Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 29178 words

Chapter 8 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ne mota ba, ba lalai ki kasance cikin wannan gidan cikin koshin lafiya ba."




Cike da rashin tsoro Izzatu ta ce


"Hmmm idan baka fasa, kai ba Nasir bane, har ka isa kaimun abunda Allah bai munba arya kake wallahi. Burin kuya kawai da kana sonta kake hulakan tata."


Batajira cewarsa ba ta koma ciki harda rufo kofa da arfi.




Da kallo Nasir ya bita cike da mamaki to meyasa kowa ya rainashine? Le anshi ya ciza da arfi yana huci kafin ya juya a fusace ya shige motar subar gurin.






Da azahar su Nafisa suka sauka a Kano, kai tsaye mai adaidaita suka tara ya tafi dasu gidan Mama Karime.




Khadija tana sauka a cikin gari ta nufo gidan su, duk da zuciyar ta, tana tsanan ta bugawa tsoro da fargaba sun mamayeta, amma ta dake dan ta fitar da Yusuf daga zargin da ake masa.




A kofar gidan suka sauka, suka shiga ciki da salama.


Mama Lube na daka a turmi taji muryar da bazata ta a mantawa da itaba,


A tsorace ta ago dan tabbatar wa kanta, abunda tagani yasata tashi da sauri tana murza ido ko mafarki takeyi, amma me da gaske kishiyarta Karime ce a gabanta, bakinta na rawa ta ce




"Karime dama kina raye?"


Murmushin takaici mama Karime tai ta ce


"Kin zata kin salwantar da rayuwata ko?"


Ido Mama Lube ta ringa zarewa, Baba ne ya shigo da salama a bakinsa.


Ai kasa arasa salamar yai cikin tsananin mamaki ya ce


"Karima!"


"Na'am Malama."


"Kece ko mafarkin da nasabayi ne naki."


"Nice Malam ba mafarki ka ke ba."


Amma Baba bai gaskata zancan ta ba, ya matsa kusa da ita ya kai hannu ya ta ata yaga da gaske ita ce saiya fashe da kuka.


"Karima rai kanga rai, ina kika shege shekaru da yawa haka, na zata kin mutu dan har na gaji da nemanki ashe zaki dawo."


"Gani Malam, ina Khadija ta?"




Kallon kallo suka farayi da Mama Lube kafin ta ce


"Tayi aure."


" arya takeyi ta saida ita ga matsafa."


A razane duk suka kale shi.






A kofar gidan sukai parking ya dubi driver nasa ya ce


"Bani key din motar ka shiga gida."


Miko masa yai ya fito ya bude masa motar ya fito ya koma mazaunin driver ya ja motar a guje yabar gurin.




* * * * * * * *


Gudu akeyi a babur din amma gani yake kamar ba tafiya akeba, sabuda yadda zuciyar sa take bugawa da arfi gani yake kamar wani abu zai faru kafin ya arasa inda Khadija take.






*** *** *** ***


Nan baba ya basu labarin komai ya ara da cewa


"Wannan munafukar matar duk ita taja na zata auran gata naiwa Khadija ashe dan a dauke mun ita ne ba ita ba mijin duk sun ata."




Dafe kirji Mama karime tai tana an baton


"Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un!"


Kafin suyi aune ta zube a gurin sumamiya.




Kanta sukayi suna salati, Baba ya fashe da kuka ya na cewa


"Kiyi hakuri Karima karki mutu ki barni."


Nafisa ce ta karfi gorar ruwan dake hannun Anwar ta fara zubawa Mama Karime a fuska tana tofa mata addu'a.




Ajiyar zuciya Mama Karime ta sauke ta bude ido a hankali, Nafisa na jero mata sannu ita kuwa Mama Lube ido kawai take zarewa tana mamakin ya akai duk sihirin da tayi ya karye lokaci guda.








*** *** *** *** ***




A kofar gidan yai parking har zai fito yaji wayarsa tana ruri, tsayawa yai ya duba, Hasina ce, tsaki yaja har ta katse bai dauka ba.


Kiran ne ya sake shigowa, har zai share sai kuma ya daure ya daga.




"Hello Nasir kana ina?"


"Ina ruwanki da ida nake?"


"Akwai matsala duk wani aikin ka an rusa shi yanzu shirin yadda za'a salwantar da rayuwarka akeyi."




"Mtsss kinga Hasina ba wannan a gabana ba yanzu haka ina kofar gidan su wannan yariyar dan iyayenta sai sun biyani kudina kuma wallahi saina daure su."




"A'a Nasir ka fara kashe wutar gabanka tukun.....!"




Wayar ya katse bai shirya ba, abunda idon sa yake gane masa kamar mafarki, Khadija ce a gabansa tana kokarin shiga gida.




Da sauri yafito yasha gabanta yana kare mata kallo cike da mamaki.




Jikin Khadija rawa ya dauka ganin abunda bata zata ba.








Mama Karime na kuka ta ce




"Bazan taba yafema ba, tunda ka salwantar mun da yata kuma wallahi sai nayi kararka."


Hakuri Baba ya fara bata amma ta tashi fa nufi hanyar fita.






Kallon ta yake ido cikin ido ya ce


"Kin gama gudun? To yau naga uban da zai kwace ki."




Hannu yakai ya fizgota da karfi, ihu ta kurma wanda yai dai-dai da fitowar Mama Karime.




Wadda ta saki baki ta ce




"Yakubu!"


Tare suka juyo, Nasir yana kallon matar wadda ta kirashi da sunan mahaifinsa, ita kuma Khadija kokarin kwace kanta take ta kasa.




Nafisa ce ta fito da jakun kunan su, ai sakin su tai a tsaye ganin Nasir rike da wata a hannunsa tsoro da fargaba suka cikata, gumi ne kawai ke tsatsafo mata.




Khadija kamar gizo haka take kallon Mama Karime, fuskar da bazata taba mantawa da itaba, wadda ta fida rai da sake ganinta a fili ta furta.




"Mama dama kina raye?"




Mama Karime kuka kawai take ganin abunda bata taba tsamani ba.






Mama Lube da Baba ne suka fito, bakin Baba har rawa yake ya ce




"Laaa gashi nan shine munafikin daya sace mun yata."




Baki Mama Lube ta saki ta kasa cewa komai dan tasan duk abunda ke faruwa.






Khadija ce tai tattara duk karfinta ta kwace daga jikin Nasir, da sauri yakai hannu zai sake rikota yaji an rike hannun sa, d'agowa yai sukayi ido 4 da Yusuf wanda ya hada gumi yai wurjan jan.................!








Sharhi ko karin haske 08166077167






Comments
And
Share








By
*Zarha*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 22






Ran Nasir ne yai mugun aci ya fusge hannun sa daga na Yusuf, ya kaiwa Yusuf wata shaka, kaucewa yai da sauri Khadija dake kusa da su ta shiga tsakane tana watsawa Nasir mugun kallo ta ce




"Duk to zarta rayuwarsa da kayi, da yi masa azafi bai isheka ba sai ka ara da takalarsa da rigima."




Nasir da idonsa ya rufe, ga acin rain su da ke ransa kawai ya sa hannu ya shaki Khadija.


A take ida nuwanta suka firfito waje ta fara ka karin mutuwa, Nafisa ce tai namijin kokarin zuwa inda yake ta rike hannunsa ta ce


"Nasir baka da hankali kashe yariyar mutane zakayi."




Sakin Khadija yai yana huci a take tai baya zata zube, Yusuf yai saurin tareta ta fa a jikinsa, tunzura Nasir ya sakeyi zai kara yin kansu Nafisa ta rikeshi sosai ta ce


"Meyake damunka ko ka fara shaye-shaye."


Kallon ta yai da idanunsa da sukai ja, ya ce


"Sakeni malama."


"Bazan sake kaba Nasir, me kake kokarin aikatawa?"


Cikin tsawa ya ce


"Ki sakeni, saina kashe su, naga uban da ya tsaya musu."


Ya ara maganar yana nuna Yusuf da Khadija.




"Me suka maka? Da kake ikirarin halaka su."




Kafin Nasir yai magana, Anwar yazo ya rungume Nasir ya ce


"Daddy."




aukan yaron yai yai murmushi ya ce


"My son ina kuka tafi kukabar Daddy 2days."




Ai kowa sakin baki yai yana kallon ikon Allah




Musaman Mama Lube da Baba.




Mama Karime ce ta ce


"Dama jikina yana bani Anwar jinin Yakubu ne."




Da sauri duk suka kaleta, ta gyada kai ta ce


"Dan Allah mu koma ciki."




Mama Lube sai lokacin ta samu bakin magana


"Eh hakan zaifi karmu tarawa kanmu jama'a."




Shiga sukayi ciki, amma Nasir ya ce bazai shigaba.




Cikin rarrashi Nafisa ta ce


"Dan Allah ka daure muje, badan komai ba sabuda mama Karime da take ikirarin tasan wani Yakubu, wata kila tasan asalinka."




Murmushin takaici yai ya kamo hannun ta ya ce


"Na santa."


Da mamaki Nafisa ta kaleshi, ya gyada mata kai ya ce




"Ina da shekara 8 mahaifiyata ta rasu, ita anwar Babana ce, ita ta rikeni har lokacin da aka aurar da ita lokacin shekarata 13 a duniya, tunda ta baro katsina nasan maraicin uwa, shekararta uku da baro katsina Babana ya rasu, na taho kano ne manta amma ban sameta ba, haka aiki ya kaini Kaduna, amma ban zauna a canba, na dawo kano dan duk na hadu da ita amma ban sameta ba sai yau."




Ajiyar zuciya ya sauke ya ce


"Sabuda wanda sukaci amanata yasa bazan shiga gidan ba."




"Suwaye su? Kuma me suka maka haka?"




ara an ame hannun ta yai ya kasa cewa komai, dan bazai iya sanar da ita abunda ke tsakaninsu da su Yusuf ba, haka kawai ya ke jin nauyinta.




Katse masa tunanin nasa tai da cewa


"Nidai kazo kawai mu shiga."




Kasa yi mata musu yai taja hannunsa suka shiga ciki.








Duk suna zaune, Khadija na jikin Mama Karime ta rasa gidan tsoma rai sabuda da i.


Zama sukayi, Baba ne yai gyaran murya ya ce


"Yanzu kai Nasiru mun dauki amana mun baka auran yar mu amma ka gudu da ita."




Kallon sa Nafisa tai da sauri, yai kasa da kai ya kasa magana.




Yusuf ne ya ce


"Baba bashi ya gudu da Khadija ba, tana gidan iyaye na."




Nan ya kwashe komai ya sanar dasu.




Salati duk suka saka, Nasir kuwa in bada gumi ba abunda ke keto masa, Nafisa kuwa kuka take kamar ranta zai fita, tana dana sanin auran Nasir.




Baba ne ya taso ya shaki wuyan Nasir ya ce




"Allah ya isa tsakanin mu dakai kuma ka sakar mun ata kaje kaida Allah tsinan...!"


Mama Karime ce tai saurin cewa




"Ka daina zagar mun yaro."




Baki duk suka saki Khadija dake jikinta tai saurin tashi tana kallon ta




" anane, duk da yai kuskure amma ku masa addu'ar shiriya ba tsinuwa ba, kuma aure shida Khadija ba saki a tsakani."




Cikin tsoro Khadija ta ce


"Mama a ina kika sanshi?"


Nan Mama Karime ta basu labarin Nasir dan yayanta ne Yakubu.




Kowa ya cika da mamaki.




Nafisa ce ta kama hannun Anwar da sauri ta fice daga gidan


Bin bayanta Nasir yai yana kiran sunan ta amma ko kulashi batai ba.




Mama Lube ido kawai take zarewa gudun tonuwar asirinta..............!








Comments
And
Share








By
*Zahra*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 24




Amma bai bari sun fahimci halin da yake ciki ba, yai musu salama ya fice daga gidan.




Baba da kansa ya wanke akin Mama aka gyareshi tasss, sannan aka sa mata katifa da kayanta.




Bayan sun koma akin, Khadija ta kali Mama murya a raunane ta ce


"Mama nidai kiyi hakuri bazan iya tafiya wani gurin na barki ba, kuma kinsan halin wannan mutumin bashi da imani, da zakice na koma gidan sa nai jinyarsa."




Dafata Mama tai cikin rarrashi ta ce


"Kiyi hakuri Khadija, nima ina tsoran abunda zai faru amma hakuri zakiyi kinji."




Gyada kai tai badan zata iya abunda Mama ta ce da ita ba.






*** *** *** *** ***




Nasir kuwa tunda aka mai dashi gidansa bai san wanda ke kansa ba, gashi duk ma'aikatan gidan sun i kula dashi yana ajiye kamar gawa a yashe ba gata bare galibu.










Mama Karime ba yadda batai da Khadija ta koma gidan Nasir tana kula dashiba amma taki sai kuka da take tayi.




Dafa ta Mama tai cikin rarrashi ta ce


"Khadija ki duba girman Allah dan Allah zakiyi ba dan halin mu ba ko abunda ya faru, Allah ma muna masa laifi ya yafe mu, bare mu da muke neman dacewa, dan Allah kiyi hakuri kije ki kula dashi zuwa gobe zan lala a babanku ya bari muje Katsina acan sai a cigaba da jiyar tasa."


Gyada kai Khadija tai ta ce


"To bari naje gurin Abida mu tafi tare."




"To shikenan Allah ya tsare."


"Amin."


Ta ce tai wa Mama sallama ta fice.








**** **** **** **** ****




Koda ta fita gidan su Abida ta huce nan take sanar da Abida abunda ke faruwa.


Dariya Abida tai ta ce


"Ai dama arshen azalumi baya kyau, amma yanzu ke mekika yanke."




"Gaskiya Abida bazan iya zuwaba, kisan halin dan Adam wata kila ma yana sani yai haka yadda idan naje ya cika burinsa a kaina."


Girgiza kai Abida tai ta ce


"A'a bana tunanin haka, dan kina ganin yanayin ciwansa kisan tsafin da sukene ya fara dawowa kansa, amma nima ban guyi bayan kije wannan BAKIN GIDA n nan nasaba ki zamanki a nan mu kwana gobe maje tare da Mama."




Shawarar Abida ta dauka tai kwanciyarta a gidan su Abida.








Washe gari




Mama da safe ta samu Baba ta ringa masa magiya akan ya bari su kai Nasir Katsina cikin dangi ai masa magani.


Saida aka kai ruwa rana kafin ya bari.


Mama Lube kuwa taji da in haka dan zata sake samun damar ka a Mama Karime ta koma yawan duniya daga ita har Khadija dan bata kaunar ganin su.






Mama tana shiri Khadija tai salama a dakin, cike da mamaki Mama ta ce


"A'a meya dawo da ke da safe haka."


Kanta a asa ta ce


"Kiyi hakuri Mama ban je ba."




Ajiye mayafin dake hannunta Mama tai ta dauke Khadija da mari, cikin fushi ta ce


"Wato ni ban isa da ke ba ko Khadija, ko da kasheki Nasiru yai kika dawo yaci darajata iya jiya bare ba abunda ya miki, yan zu har kin kawo karfin da zan saki abu ki kiyi ko Khadija? To na gode kin nuna mun matsayina da iyaka ta."




Khadija na kuka dafe da kuncin ta, ta ce


"Dan Allah Mama kiyi hakuri."


Ko kulata Mama batai ba ta fice tabarta a akin.




Da kallo ta raka Mama kawai tanajin ranta na mata suya.




Da bara ce ta fa o mata, ta koma gidan su Abida ta ce dan Allah tazo ta bawa Mama hakuri.


Hijab ta sako, ta zo ta samu Mama ta gaida ita ta ce


"Kiyi hakuri Mama bamusan ranki zai aci ba, in sha Allah haka bazata sake faruwa ba."


"Hmm na muku uzuri wannan karon amma nan gaba bazan lamunci irin wannan sakarcin ba."




"In sha Allah Mama mun gode."




"Idan taga dama tashirya zamuje Katsina kai mara lafiya."




"To."


Abida ta ce, ta sanarwa da Khadija, suka shirya da Mama suka huce gidan Nasir.




Abun tausayi yadda suka tafi suka barshi haka suka taddashi duk ya bata gadon da fitsari da yawun bakinsa da yaketa zuba.




Jikin Khadija yai sanyi ganin halin da yake ciki kuma zuciyarta me imani ta fara tausayin Nasir.




Mama ce ta kira masu aikin gidan tasa sukaiwa Nasir wanka aka sauya masa kaya sannan ta salame su tace kule gidan za'ayi ta biya kowa albashinsa suka tafi, nan tasa aka nemo mata Sada, dan ta tanbayi ma'aikatan gidan sunce shine Nasir yafi amunta dashi kawai matsalar guduwar Nafisa ce tasa ya koreshi, dan haka ta ce tare zasu tafi sabuda dole saida Namiji me kula da Nasir.








**** **** **** **** ****




Sai yamma likis suka isa Katsina, gidansu Mama tasa aka saukesu suka shiga ciki.


Duk gidan ya sauya mata, mutanan gidan sunyi mamakin ganin su amma sunyi farin ciki, anyi gashe-gashe da koke-koken wanda aka rasa sannan aka basu masauki.




Mama dakin ta da ban sai wanda akabawa Nasir.




Da dare Mama ta ce ita Khadija ta zauna da mijinta shikuma Sada ya koma dakin zaure tunda ba kowa.




Kwala ce ta cikowa Khadija amma taga Mama ta hade rai ba fuskar yin magiya ko ban hakuri, gashi ba gurin gudu.




Haka ta karaci matsar kwalarta, Mama ta i kulata, jiki a sanyaye ta tashi ta shiga dakin da Nasir ya ke.






Can nesa da katifar da yake kwance ta rakube tana kallonsa, da tausayinsa wai yanzu duk izzar nan da fadin rai shine kwance anan an jirkita halitarsa ya koma abun tausayi, kamar a mafarki taga ya bude ido.............!










Comments
And
Share








By
*Zahra*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 25






A tsorace tai baya ta murza ido, sai lokacin taga gizo idonta ke mata, ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna.
Ranar yadda taga rana haka taga dare, a zaune ta kwana sabuda tsoron kar Nasir ya farka a cewarta.




Washe gari




Da sassafe taje ta taso Sada itace ya kula da Nasir, ita kuma tai kwanciyarta a dakin Mama.




Kwanan su biyu a Katsina, Mama suka bazama neman maganin ciwan Nasir.




Har Allah ya kaisu gidan wani alarama nan ya tabbatar musu turan aljanu akaiwa Yusuf kuma ba kowa bane sai yan kungiyar Asiri da yake tare dasu, kuma a yanzu rabashi da wannan bakaken aljanu zaiyi wuya.




Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce


"Yanzu ba wata hanya da zamubi ya samu lafiya."


"Eh to hanya daya ce, dole duk abunda akasan na tsafine a gidansa aje a kone shi, sannan zaku barshi a nan aimasa magani har ya samu lafiya."




Gyada kai Mama tai ta ce


"To shike nan ba matsala, amma nawa ne kudin maganin."


"Zaku bada dubu dari uku yanzu haka."


Shiru Mama tai dan kudin da Nafisa ta bata sun kusa karewa amma zasu isa ta bashi, dan haka ta auki kudin ta bawa Alaraman.






**** **** **** **** **** ****




Tunda ya koma gida zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa, baisan haka Khadija tashiga ransa ba sai wannan lokacin da bata tare dashi, kulum yana gida ya na tunanin halin da Khadija ta ke a yanzu ita kuma Hauwa sai rawar afa take akansa tunda wadda ta tsokane mata ido tabar gidan.






Wata rana Yusuf na kwance a aki, Kawu yai salama ya shigo, amsawa yai yana tashi zaune, kawu ya ce


"Yanzu Me gari ya aiko kiranka Allah yasa ba rigima ka arayi da Haliru ba?"


"A'a Kawu, saidai in wani abu daban."


"To shike nan, ka tashi kaje, Allah yasa lafiya."


"Amin."


Nasir ya ce, ya tashi ya sauya kaya ya nufi gidan me gari.








Shake ya tadda fadar me garin da mutane, salama ya yi yasamu guri ya zauna ya gaida su me gari, da fara'a me gari ya amsa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads