Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 119225 words

Chapter 26 - TSUTSAR NAMA BOOK 2 By Bilyn Abdul.txt

Ads the beginning of article before Image

27 Jun 2024

5247

Ads at the middle of Article

ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_




........Sosai mamaki ya kama Paah jin wai Maash ya sake barin gidan. A take ya ɗaga waya yay kiran Hayatu dan yasan ko kiran Maash ɗin yay a yanzu ba lallai ya ɗaga ba. Dan a ganinsa har yanzu fushi yake akan abinda ya faru. Amsar da Hayatun ya bashi na tabbacin sun wuce ya sake tsaya masa a rai. Sai kawai yaji duk yana ƙara zargin kansa da kansa. Da sauri ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Babba. Sai dai me ya samu sashen a kulle. Kai tsaye zargin Maash ne ya kulle yazo masa. Jiki a sanyaye ya sakko yana jin lallai dole shima ya nufi Chaina a yau ko gobe su haɗu da Maash ɗin.




🌟🌟🌟




Cikin barci ya farka da matsanancin ciwon kai. Duk da yanda yaso samun nutsuwa hakan ya gagara. Har magani yasha duk da tsanar da yay masa amma ina. Ya jima yana tsintar kansa a irin wannan halin a mabanbanta lokuta. Sai dai na yau ya tsananta sosai. Dan duk yanda yaso sake komawa ya duba Ummie ya gagara hakan. Har dare yana cikin mawuyacin hali. Salla kawai ke tada shi. Ai kusan ƙarfe ɗaya babu shiri dole yabar gidan. Dan ji ya dinga yi tamkar ana masa yayyafi da garwashin wuta. Ya tsani gidan da komai na cikinsa matuƙa. Kasancewar cikin dare sosai ya fita a gidan babu wanda ya sani da ga ALLAH sai shi sai mijin Mama Balki da ya kira ta waya. Hatta da securitys ɗin gate sanin matsayin Malam Baba agidan yasa koda zai fita da baƙo babu wanda ya iya cewa komai. Azatonsu ma ko mai magani ne tunda yau ciwon Hajiya Babba ya tashi sosai tun safe aketa fama..
Can wani gidansa ƙarami dake a wata anguwa daban dole Malam Baba ya kaisa, anan yay jiyyar kwanaki uku ya dawo ragal, sai sannan yake ji a bakin Malam Baba ai jikin Ummie ya motsa sosai amma itama dai da sauƙi. Dan baƙuwar yarinyar nan na tsaye akan al'amarin dan ma taji mata ciwo. Kasa cewa komai Maash ɗin yayi, sai guri ɗaya daya zubama idanu kawai a yanayin da baka isa tantancewa a kansa ba....


★★★★


Sam gidan babu kwanciyar hankali. Dan tun washe garin da naima Ummie kitso jikinta ya birkice. Sai ma abin ya nema fin na baya. Dan a ranar naci ɗan karan dukan da kowa sai da ya tausaya min. Dan har asibiti sai da aka kaini. Duk da azabar wahalar da naci a hannunta hankalina nakanta. Sam na kasa samun nutsuwa. Akoda yaushe cikin nazari da aune-aunen abubuwa nake. Dan motsawar ciwon nata ya tsaya min a rai. Ga duk wannan abun da akeyi banga ko giccin ɗanta ba a gida. Alamu kuma sun tabbatar da baya nan kenan. Sosai naji takaicinsa ya mamayeni. Har inaji a raina anya mutumin nan da curin hankali a brain ɗinsa kuwa. Rashin man kan yayi yawa matuƙa. Mahaifiya ai tafi gaban wasa. Amma shi duk motsinsa dai a neman kuɗi yake kawai baya tuna gabansa da bayansa. Kai dolene na saita masa layi ko zai tsireni, tunda na fahimci maganata ta ranar bata dawo dashi a hayyacinsa ba.
Bayan kwanaki uku jikinta yayi sauƙi Alhamdullah. Haka na sake komawa gareta. Ranar kuka nayi sosai ganin sun ɗaureta. Haka na kwanceta ina zubda hawaye. Na rungumeta a jikina duk da nasan komai zai iya faruwa. Sai dai alhmdllh babu abinda tai min face kukan yunwa-yunwa. Yau ma kamar ranar haka na fita na nemo mata abinci, ina bata ta ɓingire barci. Gyaran sashen na shiga yi bayan nayi kiran Mama Bilki ita kuma ta taimaka ta mata wanka. Dan sabbin masu aikin nan da aka kawo fa sun gudu tun daren da abin ya faru ta fashema ɗaya kai. Bayan Mama Balki ta mata wanka da taimakonta na ƙarasa gyaran sashen. Sai ko gashi ita da shi duk sun dawo a hayyacinsu. Duk wanda ya shigo ma sai yayi sha'awa. Nata yima Mama Balki tambayoyi akan wannan al'amari sai dai bata ce da ni komai ba. Dan haka nima na haƙura na duƙufa kula da al'amarin Ummie ɗin tare da ƙara ƙaimi. Dan yanzu ruwa na samu na ajiye na gorori a cikin kowane kwana biyu saina sauke Alkur'ani a ɗakin da tofawa cikin ruwan. Sam na hana kaina isashen barci. Nama daina fita a sashen gaba ɗaya sai neman abinci. Da farko Hajiya ƙarama taso taka min birki akan abinda nake yi ɗin, sai Hajiya Mammah tace ta barni. Duk da abin ya bani mamaki dan ita ma nai zaton zata hanani sai bance dai komai ba. Sai daga baya nakema Mama Balki zancen, shine tace ai Paah ne yace a barni na cigaba da kula da Ummie ɗin, sai dai bata san dalilin Hajiya ƙarama na son hanani ba. Kodan ita likitace tana ganin kamar Ummie zata iya cutar dani ne oho.
Na gamsu da hakan, dan haka na cigaba da sabgata. Sai dai na sakama kowa na gidan ido dan ina son sanin wanda ke ɗaure Ummie ɗin a duk lokacin da ciwonta ya motsa....

✨✨✨💫


Tun asubar fari Mom ke bugama su Abba ƙofa. Amma babu alamar ma ya jita balle amaryar tashi. Sai dai abinda bata sani ba duk zagi da bugun da take musu yana jinta. Bashi da lokacinta ne kawai dan hankalinsa nakan Hamile dake faman masa kuka har yanzu. Babu irin taimakon da bai bata ba harda su magani amma yarinyar nan ta tasashi da kukan iya shege da duk ya hargitsashi. ALLAH ya soshi ma har kayan shayi ya shigo mata da su, akwai kuma kettle a ɗakin nata kasancewar ba'a haɗa mata hitter ɗinta ba na toilet yasa yayi dabarar ajiye mata kettle ɗin.
Tsabar iya shege irin na Halime Mom na buga ƙofar ɗakin tana zaginsu sai ta sake sakama Abba sabon kuka. A rikice ya riƙota jikinsa yana tambayarta mi take so. Baki ta laɓe tana sake saka kukan da turza ƙafafunta. “Ai dai Abba kai kace na girmamata. Amma gashi can tana zagar Innata da Babana bayan kuma Innata ta rasu. Ni wlhy bazan yarda ba.”
Cike da lallashi Abba ya sake sakata a jikinsa yana faɗin, “Kinga yi haƙuri barta, haba Halimatussa'adiyya na. Keda kike tare da mijinki ina ruwanki da duk abinda take. Ko kina so nima nayi miki kukan ne. Jibafa jikinki zazzaɓi ne ki kwanta ki huta ko na sake sakaki a ruwan ɗumin”.
“Uhm uhm” ta faɗa tana maƙe kafada da tura masa baki. Murmushi yayi da sake sakata sosai jikin nasa. Komai yarinyar tayi sake shiga masa rai take. Ga alkairin data kawo masa har gadon barcinsa na ƙara sakashi jin ƙaunarta mai tsanani da kimarta harma da mutuncin iyayenta. Shagala a lallashin Halime yasa bai san lokacin da Mom ta bar buga ƙofar ba ma. Yana samu tayi barci ya tashi yayi shirin massalaci ya fita sallar asuba. Da yakan bari gari yay haske sannan ya dawo gida. Amma yau ana idarwa ya dawo gidan. Wajen Halime ya koma sai da ya tadata tayi salla ya bata shayi tasha da magani tana masa taɓara yana lallashi, bayan ta koma barci sannan ya sauke ajiyar zuciya ya fito. Ɗakin ya rufe mata ya nufi ɗakin da Gwaggo Gudidi ta kwana suka gaisa. Acan ya samu Musaddiq wajen Gwaggo suna hirarsu hankali kwance. Dan haka ya zauna ana hirar da shi. Anan ne yake jin wai Musaddiq ɗin ya samu aiki a companyn Maash na ƙera motoci. Kusan satinsa uku kenan ma yana zuwa. A yanzu haka ma company ya masa alƙawarin turashi ƙarin karatu ƙasar Chaina. Gaba ɗaya sai yaji kunya ta rufesa. Yay ƙasa da kansa kawai yanata jinjinawa.
Daga Musaddiq har Gwaggo Gudidi sun fahimci kunya ta rufe Abba, dan haka Musaddiq ya saki zancen ya kama wani. Itama sai Gwaggon ta koma masa nasiha akan kada ya biyema Mom duk haukan da take a gidan kodan darajarsa matsayin namiji uba da kuma yaƴansu. Ya mata alƙawarin in sha ALLAHU bazai biye mata ba. Daga nan suka ɗan ƙara taɓa hira ya tashi ya fita zuwa ɗakin Mom ɗin.
A falo ya sami Auta da Bibaa. Auta yazo garesa da gudu yana murnar ganinsa. Bibaa kuwa sai ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba sai da shi da kansa ya kira sunanta sannan ta gaishesa tana faman fushi. Murmushi kawai yayi ya wuce dan ya fahimci kishi take taya uwarta. Hannunsa riƙe dana Auta ya shiga bedroom ɗin Mom. Dai-dai lokacin take fitowa daga wankan da Umma ta sakata yi dole. Sosai ya ƙura mata udanu yana kallon yanda idonta suka kumbura sunyi jazur je dama fuskarta. Itama wani mugun kallo take watsa masa mai cike da tsana da takaicinsa. Dan wani irin ƙyau da kwarjini taga ya ƙara mata. Daka gansa kaga sabon ango shar daya sha sharafinsa. A take abinda ya ringa musu a gida jiya ya shiga dawo mata. Fashewa da kuka tayi tana rarumar kwalbar turare ta jefesa. Da sauri ya kauce yana tura Auta bayansa. Cigaba da rarumo duk abinda ya tare mata gaba tayi tana jeho masa. Tun yana kaucewa har dai ta samesa. Dole ya fito yana dariyar data sake kular da ita. Dan harga ALLAH shifa dariya borin nata ke bashi yanzu. Da Ummanta yaci karo tana ƙoƙarin shigowa da shayi a hannunta. Haɗiye dariyar yayi ya rissina yana gaisheta. Da ƙyar ta iya amsa masa tana wucewa ko kallonsa batai ba dan itama dai al'amarin nasa na jiya ne ya shiga dawo mata a rai tamkar yanzu komai ke faruwa.......✍️




_🤣Maganin mai zama gidan suruki kenan ai Umma._




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_




.......Alhamdullah sati biyu kenan da fara maida akalar al'amurana sashen Hajiya Babba. Tun ina ɗari-ɗari har na fara sakin jikina. Nayi tunanin Hajiya Mammah ko sauran matan gidan wani zai hana amma sai naji shiru. Sai ma jana da Hajiya Mammah ɗin ta farayi jikinta yanzu. Dan ta daina min faɗa sosai. Aikin sashenta ma idan naje yi iya bedroom take cewa na gyara kawai. Tun al'amarin nata naɗan bani mamaki har dai na tattara na watsar da tunanin ALLAH ne ya amsa addu'ata na fara samun sauƙi daga kowa.
Abinda na fara fahimta ga lalurar Ummie shine tana ƙarfafa ne a duk sanda Awwab ya shigo inda take ko kuma yama zo gidan zance. Dan a kwanki ukun nan da yake a gidan gaba ɗaya mun kasa gane kanta. Yau da safe har ciwo ta jimin da ƙyar aka fito dani a wajenta. Dalilin hakanne ma na yini a sashenmu da zazzaɓi shine nake kwance har yanzu. Ban samu ɗagawar jikin ba sai dare. Kwanciyar ce ta isheni na tashi na fito. Shiru sashen dan kowa har ya kwanta. Harna zauna a falo sai kuma na tashi na fita gaba ɗaya. Ko'ina akwai haske a gidan kai kace rana ce, sai dai babu hayaniya mai ƙarfi dan wanda ma basuyi barci ba duk sun nutsu a ɗakunansu. Tsamin da jikina yay ya sani ɗan fara tattakawa ko zai sake min, duk da ina kwaɗayin zuwa na duba Ummie sai dai babu yanda zanyi dan yau ɗin kam zuwa kusa da ita haɗari ne babba. Cinkushewar zuciya da son mantar da kaina damuwata ya sani nufar garden ɗin gidan. Shi kam akwai ƙarancin haske a cikinsa, amma ko ɗar banji tsiro ba na samu kujera na zauna ina mai ƙurama korayen gayyakin cikinsa da ƙarancin haske ya sakasu yin duhu ido. Kamar da ga sama naji ana wata ƙara mara daɗin ji, gabana ne ya faɗi. Sai kuma na fara jin sambatu dake fita da wasu irin kalamai marasa daɗin saurare. Neman rikicewa nayi, da sauri na kai hannu na toshe kunnuwana. Ban san adadin mintinan dana ɗauka ba a haka kafin na buɗe kunnen. Yanzu kam shiru babu ihun, sai magana ƙasa-ƙasa da akeyi cikin raɗa. Miƙewa nayi cikin sanɗa na nufi inda nake jin maganar. Hango mutane tsaye mace da namiji, namijin na ƙoƙarin sakama macen kaya a jikinta ya sani lafewa jikin fulawoyi.
Cikin shagwaɓa macen ke faɗin, “Wlhy ni na faɗama ban gaji ba. Miyasa yau duk baka son kasancewa da ni ne? Ko dai ka samu wata ne a cikin sabbin masu aikin nan?”.
Da ɗan kaushin murya namijin ya bata amsa da, “Miyasa kike da zargi ne wai? Kin san fa minene matsalar. Muhammad na gidan nan ke miyasa baƙya lissafi ne! Kije sai da safe bana son damuwa”.
Magana ta yunƙura zata sake masa ya ɗaga mata hannu. Sai naga ta faɗa jikinsa ta rungumesa. Niko tunda ya ambaci Muhammad zuciyata ke wani irin rawa. Dan kuwa a bakin mutum ɗaya ne nake jin sunan nan. Kuma ɗansa kawai yake kira da shi wato Awwab. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” na faɗa cikin rawar baki sakamakon ganin wanda zuciyar tawa ke ayyana min. Paah tare da Siyama a garden suna aikata z... kasa ƙarasawa nayi, sai ma wani irin kuka daya kufce min. Dole nakai hannuna na toshe bakina har sai da suka fice sannan na durƙushe a wajen nayisa. Wannan wane irin zubar da mutunci ne. Mutum mai daraja da kima kamar Paah ace yana bin masu aiki. Kai ya Arrahaman. Gaskiya ya kamata nasan tarihin wannan gida, ko hakan zai taimakeni wajen fara rarrabe ƙarya da gaskiya. Tare da kallon kowa na gidan nan da siffarsa.


Bayan kamar tazarar mintuna ashirin da fitarsu sannan na fita. Sashenmu nayi nufin komawa, amma sai naci karo da Mama balki da alama daga sashen namu ta fito. Idanu ta waro sosai a kaina. Sai kuma ta kama hannuna cikin sauke ajiyar zuciya tana tambayata “Daga ina haka? Yaya jikin naki? Badai sashen Hajiya Babba kika koma ba?”.
Kaina na shiga girgiza mata. Hawayen da nake makalewa na kufcemin. Sake tashin hankalin ta yayi. Babu shiri taja hannuna. Siririyar hanyar sashensu da mijinta tabi dani. Sai gamu a madaidaicin falonsu da yau ne shigowata cikinsa na farko. A saman kujera ta zaunar dani itama ta zauna. Sai da ta bani ruwa nasha sannan ta fara jeramin sabuwar tambaya.
Kaina na girgiza mata kawai. Tare da faɗin, “Mama babu komai. Amma dan ALLAH idan bazaki damu ba ki bani tarihin wannan gida a yau”.
Ɗan jimm tayi kamar mai nazari. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wani abune ya sake faruwa kuma?”.
Kamar zan faɗa mata sai kuma na fasa saboda kwaɓar da zuciyata tayi min. “Babu komai Mama. Kawai dai ina son jine saboda nasan ta hanyar dazan ɓullo wajen taimakon Ummie game da wannan ciwon nata.”
Nan ma shiru tayi kamar bazata tanka min ba. Kafin ta nisa tana mai jinjina kanta. “Zan sanar miki duk abinda na sani Kandala. Saboda harga ALLAH tun randa na fara ganinki a gidan nan zuciyata ta sami nutsuwa dake. A kuma kwanakin nan da kikayi na gwadaki ta hanyoyi da dama banga wata alamar cin amana ko kasancewarki ba mutuniyar kirki ba. Amma duk da haka ina roƙonki ki riƙe min dukkan abinda zan faɗa miki amana dan ALLAH. Sannan zan taimakeki da abinda zan iya domin ganin munyi wani yunƙuri akan Hajiya Babba ko ALLAH zaisa mu dace.”
“Nagode Mama.”


*_Alonso_* aƙon haure daga ƙasar Spain zuwa Nigeria. Kwara-kwara, bature-batture, balarabe-balarabe gashi nan dai bamu san takamaimai ɗan wane ƙabila bane ko yare, kawai dai daga ƙasar Spain yazo. Abinda kawai kowa yake kallo a tattare da shi shine bashi da alaƙa da Africa sam. Alonso ba musulmi bane ba, baya kuma jin hausa ko zo na kasheka, daga turanci sai yaren Spanish. Da farko harkar kasuwanci ce ta shigo da shi ƙasar Nigeria. Dan yana kawo irin dish ɗin nan na kwanika kala-kala da mutanen da ke jere da su. Kafin a hankali ya samar da wajen yinsu anan cikin garin Lagos ya ɗauki yaranmu aiki yana kuma koyar dasu. Sannu a hankali kamfani ya fara bunƙasa kafin cikar shekara biyu duk yaran daya hora sun gama ƙwarewa har suma suna koyar da wasu. Adams shine kusan babban yaron Alonso saboda ƙwazonsa, ga biyayya da ya kema uban gidan nasa tamkar yaya da ƙane duk da kuwa Adams nada mata acan ƙauyensu dake Kano mai suna kwanar-mashi harda ƴaƴa biyu. Dan neman kuɗi ne ya kaisa garin na Lagos. Ƙyaƙyƙyawan halin Adams yasa Alonso yanke hukuncin kaisa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads