Header Ads
Showing 27001 words to 29178 words out of 29178 words

Chapter 10 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Yusuf ya siya masa.






Mama taje sunyi magana da iyayen Nafisa, kuma sun fahimceta koma, Mama taji dadi ta musu godiya ta huce gida da farin ciki taiwa Nasir albishir, ai harda ihun murna, yaiwa Mama godiya sosai ya koma gida.




A daran Nasir yaje zai taho da matarsa amma Nafisa ta ce bazata biyoshi har saiya tare da Khadija na sati 2 sannan itama zata dawo.




Duk yadda ya so da ita kin amuncewa tai dole tasa ya hakura ya koma gida jiki a sanyaye.






Washe gari Nasir yaje ya samu Mama da maganar tarewar Khadija Mama taji dadi amma bata nuna masaba, sai cewa tai "Allah ya kaimu yasa albarka."
"Ameen."


Yusuf ya ce, sannan ya mata salama ya huce.




Kwana biyu da haka Khadija ta tare bayan ansha sabon biki da taro aka kai Amarya dakinta...............








Comments
And
Share








By
*Zahra*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 29






Abida dake kusa da ita a zaune ta kamo hannunta cikin rarrashi da ban hakuri ta ce


"Khadija kiyi hakuri komai na rayuwa da kike gani rubutacan al'amari ne, dan haka kiyi hakuri kuma kiyi tawakali a duk halin da kika tsinci kanki a ciki."


Dafa hannunta Khadija tai ta ce


"Abida tsoro nakeji wallahi, ina gudun ko ya Nasir ba tuba yai ba ya mana hakane dan mu yarda da shi."


Girgiza kai Abida tai ta ce




"A'a Khadija ki kyautata masa zato kila ba haka bane a cikin ransa, ki maida lamarinki ga uban giji sai Allah ya dafa miki."




Gyada kai Khadija tai tana kwanciya a kafadar Abida ta saki kuka me sauti.




Rarrashin ta Abida ta farayi tana bata hakuri.






Yana rike da hannun amininsa Yusuf suka shiga gidan, duk da cikin ransa ba dadi amma fuskarsa cike take da annuri.


A haka suka tadda Khadija da Abida, Yusuf ne ya kara yiwa Khadija nasiha akan hakuri da tawakali, kuma ta manta da abubuwan da suka faru a baya komai na RAYUWA me hucewa ne.




Godiya Nasir ya masa Abida ta mike da niyar tafiya da sauri Khadija ta riketa, kallonta Abida tai ta ce


"Lafiya?"


Murya a sanyaye ta ce


"Muje na rakaku."


Ba musu suka huce gaba Khadija da Nasir suka musu rakiya har waje saida motarsu ta kule sannan suka dawo gida.








Duk yadda Nafisa ta so jurewa zuciyar ta kasawa tai dan dazu Nasir ya kirata ya ce mata yau zai cika mata alkawari zai maida Khadija matsayin matarsa wanda ba da san ransa ba, a bayama badan soyayya ya aure ta ba, har tabar hannunsa yanzu ma sabuda ita kawai zai maida Khadija badan son ransa ba."




Hawaye taji sun wanke mata fuska, kishi da bakin ciki suka taru sukai mata katutu, Anwar dake kusa da ita takara rungumewa a jikinta tanajin kaunar yaron nata da ta mahaifinsa tana shigartaaddu'
Nasir yasa Khadija tai alwala sukai Nafila raka'a 2 tare da addu'o'i, sannan ya gabatar musu da kayan lashe-lashe, Khadija kasa sakewa tai, shi kuwa Nasir bai damuba yai tafiyarsa dakin baccinsa ya kwanta.




Washe gari kafin Nasir ya tashi Khadija ta gyara ko ina ta hada breakfast tayi wanka ta shirya.


Bai tashi ba sai 10:30am sabuda bazai je office ba ya dauki hutu.




Wanka yai ya shirya, bai tsaya yin bearkfast ba ya ce mata fita zai addu'a ta masa har waje ta rakashi, yaji dadin addu'arta ya hau motarsa ya bar gidan.




Kai tsaye gidan su Nafisa ya huce, tayi mamakin ganinsa amma taji dadi sosai hakan ya nuna mata ko nan gaba Nasir bazai juya mata baya ba.




Bayan sun gaisa yake tanbayarta yaushe zata komai.


Murmushi tai ta ce


"Ka manta alkawarin da mukai da kai, sai Khadija tayi 2weeks sannan zan dawo."


Fuska ya murtuke sannan ya ce


"Bazan iya jiran har na 2weeks ba tare da keba akwai matsala Madam ki taimaka gobe ki koma."




Dariya sosai Nafisa tai ta ce


"Haba Abu Anwar kai dake da Amarya a gida amma kake rokon tsohuwa ta koma."


Harara ya watsa mata ya ce


"Na gaji gaskiya da Baba zan hadaki."


Baki ta turo ta ce


"Naji amma dole Khadija zatai sati dayanta sannan zan koma."


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce


"Naji kamar yaune."


Dariya ta masa, ya ce


"Yauwa madam yinwa nakeji wallahi."


Murtuke fuska tai ta ce


"Nifa baza ayi wannan son zuciyar da niba, ka baro matarka a gida kazo kana cewa na baka abunci tashi ka tafi na salame ka."




Duk yadda Nasir ya so ta bashi abunci ki tai, shi badan komai yaki cin girkin Khadija ba sabuda yana tsoron ko ba dadi kar yaci jagwalgwalo, amma ba yadda ya iya haka ya tashi yabar gidan su Nafisa da yinwa.


Haka zamansu ya kasan ce da Nasir har ta cika kwana 4 baya hade mata rai amma baya sakewa su zauna guri daya itama kuma Khadija haka take so sabuda tsoron ganinsa ma takeyi.






Yausai gurin karfe 9 ya baro gurin Nafisa wanda saida sukai fadama ya taho, dalilin fadan nasu kuwa dan yace ta taimaka ta bishi ko hotel ne ta sama masa nutsuwa dan yana ganin kamar zama da Khadija a haka ba abunda zai masa amma kwanaki biyun nan ko bacci baya iyayi, duk da ba soyayya a tsakani amma sun banbanta a jinsi dole wani abu ya darsu a ransa.






Iskar ya furzar da karfi yana jin haushin kansa da yaje gurinta harta raina masa wayo.




Fitowa yai daga cikin motar tasa ya nufi cikin gidan, yana da mukuli a hannunsa amma yaki sawa ya bude ya fara kwankwasawa sabuda Khadija ta fito ya ganta ko zai samu wata nutsuwar.






Tana cikin bacci taji ana buga gidan tashi tai a tsorace ta fito cikin muryar bacci ta ce


"Waye?"


Saida ya dan jima kadan ya ce


"Nasir ne."


Tanajin muryarsa ta bude masa kofar, saida ya shigo sannan ta maida ta rufe.




Juyowa yai yana kallonta ya ce


"Yanzu koda bakone a haka zaki fito ki bude masa kofa."




Kallon kanta tai ta tabe baki ta ce


"To ya Nasir wazai zo da daran nan."




Baki ya tabe yana girgiza kai ya ce


"Umm gaskiya."


Yai gaba tana binsa a baya...............






Comments
And
Share






By
*Zahra*

*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 30













Tsayawa yai ta huce nata d'akin sannan ya huce nashi
Wanka yai ya sanya jarabiyarsa ya kwanta, amma duk yadda ya so bacci ya sureshi hakan ya gagara juyi kawai yake yarasa abunda ke basa dadi a gidan duniya.


Tashi yai saya nufi akin Khadija, sai kuma ya dawo ya yi haka yafi sau 10 tsaki kawai yake ja yanajin takaicin abunda Nafisa ta masa, kuma ya tabbatar yanzu akan Khadija da bataji bata ganiba zai huce.




Key ya dauka ya nufi dakin, lokacin dayasa key ya bude dakin Khadija bacci take hankali kwance, batasan da shigowarsa bama.


Haurawa yai kan gadon ya fara tashinta.


A tsorace ta tashi tana zare ido, tana kallonsa.


Fuska ya hade duk da a zuciyarsa wani sanyi ne yake ratsashi iya ganinta da yai yaji zuciyarsa tamasa sanyi sosai.


Murtike fuska ya karayi ya ce


"Meyasa kinsan hakkin miji akan matarsa amma baki taba sauke koda guda daya ba? Ko bakije Islamiyya ba?"


Idon Khadija ne ya kawo ruwa, tai saurin cewa


"A'a amma ni bansan abunda banai maka a zaman da mukayi b......!"


aga mata hannu yai da yake da fitila dakin yana kallonta tana kallonsa, sai tai saurin rufe bakinta, tana sunkuyar da kai.


"Kada ki maidani karamin yaro da bansan abunda nakeba, kinga bazan zauna ina bata lokaci na a gurinki ba minti 3 na baki kizo ina nemanki, idan kuma kika sake na dawo da kaina, hmmm sunanki sorry yarinya."


Mi ewa yai ya fice, Khadija ta rakashi da ido kawai tanajin wata fa uwar gaba na ziyartar ta.


Ta bata lokaci a zaune kafin ta tashi jiki a sanyaye tabi bayansa.




A dakin ma saida yaja mata aji sosai sannan ya dawo kuma ya kulata, cikin da bara ya lalaba Khadija har ya samu ya biya bukatarsa.




Kiran sallar asuba ya tayar dashi daga bacci me dadi daya kwasheshi, tashi ya yi yashiga baya yai wanka sannan ya sauya kaya ya huce masalaci.


Sada ya dawo lokacin yabi takan Khadija.


Wadda duk baccin da yai ita bata samu ta rintsa ba sabuda halin da take ciki gashi ko yatsanta ta kasa dagawa bare ta tashi ta nemi gurin tsira.




A hankali ya haura gadon ya dago ta jikinsa, saida ta sauke ajiyar zuciya, idonta a rufe tana zubda kwala.




Murmushi Nasir yai yana kallon fuskarta dayaga tana annuri ya ce




"Saura kiris nai wani kuskure a rayuwata wadda da hakan ta kasance da bazan yafewa kaina ba."


Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa


"Khadija na so lalata rayuwarki ta hanyar da bata dace ba wadda bai kamata aiwa duk wata ya da ka rike mutuncinta na amace kamar kiba, nayi dana sanin abunda ya faru a baya, amma na miki alkawari bazan taba bari wani abu ya taba mutuncin ki ko kimarki ba, na gode my wife Allah ya miki albarka duniya da lahira.




Ranar Khadija taga kulawa da tarairaya, dan ko kofar gida Nasir bai laikaba.




Saida ya kwana biyu ko gurin Nafisa baya zuwa saidai yakira a waya su gaisa.




Haka RAYUWA ta cigaba da juyawa har lokaci dawowar Nafisa yai ta dawo cikin gidan tare da Khadija.


Zaman Khadija da Nafisa zamane irin na mutunta juna, basa nuna kishi irin na jahilci kishinsu gurin kyautatawa mijine a turaka, amma baka taba jin kansu, dan sunyi koyi da matan Annabi Muhammad s.a.w, kuma suna ganin rabar hakan dan kulum arzikin mijinsu karuwa da albarka yake da ayi.




Zumunci kuwa tsakanin Nasir da Yusuf saidai son barka indai ba sanin su kayi a baya ba bazaka ta a cewa ba uwa aya uba aya suke ba, komai nasu tare suke gwanin sha'awa.




Tana kwance a dakinta yashigo da salama amsawa tai tana fa a a fara'arta ta ce


"Barka da dawowa mijina."




Murmushi ya yi ya ce


"Yau matar aljana ya gidan?"


"Kowa lafiya aunty ta tafi dakko Anwar a school kaga ni banda lafiya."


"Gaskiya ne, ya Babyn nawa."


Murmushi tai ta ce


"Ya fara motsi fa."


Zama yai a kusa da ita ya ce


"So yake yaji dumin Babansa bari muyi hira."


Nan ya kara kune ajikin cikin nata yana magana shi kadai wai da Baby yake hira itadai Khadija dariya kawai takeyi ganin irin sakarcin da Nasir yakeyi.


Yajima a haka kafin ya dago yana kallonta ya ce


"Kinsan me nake fata kuwa?"


Kai ta girgiza ya ce


"So nake ki haifi Baby girl me kama dake sosai na riga kallonta ina farin ciki kamar yadda duk sanda na saki a idona nakejin farin ciki."




Murmushi Khadija tai tana shafa fuskarsa ta ce


"Allah ya cikama burinka mijina, amma nima zanso haifar me kama da kai."


"Zaki haifa abunda yanzu kika fara, kuma duk shekara saikinyi."


Ido ta zaro ya gyada mata kai ya ce


"Sosai kuwa yarinya."


Baki ta turo, yana ganin haka ya fara mata wasa harda kamota nan kamota nan, saida yasata dariya sosai sannan ya rabu da ita.




A hankali kwanaki suka ringa shudewa har cikin Khadija ya isa haihu, ya zama aikin gidan duk yana gurin Nafisa duk da itama tanada nata juna biyun amma yaro ne bai girmaba.




Ahaka har Allah ya sauki Khadija lafiya, abunda Nasir yake buri shi Allah ya basa baby girl me kama da Khadija ranar suna akasawa Baby suna Nafisa suna ce mata Awara, Nafisa harda kukan dadi an mata takwara, shiyasa ta zama yar dakinta bacci ne kawai ko in tanajin yinwa take kaita gurin Khadija amma tana gunta.






Bayan shewara uku




Yanzu Nasir yanada yara biyar Khadija nada biyu Nafisa nada uku ciki harda me sunan Mama Karima.




Yusuf ma ya hada iyali dan Abida ma yaranta 2 banda yaran Hauwa.






Yau suke tsara duk ranar Lahadin karshen wata, za'a hadu a gida daya aci asha ai zumunci.


Yauma hakace ta kasance duk suna zaune a gidan Yusuf bayan anci ansha.




Hauwa ce da surutu ta ce


"Nikuwa Khadija kallon me ciki nake miki wallahi."




Khadija kuwa kamar jira rake ta kalli Nasir aikuwa ya kama dariya harda yi mata gwalo.


Kwalla ce ta cika mata ido ta ce


"Wallahi banason sake haihu."


Da sauri Nasir ya ce


"Haba yarinya me na ce miki haihuwa yanzu kika fara, saikinyi 12 dozun guda zan barki ki huta ma."


Kafin tai magana Abida ta ce


"Dan baku kuke haihuwar ba bakusan wahalar da muke shaba shiyasa kuke mana izaya da wai sai mun dinga haihuwa kamar kaji, haka na kusa da kaima ya kecin alwashi."




A hankali Yusuf ya ce


"A to mene anfanin ku in baku haihu ba."


Zatai magana Nafisa ta ce


"Kinga rabu dasu zamu dau mataki badai haihuwa bace, to kowane a cikin mu ya hana mijin shiga dakinsa sai muga ta inda za'a cigaba da haihuwar."




Ai a tare Nasir da Yusuf suka hada baki gurin furta.




"Wallahi baku isaba."




Sai kuma gaba daya sukasa dariya harda matan nasu.






ALHADULILAH




Ina bawa ma'abota bibiyar wannan litafi hakuri na so labarin yai tsayi amma sabuda wani abu daya taso mun yasa dole na takai tashi, kumun afuwa dan Allah.


Masoya mu kasance tare daku duk ranar Lahadi da Alhamis da misalin karfe 9:30pm dan sauraran shirin GARIN MASOYI wanda ni Fatima S Umar Jajira zan riga gabatar muku a tashar Raypower 105.6 na gode


Sharhi ko arin haske 08166077167




Share please

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads