Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 29178 words

Chapter 9 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ya ce


"Malam Yusufa wannan muta nan ne suka zo gurinka, ka gane su?"


Kallon su Yusuf yai ya ce


"Kamar na so na gano ku amma na sha'afa."


Murmushi wani a cikin su yai ya ce




"Sunana Alhaji Munir, can da da ewa na ta a zuwa na siri shinkafa a gurinka kuma Alhadulilah na samu nasibi sosai a ciki, shiyasa da abuki na ya bude company na shinkafa na ce bari na rakoshi gurinka dan kaima ka zama daya daga cikin masu bawa company shinkafa tana sarafawa."




Baki Yusuf ya washe ya ce




"Masha Allah Alhadulilah, naji da i sosai."




"Bakomai, shiyasa muka taho gaban me gari ayi komai a gabansa, kuma idan kana da wani dan uwa ko aboki da kasan zai ringa bamu shinkafa ba ha'inci to kofa a bu e ta ke zaka iya kawoshi gare mu."




"Na gode sosai kuma naji da in zuwanku."


Nan suka bashi number wayarsu, da address in company sukai wa me gari godiya suka tafi.




Me gari sai washewa Yusuf baki ya ke dan yaga arziki ya zo gareshi, yai wa me gari Salama ya tafi gida.




Nan aikaita zuwa tayashi murna harda Haliru ba kunya ba tsoran Allah, Yusuf bai nuna masa komai ba suka gaisa ya ce




"Munji abun arziki Allah ya sanya alkairi."


"Amin, na gode."


"Dama naji sunce in kana da wani naka kuje tare, to naga muma muna noman shinkafar nan duk garin kura kowa yasan munfi kowa numa shinkafa dan Allah kasa da sunana."


Murmushi Yusuf yai ya ce


"Zanyi shawara."


Jiki a sanyaye Haliru ya huce, Yusuf ya bishi da kallon mamaki dan Adam kenan, wai yanzu shine mutum har ana zuwa neman alfarma gurinsa.






**** **** **** **** ****




Mama da kanta ta kira Nafisa ta roki alfarma akan ta je ko ta tura gidan Nasir duk wani abu na tsafi koda kudine a kone su.


To, Nafisa ta ce ta aiwatar da abunda Mama ta Sada.



Satin Nasir uku a gidan wannan Alarama aka dawo dawo dashi dan ya daina zubar da wannan yahun bakinshi ya dawo dai-dai haka numfashinsa kawai farkawa ce har yanzu ya gaza yi.




Dakin da aka fara kaishi Mama tasa aka maidashi Khadija ta cigaba da jinyarsa da dare shi kuma Sada da rana.




Tun Khadija tana san ran farkawar Nasir harta fidarai da zai tashi kuma ta sake tana iya bacci amma can gefe take shinfi a ta kwanta.








Mama dama ta shirya haka ne dan Khadija ta daina gudun Nasir ta saba da zama dashin tun kafin ya warke dan baza ta bari wannan ha in da Allah ya adara a rabuba.






Sun gama cin abuncin dare Mama ta ce


"Yanzu Kabiru ya turo matarsa na nakuda Asiya, zanje mu tafi Asibiti yanzu."


"Amma Mama gasu Inna Saude suje tare mana."


"Tunda har ya tuna dani yazo ya sanar dani ai ya kamata naje matsayina na uwa ko?"


"To shike nan, sai kun dawo Allah ya tsare."


"Amin."


Mama ta ce tasa hijab ta fice.




Zaman ta Khadija tai a dakin Mama dan ta ce yau ba inda zata.


Sai 9:30pm ta tashi wanka ta yi tashiga dakin Mama, nan ta tuna kayanta suna akin su, tsaki ta ja, ganin ba kowa a gidan tai fitarta daga ita sai zani data daura a jikinta.




Kwan akin ta kuna da ya ke da wutar nefa, ta jawo jakarta ta fara duba kayanta.




Ba zato ba tsamani ta ji saukar muryarsa a kunanta kamar saukar aradu, a tsorace ta kalli inda ya ke dan aukanta gizon da yake mata ne, amma me a zaune ta kanshi ya zuba mata manyan idanuwansa wanda suka ka a mata hantar cikinta...............!






Comments
And
Share








By
*Zahra*





*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 26




Ja da baya ta farayi har Allah ya bata sa'a kafin ya ara magana, ta fita da gudu.
Tashi yai ya bi bayanta, hanyar fita yaga ta nufa, wata uwar tsawa ya daka mata wadda tasa saida ta tsaya ma shiri.


"Gidan ubanwa zaki fita a haka? Baki da hankali zaki fita waje a daran nan ba kaya a jikinki."




Da mamaki ta kalli jikinta dan ta manta da mene a jikinta, kunya da tsoro ne suka ara rufeta taja afa a sanyaye ta shige akin Mama.




Hijab kawai ta sako, tana le ensa ta taga, taga ya shiga bayi, Mamaki take taya yasan gidan sosai da haryasan azu hanyar fita tabi kuma yasan bayi ba tanbaya, shida aka tahu dashi kamar matace, koda yake a garin ya rayu ilama nan ne gidan su.


Saurin kawar da tunanin tayi, tana san a ta koma akin, kayanta ta ako a guje ta koma cikin akin Mama.




Duk abunda take yana kallonta, amma bai kulata ba danshi mamaki yakeyi me ya dawo dashi wannan garin da ya bari shekara da shekaru, kuma ya akai basan ya zo ba? Mama Karime ya ayana a ransa dan tunda yaga Khadija yasan itace zata kawoshi garin nan.




Fitowa yai ya koma akin nasa, sai yanzu mutuwar iyayensa ta dawo masa sabuwa fill, kuma yakejin ciwan maraici, da badan maraici ba bazai shiga halin da yashiya ba a rayuwarsa.






Hawayen da suke sako masa ya share, yasan ya aikata babban kuskure shiga kungiyar Asiri amma ba yadda zaiyi, basan me yasa yanzu komai yafita a ransa ba, inba Nafisa da Anwar ba, ba abunda yake so ya ra eshi, sai Mama Karime da ta dawo rayuwarsa wadda yasan rashinta ne a baya ya jebashi halin ha'ula'i.






Wannan dare shida Khadija kwanan zaune sukai shina tunanin halin da yake, ita kuma na tsoro da bargabar abunda zai je ya dawo.






Washe gari


Da safe su Mama suka dawo daga asibiti tunda wadda suka kai ta sauka lafiya tun dare.


Da salama ta shigo gidan, Khadija najin salamarta ta bu e akin da tun jiya ta kule kanta a ciki,


Da gudu ta fa a jikin Mama tana nuna mata akin da Nasir ke ciki.


Da mamaki Mama ta ce




"Lafiya ko mutuwa Nasir yai?"


Da sauri ta girgiza kai murya na rawa ta ce


"A'a farkawa yai."


Tana rufe baki Nasir yana fitowa dan yaji maganar Mama.




Da tsananin farin ciki Mama take kallonsa ta ce


"Alhadulilah, Allah na gode ma da ka nunamun wannan ranar."


Khadija ta zame daga jikinta ta arasa gaban Nasir ta ce


"Sannu Nasiru ya jikin naka?"


"Ni lafiya nake yanzu."


"To masha Allah."


Nasir yana kallon Mama ya ce


"Am tunda Allah yasa naji sauki, ni zan koma gida sabuda matata."


Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce




"Bazan hanaka tafiya ba amma zan ha aka da matarka ku tafi, ni sai zuwa jibi zan taho."


Shiru Nasir yai kafin ya ce


"Jibin kwataho da ita kawai."


Mama bata son takura masa dan haka ta rabu dashi ya tafi shida Sada.


A hanya Sada ya bashi labarin komai da ya faru da tafiya da iyayen Nafisa sukayi da ita, da jinyarsa da Mama Karime tasha da Khadija, jinjina kai kawai Nasir yai yana ayana abubuwa da yawa a ransa




_Kano state_




A Kano Nasir ya samu sallar Azahar ko gida bai jeba ya zarce gidan su Nafisa.


Yafi awa 3 a waje ba wanda yafito ya saurareshi a cikin gidan nasu, sai daga baya Babansu Nafisa ya fito, dukawa har asa Nasir yai ya gaidashi, sama-sama ya amsa ya ce


"Dama na jima ina zuba idon ganin ka."


Da sauri Nasir ya ce


"Bani da lafiya amma yanzu naji sauki shiyasa nazo."


Gyada kai Babansu Nafisa yai ya ce


"Yauwa to yau bazaka bar ofar gidan nan ba saika bani takardar sakin ata."


A tsorace Nasir ya ce


"Saki kuma Baba, meya kawo zancen saki ana zaune alau."


aure fuska tamau Baba yai ya ce


"Kada ka maidamu wanda basusan abunda suke ba, taya zan barmaka ata kana cida ita da haram kana shayar da ita da haram kana tufatar da ita da haram, kuma shine sabuda mu bamuna tunani zamu bar armu a sannun matsafi nan gaba yai tsafi da ita."


Rintse ido Nasir yai cike da tashin hankali ya ce


"Dan Allah Baba ku tausaya mun wallahi bazan iya rayuwa ba Nafisa ba na muku alkairi na daina abunda nake kuma duk abunda nasan nasamu ta hanyar da ba dai-dai ba zanyi sadaka dasu."




"Kaga nifa ba sa'an wasanka bane idan zaka bani takardar Nafisa ka bani in bazaka bani ba, to kajira samaci a koto."


Ai tuni hawaye sun wankewa Nasir idanu, zaman dirshan yai ya ri e afar Baba yana cewa


"Dan darajar Manzon Allah s.a.w Baba karka rabani da Nafisa ina son matata Baba karku rabamu dan Allah."


Kwace kafa funsa Baba yai ya ce


"Na kula taurin kanka bazaisa mu rabu lafiya ba, dan haka sai kaji samaci."


Daga haka Baba ya shige warsa ya bar Nasir a gurin a zaune yana kuka kamar yaro.
Abune ya taru yai masa yawa yanzu ina zaisa kansa?








Duk abunda ya faru tsakanin Baba da Nasir, Nafisa tana zaure tana jinsu, abunda take tanbayar kanta dama Nasir yana son ta haka yake hula an tata, ya maida ita kamar baiwa? hawayen fuskarta ta share ta koma gida da gudu lokacin da taji alamun tahowar Baba.






**** **** **** **** ****






A kura kuwa, Yusuf har ya gaji da sintirin da Haliru yake masa kulum yana makale dashi da yaji arziki ya sameshi, duk da Yusuf yasan company da zai ringa kaiwa shinkafa suna bukatar masu kaiwa da yawa amma ba zai kai Haliru ba sabuda yasan halinsa ba mutumin kirki bane.




Nasir tun washe gari ya saida duk wata kadara daya malaka ya raba kudin a gidan marayu da nakasasu da masu bukata, ya tashi bashida biyar ta kansa, dan haka ya auri aniyar niman Halakkkk yanzu...............








Comments
And
Share








By
*Zahra*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 27






Kwanaki biyu da tahowar Nasir Mama taiwa dangi salama ta sako iyarta a gaba suka taho gida.


Mama Lube bata ji da in dawowarsu ba dan dai ba yadda zatayi ne.




Nasir ya koma kasuwar Singa idan ya samu dako ya yi su sauke kaya a mota a biyasu, da haka yake samun nakai abunci bakin salati, kuma a kulum yana tashi daga Kasuwa, to gidansu Nafisa zaije amma har gobe Baba bai yarda ya sako ba, shi Nasir ma haka ya ce Baban ya yi hakuri baice a bashi Nafisa ba bashida gidan da zai sakata, amma su fahimci ya shiryu yanzu ya zama mutum kamar kowa.




**** **** **** **** ****


Cikin nutsuwa ya ce da driver n babur in adaidaita sahun ya tsaya, sauka yai ya ce ya jirashi yanzu zai fito su tafi, "to." Me babur din ya ce, shikuma ya arasa ofar gidan.




Salama yai aka amsa, ya jira har Maniru ya fito, da mamaki Maniru ya bashi hannu suka gaisa ya ce


"Abokina kwana da yawa."


"Ina lafiya ya gida?"


"Kowa lafiya lau."


Cikin nutsuwa Yusuf ya fara magana


"Dama Hausawa suna cewa duk dan halak baya manta alkairi, shiyasa nima ban manta da alherinka a gareni ba, na samu aiki da company na rice har mun fara aiki dasu ina kai musu shinkafa, Alhadulilah ina samun nasibi a ciki dan yanzu haka na siyi gida a nan birnin Kano a unguwar Janbulo wadda zamu zauna da matata da iyayena abun hawa kawai ya ragemun yanzu kuma shima in sha Allah muna saran malakarsa nan ba da jimawa ba."


Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa


"Yanzu haka company sun bukaci ma'aikata da wanda zasu ringa kawo musu rice, sun yarda dani 100% shiyasa suka nemi na kawo musu duk wanda naga ya dace, shine naga ya dace na nemeka."


Murmushi Maniru yai ya ce


"Gaskiya naji dadin wannan al'amari kuma na gode sosai."


"Ba komai a baya kaima ka taimake ni, kaso na samu aiki gurin Alhaji Nasir kuma aka samu akasi."


Dariya Maniru yai ya ce


"Kasan me yake faruwa kuwa?"


Girgiza kai Yusuf yai ya ce


"A'a."


"Naga Alhaji Nasir da idona a kasuwar singa yana dako."


Cike da mamaki Yusuf ya ce


"Anya Maniru shikagani."


"Wallahi Allah shi na gani da idona, na tanbayi wani abokin lebirancinsa ya ce kulum yana zuwa kasu neman na abunci."


Gyada kai Yusuf yai cike da gamsuwa ya ce


"Allah ya kyauta, ni zan huce duk lokacin daka shirya sai muje company tare."


"To na gode na gode na gode."


Murmushi Yusuf ya sakar masa ya ce


"Karka damu an zama aya."


Nan sukai salama Yusuf ya hau adaidaita sahun suka huce.






**** **** **** **** ****


A jima a ofar gidan yana neman yaron da zai aika ya kira masa mama su gaisa, yanata wage-wage ya gano wata yariya zata shiga gidan.


Da sauri ya ce


"Dan Allah ammata kice ina samala da Mama Karime."


A tsorace take kallonsa duk da taga ya sauya sosai amma ta ganeshi, duk da tana tunanin ita bai tunata ba.


"To." Kawai ta ce ta shiga gidan.




A tsakar gidan ta tadda Khadija da sauri ta ce


"Khadija kinsan wa nagani a kofar gidan nan?"


"A'a waye?"


"Alhaji Nasir fa na gani wai na kira masa Mama."


Baki Khadija ta ce


"Saiki sanar da ita."


Baki Abida ta saki amma ta kasa cewa komai sai lekawa da tai ta kira Mama.




Hijab Mama tasa ta fita gurin Nasir ya gaida ita a ladab ce ta amsa yana sosa kai ya ce


"Am dama maganar Nafisa ce naga banda kowa sai ke a duniya dan Allah kije ki bawa iyayenta hakuri."




"Shikenan Nasir ba damu zanje na samesu in sha Allah."


Godiya ya mata zai huce, adaidaita sahu ta tsaya a gabansu, fitowa Yusuf yai ya araso inda suke ya gaida Mama ya bawa Nasir hannu suka gaisa sannan ya ce


"Magana nazo muyi me mihim manci."


Duk da Nasir yana tsananin jin haushin Yusuf amma da yaji Mama ta ce to kawai saiya samu guri suka zauna.


Cikin nutsuwa Yusuf ya zauna ya basu labarin yadda sukayi da masu company shinkafa ya ara da cewa


"Naji labarin kafara zuwa kasuwa dan haka nazo na sanar dakai ko zaka bini mujecan kanemi aiki."


Shiru Nasir yai sabuda tsananin kunyar Yusuf data kamashi, Mama ce ta ce


"Ai wannan abun alkairi ne bazamuyi wasa da wannan damar ba in sha Allah yanzu ba zai bika kuje tare."




Ajiyar zuciya Nasir ya sauke ya ce


"Na gode amma da nafison aikin kasuwata."


"Haba Nasiru yanzu da sana'ar dakon zaka cida mata biyu harda mahali? Bana son shashanci ka karbi aikinka duk matanka su dawo hannunka ba bin gidajan iyaye ba."




Murya a sanyaye ya ce


"Mama ina tunanin bazan iya bada mata biyu ba a halin yanzu, kiyi hakuri bazan iya hada Nafisa da kowace mace ba a duniya."




Kunya ce ta lulube Mama tama kasa cewa komai, Yusuf da zuciyarsa ta tsananta bugawa kamar zata faso kirjinsa ya ce


"Koda mace daya kakeson rikewa ya dace ka samu abunyi me kyau Nasir."


Kai Nasir ya gyada ya ce


"To na gode Yusuf in sha Allah zan zo muje company."


Murmushi Yusuf yai ya ce


"Ba komai."


Ya kalli Mama ya ce


"Mama a sha'ani na aure ba dole a ciki kibar Nasir da zabinsa zaifi."


Kai mama ta gyada ta ce


"Shikenan Yusuf amma anan zai bawa Khadija takardar sakinta."


Gaban Nasir ne ya fadi sai yanzu yaga tsantar rashin hankalin da yai tuno irin dawai niyar da Mama da Khadija sukai dashi lokacin da bashi da lafiya,lokacin da kowa ya gujeshi, lokacin da arziki daya tara yana ganin sune komai na rayuwa bazasu iyai masa komai ba.


Girgiza kai yai da sauri dan bazai iya sakin Khadija ba inyai haka ya yi buturci cikin rawar murya ya ce............!










Comments
And
Share




By
*Zahra*



*WATA RAYUWA*





Na


Fatima S Umar Jajira




Free book




Episode 28




"A'a Mama bazan iya sakin taba gaskiya."


Shiru duk sukayi, ba wanda ya tanka masa har ya mike ya bar zurin.


Suka bishi da kallo, Mama ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Yusuf ta ce


"To Yusufa mun gode da taimako Allah ya yi albarka."


"Amin Mama nima na gode."


Daga haka sukai salama ya huce shima.






********** **********






Zaman gida yaiwa Nafisa zafi, batasan haka take kaunar Nasir ba sai yanzu da bata tare dashi, bata ganinsa a kusa da ita, har wata rama tai sabuda tashin hankali na rashin ganin mijin nata.




Mahaifiyarta ta kula da halin da take ciki amma ta shareta dan tasa ba abune me sauki ba Baba ya sauka ya barta ta koma gidan Nasir ba amma tana taya iyar tata addu'a Allah ya za a mata abunda yafi alkairi a rayuwata.








Koda ya koma gida abun duniya ne ya taru ya masa yawa, yana aunar matarsa ba ya so ya ha a ta da kowace a mace amma yana jin kuyar Mama bazai iya sakin Khadija ba, in ya yi haka yai butulci.




Dafa kansa yai yana rintse idanunsa cike da tashin hankali.


Yanzu ba abunda yake muradi irin yaga matarsa ta dawo gareshi, ya rasa wace hanya zaibi ya dawo da Nafisa gareshi.




Bayan kwana biyu


Sunje company da Yusuf kuma ya samu aiki, da yake manager company ma ya san Nasir dan haka baisha wata walaba ya samu aiki da albashi me tsoka.








Yusuf zuwa yanzu ya fara cire Khadija acikin ransa tunda yaga alamun Nasir bazai iya sadaukar masa da ita ba dole tasa ya fara shigewa Abida har suka saba sabuda bazai iya zama da Hauwa a hakaba yana bukatar mace me tarbiya ba Hauwa da batasan darajarsa ba.






Cikin kankanin lokaci Yusuf ya zama hamshakin me kudi kuma ya auri Abida harta tare a dakinta.


Amma har lokacin Nasir yana nan gwaro Nafisa bata dawo ba haka Khadija tana gida duk da yanzu Alhadulilah yana samun kudi amma ya jingine zancan mata a wannan lokacin.






Mama ce ta sameshi ta masa nasiha sosai sannan ta ce zata samu iyayen Nafisa in sha Allah.




Nasir yaji dadi dan haka ya fara gyaran gidan da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads