawa suna fuskan tar hakan amma suke rufawa maza jansu asiri sabuda sunsan halin da ake ciki a yanzu."
"To ni bazan iya ba na gaji."
Ganin zata tara masa jama'a yasa ya rabu da ita ya koma É—aki yana tunanin halin daya tsinci kansa a ciki ga talauci ga mata mara mutunci, yanaji tana ta masa habai ci amma bai ko kula iskar ta ba.
A ƙofar layinsu aka sauketa, ta ƙarasa gidan nasu ta shiga ciki da Salama, kallon sama da ƙasa ta mata ta ce
"Sannu gan ta laliya kin dawo daga gantalin?"
Cikin ƙunar rai ta ce
"Naje siyo yadin hijabi ne tunda next week za'a koma Islamiyya."
Wata uwar tsawa ta daka mata
"Uban wane zai barki kikoma Makaranta ki cigaba da gantalin naki na hali ko? To baki isaba wallahi."
Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta ta tsuguna ta ce
"Dan Allah Mama karki sa a hanani zuwa Makaranta kiyi hakuri karki hukun tani ta wannan hanyar."
"Hmmm Khadija kenan ai azaba kala-kala zan ta gana miki har sai kin yarda da kudirina."
Kuka me sauti Khadija ta sa tana girgiza kai
"Banzan iya ba walahi kiyi hakuri."
A fusace Mama ta warce ledar hannun ta, ta buɗa taga yadin hijabi ne ta yi murmushin mugunta ta miƙe ta ce
"Munafuka zakiyi bayanin inda kika samu kudi kika soyo shi idan Baban ku ya dawo."
"Allah Mama kudin taruna ne na gidan su Abida na....!"
Ko kulata Mama bata yi ba ta shige warta É—aki.
A sanya ye ta miƙe ta shiga ɗan karamun ɗakin su da suke kwana ta samu guri ta zauna, ta yi tagumi.
Tana tunani Wannan Rayuwa da ta juya mata baya, da yanzu tana gaban mahaifiyar ta wazai ringa cuzguna mata haka? Hawayen da suka zubo mata ta share a fili ta furta.
"Allah sarki Ummi na, ko kina raye ko kin mutu? Allah ne masani, Allah ya kareki a duk inda kike indai kina raye ya dawo mana dake cikin koshin lafiya, idan kuma kin rigamu gidan gaskiya Allah ya kyauta makwanci Ummina."
Ta ƙarasa maganar tana kuka me ban tausayi.
*********
Cike da isa ya na tako ɗai-ɗai ya zauna kan dining table ɗin yana ƙarewa kayan kai kallo, fuska ya haɗe cikin isa ya fara magana.
"Nafisa! Nafisa."
"Na'am."
Ta amsa da sauri ta na fitowa daga É—aki.
Matashiya ce da bazata haura shekara 24 ba fara ce amma bada tsayi sosai amma kyakykyawa ce ga fara'a da tarbiya.
Har ƙasa ta tsuguna na ta ce
"Gani Abu Anwar."
Kafin ta rufe baki taji saukar ya tsunsa a kuncin ta, dafe kuncin ta yi tana kallon sa hawaye na bin kuncin ta.
"Ke wace irin jaka ce da kulu saina sanar da ke abunda bana so? Wace irin jakar kwakwalwa gareki da ba ta riƙe abunda ake biya mata, so nawa zance da ke bana son cin wannan ƙazan tar abuncin naki, me kama da amai. Na sanar da ke inba tea ba ban yarda a dafa wani abu da safe a gidan nan ba, amma baki yarda ba ko? To wannan haukar da kika dafa ita ce abuncin ki na kwana 2 bani mukulin store."
Tashi ta yi jiki na rawa ta kawo masa key É—in tana kuka, ya wurga mata harara ya fice daga gidan. Tana masa addu'a amma ko kula iskarta bai ba ya wuce.
Tashi ta yi ta share hawayan ta inda sabo ta saba da halin mijin nata, kwata-kwata bashida hali me kyau.
**********
Abokin nasa ya tsirawa ido kafin ya ce
"Yanzu ya zamuyi da wannan yaron."
Dafa shi Salim ya yi ya ce
"Karka tada hankalin ka akan Nasir zamu ji dashi, da ƙafar sa zai gudu ya bar mana company mu muci gashin kanmu."
Ajiyar zuciya ya yi ya ce
"Nasani amma tayaya?"
Murmushi Samir ya yi ya ce
"Zan sanar dakai idan na gama tsara komai."
Zaiyi magana sukaji an buɗe kofar an shigo, a tare suka miƙe suna masa sannu da zuwa.
Ya amsa cike da izza harararsa sukeyi ƙasa-ƙasa, a fili kuma sunata washe baki.
Ya zauna yana cika yana batsewa, suka zauna Samir ya ce
"Barka da isowa Alhaji."
Kai ya gyada ba tare da ya yi magana ba Isyaqu ne ya ce
"Barka da zuwa Abu Anwar."
Fuska ya saki ya amsa masa kafin ya ce
"Ba wanda ya zo nemana?"
"Eh ba wanda ya zo."
Kai ya girgiza ya ce
"Okay ina son hutawa."
Sum-sum suka miƙe suka fice.
Ya zaro wayar sa ya lalubo wata number ya kara akune.
Saida ta kusa katse wa sannan aka dauka murya na rawa ta yi salama tare da cewa
"Kayi hakuri Alhaji har yanzu yarinyar nan taki bani haÉ—in kai, na rasa yadda zanyi da ita."
"Kinga na gaji da ƙarairayinki idan baza ki iya ba zan hakura gaba ɗaya."
"A'a Alhaji yanzu haka na matsa mata har makaranta na hanata zuwa kuma na fara mata sharri gurin babanta kaga wuya zata sa ta amsa da kanta."
Cikin isa da gadara ya ce.............!
Comment
And
Share
WhatsApp number 08166077167
By
*XAHRA*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Pree book
Episode 2
___________ "Wannan ita ce dama ta arshe da zan baki, idan kika sake na sake ne manki ba wata tsayayiyar magana hmmmm, basai na sanar dake abunda zai biyo bayaba kin sani."
Bai jira ta yi magana ba ya katse wayar.
Mama da take kule a aki ta ringa goge gumi kar yarinyar nan ta tona mata asiri fa, tashi ta yi da sauri ta fito tsakar gidan ta fara kiran Khadija.
Khadija da ta fara bacci bayan kukan da tasha, taji anata kiranta, ba shiri ta mi e ta fito gurin Mama, jikinta har rawa ya ke sabuda tsoro ta ce
"Gani Mama."
Mama tana kunfar baki ta ce
"Nagaji da rashin mutunci da kike mun kina sawa mutuncina yana zubewa har wani gata gareki da bazaki yarda da kudirina ba to wallahi sai dai ki bar gidan nan."
A razane Khadija take kallon Mama, mama ta gyada kai ta ce
"Ko kina tantama ne?"
Kai ta girgiza alamun a'a
"Idan ma kinayi to ki tuna yanzu ina uwarki take? Ta salwanta, to kema kibini a hankali kona sabautaki wallahi."
Kuka Khadija ta ke ta ce
"Kiji tsoron Allah Mama kisani akwai ranar da zaki koma ga Ubangiji kuma zaki girbi duk abunda kika shuka."
Bata rufe baki ba, sukaga shigowar Baba ya na ta ce
"Lafiya nakejin maganar ku har zaure?"
Kuka Mama ta saka harda majina ta na cewa
"Waini Khadija zata zaga harda ni nasa uwarta ta tafi karuwanci ta barta harda zagidana tana cimun mutunci."
Zaro ido Baba ya yi ya ce
"Yanzu Khadija ce ta ke fa a miki wannan magan ganun."
"Allah Baba ba haka na ce ba."
"Kaji ko? To na mata arya."
A fusa ce Baba ya ako tsabga ya fara jibgar Khadija tana ihu ta na bashi hakuri.
Mama tana gefe tana dariya, da taga dukan ya yi yawa sai ta fara bashi hakuri tana cewa
"Ni da kasani baka daketa ba kabarta taje taitayi bakin rai bakin fama nan gaba zata haifa ita ma."
Sai da Baba ya farfasawa Khadija jiki ya rabu da ita ya ce da ita
"Daga yau idan kika ara zagin Lube saikin bi uwarki yawan duniya shegiya me kama da mujiya."
Ya fice yana ta huci,ita kuma Mama ta rakashi tana
"Allah ya huci zuciyar ka kayi hakuri."
Yana ficewa ta joyo ta kalli Khadija ta ce
"Khadija naga alama bakya so mu rabu alau da ke amma tunda haka kike so muzuba mu gani."
Ta shige aki tana ta rera wa a harda rausaya wa.
Khadija jiki na tsami ta tashi ta koma akin na su da duk sako ne a ciki tana cigaba da kuka me ban tausayi, abu buyu ne sukafi tsaya mata a rai, wai Ummi ta karuwanci ta tafi da iskanta ta da Baba ya yi taji ciwan abun amma ba yadda zatayi.
*************
Sauke miyar kukan tayi tana ara ice yarinyar ta zo kusa da ita
"Umma yinwa nake ji."
Ture yarinyar Hauwa ta yi cikin masifa ta ce
"Dan ubanki ba gashi kina kallo ina girkin ba, zaki adabe ni, idan biyewa sakaran ubanku zanyi tukunya bazamu ara acikin gidan nan ba."
Matar da ke tsakar gidan ta na wanki ta ce
"Haba Hauwa kiringa sassautawa kanki mana kulum cikin fa a kiyiwa miji kiyiwa yara sabuda Allah."
"To naji ar sa ido mijin ki nayiwa ko yaran ki, da zaki samun ido, ko ba kya ganin laifin sa daya barni da yinwa nida yara saini dan nayi fa a nayi laifi."
"Kowa fa zaman hakuri yake dana sa mijin a wannan hali da muke ciki, gara kema ga mijin a kusa dake kya ringa ganinshi kina jin dadi kuma garkuwane a gareku, amma wata ko inda nata mijin ya ke bata saniba."
"Mtsss to sai me da zai shiga Duniyar ma ya ne mo ku i da yafi wannan zaman asarar da yakeyi."
Girgiza kai matar ta yi ta kasa cewa komai ta kula Hauwa ta yi nisa batajin kira, saidai a tayata da addu'a Allah ya ganar da ita.
Habai ci Hauwa ta cigaba dayi tana masifa ita ka ai. Yusuf yana aki duk yanajin ta, yaga alama inba wani mataki ya auka da gaggawa ba fita tsakar gida ma saita gagareshi, duniyar tunani ya lula yadda zai samawa kansa mafuta.
*************
Alhaji Nasir yana ajiye waya ya mi e yasa wa office in nasa key ya kule, ya bu e wata ofa a cikin office in sa ya shiga, ya jima aciki kafin ya fito fuskarsa cike da damuwa ya jawo wayarsa akan table ya kira wata number ana agawa ya ce
"Akwai matsala ina so mu ha u yanzu."
"Okay."
Ya ce ya ajiye wayar ya auki car key in sa ya fice daga Company.
Ya yi tafiya me nisa har ya fita daga cikin gari, gidaje sai ai- ai, kafin ya parking a ofar wani gida ya fito.
knocking ya yi, aka bu e ya shiga har falon gidan ya samu guri ya zauna.
Wata hamsha iyar mata ce ta shigo falon, mi ewa ya yi yana mata sannu da zuwa, ta zauna shima ya samu guri ya zauna.
Cikin damuwa ya ce
"Na fara ganin canji tun yanzu wai meyake faruwa ne?"
Wani kallo ta watsa masa ta ce
"Haba Nasir meyasa kake son sa kanka cikin matsala muma kasamu, kasan fa idan baka cika al awarin da ka auka ba muma zata shafe mu kajima a harkar nan amma wannan karon kana so ka bamu matsala me yasa?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce
"Ina iyakar o arina akan haka, yarinyar da nake tunani ta yi dai-dai da a idar abun ta i bamu ha in kai wallahi."
"Kuma ita ka ai ce ka gani da wannan sifofin?"
Kai ya gya a, ta ce
"Okay abunda zai faru yanzu tunda matsala zata baka ka nemi auranta shikenan."
Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce
"Ba matsa hakan."
"Eh kawai idan kayi abunda akace ba ruwansu da nasaba ko da Nafisa ce ko Anwar."
Gabansa ne ya fa in ba yaso yaji suna ambato sunan Anwar da Nafisa duk da yana azabtar da Nafisa yana son matar sa, gani ya ke idan har aikin su zai shafi Anwar ko Nafisa to duk abunda zai faru saidai ya faru dan bazai ta a lamunta ba.
Maganar da tayi ce ya katse masa tunani
"Ya kamata ka hanzarta aukan mataki Nasir."
"In sha Allah."
Ya ce yana mi ewa ya mata godiya sukayi salama ya fice daga gidan.
Zazzab'i ne sosai ya rufe Khadija ta ringa rawar sanyi, amma Mama bata duba halin da take ciki ba tasa ta wanki tanayi tana kuka jikinta nata rawa.
Mama ce tasa hijib ta fita a ofar gidan ta tadda Alhaji Nasir cike da tsoro ta ce
"Me ya yi zafi haka har kazo cikin gidan nan Nasir?"
"Tunda kin kasa aikin da na baki bayan magudan kudin dana baki to na yanke shawarar auran ta inya so na saketa daga baya."
Shiru Mama ta yi ta ce
"Da kayi hakuri, aure nawa zaka kashe akanta."
"Ba abunda ya shafe ki da haka ina mahaifinta?"
Kafin Mama ta yi magana saiga Baba ya dawo a tsora ce Mama ta shiga gida shi kuma Nasir ya kalli Baba a gadaran ce yace............
Comments
And
Share
WhatsApp number 08166077167
By
*XAHRA*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Pree book
Episode 3
__________ "Malam dama gurinka na zo."
Cike da mamaki Baba ya ce
"Ni kuma Alhaji."
"Eh."
Matsowa Baba ya yi suka gaisa da Alhaji Nasir, ya tanbayeshi lafiya?
"Naga yariyar gidan nan kuma na yaba da tarbiyar ta ari bisa ari, dan haka nake son a bani auran ta."
Washe baki Baba ya yi ya ce
"Ai kuwa Khadija akwai hankali da tarbiya masha Allah."
Baki Nasir ya ta e ya ce
"Bana so maganar ta au wani lokaci, nan da 1 week na ke so ayi komai a gama ko nawa ne zan kashe bakuda matsala."
Ya bu e motar ya ako ku i masu yawa a jaka ya mi awa Baba ya ce
"Miliyan 2 ce a ciki zata isheku duk hidimar biki, bana bu atar komai daga gurin ku, yarinyar kawai za'a kawo ko spoon karku wahalar da kanku ku siya."
Jikin Baba na rawa ya amshi jakar ya ce
"Allah ya kai mu, mungode mungode."
Hannu Nasir ya aga masa ya ce
"Ya isa haka, idan kuna bu atar wa ni abu matar gidan tanada number ta kune meni."
Bai jira abunda Baba zai ce ba ya shige motarsa ya bar gurin.
Jiki na rawa Baba ya shiga cikin gidan, Mama na ganin sa da jaka ta ce
"Menene a ciki wannan jakar."
Baba na zare ido ya ce
"Ku i ne Lube, arziki ya zo mana."
Baki Mama ta washe ta ce
"Alhadulilah, amma dai ba gidan nan ka saida ba ko?"
Dariya Baba ya yi ya ce
"Ko aya auran wannan yarinyar me idon mujiya ya zo, kuma dama neman kai nake da ita shine kawai na amunce."
Bu a Mama tasa ta ce
"Kayi dai-dai Malam ai dama auran shi ya dace da ita, Allah yasa idan ta je ta zauna karta musu halin nata na tsiya a korota."
"Ai wallahi ta kaso auran nan bata isa ta dawo mun gida ba, saidai ta shiga duniya badai gidana ba."
Murmushin mugunta Mama ta yi ta ce
"Gaskiya ne kayi dai-dai wallahi."
Duk abunda suke cewa Khadija dake wanki tana jinsu, ba abunda takeyi sai kuka me sauti, yanzu abuda ta keji wai-wai a gari shine ya ke shirin faruwa da ita, itama iyayenta saida ita zasuyi, sabuda rashin adalci basu san mutum ba basusan asalinsa ba basusan waye shiba, zasu aura mata shi sabuda bata da gata, ba tada Uwa wadda zata kwato mata anci.
Dur kushewa ta yi ta saki wani irin kuka me cin rai.
A tare suka juyo suna kallon ta, Baba zai fara masifa, Mama ta ce
"Rabu da ita Malam, aidai bata isa ta tsalake abunda muka gindaya mata ba ko?"
Baki ya washe ya ce
"Tabbas ita in banza ai ko Malam Rabe ne (Mahaifinsa) zai dawo Duniya yau ya ce a fasa auran nan wallahi ba zai fasuba bare ita aramun alhaki."
Mama ce ta cigaba da zugashi yana hawa kai, ita kuwa Khadija kuka kawai takeyi me ban tausayi.
*************
Da murmushi Nafisa ta tareshi zata kar i jarkan hannun sa yai saurin da katar da ita, ya ratsa da gefanta ya wuce, da kallo ta bishi ta rasa yaushe Nasir zai canza hali kulum girma yake yana cin asa, kulum addu'a ta ke masa Allah ya ganar dashi ta daina irin wannan halin nasa.
Bayan sa tabi har cikin badroom in sa yana zauna bakin gado tana kallon sa ta ce
"Dama jiranka nake ka dawo muyi magana."
Bai kalli inda take ba ya ce
"Menene kuma?"
Saida ta yi jim kafin ta ce
"Ina so wannan weekend in muje gida da Anwar, mun kwana biyu bamuje ba."
Saida ya gama rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita ya kafeta da ido ya ce
"Nagaji da irin abubuwan da kike mun Nafisa,