Showing 18001 words to 21000 words out of 29178 words
Chapter 7 - WATA RAYUWA Latest by Fatima S Umar Jajira.txt
a katsina ya ke, kuma na jima banje canba. Amma naki mijin a ina yake."
Shiru Nafisa tai dan bata da amsar da zata bawa Mama Karime.
Tsawan zaman su da Nasir, ba wanda ya ta a zuwa da sunan an uwansa ne, ko ta tanbayesa iyayensa to ranta ne zai aci a banza.
Maganar Mama Karime ce ta katse mata tunaninta.
"Ko da yake naji Hajiya ta ce, daga garinsu zakuzo kila shima mijin naki a Kano ya ke, kinga kuwa kamace kawai."
Murmushin ya e Nafisa ta yi ta ce
"Eh hakane."
Hira suka cigaba dayi da Mama Karime ta duniya dan kowa a cikinsu baya so a tanbayeshi ahalinsa.
* * * * * * * * *
Da salama ya shigo gidan ba kowa a tsakar gidan dan haka ya zarce akin Inna.
Khadija na zaune a gefan gadon Inna tai tagumi.
Har yai salama batasan ya yi ba, arasowa ya yi gaban ta ya ce
"Khadija!"
A tsorace ta kalleshi.
Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, ta ce
"Ina kwana."
Bai amsa ba sai ya ce
"Tunanin me kikeyi haka? har na shigo baki sani ba."
Hawayen da take o arin maidawa ne suka zubo mata ta ce
"Ba komai."
"Amma kike kuka."
Hawaye ta share cikin raunin murya ta ce
"Kuka ya zama dole a gareni, ace kwana da kwanaki ina hannunku amma iyayena basu ta a neman inda nake ba."
Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce
"A'a Khadija nasan yanzu haka mahaifanki suna can suna nemanki, kawai Allah ne baisa sun riski inda muke ba."
Girgiza kai ta yi ta ce
"A'a wallah ba wanda ya damu dani da zai nemi inda nake, da dai Mahaifiyata tana raye ne a kusa dani da ita zata damu."
Zama Yusuf ya yi a kusa da ita cikin rarrashi ya ce
"Kiyi hakuri komai yai farko yanada arshe, zaman mu a nan garin ma zai zo arshe ki koma gaban iyayenki cikin aminci in sha Allah."
Kai ta gya a ta ce
"Allah yasa."
"Amin."
Yusuf ya ce, yana cigaba da rarrashinta.
* * * * * * * * *
Cikin nutsuwa tai faka motarta a ofar gidan, ta zaro wayarta ta lalubo number sa ta kara a kune.
"Hello ina ofar gidanka."
Daga can ya ce
"Okay ina zuwa."
Bai auki wani dogon lokaci ba ya fito, sanye da jalabiya ruwan toka a jikinsa, kana ganin fuskarsa ba alamun rahama a cikinta.
Murfin motar ya fu e ya shiga.
A hankali ta kalle shi ta ce
"Nasir!"
Kallon ta ya yi cike da damuwa ya ce
"Duniyar gaba aya ta isheni Hasina."
Ajiyar zuciya ta yi ta ce
"Idan rai ya aci hankali baya gushewa Nasir, me yasa ka baro gurin nan, cikin fushi?"
"Hasina komai ya dagule mun lisafina ya kwace gaba aya shiyasa na baro gurin dan bana fahimtar komai ma."
Jinjina kai Hasina ta yi ta ce
"Kasan hakan ba aramun kuskure ka aikata ba, kuma gaba aya kungiya anyi fushi da kai."
"Look Hasina, nifa ba sake komawa wannan gurin zanyi ba, na rasa matata da ana dalilin wannan tsinan nan aikin."
Cike da mamaki Hasina ta ce
"Nasir kasan me kake cewa kowa? Kabar kungiya kenan?"
"Haka nake nufi."
Gya a kai ya yi, ta jinjina kai ta ce
"Ba sai na sanar da kai abunda zai faruba Nasir kasan makomarka."
Wani mugun kallo ya watsa mata ya ce
"Ba kune a gaba na ba ta matata nakeyi yanzu da wanda sukaci Amanata."
"Okay to, amma shawarar da zan baka kacire wannan tunanin a ranka dan ba hanya bace me ilewa ba."
"Naji zanyi tunani."
Daga haka ya bu e murfin motar yai ficewarsa ya koma gida.
Girgiza kai Hasina ta yi taja motarta ta bar gurin.
* * * * * * * * *
Kawu ya kalla cikin kulawa ya ce
"In sha Allah, kan dare zan dawo gida kaga gidan da muke ciki na haya ne kuma kayan mu suna can, masu gidan sai kirana suke suna bu atar gidan su, yanzu dole naje na ibokayan Hauwa."
"To shike nan ka kula sosai."
"In sha Allah."
Daga haka Yusuf yaiwa kawu salama ya huce tasha dan ya hau mota.
Lokacin da ya isa gidan da suke haya, azahar tayi dan haka saida ya tsaya yai sallar Azahar sannan ya taro me mota suka loda kayan Hauwa tsaf ya koma gidan ya ako randar kwaro, yana fitowa yaga police sun cika ofar gidan.
Gaban sane ya fa i, sai lokacin ya tuno shifa mai laifi ne tafiya da Khadija da ya yi.
Police ne suka hangoshi suka tin karo inda ya ke, yana ganin haka ya dire robar ruwan daga hannunsa ya juya a guje yai wata kwana da uban gudu, suma kwalawan suka take masa baya............!
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
By
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 19
Wata katanga ya gani ai kuwa ba ata lokaci ya ane katangar ya haure, sukuma police in suka huce ba tare da sunga inda ya shige ba.
Ajiyar zuciya ya sauke jin sun huce basu ganshiba, da fashi yaji anyi a tsorace ya juya.
Ido ya zazzaro ya ce
"Kai ne?"
* * * * * * * *
Suna zaune a falo Mama Karime da kulum tana makale da Anwar bacci ne kawai yake rabasu, tana zane a kan carpet Anwar nakan ciyarta.
Wayarta ce ta fara ruri a hankali ta duba me kiran murmushi ta yi ta kara a kune.
"Manyan asa dama kina nan kwana biyu shiru."
Murmushi Izzatu tayi ta ce
"Ai dole ki jini shiru sabuda tsaro badan tsoro ba kinsan me gadin gidanki yaga fuskata dole nayi taka tsantsan."
"Gaskiya ne to ya gidan?"
"Komai normal, ya Yobe?"
"Yobe akwai da i sosai amma saidai kawai matsala."
Izzatu dake kwance ta tashi zaune ta ce
"Matsala kuma? Wace iri?"
Nafisa na kwala ta saci kallon Mama Karime da taga anhalinta ba a gurinta yake ba ta ce
"Ciki gareni Izzatu, kuma wallahi banaso na ara hada zuri'a da Nasir."
"Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un, yanzu ke wane mataki kika yanke."
"Zubar da cikin zanyi."
Girgiza kai Izzatu tai kamar Nafisa na ganinta ta ce
"A'a Nafisa bazamuyi kisan kai ba, kiyi hakuri ki haihu amma aure ne da Nasir babu shi."
"Yanzu Izzatu haka kike so na dawama da auran Nasir a kaina sannan ga a ansa ina yawo dasu a gari."
"Ya zakiyi hakuri zakiyi kafin mu samu mafita."
"To shikenan nagode Izzatu."
"Ki kula da kanki, karki ringa sa damuwa a ranki dan Allah."
"In sha Allah."
Nafisa ta ce. Sukayi salama ta ajiye wayar.
* * * * * * * * * *
"Sada wannan itace tanbaya ta arshe da zan maka cikin da in rai, wacece ta gudu da matata."
Hawaye Sada ya tsare ya ce
"Wallahi ranka shi dade basan sunan ta ba, amma naga akan number ta danakira a wayar Hajiya, Izzatu naga ansa."
Kai Nasir ya gyada dan yasan Izzatu farin sani kuma yasan zata aikata tunda komai tare sukeyi da Nafisa kafin ya aureta.
Kallon Sada ya yi ya ce
"Afuwa aya zanma ta sakacin da kaiyi shine na salameka daga gidan nan."
Rokanshi Sada ya ringayi yana masa magiya amma ya tashi yabar gurin, yabar Sada yanata kuka.
* * * * * * * * *
"Eh nine."
"Dama kana nan Maniru."
"Ina nan yauma naganka a masalaci shiyasa nakira police sukamaka tunda kazama megarkuwa da mutane."
Cike da mamaki Yusuf ke kallon Maniru ya ce
"Waye yace ina garkuwa da mutane?"
"Waye a garin nan baisan kayi garkuwa da matar aure ba."
Cikin tashin hankali Yusuf ya ce
"Yanzu kana nufin kai ka kira police su kamani, bayan duk halin danake ciki kaine kasanya ni aciki shine yanzu kakeson ara salwantar da RAYUWA ta."
Nan Yusuf ya bashi labari duk abunda ya faru tunda ga kaishi gurin Nasir neman aiki har kawo yanzu da suke tsaye suna magana.
Hawaye Maniru ya share ya ce
"Kayi hakuri Yusuf duk nine silar shigarka wannan masifar, danasani ban kaika gurin wannan azalumin ba."
"Balaifika bane Allah ne yatsara hakan da rabon na ceci yariyar mutane da ake so a lalata rayuwarta."
"Hakane amma....!"
Maganar matarsa ce tasa ya kasa arasa tasa maganar
"Ga an sanda nan a waje wai anga haurowar Yusuf gidan nan."
Ido Yusuf ya zaro, Maniru ya dafashi ya ce
"Karka damu zanji dasu, kashiga wance akin ka zauna, Raliya zata kawoma abunci kaci karka damu kaji."
Kai Yusuf ya gyada, shikuma Maniru yai waje gurin police din.
Abuda Maniru ya ce yai shi ya yi gudun samun matsala.
* * * * * * * * * *
"Barkan ku da zuwa yalabe, lafiya kuwa?"
"Lafiya, amma an tabbatar mana da shigowar Yusuf cikin gidan ka."
"A'a ranka shidade ba wanda ya shigo gidana."
Tsawa ya daga masa ya ce
"Maganar banza mu zaka rainawa hankali a tabbatar mana da haurowarsa kace baka ganshiba to inma biyeshi kayi ka fito dashi tun hukuma bata dau mataki akanka ba."
Wani daga cikin yan sandan ya ce
"A'a Sir Maniru bazai oye me lefi a gidansa ba, sabuda shine ma ya bamu masaniyar zuwan Yusuf."
"Gaskiya ne wannan."
Sauran ma suka fa a.
"Okay to, amma idan ka ganshi ka sanar damu."
"In sha Allah."
Daga haka suka bar gurin.
Maniru bai koma gida ba, sai ya zarce gidan da Yusuf ya zauna, nan ya samu driver da aka lodawa kayan Hauwa ya bashi kudinsa ya amshi labar wayarsa yai masa kwatancan garinsu Yusuf.
Yana komawa gida ya sanar da Yusuf abunda ya faru, Yusuf ya yi mamakin ganin yan sandan basu kula da kayan Hauwa ba, dan yasan da sun ga kayan da yanzu sun kama kayan sun tafi dasu.
Da dare Maniru da kansa ya raka Yusuf har tasha ya hau motar garin su, saida Maniru ya tabatar motar ta tafi sannan ya dawo gida.
* * * * * * * * *
Anwar ta kwantar akan gadon sannan ta kalli Nafisa da tai tagumi ta ce
"Duk naji wayar da kukayi da Hajiya Izzatu azu."
A tsorace Nafisa ta kalli Mama Karime, kai Mama Karime ta gyada ta ce
"Matsalarki irin tawace, saidai bansan ba ko kema kishiya ce ta hanaki zaman gidan aure."
Cikin damuwa Nafisa ta ce
"A'a banda kishiya."
Da mamaki Mama Karime ta kaleta ta ce
"Iya bakin cikin mijine ya naki zama dashi? Ai taki da sauki, amma har kike ikirarin zubarda ciki."
Ajiyar zuciya Nafisa tai ta kasa cewa komai.
Mama Karime na kwala ta ce
"Ni kishiya ita ta rabani da mijina da ata guda daya Khadija, ta rabani da gidan mijina...............!
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
By
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 20
"Shekara uku da ta huce ina zaune a garin Kano da mijina da ata Khadija lokacin tanada shekara 14 a duniya, dangin mijina suka takura masa sai ya yi aure, shine ya auro wata me suna Lube, tunda lube ta shigo gidana na dainajin dadin zaman aure, mijina ya daina kaunata da Khadija, har takai wata rana bansan inda kaina yake ba na baro gidan na shigo duniya, nasha wahala sosai kan hankali na ya dawo jikina. Duk da halin da nake ciki baisa na manta da komai daya faru a baya ba amma nakasa sanar da kowa, tun da na ganki naji nauyin dake kaina ya ragu kuma har na iya bude baki na sanar dake komai, yanzu ha zuciya ta cike take da begen komawa gida."
Ajiyar zuciya Nafisa ta sauke ta dubi Mama Karime ta ce
"Dole ne na koma Kano koda hakan zai sake hadani da Nasir amma saina sadaki da arki da mijinki."
Mama Karime na hawaye ta ce
"Allah ya miki albarka nagode nagode nagode, har banda bakin gode miki."
"Ba komai Mama kamar uwa kike a gurina."
Nan suka cigaba da tattauna sanda zasuje kano cikin wannan satin.
* * * * * * * * *
Lokacin da Yusuf ya koma gida, duk yan gidan sunyi bacci, dan haka saida safe suka ganshi.
Da safe ya shigo Khadija da suka fara zuwa makaranta da Murja sun shirya domin tafiya, sukaci karo dashi a kofar gida.
Sun gaidashi, Murja tai gaba ita kuma Khadija ta tsaya kanta a asa ta ce
"Jiya har dare ina jiranka baka dawo ba, hankali duk ya tashi kar wani abun ne ya sameka."
Murmushi ya sakar mata ya ce
"A abunda ya faru anwata."
Kallonsa tayi ido cikin ido ta ce
"Banka ta a yimun karya ba Yayana, amma meyasa kakeso karinga oyemun gaskiyar abunda ke faruwa. Jiya driver da ya kawo kayan aunty Hauwa ya tabbatar mun da police sun kamaka, shiyasa ban iya bacci ba saida naga shigowarka, na zata zaka fa amun gaskiya, tunda duk abunda ke faruwa ya shafeni amma ka oye mun."
Nunfashi ya sauke ya ce
"Khadija, tabbas muna cikin bala'i, police da laifin garkuwa da mutane suke zargina, kuma nasan Nasir shine ya shirya wannan abun."
Cike da tsoro Khadija ta ce
"Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un! Ya Yusuf, zamana a gurin ku ba alheri bane, dan haka zan koma gida, na wankeka daga zargin da akema, koda hakan zai bawa Nasir damar cima burinsa a kaina, ai ba akaina aka fara zan jure duk wani wulakanci tunda ba galibu gareni ba. Koda Nasir ya kusanceni da manufarsa, ai ba zina yai daniba akwai aure a tsakanin mu idai tsafinsa zai tasiri a kwaina idan mukaje gaban ubangiji zai mana shara.......!"
Saukar marin da taji a fuskarta yasa ta durkushe ba shiri ta saki kuka me sauti.
Cikin tsananin acin rai da masifa ya ke magana.
"Uban wa yace miki bansan da aure a tsakanin ku, ko kina zaton basan darajar aure ba na nemi salwantar da nawa mutuncin dan na ceci naki, Khadija bazan hanaki tafiya ba wannan karon duk inda zakije kije, koda kanki zaki kawai Nasir bazan dakatar da keba."
Yana gama fa in haka, ya juya yashige gida a fusace.
Kuka sosai Khadija takeyi duk da tasan Yusuf ya mata halaci amma bazata zuba ido a ringa zargisa da laifin da bashi a aikata ba dan haka dole ta koma gida yau koda hakan zai zamo silar salwantar rayuwarta.
Tana tashi bata shiga gidan ba, dan haka tai hanyar da zata sadata da inda zatahau motar garinsu.
* * * * * * * * * * *
Mama Karime ta fito da jakar tasu, anwar Izzatu dake tsaye ta ce
"Gaskiya zanyi kewarki Mama Karime."
Murmushi Mama Karime tai ya ce
"Ai ba zama zanyi ba, yarinyata kawai zanje na gani, kila na wuce katsina naga lafiyar yaron an uwana Nasiru, ta barsu shekara da shekaru."
"To Allah ya tsare."
"Amin."
Nafisa ta ce, wanda ke rike da hannun Anwar sukayi mata salama suka ako hanyar Kano.
* * * * * * * * * *
A kofar gidan sukai parking, Nasir ya kali driver ya ce
"Nan ne gidan Izzatu, kashiga ka kamun salama da ita, idan taki fitowa to kadawo ka sanar dani."
To driver ya ce, ya fito ya shiga gidan Izzatu.
Izzatu na zaune a falo dayake mijinta ya yi tafiya sai ita kadai dan haka koda taji salama hijab tasa ta fito dan ganin waye.
Ganin bata san shiba ta ce
"Lafiya kuwa, ban ganeka ba."
"Sunana Kamal, ni driver Alhaji Nasir ne, yana waje yana son ganin matar gidan Izzatu."
Zaro ido Izzatu ta yi ta ce
"Kaje kace bata nan."
Bata jira me zai ce ba ta rufo gidan ta koma ciki.
Komawa kamal ya yi ya ce wa Nasir.
"Oga wata mata tafito ta ce bata nan."
Kai Nasir ya girgiza ya ce
"Ya kamanin ta suke."
"Fara ce me jiki a shekaru zatayi Hajiya."
Murmushi Nasir ya yi ya ce
"Bude mun kofa muje tare."
Bude kofar Kamal yai, suka shiga gidan tare da Nasir.
* * * * * * * * * *
Murja ce tai salama, Nasir najin salamarta ya fito daga dakin, dan tunda ya baro Khadija tana kuka yakasa samun nutsuwa.
Ganinta ba Khadija ya ce
"Murja ina kika baro Khadija?"
"Yaya ai ba tare muka tafi ba, tunda na barta a gurinka, natafi kuma ban ga taje makaranta ba."
Gabansa ne ya fadi, kenan da gaske ta ke tafiya ta yi.
Me yake shirin faruwa Khadija zatakai kanta ga halaka, yasan koda Nasir yayi anfani da Khadija to bazai rabu da itaba tunda ta ata masa komai, zai iya halakata gaba aya.
Zuciyarsa ce ta fara tsinkewa, wani irin gumi na keto masa, a hankali ya ce
"Okay to."
Daga haka ya koma ciki, kaya ya sauya a dauki kudin da zasu kaishi cikin gari, yabar gidan ba tare da yaiwa kowa salama ba.
Dan ya kudiri aniyar bazai bari Nasir ya cutar da Khadija ba koda zai kashe su gara ya kashesu tare................!
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
By
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 21
Har cikin gidan suka shiga tare, driver nashi ya kwankwasa kofar gidan.
Izzatu dake zaune tanaji amma tsoro da fargaba sun hanata bude kofar, cikin dakewa ta taso har jikin kofar ta ce
"Waye?"
Muryar wanda taji yasa ta zaro ido, ya ce
"Munason magana dake ko zaki iya bude kofar?"
Jiki a sanyaye ta bude, ta gaidashi ya amsa ta ce
"Kayi hakuri Nasir mijina baya nan bazai yiyu mu shiga ciki bada izininsa ba, duk maganar da zamuyi muyita a nan dan Allah."
Murmushi yai ya ce
"Tanbaya aya zan miki, bayan ita bazan sake tanbayarki ba, wata kila tuhuma ta biyo baya, bayan tuhuma kuma abu na gaba bazai da i ba."
Baki Izzatu ta ta e ta ce
"Ina jinka."
"Ina matata da yarona."
"Basan ida suke ba, nasan dai ni natayata yakin fita daga gidan ka amma bansan inda ta tafi ba."
Wani mayaudarin murmushi Nasir yai ya ce
"Na baki nan da awa 1 idan baki