Header Ads
Showing 96001 words to 99000 words out of 119225 words

Chapter 33 - TSUTSAR NAMA BOOK 2 By Bilyn Abdul.txt

Ads the beginning of article before Image

27 Jun 2024

5256

Ads at the middle of Article

ido sannan na nufesa, hannu na kai zan ɗauka amma sai ya gyara zama ta yanda ribbon ɗin ta koma tsakkiyar ƙafafunsa. Kauda kaina nayi da sauri, tare da juyawa cikin sassarfa nabar wajen dan ni kaɗai nasan abinda idanuna suka gane min. A mamakina ina kaiwa ƙofa na murɗa handle ɗin sai gashi ta buɗe. Ƙoƙarin juyowa nayi na kallesa sai naga yana ajiye remote alamar shine ya buɗe ɗin kenan. Harara na watsa masa dayin ƙwafa cike da tsiwa na ce, “Kuma ALLAH ya isa na, sai na gayama Ummie”. Na ƙarasa fita da sauri har ina bugewa da ƙaton flowers base dake gefen ƙofar anyi decorretion da su.......✍️


_🤣Koba ALLAH ya isa ba. Muma to ALLAH ya isanmu jikinmu da aka hau🥱😜. Bara na ware kafin danginta su caskala ni🚴🚴🚴._




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_




.....Tana fita ya runtse idanunsa da karfi, sai kuma ya fisgi gorar ruwan data ajiye masa ya ɓalle murfin tare da kafa bakinsa ya hau kwankwaɗa. Tass ya shanye ruwan yay jifa da robar tamkar itace tai masa abinda ya harmutsasan, sai kuma ya miƙe da hanzarinsa ya nufi side ɗin da bedroom ɗinsa yake yana famar haɗa hanya da furzar da huci a jajjere da taunar lips kamar zai huda su da haƙori.


★Kai tsaye nima side ɗinmu na nufa maimakon komawa ƙarasa abincin Ummie. Ko kallon waɗanda ke a falo banyi ba na afka bedroom. Karo mukaci da Bahijja, dan haka ta riƙeni gam cikin kiɗima da ganin yanayina ta ke furta, “Aunty Kandala lafiya kuwa? Mike faruwa dake na gankai haka a birkice? Ko hajiya babba ce?.”
Hannunta na ture daga jikina batare dana iya magana ba. Cikin sassarfa na nufi bathroom ɗinmu dan bana fatan taji ƙamshin turarensa daba ɓoyayye ba a gidan a jikina. Ina shiga kai tsaye ƙarƙashin shower na shige na sakarma kaina ruwa kawai. Dan bani da wani zaɓin daya wuce hakan. A jajjere na dinga sauke ajiyar numfashi sai ga hawaye sharrr-sharrr kamar an buɗe fanfo....


💦💦💦💦


Tun fitowar Samraah da ga sashen Maash Hajiya Mammah dake laɓe ta bita da kallo. Duk da ƙamshin turarensa da yanda Samraahn ta fito ya sata farin ciki dan ta tabbatar akwai abinda ya faru koda ba wanda sukayi fata bane. Amma dai ba haka taso ba. Taso a yau komai da suka shirya ya faru kawai dan itafa tafi son idan ta saka abu a gaba kawai tayisa a wuce wajen. Har ta nufi barin wajen sai kuma ta fasa. Part ɗin Maash ɗin ta nufa, kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon sai uban ƙamshinsa da sanyin ac. Sai television dake aiki sai dai babu ƙara sosai. Idanunta ne suka sauka akan tray ɗin abincinta. Trayn ta zubama ido na tsawon sakanni, sai kuma ta nufi inda yake. Tana gab da kaiwa ta tsaya cak, tabbacin jin motsi ya sata komawa da baya da sauri ta fita a sashen gaba ɗaya.
Sai kuma abinda tayi ɗin ya sakata dariya. Kaɗan ta dara tana nufar nata part ɗin.


Da kallo Hajiya ƙarama da komai ya faru akan idonta ta bita. Lips ɗinta ta cije da ƙarfi sai kuma ta saki ƙwafa. A zuciyarta tana ayyana lokaci fa yayi da zata amshi kayanta kafin wannan matar ta mata shigar sauri. Amma dolene ta bincika mi take ƙullawa akan Maash ɗin haka ne. Gaba tayi da yanzu bata da wannan lokacin asibiti ta nufa. Tanada aikin da zatayi na kuɗaɗe masu nauyin gaske. Dan haka tai ficewarta cike da takun kasaita irin na manyan mata gogaggun kuma ƴan boko...


Hajiya ƙarama ke kuma....🤔 (To Bara dai nayi hiru.🥱

✨💫✨💫


A ƙofar gate Mansoor yaci karo da Mamy. Ɗauke kansa yay tamkar bai ganta ba zai wuce. Amma sai ta riƙo masa hannu cikin tashin hankali. “Mansoor mika aikata?”.
Kansa tsaye ya bata amsa da, “Sakinta nayi. Dan bazan iya koda zaman minti ɗaya da ita ba Mamy”.
“Baka da hankali Mansoor. Kasan muhimmancin auren nan a garemu baki ɗaya?”.
“Bana son na sani Mamy kiyi haƙuri”.
Daga haka ya zare hannunsa yay gaba abinsa yana ƙoƙarin shiga taxi ɗin da yazo. Dan dama bai sallamesa ba. Binsa kawai Mamy keyi da kallo komai ya ƙwace mata. Har motar tabar wajen bata iya taɓuka komai ba. Sai da motar su Hajiya Sakeena da zasu wuce asibiti ta fito sannan ta dawo firgigit. Ƙoƙarin isa ga motar tai tana tambayar mike faruwa. Dan taga Hajiya Sakeenar na kuka. Cikin masifa da hayayyaƙowa tamkar ba yayarta ba ta ce, “Koma miya faru ba huruminki bane ba. Kije ki zauna gida ki jirani. Dan wlhy in har yarinyata ta mutu kota nakasa sai ke da ɗanki kunyi dana sani” daga haka ta dakama driver tsawa akan su je. Nan ɗin ma sake sumar wucin gadi Mamy tayi, ba kuma ta dawo a hayyacinta ba har sai da sukai nisa.


Mansoor kam kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa. Ya ɗan jima tsaye a ƙofar gidan sai ga wata mata ta fito tana ƴar dariya. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Jikin gate ɗin ya matsa zaiyi knocking sai ya jiyo kamar hayaniya. Fasawa yay yayi ɗan jimm alamar saurare. Masifa wata mata keyi harda zagi, sai kuma wata siririyar murya na dariya cikin shaƙiyanci. Mamaki hakan ya basa, sai dai yaji nutsuwa a cikin muryoyin babu na Samraah. Amma kuma bai taɓa zuwa gidan nan yaji haka ba. Yana tsaye a wajen sai ga matar ɗazun ta dawo. Daurewa yay ya gaisheta ta amsa masa da ɗan kallon mamaki. Dan kuwa dai ta ganeshi sosai. Ai Mansoor ɗin Samraah ba ɓoyayye bane a layin nasu kodan aikin gidan tv da sukeyi tare.
“Ihmm niko kamar Mansoor?”.
Cikin jin daɗin ta ganesa ya amsa mata da cewar shine. Tare da roƙonta ta turo masa Samraah dan ALLAH”.
Murmushi tayi tana ɗan girgiza kai. Sai kuma ta amsa masa da, “Ayya Mansoor ai Samraah bata nan tana Lagos ne ko Abuja naji ance. Amma dai kamar Lagos ɗin”.
Da mamaki yace, “Lagos? To yin me?”.
Ɗan jimm tayi alamar tunani. Sai kuma ta kaɗa kanta da faɗin, “Tare da mijinta mana. Amma dai ka nema Abban nasu ko ƴaƴanta Musaddiq mana”. Daga haka tayi shigewarta tabar Mansoor da sakakken baki....

❤️💦❤️💦❤️


A ciki kam Mom ce ke fitina akan Halime bata isa yin girki a gidan ba yau. Dan tun randa ta tabbatar itace sukai uwar fitina da Abba har takai ya shashsheka mata maruka tare da gargaɗi mai ƙarfi akan iskancin kai hannu jikinsa da take sonyi a kwanakin nan, zata shaƙe masa kwala, ko zata cutar da shi. Acewarta gara ta murɗe kowa ya huta. Wannan mari ya girgiza Mom har ma da Ummanta. Yayinda Halime take ɗaki tana kwasar dariya. Bawai marin bane ya bata dariya itafa. Firgicewar Mom da ganinta matsayin matar mijinta ne kawai ke bata nishaɗi. Dan a take abubuwa data ɗan sani a gidan na ƙarfin Mom ya shiga dawo mata. Tana ji Abba zai shigo ta haɗiye dariyar ta.


Umma itace ta killafa Mom ta ƙarfi, ta kuma tabbatar mata idan fa bata kwantar da hankalinta ba har aurenta ya mutu to gaskiya kada tazo mata gida. Wannan hauka har ina aita tarota tana ƙwacewa kamar wata ƙaramar yarinya. Su nutsu su fuskanci abinda ya dace suyi amma ta zauna yin hauka akan wanda shi sam hankalinsa ma baya a kanta yanzu. Wannan faɗa ya sakata nutsuwa. Har Abba ya gama kwanakin angwanci a ɗakin Halime bata sake kula kowa ba. Da ya dawo ɗakinta kuma yaso nuna ɗaukar fishi da ita. Sai dai roƙon da Musaddiq yay masa ya sassauta abun. Dan haka ya haɗasu su duka gidan har Nabil dake makaranta yay musu nasiha tare da tabbatar musu da Halime itama yanzu ɗaya daga cikin family ɗinsu ce, sannan baya buƙatar damuwa daga kowa.
Abbas da Musaddiq da Nabil ne kawai sukai magana da amsar Halime. Amma Baby da Bibaa ko kallon uban ma basuyi ba. Watsar dasu Abba yayi, sai ma maganar bikin Baby daya tabbatar musu ya gama tsayar wa nan da wata biyu, tare da sanar musu alkairin daya samu Musaddiq dan nan da sati biyu shi kuma zai wuce ƙasar Chaina. Yaso ayi bikin Baby da Musaddiq ɗin, sai dai hakan bazai yiwu ba saboda komai na tafiyarsa ya gama kammala. Wannan magana itace ta hargitsa Mom matuƙa har ta danne mata al'amarin Halime a kwanaki biyun nan.
Ummanta ce ta bazama wajen teachers ɗin su. Shine jiya da dare aka kawo abinda zatai amfani da shi akan Musaddiq dan daƙile wannan batun tafiya. Yau kuma ake son yaci a cikin abinci. Da rana baya gida, dan haka ta gama shiryama girkin dare gashi ba itace da girkin ba. Sai kuma ga Halime ta shiga domin ɗorawa saboda kowa yasan ita ya kamata tayi girkin daren. Ga kuma Abba yay kiranta da sake tabbatar mata dan har ma ya aiko yaro da cefane. Shine Mom tace bata isa ba itace zatai girkin. A lokacin makwafciyarsu da sukai magana da Mansoor na gidan. Shine ta raba gardamar ta sake tabbatarma Mom cewar Halime dai ya kamata tayi girkin daren. Kawai sai Mom ta fara tura mata ashariya. Shine ta fito tana Murmushi yayinda Halime ke dariya. Dan ita al'amarin Mom ɗin yanzu dariya ma ya koma bata. Mace kamar mai mutsukku a cikin kai. Murhun gawayi makwafciyar tasu ta kawo ma Halime tunda dama abin girkin kawai take buƙata komai na ma'aikaci itama tana da shi. Harda ƙullin gawayi biyu...


💕🌟💕


Bluetooth ɗin dake cikin kunnensa ya zare yana mai sakin wani kalar lalataccen murmushi. Sai kuma ya sake maida fuskarsa ya tsuke tamkar bashi ba. Tamkar ba wanda ake jira ba ya shiga zare kayan jikinsa a nutse dan babu alamar wani gaggawa a tare da shi. Dogon wandon jikinsa kawai ya bari batare da ya cire ba ya nufi closet ɗinsa. Daga can kusurwar bango Ya danna wani maɓalli, a take adon wutsiyar wadrobe ɗin dake ta dai-dai kona ɗin ya shiga naɗe kansa. Zallar gilashi garai-garai da haskensa kesa a iya ganin komai dake a cikin wajen ya bayyana. Nan ɗin ma dai wani abu ya danna, a take gilashin yaja kansa ya shige cikin wadrobe ɗin. Zallar adon golden ya bayyana da bindigu har guda uku da aka manna a bangon wajen tamkar an zana sune. Hannunsa duk biyu ya tura a cikin aljihun wandon, tare da gyara tsaiwarsa ya zubama bindugun ido. Biyu ƙananu ne, ɗaya ƴar babba hakannan daka ganta kasan zatai haɗari da tsada. Cike da wani salon taƙadaranci ya cije lips ɗinsa tare da zare hannunsa ɗaya ya maida gashinsa daya sakko masa a fuska kaɗan saboda salon gyaran dayay masa ɗazun da yamma. Sauke hannun yay a hankali ya kai yatsarsa ɗaya saman bindigar farko, tamkar mai zana abu sannu-sannu ya dinga sakkoshi ƙasa har ya dire akan ta tsakkiya, nanma bai tsaya ba yay ƙasa har sai da yaje ta ƙarshe. Zagaya kan bindigar ya cigaba dayi da yatsar tasa kusan sakan biyu sai kuma ya sake maidashi sama ya ɗora akan ta tsakkiyar. Nan ma yaja kusan sakanni biyar ma tamkar mai nazari sai kuma ya laɓe baki cike da salon ɗage kafaɗu ya ciro bindigar alamar zuciyarsa tafi aminta da ɗaukar tata. Sauran mahaɗanta dake gefenta suma kowanne a mahallinsa ya cicciro harda bullet kusan biyar sannan ya maida komai a yanda yake ya fito. Cikin bedroom ɗin nasa ya dawo, ya zauna a katafaren bakin gadonsa ya haɗa bindigar tsaff cike da ƙwarewa ya ajiye, sai dai bai saka bullets ɗin ba ya jawo side drawer ɗinsa ta gado ya zuba su ciki. Bathroom ɗin ya nufa abinsa cike da takunsa na mazantaka da nutsuwa.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


......Ina kitchen ina ƙoƙarin haɗama Ummie madara kamar yanda na saba a kowanne dare yanzu saboda naga tana sonta sosai Hajiya Mammah ta shigo. Kamar ko yaushe tsaff take cikin kwalliya mai ɗaukar ido da ke nuna ita ɗin wacece. Sosai take matuƙar bani mamaki matar nan. Itafa dare baya hanata kwalliya kamar jikanyar ifiritai, musamman idan akace tana da baƙuwa da zata kwana a gidan. Gaisheta nai a ɗarare da ƙoƙarin kauda kai daga kallon ƙurillar da take bina da shi daga sama har ƙasa. Kadaran kadahan ta amsa min sai dai fuskarta a sake. Juice ta ɗauka ta ɗaura a samar tray tare da glass cup, sai ƙaramin bowl da aka yanka fruit yay ƙyau sosai musamman yanda kalolinsu suka fito a farin glass bowl ɗin kamar an zana, sai kuma wani haɗaɗɗen kula shima mai ƙyau duk ta ɗora, har zata ɗauka sai kuma ta dakata. Kallona tai tare da tukunyar da nake dafa madarar.
“Kandala mi kike dafawa anan?”.
Fuskata a ɗan cinkushe, na ce, “Hajiya madarar Ummie ce”.
Kanta ta jinjina tare da faɗin, “Okay Masha ALLAH. Ta kusa kammaluwa ne?”.
“A'a yanzu na ɗora ai babu jimawa”.
“Okay! To kinga zonan kimin wani aiki sai na jire miki. Awwab zaki miƙama wannan part ɗinsa. Azizat ya saka Paah ɗinsu kuma ya sakata aiki, Awwab kuma baya son jira zai iya fasa sha kuma nasan ba wani abu yaci ba”.
Ji nai kamar na fasa ihu, sai dai nasan ban isa cewa bazanyi ba. Amma a cikin raina na ɗan yi mamaki, to amma ina ruwana ba yayar babansa bace. Cikin haɗiye yawu da ƙyar na amsa tray ɗin, ɗauke juice ɗin tayi da glass cup ɗin tana faɗin, “Banda wannan nawane. Kiyi maza zan koma sama ne”.
“Okay maa”. Na amsa mata cike da jin haushi. Acan ƙasan raina kuwa jinake kamar na haɗiyi zuciyata na huta. Amma dai ba komai, dan nima kai fruit salad ɗin zai min amfani, dan dama ina son ganinsa. Dan akwai bashina a kansa, bazan taɓa barin maganar daya gasamin ɗazun da safe ba sai na maida murtani, idan ba hakaba zan iya kasa barci ma wlhy. Kamar koyaushe a nutsena nake tafiyata. Jikina da hijjab iya gwiwa mai hannu kamar kullum. Duk fa amatsayin ƴar aiki nake gidan kamar yanda shaiɗanin ya ƙalabamin akoda yaushe zaka sameni cikin tsaftata, dan inada ƙyanƙyami, ga son wanka kamar ƴar agwagwa. Komai a gidan free ne har gamu masu aiki, banbancin kawai komai zakayi kai da kanka ne masu gidan kuwa mune ke musu. A hankalin ƙamshin turaren da Ummie ta fesamin ɗazun har a cikin gashina ke tashi, sosai turaren ya kwanta min a zuciya. dan yana fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa harma da kai daka saka. Na ɗakko ne zan saka mata ta fisge ta hau min feshi da shi a jikina tana dariya, bata kuwa barsa ba sai da nayi dabarar amshewa. Koba'a faɗa ba nasan an sayesa ne da kuɗaɗe masu nauyi. Murmushi na saki mai sanyi, dan yanda yake bama Ummien kulawa a gidan da kowanne nau'in abubuwan more rayuwa duk da lalurar dake tare da ita na ƙayatar dani. Sau kusan uku ina knocking amma babu alamar za'a buɗe min. “Ɗan wulaƙanci fitinanne mai girman kai”. Na faɗa a hankali ina murguɗa baki da hararar ƙofar. Cikin jin zafi na murɗa handle ɗin ƙofar na shiga falon. Kamar kullum babu yawaitar haske. Sai uban sanyin ac da mayataccen ƙamshinsa daya gama mamaye komai. Hatta kusa da mutum idan ya tsaya ko wani dalili yasa ya taɓaka koya zauna guri ya tashi ka zauna sai ka ɗeba mayen ƙamshin nan nashi. Narasa da wane shegen turare yake amfani haka. Koda yake ya wuce na tsafi. Na bama kaina amsa ina murguɗa baki. Ƙoƙarin ajiyewa nake a Centre table ɗin falon aka shigo da sallama bayan anyi knocking. Bakowa bane face Hayatu, dan haka na amsa sallamar tasa a zuciyata kawai batare dana kallesa ba na ƙarasa ajiye tray

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads