Showing 9001 words to 12000 words out of 29178 words
Chapter 4 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt
masa ne, kuma bawa ya nemi lahirar sa. Karka bari karasa duniya lahirar ma haka, kaji tsoron Allah, karka cutar da ni, duk da komai ya sameni laifin iyayena ne amma akwai Allah."
Maganar ta, ta daki zuciyar Nasir amma bazai iya ketar ka'idar kungiya ba sabuda idan ya sake jibi, bai cika aikin sa ba, to matakin da kungiya zata dauka a kansa ba mai kyau bane, dan haka cikin acin rai ya ce
"Ya isa, waya ce miki duk bansan wannan ba, to ki adana kalamanki dan nan gaba zasu iya yimiki anfani."
Yana gama fadin haka ya nuna mata hani aki ya ce
"Ga akin ki idan kinga dama kishiga."
Daga haka ya fice ya bar su da Yusuf a zaune wadda zuciyar sa ta ke ta bugawa, yana so ya mata magana amma ya na tsoron kar wani tarkon Nasir ya sa musu dan haka ya yi shiru ya rabuda ita.
Kamar yadda Yusuf ya yi tunani hakan ce ta kasan ce domin kuwa, Nasir ya na kallon duk abunda sukeyi ta cikin camera.
Ya kula yau Yusuf duk ya sauya kuma duk a firgice ya ke dashi, shiyasa ya yi tunanin ya shirya wani abu, da yaga ba abuda suka tattauna Yusuf din ma ya bar gurin sai ankalinsa ya kwanta ya rage zargin da yakeyi akan Yusuf in.
Saida Nasir ya dawo sannan Khadija ta tashi ta shiga akin da ya nuna mata azu.
arwa akin kallo ta yi ya hadu sosai, kawar da wannan tunanin ta yi ta zauna gefan gado, a jikin ta ta lalubo wata waya, wadda Abida ta bata.
Kiran layin Abidar ta yi, bugu biyu ta aga.
"Hello Khadija, kun isa gidan?"
"Mun isa Abida, amma a garin kano ne ba Abuja ba kamar yadda Mama Lube ta ce."
"Nasan za'a rina, kawai ba'aso asan inda aka kaiki ne, amma kiyi kokari ki samo mana wata makama da zamusan a ina kike?"
"Okay zanyi kokari yanzu nasan a inda nake."
Kashe wayar Khadija ta yi ta zuge window in akin ta fara kale-kale, ta na so ta gano wani abu amma ta kasa.
Nasir ne ya dubi Yusuf ya ce
"Zanje gidan Hajiya Hasina, zamu taho da su baki aya dan gudanar da aikin mu, kaima zaka shiga ciki ayi da kai, kafin na dawo ka kulamun da ajiya ta."
Murmushi Yusuf ya a alo ya ce
"To saika dawo."
Fita Nasir ya yi
Yana fita Yusuf ya leka ta, taga ya tabbatar da fitar sa, da sauri ya shiga akin da Khadija ta ke.
Ta na ganin sa ta mi e a tsorace, jikin sa na rawa ya ce.
"Ba cutar dake zanyi ba taimakon ki zanyi, me gidan nan ya kawoki ne domin ya yi anfani da kuruciyar ki ya yi wani tsafi da suke samun ku i, amma bazan bari haka ta faruba, ki biyoni akwai hanyar da na gani a bayan gidan nan mugudu, tunkan ya dawo."
Girgiza kai Khadija ta yi ta ce
"Bazan iya binka ba, ka tafi kawai, ban sanka ba bazan bika ka cutar da niba, nayi hakuri da yadda Allah ya yi dani."
Cikin fa a Yusuf ya ce
"Ina o arin tseratar da mutuncin ki, kina cewa baza ki bini ba, kiyar da dani wallahi ba cutar dake zanyi ba."
Ja da baya ta farayi ta na girgiza zai.
Ran Yusuf ya yi matu ar aci, zaiyi yi tafiyar sa ya barta, amma saiya tuna dan Allah, zai taimake ta.
Kauda komai ya yi a ransa ya fisgota da arfi ya yi waje da ita.
Ta na ganin da gaske fitar da ita zaiyi saita bishi a baya suka fita ta ofar baya.
Turus suka tsaya ganin Nasir a gaban su, ya na sakar musu murmushin mugunta. Kafin kace me, an zagaye su.
Murmushi Nasir ya yi ya ce
"Najima a raina ina wannan tunani saidai, ba wanda yake nasara a kaina, kuma ba wanda ya isa ya hanani abunda naga dama dan haka kashinku ya bushe..............
Gamasu gyara ko arin haske ga number ta 08166077167 Nagode
Comments
And
Share
By
*ZAHRA*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Pree book
Episode 9
Acikin arfin hali Yusuf ya ce
"Ba abunda ka isa ka mana Nasir ka sani Allah ba zai baka nasara akan wannan yarinyar ba, kuma idai ina raye baka isa ka ida mugun nufika a kantaba."
"Idan ka mutu fa?"
Nasir ya fa a yana ha e rai
"Baka isa ka mun abunda Allah bai munba inkaga na mutu to kwanana ya are."
Kafa a ya aga alamar ko a jikin sa.
Yai wa yarasa nuni da su kamo masa Yusuf.
Khadija da ke rike a hannun sa, ta ara a ameshi ta na Girgiza kai. Mutum biyu ne suka araso inda suke suka fara jan Yusuf, kuka me sauti Khadija ta saka, ta na cewa
"Dan Allah karku cutar dashi ku rabu dashi dan Allah."
Wani irin tu o in ba in ciki ne ya rufe Nasir gani Khadija ta i sakin Yusuf, a fusace ya fara takowa inda suke.
Ihu suka faraji da jiniya ta na tashi, nan yaran gurin suka fara gudu suna barin gurin, motocin police ne suka araso gurin kafin suyi wani abun kowa ya kama gabansa, ba Nasir ba su Yusuf, cike da mamaki, Abida ta sako daga motar police in ta na kallon filin gurin ba kowa, itadai idon ta ya hango mata su Khadija da Nasir, amma kamar wanda sukayi layar zana duk sun ace.
Police in ne suka bi bayan wanda suka gudu an kama wasu, wasu sun tsere, haka suka bar gurin ita ma Abida tabar gurin jiki a sanyaye.
Hauwa ta sauka a kura lafiya, kai tsaye gidan iyayen Yusuf ta tafi.
Da salama ta shiga gidan.
Inna da ke hura wuta ta amsa da mamaki ta ce
"Hauwa meya dawo daku cikin garin nan?"
Baki ta turo ta ce
"Nima bansan dalilin sa na cewa mu taho ba."
Jiki a sanyaye Inna ta ce
"To lalanku."
Ta ako musu ta barma ta shiga da kayan su ciki, ta zo suka gaisa, Hauwa ta ce
"Ina Kawu da Murja?"
"Murja ta je makaranta shi kuma Malam ya je kasuwa."
Hirar su suka cigaba dayi ta yaushe gamo.
Murja ce ta shigo gidan da kayan makaranta a jikinta, ta sakalo jakarta, baki ta saki ta na zaro ido ta ce
"Hauwa meya dawo daku garin nan kura bata gama lafawa ba, wallahi yanzu naga Haliru ya huce ta ofar gidan nan."
Kirji Hauwa ta dafe ta ce
"Nashiga uku Allah ya sa baisan muzo garin nan ba."
"Gaskiya bai kamata kuzo yanzu ba kinsa hali Haliru zai kashe yaya Yusuf akan gabar su, kuma ba abuda za'ayi tunda baban sane megari."
Itadai Hauwa duk a tsorace ta ke tarasa ta inda zata fara ma, wayar ta ta lalubo ta fara kiran Yusuf amma a kashe tayi jifa da wayar ta na cewa
"Nakirashi a kashe bare nace karya sake yazo garin nan kar wani abu ya sameshi."
Jugum-jugum sukayi kowa ya rasa abun da ke masa da i.
Sai bayan magrib Kawu ya dawo daga kasuwa, shima ya yi mamakin ganin Hauwa, ya tanbaye ta Yusuf ta ce itama ba tasan inda ya keba itadai ya ce mata ta taho shima zai biyota daga baya.
"Allah ya kyauta."
Kawu ya ce sannan ya ce kar asake wani ya fa i zuwan Hauwa a cikin gari sabuda tsaro suma yaran nata kar a bari su ringa fita.
Da to suka bishi dan kowa ya gamsu da maganar Kawun.
Gumi ne kawai yake keto masa, yana kallon Lailah da take zagaye akin, da fashi Alhaji Nuhu ya yi cikin matsanacin tashin hankali ya ce
"Yanzu mene abunyi?"
Kansa a asa ya kasa furta komai, Laila da ke tsaye ta ce
"Haba Nasir ya mun taru a kanka dan mu nemi manufa, amma ka i yiwa kowa magana."
Hajiya Hasina da take kusa da Nasir cikin rarrashi ta ce
"Bamu da lokaci Nasir, idan wannan yariyar ta kubce a daran yau a samu wata sabuda akwai matsala, idan ba'ayiwa dodo abunda yake so ba."
Sai lokacin Nasir ya bu e baki ya ce
"Yanzu ku acikin ku ba wanda zamu samu abunda muke nema a gurin Khadija."
Harara Laila ta watsa masa ta ce
"Taya zaka samu wannan a gurin mu bayan mu ba Yammata ba."
Jinjina kai ya yi ya ce
"Gara Hajiya Hasina ta yi aure harda yara kefa?"
Shiru Laila ta yi, Alhaji Hassan ya ce
"Nasir duk bamu da lokacin wannan, maganar mafita mukeyi ba kai ka ai abun ya shafa ba."
Kallon Alhaji Hassan ya yi ya ce
"Mezai hana ka bani arka nayi anfani da ita, nasan dai ita baka bari talalace ba ko?"
Tsawa Alhaji Nuhu ya daka masa ya ce
"Haba Nasir ka bamu hankalin ka bafa shirme muka zoyi ba."
Sumar kansa ya shafa yanajin zuciyarsa na masa zafi.
Magana suke amma baya iya gane abunda suke tattaunawa, hankalin sa yanaga Yusuf da Khadija da irin kisan da zai musu in suka shigo hannun sa.
Khadija ya kalla cikin tashin hankali ganin halinda take ci na.............!
Comments
And
Share
By
*ZAHRA*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 10
Na damuwa sai kuka takeyi, jikin sa duk ya yi sanya. Amma cikin ransa godiya keyi ga Allah daya ku utar da su a hannun Nasir, da hayaniya ba ta tashi sun tsereba, da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba, a fili ya furta
"Alhadulilah."
Ya dubi Khadija dake kuka ya ce
"Ya kamata ki daina wannan kukan haka, kiciga da addu'a Allah ya tsare mana gaba, yanzu komai ya huce, bazan maidake gida ba kura zamu tafi gidan iyaye na har komai ya lafa saiki koma gida."
Muryar ta na rawa ta ce
"Nagode sosai da taimakon ka gareni, Allah yasaka da alkairi."
Murmushi ya sakar mata, itama ta maida masa da martanin murmushin nasa.
Motar kura suka hau ta kaisu garin kura lokacin dare ya yi sosai dan haka, da suka shiga gidan ba wanda yasan sun dawo, akin sa kawai ya bu e mata tashiga shi kuma yaje masalaci ya kwana.
Da asuba bayan an idar da sallah, kawu suka ha u da Yusuf.
Har asa Yusuf ya duka ya gaida kawu, kawu ya amsa da cewa.
"Yusuf da hankalin ka kadawo cikin garin nan?"
"Lafiya kawu, zan maka bayani mushiga ciki bani ka ai ba ne."
Shiga sukayi lokacin Khadija ta idar da sallah kenan, Inna ta taso Hauwa.
Hauwa na fitowa ta dafe kirji ta ce
"Dan Allah tunda da safe kashigo garin nan ba wanda yasan kazo, ka koma kar Haliru ya ganka ko yaransa."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce
"Malama ki zo muyi magana ba hauka ba, abunda na baro acan yafi na nan muni."
arasowa ta yi ta zauna kusa da Inna sai lokacin idon ta ya sauka akan Khadija dake zaune kanta a asa.
Gaban ta, taji ya fa i, hakan nan taji wani irin kishi na taso mata.
Yusuf ne ya gyaran murya ya ce
"Ban so dawowa garin nan ba, amma dole tasa na dayo, kuma da yiyiwar daga nan nasake gaba."
Kawu ne ya ce
"So muke muji dalilin ka na dawowa garin nan da iyalinka harda wata bakuwa ba."
Saida ya sake numfashi ya ce
"Tunda na bar garin nan, iftila'i yaketa samuna, mun rayu da Hauwa cikin talauci, tun tana hakuri har takai ta fara cimun mutunci dole tasani fita neman halak."
Nan ya kwashe komai da yadda sukayi da Nasir da taimakon da yazo yaiwa Khadija, da zuwan sa garin nan.
"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!"
Kawu ya ringa maimai tawa, ita kuwa Hauwa nadama ce ta kamata, yanzu duk itace sanadin shigar Yusuf cikin wannan halin, Khadija ta ke kallo wadda taketa faman rusa kuka, taji tausayin yariyar amma wani angare na zuciyar ta, cike yake da kishinta duk da taje cewa matar aure ce a halin yanzu.
Inna cikin jimami ta ce
"Lalai kayi jahadi Yusuf, kuma naji da in sadaukar warka. Kekuma yariya Allah ya tsareki."
Muryar Khadija na rawa ta ce
"Amin Mama na gode."
Murmushi Inna ta yi dan lokaci guda ta ji Khadija ta kwanta mata a rai.
Kawu ne ya ce
"Kayi dai-dai daka kawo iyalinka gida. Ku cigaba da zama anan gidan har muga abunda hali ya yi. Zamu dage aita addu'a a masalatai da tsangayoyi Allah ya tsare ku. Kuma ku dage da addu'a, in sha Allah komai zai dai-dai ta."
"Allah ya sa Kawu nagode."
"Bakomai amma ka ringa kula sosai, sabuda wannan yaron Haliru."
"In sha Allah kawu."
Nan suka cigaba da jajan tawa juna.
Suna zaune a wani kango suna zuke-zuke aya daga ciki ya kalli wani wanda ga dukan alamu shine, oga a gurin, ya ce
"Gaskiya Yarima ya kamata kayi aure, tunda dai ka rasa wannan yariyar ya dace ka samu wata."
Murmushi Haliru ya yi ya ce
"Nima ina wannan tunanin ga Baba ya kusa mutuwa, kaga yana mutuwa ni za'a na a matsayin mai gari, kuma ba za'a bani mulki ba sai inada aure, dan haka dole nayi aure kwanan nan."
Dariya yaron Haliru ya yi zaiyi magana, wani ya shigo kangon da gudu yana haki ya durkusa gaban Haliru yana haki ya ce
"Yarima yanzu na samu labari wannan yaron Yusuf da ya auri Hauwa, ya zo an tabbatar mun an ganshi a masalaci da Asuba."
Zabura Haliru ya yi ya tashi tsaye ya ce
"Ka tabbatar da abuda kake fa a gaskiya."
"Na rantse da Allah da gaske nake."
Wani irin ihu Haliru ya yi ya ce
"Wihuhuuuu saini Haliru a ga megari Usmanu, saini magajin garin Kura, saini yarima sarkin gobe, idan wannan yaron ya ara kwana a duniya to nine bana raye."
Yana gama fa in haka ya yi gaba duk tawagar gurin suka taka masa baya.
Yaron dake kusa da ita ta kalla, bacci yakeyi hankali kwance, ita kuwa, tun daran shekaran jiya rabonta na rintsawa. Hakan nan takeji ajikinta ba lafiya ba.
Tunda take da Nasir duk yawansa na dare dana rana, bai ta a tafiya ya barsu kwana aya da wuni aya ba tare da yazo inda suke ba sai yau, gashi yanzu ko wayarsa bashiga takeyi ba. Tarasa ina zata sa kanta.
Wayar ta dake kan stool ta ako ta ara kiran number Nasir amma a kashe.
Batasan sanda hawaye suka wanke mata fuska ba. Yanzu ta ina zata fara neman Nasir? Addu'a ya kamata ki masa.
Wani an gare na zuciyar ta ya bata amsa.
Bako Salama suka banko, ofar suka shigo gidan, Inna ce kawai a tsakar gidan sai Khadija da take mata wanke-wanke.
A tsorace Inna take kallon su Haliru da suke shigowa gidan, salati tasaka da arfi, wanda ya jawo hankalin Murja da Hauwa da suke aki suka fito a guje.
Hannu Hauwa ta ora a kai tana cewa
"Nashiga uku me yakawo ku gidan nan."
Haliru da tunda ya shigo yake kallon Khadija da taketa muzurai, ya dubi Hauwa ya ce
"Rufemun baki munafuka ba harda ke aka ha a baki gurin yimun shari ba, to yau nazo aukar fansa, ina lusarin mijin naki yake ya aikasa kiya yanzu."
Jikin Inna yana rawa ta ce
"Yaro jiya yazo kuma har ya koma kano yau kuyi hakuri yariga ya tafi."
Murmushin mugunta Haliru ya yi ya ce
"Ashe ya gudu ba matsala zan tafi da wannan bakuwar dan nasan tare suka zo idan yaso shi yadawo ya fansheta."
A tare duk suka juya suka kalli Khadija wace keta zubar da kwala...........!
Gamasu shawara ko arin haske ga Number ta 08166077167 nagode
Comments
And
Share
By
*ZAHRA*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 11
Haliru bai jira ce warsu ba ya arasa inda Khadija take ya kai hannu zai kamota, kawai sai ya ga an rike hannun nasa.
Cike da mamaki ya ago yaga wane me arfin halin ne.
Ido suka ha a da Yusuf, wanda ya ke huci, shima Haliru hucin ya keyi.
Ya warce hannun sa daga na Yusuf ya ce
"Nayi wa kaina alkairin duk randa mukayi ido biyu da kai saina aikaka lahira, inba hakaba bancika jinin Megari Usmanu ba."
Murmushin ta kaici Yusuf ya yi ya ce
"Idai baka kasheni ba, baka cika dan halak haihuwar Saratu da Usmanu ba."
WAIWAYE ADON TAFIYA
Shekarun baya da suka huce, Haliru da Yusuf aminan junane, har makaranta tare suke zuwa har suka gama. Tunda sukagama Secondary school, Haliru ya ha u da miyagun abokai, tun Yusuf yana masa nasiya har ya gaji ya zuba masa Ido.
Haliru yana da wata budurwa da yake auna a rayuwar sa, sunanta Hauwa'u.
Duk duniya ba wanda Haliru ke so sama da Hauwa, kulum yana zuwa gurinta hira.
Wata rana Haliru zaije ta i gidan su Hauwa, ya taho a hanya suka ha u da Yusuf.
"Abokina ina zuwa haka kaci wannan kwaliyar."
Murmushi Haliru ya ringayi ya ce
"Zanje ta i gidan su Hauwa'u."
"Gaskiya ne to a gaida ita."
"A'a aboki baza ayi hakaba kazo ka rakani muje kaganta, kaga kar sai anyi baiko kazo kanace mun baka santa ba."
Da farko Yusuf cewa ya yi a'a, amma Haliru ya matsa suka tafi tare.
Yaro suka sa ya kira musu Hauwa.
Tasha kwaliyar ta, ta yi kyau ta fito ta na sakar musu murmushi.
Gaida Haliru ta yi, ya amsa yana washe baki.
Kamar a mafarki taji zazzakar muryarsa ya mata salama.
A tsorace ta ago ta kali Yusuf.
Lokaci guda ta ji son Yusuf ya shiga ranta, amma nata nuna ba, suka gaisa da shi.
Haliru ya gabatar mata dashi, ta ce
"Allah sarki kulum Haliru yana bani labarin ka ashe ganin ka yafi jinka."
Ba wanda ya kawo komai a ransa, suka she e da dariya.
Haliru ya ce
"Ai Yusuf mutumin kirkine sosai."
Shidai Yusuf salama ya musu ya tafi, harya kule Hauwa tana satar kallon sa. Tun a ranar Haliru ya fara ganin sauyi amma saita ce kanta ne yake ciwo, da haka suka rabu ta koma cikin gida.
Tundaga ranar Hauwa ta daina zancen kowa saina Yusuf, ta ringa wula anta Haliru, ta ce yanzu ba ta sanshi da wanda take so, kuma shi zata