Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 29178 words

Chapter 2 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kulum naita biya biki abu kamar karatu, to daga yau na arajin maganar fita a bakin ki ranki zai a."


Wannan karon Nasir ya kaita bango dan haka ta ce


"Gaskiya Nasir rayuwa bazata yiyu hakaba ka hanani fita cikin mutane sannan zuwa naga iyaye na ma bazaka barni b......!"


Kafin ta arasa ta ji saukar mari a fuskar ta cikin tsawa ya ce


"Yaushe kikayi girman da har zan fa a kina maida wa, na kula kulum karo wula aci kekiyi idan zaman gidan ne ya isheki to ki kagama gaban ki amma ki sani ko zaki shekara dubu a duniya ba a namijin da zai kaleki da sunan aure shashasha bagidajiya."


Ya tashi a fusace ya shige bayi, tagumi Nafisa ta yi har ta saba da tozarcin Nasir, amma ba ta ganin laifin sa tafi ganin na iyayenta da sukaga ku i ba binki ce ba komai suka aura mata shi, tunda ta auri Nasir ba ta gane kan sa mutum ne mara al ibila gashi ba wanda ya sa asalisa ko sirrinsa sana'a ma tasan dai Manager ne a wani Company takalma amma ku in da Nasir ya tara bata tunanin shugaban asar America yana da su, ta rasa ida yake samun ku i, kuma duk lokacin da ta tuhume shi ranar me kwatar ta a hannun sa sai Allah har ta saba da mari da dukan Nasir abun ya zame mata jiki ma.




Yajima a bayin ya fito da alama wanka ya yi, tashi ta yi ta ako masa kayan da zai saka ta taimaka masa ya shirya ko dinner bai zauna ya ci ba ya auki motar sa arfe 8:30pm ya bar gidan.




Inda sabo Nafisa ta saba da fitar dare da Nasir ya keyi dan wataran har 12 fita yakeyi kuma ba dama ta tanbayeshi jikinta ya fa a mata.






Da safe bayan an idar da Sallar asuba Yusuf ya samu wani abokinsa Maniru bayan su gaisa ya ce


"Abokina wallahi na gaji da cin kashin da Hauwa take mun a cikin gidana, ni yanzu aiki ko kwasar kashice na samu yi zanyi."




"Gaskiya Yusuf kana cikin wani hali, amma inada shawara guda aya, mezai hana kabini Company da nake aiki na takalma muringa aiki tareba suna neman ma'aikata sosai."




Baki Yusuf ya washe ya ce


"Masha Allah, ai wannan fa uwa ta zo dai-dai da zama naji da in wannan shawara taka nagode abokina sosai da sosai."


Nan suka rabu akan cewa gobe Yusuf zaibi Maniru Company takalma dan ya nemi aiki acan shima.






Yadda taga dare haka taga rana, zuciyar ta cike da zulumi da tsoron makomar rayuwarta, itadai tasan wannan shirin Mama Lube ne, kardai sa au ta tan da tace zatayi shine ta biyo ta wannan hanya? To amma ina tasamo me ku in haka zuwa aya ya siye Baba da miliyoyin ku i? Tashi tayi cikin dare ta ringa nafila da ro on Allah ya tsareta daga sharin me sharri, Allah ya kawo mata mafuta cikin wannan rikitacan al-amarin.




Washe gari da sassafe Yusuf da Maniru suka shirya suka tafi companyn takalma, Maniru ne yaima Yusuf jagora har zuwa office in Alhaji Nasir, bayanan haka suka zauna jiransa har 12:00pm sannan ya zo, nan ma saida suka jira sannan ya ce su shigo.




Da salama suka shiga suka zazzauna suka gaidashi bai amsa ba ya ce


"Lafiya?"


Murya na rawa Maniru ya ce


"Dama wannan aboki na ne ya ke neman aiki ko sharace a taimaka yana cikin wani hali."


Kallon Yusuf, Nasir ya yi kafin ya ce


"Matsayin karatunka fa?"


"N.S.E nayi."


"Okay wace sana'a kakeyi."


"Ba sana'ar da nakeyi ga mata da yara bani da abunda nake basu."


Ya arasa maganar yana hawaye


Murmushi Nasir ya yi ya ce


"Ba damuwa akwai aikin da zakamun, zaka samu ku i sosai amma ka sameni a gida kai ka ai muyi magana."


Bakin Yusuf kasa rufuwa ya yi ya ringa yiwa Alhaji Nasir godiya suka masa salama suka tafi.




Suna fita Alhaji Nasir ya kira Hajiya Hasina ya ce


"Na samu wani miskini nasan zai iya komai akan kudi dan haka ban bashi tayin aikin ki..........!








Comments
And
Share






Ga masu gyara ko karin haske WhatsApp number 08166077167








By
*XAHRA*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Pree book




Episode 4






Daga can Hajiya Hasina ta ce
"Indai har ya yi aiki na ba wata matsala ka masa ta yin shiga kungiya, amma ka sanar dashi tsarin mu."


"In sha Allah, sai kin jini."
Salama sukayi Nasir ya kashe wayar sa yana tsara yadda zai shawo kan Yusuf cikin sauki.




Yusuf suna fita ya dubi Maniru ya ce


"Amma abokina wane irin aiki kake tunanin Alhaji Nasir zai samomin?"


Murmushi Maniru ya yi ya ce


"Wata kila gadi ne ko aikin gida tunda ya ce ka sameshi a gida."


"To amma cewa ya yi fa zan samu kudi sosai."


Dafashi Maniru ya yi ya ce


"Yusuf wai ba ne man ku i ka fito ba?"


"Nema na fito yi mana."


"To duk aikin da ya baka kayi ko yankan kaine."


Dariya sukayi duka, Maniru ya ja hannun sa suka fice ya rakashi bakin titi ya hau mota shi kuma ya koma bakin aikin sa.








Mama ce ta samu Khadija a aki tana zaune ta yi tagumi, dariya ta yi ta ce


"Yarinya idan zaki kwantar da hankalin ki, ki kwantar domin aikin gama ya gama ubanki yaga ku i ya badake."


Hawayen fuskar ta ta shafe ta ce


"Yanzu rashin galibuna har ya kai ayi mun irin wannan auran da ko kaza me gata baza a mata shiba, bakusan mutum ba, sama taka yazo kuma ku bashi aure na."




Tsaki Mama ta yi ta ce


"Mtssss wa ya ce dake bansa Alhaji Nasir, to na sanshi ciki da bai har dalilin auran ki ma na sani, sabuda ni nace ya zo gurin ki zai samu abuda ya ke so."


Kuka sosai Khadija tasaka ta kasa cewa komai, ita kuwa Mama dariya ta ke yi ta ce


"Ba yau zaki yi kuka ba sai nan da kwana 6 zakiyi kuka mai dalili yarinya. Bama wannan abun ya kawoni gurin ki ba ubanki ya bar miki gugar kayansa ya ce kan ya dawo kiyi masa, idan kuma bazakiyi ba kedashi idan ya dawo."




Tana gama fa in haka ta fice tabar akin tabar Khadija na gurzar kukanta.






Suna zaune a tsakar gidan ya shigo gidan da salama, Atine abokiyar hayar su Hauwa ita ta amsa salamar amma Hauwa ko kallon inda Yusuf ya ke batayi ba, girgiza kai kawai ya yi ya shige aki.




Tashi ta yi ta bishi cikin akin ta tsaya a kansa ta ce


"To me mataciyar zuciya, na auka kayi zuciya ka tafi ne man nakai shine ka dawo hannu rabana."


Tashi ya yi ya tsaya a gaban ta ya ce


"Hauwa kenan, da kin kwantar da hankalin ki na samu aikin yi yau na wuce gorin da kike mun, yanzu zan iya ri e iyalina da kaina."


Shewa Hauwa ta yi ta ce


"Ahayee Allah ya nuna mun ranar da zaka kawo cefane a gidan nan Yusuf."


Dariya ya yi ya ce


"Zaki gani kuwa."


Daga haka bai sake kulata ba ita kuma ta zauna sai ana nan magan ganu shidai Yusuf bace mata ci kanki ba.




Ajiyar zuciya ya sauke ya ce


"Najima da wannan tunanin Salim anya ba zancan ka gaskiya ba ne, Alhaji Nasir yanada alaka da kungiyoyin asiri."


Murmushin ta kaici Salim ya yi ya ce


"Na jima ina bincike akan sa, kuma bazan daina ba harsai na gano asalin shiwaye."


"Amma baka tsoro garin bincike wani abu ya sameka."


"Isyaku kenan, kaine kake tsoran wannan yaron ni baya bani tsoro kuma sai na nuna masa mu rigashi zuwa duniya."


"To shikenan Allah ya taimaka."


"Amin."


Salim ya ce suka cigaba da tattauna yadda zasu kawo arshen Nasir.






Abida ce ta shigo gidan bakinta auke da salama, Mama Lube tana tsakar gidan amma ko kallon arziki bata mataba.


Da yake Abida tasan hali, kawai saita huce akin da tasan anan Khadija take zama.




A zaune ta tadda ita tana ta aikin kuka, da sauri ta zauna kusa da ita ta ce


"Lafiya Khadija meya faru?"


Cikin kuka Khadija ta ce


"Ina cikin tashin hankali Abida."


"Me yake faruwa, tunda kika zo na baki ku in tarunki kikace zakije siyo hijab in makaranta baki sake komawa gidan mu ba, yau kuma naje school naga baki zoba, shiyasa nace akwai matsala bari na dubaki."


Ajiyar zuciya Khadija ta yi ta gyara zama, nan ta sanar da Abida duk abunda ya ke faruwa da auran da za'a mata.


Salati Abida ta yi ta ce


"Tunda nake ban taba jin irin wannan abun ba, amma ke wane mataki kika auka?"


Ajiyar zuciya Khadija ta yi ta ce


"Wane irin mataki kuma Abida."


"Haba Khadija da zama zakiyi a lalata rayuwar ki a banza, ai ba bari zakiyi ba, akwai hanyar da zamubi mu samu mafita."


Cikin zakuwa Khadija ta ce


"Wace hanya kike tunani?"


Abida zatayi magana, Mama ta shigo ta ce


"To hakima, gidan ubakin kine nan da zaki shigo ba salama ba gaisuwa ki shige ciki sabuda kin isa."


"Haba Mama Lebe, naga nayi salama kinaji amma baki amsa ba."


"To bazan amsabar shugaban marasa kunya, to wallahi tunkafin ranki ya aci ma, ki tashi ki fitar mun daga gida."


Khadija ce ta yi magana


"Haba Mama dan Allah ki rabu da ita, ko bakisan Abida ba ai bazaki mata haka ba bare kinsanta kinsan matsayin ta a gurina."




"Dalla malama rufemun baki, uban ku zan ha a inci, idan bata tashi tabar gidan nan ba."


Abida zatayi magana, Khadija ta ce


"Dan Allah Abida kiyi hakuri, kije zamuyi magana daga baya."


"Hmm to shikenan."


Abida ta ce, ta fice suna hararar juna da Mama Lube.




Tana fita Baba ya na shigowa ya ce


"Wannan ba Abida ce ta fita ba?"


"Ita ce mana."


"Amma ta wuce ko gaidani ba ta yi ba."


"Ai bazata gaida kaiba nima yanzu ta gama yimun rashin kunya ta fita,dan na mata magana, tazo ta sa wannan saunar a gaba tana hure mata kune."


Kai Baba ya girgiza ya ce


"To daga yau na haram ta mata zuwa gida na, kuma itama wannan yarinyar Khadija ban yarda ta sake fita ko ofar gida ba, kuma aure ba fashi dan ko yau yaron ya kirani munyi maganar abuncin biki duk zai kawo."


Murmushi Mama ta yi ta ce


"To Alhadulilah, Allah ya nuna mana bikin lafiya."


"Amin."


Baba ya ce. Mama ta zuba masa ruwan alwala a buta ya amsa ya yi alwalar ya fice daga gidan ya nufi Masalaci.






Washe gari.


Gari na wayewa Yusuf ya tafi gidan Alhaji Nasir, ba a gida ya kwana ba amma haka ya zauna jiransa har 11:40am sannan ya dawo.




Falon gidan Nasir ya sa aka kawo shi ya shigo yana ta kale-kale, bayan sun gaisa, Nasir ya yi ajiyar zuciya ya ce


"Malam Yusuf, nasan kana bu atar ku i, Allah ya sa ka shirya samunsu ko ta wace hanya?"


"Ranka shi da e indai zan cida iyali ai Alhadulilah burina ya cika."


Saida Nasir ya yi jim kafin ya ce


"Ni mutum ne da ba kowane yasan ni waye ba, amma idan har ka sake kasan ni waye to dole kashigo cikin tafiyata ka amunce?"




Yusuf baiyi tunanin komai ba ya ce


"Na amince."


"Good, ina da aiki guda biyu da zan baka, aya na wane aya na abokiyar aikina. Kafin kayi wannan kana bu atar kasan ni waye..........!






Comments
And
Share








Ga masu shawara ko arin haske ga number ta 08166077167 nagode










By
*XAHRA*







*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Pree book




Episode 5






"Hakane Alhaji."


Tashi Nasir ya yi yana zagaye falon kafin ya fuskan ci Yusuf ya ce


"Maganar gaskiya ni ba aikin Company Kalama nake ba hasalima company nin na yaro na ne a kungiya. Na kasan ce na taso bani da gatan uwa bare na uba daga baya ma na rasa su gaba aya da ina rayuwa a garin mu can Katsina da zaman can ya gagareni shine da dawo Kano da zama, nayi sana'a kala-kala amma ba nasara, ta hanyar aboki na mukaje Kaduna, nan naga cajin a gurin wani uban gidan mu yana bamu ku i sosai, wata rana ya ta a aika mu gidan sa, da mukaje matarsa ta gani tunda ga lokacin ta like mun, tun ba ta yi nasara a kaina ba har Allah ya bata sa'a taci galaba a kaina, tashiga jikina sosai tasan komai nawa kuma tasan damuwa ta nayi ku i, shine watarana ta jani wani gida ta ce ga ida zan samu ku i ko wane irin ne, mutane ne irina amma kallon Aljanu nake musu har takai, kaina ya juye na rasa abunda ke faruwa dani a gidan, ashe kungiya ce ta asiri ta kawoni, sumun bayani zan samu ku i masu yawa ta hanya me sauki, amma saina kikaye abu guda uku. Dole idan kungiya ta bu aci kayi abu sai kayi, kuma idai ka shiga kungiya ba fita, kuma baza ka fitar sa sirrin kungiyaba, idan ka sake ka karya doka aya daga ciki, to zaka iya rasa rayuwar ka, ko kazama galimar matsafiya, ma'ana zasuyi wani sidabarun da jininka. Na harda da wannan tsarin ban bar gidan ba saida miliyan 10."


Ido Yusuf ya zaro ya ce


"What miliyan Goma fa."


Kai Nasir ya gyada ya ce


"Tunda lokacin nayi mahaukatan ku i na dawo Kano da zama sabuda yawanci yan kungiya ba a zaune muke jaha guda ba kowa da inda yake amma duk wata muna zuwa duk wanda aiki ya biyo ta kansa za'a bashi kafin wani watan ya tabbatar ya yi sabuda tsaro, amma ban ta ajin ace abada jinin wani naka ba ko wani saidai ayika masu hadarin gaske, a kano nasamu matar da ta kwanta mun a rai Nafisa na aureta har ma mun haihu da ita, amma ko sau aya banji anyi magana a kansuba, saidai wannan zaman da mukayi, an bani aikin da dole saina samu yariya budurwa da bata ta a sanin a namiji ba, nayi anfani da ita, da wani sihiri da suka bani da bazan sanar da kai shiba, to na samu yariyar amma ta bani matsala shine na yanke shawarar auranta nan da 5days sabuda saura 7days wata na ya cika."




Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke, gaban sa na tsananta fa uwa ya ce


"Tunda bakwa kisa nima na amunce."


Rugume shi Nasir ya yi ya ce


"Nagode abokina."




Nan ya zauna ya ce


"Nan da kwana biyar in zaka kasan ce a gidan da zankai yariyar sabuda tsaro."


"Okay ba damuwa."


"Yauwa dama shine aikin nawa, aikin Hajiya Hasina zance ta nemi wani."


Jaka ya ako fal da ku i ya mi e wa Yusuf ya ce


"Gashi ka hau mota."


Jiki na rawa ya amsa ya yi godiya sukayi salama da Nasir ya wuce gida.




Da salama ya shiga gidan, kamar yadda ta saba wula an tashi bata amsaba, murmushi ya yi ya riko hannun ta har cikin akin ya zaunar da ita.


Baki ta ta e ta ce


"Da kana abun arziki sai kamun burga kamar wani abun kirki ka kawo."


Murmushi ya yi ya danka mata jakar a nannun ta.


Amsa ta yi ta zuge jakar, ido ta zaro ta ce


"Nashiga uku Yusuf ai ku i ne a ciki, tsita kayi?."


Harara ya wurga mata ya ce


"Ba ruwanki da inda na samo, badai burinki a samoba gashi to kiyi abunda zakiyi dasu."




Idon Hauwa ya rufe kawai saita fara murna harda rungeme shi tana masa godiya, shidai Yusuf hankalin sa ba a nan ya ke ba yanaga yadda zaiyi ya ceci yariyar mutane da akeso ayi tsafi da kuruciyar ta, so yake ya kubutar da ita koda hakan zaiza ma sanadiyar ajalisa, shiyasa ma ya amunce da zuwansa gidan ranar da za'akai yariyar, dan zai tsara yadda zai gudu da ita kafin Nasir ya yi tsafi da ita.




A an garan Abida ma hakan take ta ci alwashi baza ta bari rayuwar Khadija ta lalace a banza ba duk yadda za tayi ta hana auran nan sai ta yi, dan tseratar da awar tata.






Yana zaune a falo Anwar yana kan ciyar sa, suna wasa Nafisa ta shigo da salama a bakinta. Kasa-kasa ya amsa ta samu guri ta zauna ta ce




"Barka da dare Abu Anwar, yau baza ka fita bane?"


Kallo ta ya yi ya ce


"Kin gaji da ganina ne?"


Kaita girguza, shi kuma ya ce


"To kar ki kuskura ki ara yimun irin wannan tanbayar tunda ba'a kanki nake zaune ba."


Jiki a sanyaye ta ce


"Ba haka bane Abu Anwar kawai kwana biyun nan ina mugayan mafarkai akan ka, shine nake so ka rage fitar daran nan kuma ka tsanan ta addu'a."




Ransa ne ya aci ya ce


"Kai kulum sai kin sa raina ya aci, hankalin ki yake kwanciya, na fara gajiya da halinki Nafisa, na gaji! Na gaji."




Ya arasa maganar kamar zai dake ta, Anwar da ke kan ciyarsa ne ya fashe da kuka, dai-dai lokacin da kwala ta sako a idon mahaifiyar tasa.


Tsaki Nasir ya ja ya auki Anwar ya shige aki da shi yana rarrashinsa.




Da kallo Nafisa ta bisu, halin Nasir ya fara isarta ita ba jaka ba ko baiwa, amma yake azabtar da ita haka, itama a fili ta ce


"Na gaji Abu Anwar na gaji wallahi."


Da gudu ta ta shi ta shige nata akin ta na kuka.








Kwana biyu a tsakani Abida ta je ta shigar da arar Baba a police station a madadin Khadija, har gida police suka zo suka tafi da Baba da Khadija, itama Mama ta ce bataga ta zama ba ta rufa mayafi tabi bayansu.






Acan suka tadda Abida aikuwa tasha tsinuwa da zagi, saida police suka takawa Mama burki ta daina magana, nan D.P.O ya ce


"Wannan yarinyar ta kawo arar ka, gurin mu sabuda auran dole da zakayiwa arka."


Cikin Masifa Mama ta ce


"To uwar ta ce, ta haifa mana ita."


Nan D.P.O ya ce ayi waje da Mama ya ce da Baba dole a fasa wannan aure.


Baba ya na jin haka ya kira Nasir ya sanar dashi duk abuda yake faruwa.




D.P.O aka kira a waya nan aka sanar da shi ya salami arar su Baba yan zu subar gurin, ba musu ya salami su Baba suka tafi. Dan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads