Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 119225 words

Chapter 30 - TSUTSAR NAMA BOOK 2 By Bilyn Abdul.txt

Ads the beginning of article before Image

27 Jun 2024

5248

Ads at the middle of Article

kamar dai baya. Da lafiya ta samu sai kuma jiki ya sake rikicewa.
Wani bawan ALLAH ne ya bada shawarar gwada mata maganin Islamic da namu na gargajiya, dan acewarsa babu wani ciwon damuwa manyan aljanu ne ke damunta, basuyi jayayya ba kuwa suka sa aka fara kawo musu masana akan hakan. Kamar dai yanda kika sani, magani dace ne, kowa nata gwada tashi sa'ar, sai dai tsahon lokaci ba'a dace ba. Amma dai ana ganin ɗan sauƙi a wasu lokutan. Gaba ɗaya ragamar kula da Ummie a hannun Awwab take, dan tun bai iya wasu abubuwan ba har ya iya. Hatta da kitso zama yake yay mata kiga tamkar mace tayi mata shi. Sai dai me yana da shekara goma sha bakwai komai ya fara sassautawa. A hankali ya fara ja baya da al'amuran mahaifiyar tasa. Takai ma idan yaje gareta sai ta hausa da duka da jifa har saita jimasa ciwo. Idan ya matsama kansa da damuwa sai shi kuma ya hau ciwon kai koya yanke jiki ya faɗi babu rai. Tun kowa na ɗaukar abin wasa dai har ta tabbatar zamansu waje ɗaya bazai yuwuba. Sosai hankalinmu ya tashi da wannan al'amari nasu, musamman ma ni da sukafi shaƙuwa da ni.
Canjawar al'amuran ya saka mijina na yanzu bama Awwab shawarar komawa makaranta ya cigaba da karatunsa. Amma sai ya nuna mana shi babu inda zaije. Ya haƙura da komai na rayuwa zai cigaba da kula da Ummiensa. Munta lallashinsa harda Yayar Mahaifinsa Hajiya Nafisa. (Hajiya Mammah). Kunyarmu da yake ji da addu'ar da muka duƙufa a kansa ta sanya ya amince zai koma. Dan haka da kansa ma yayma Baba prof.. da mahaifinsa maganar komawa makarantar. Sun nuna farin cikinsu suma, a take kuma suka shiga suka fita ya zana ssce ɗinsa. Cikin amincin UBANGIJI aka dace ya samu result mai ƙyau. Awwab ya shiga jami'a, kuma har lokacin yana nacin taimakon mahaifiyarsa amma dai babu daɗi dan wahala kawai yake sha. Yayinda Fahad ƙaninsa da shima a lokacin ya ke gab da kammala secondary. Hakama Hayatu suke ƙarƙashin kulawarsa. A farkon fara karatun Awwab ya ɗan fara kula da Companys ɗin mahaifiyarsa da ke neman durƙushewa duk da mahaifinsa tsaye yake akan komai, sai dai aikin ya masa yawa matuƙa dole sai da Awwab ɗin ya fara taimaka masa abubuwan suka fara dai-daita da dawowa fiye ma da yanda ya kamata. Dan shima UBANGIJI ya saka nasibi a hannunsa komai ya taɓa sai ya zama kuɗi. Yanda al'amuran nasa ke haɓaka sai ma ya fara danne na mahaifiyarsa. A haka ya kammala jami'a, yayinda ƙaninsa da Hayatu suke can ƙasar turai suna nasu karatun. Anan ɓangaren kuma Falak na nata a gida Nigeria, dan yanda Paah ya tsaya akan karatunsu itama bai banbanta da ita ba. A hankali ragamar kasuwancin ya koma hannun Awwab, yayinda yake kuma cigaba da karatunsa. Cikin amincin UBANGIJI a wannan lokaci kuma sai aka dace ta hanyar wani bawan ALLAH daga ƙasar Togo Ummie ta fara samun lafiya. Hakama al'amarin Awwab ya fara dai'daita..


Alhamdullah komai ya dawo dai-dai, farin cikinmu da duk zuri'ar Baba prof.. ma haka. Dan samun lafiyar Ummie ba ƙaramin kwanciyar hankali ya kawoma kowa ba. A lokacinne Hayatu ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria. Saura Fahad da zai ƙara shekara ɗaya. Sai dai yana zuwa hutu musamman ma yanzu da Ummie ta samu sauƙi. Wannan gidan da kike gani itace da kanta ta fara ginashi a lokacin data samu lafiya. Acewarta tana fatan haɗa kan iyalinta waje guda idan su Awwab sunyi aure duk nan zasu zauna da matansu. Muma ta ware mana sashenmu tana mai tabbatar mana mune zuri'arta na ɓangaren mahaifa. Jin daɗin samun lafiyarta yasa Awwab sake maida hankakinsa akan harkar kasuwancin sosai. Yayinda itama take ƙara masa ƙarfin gwiwa. Sai dai me, ana murna ɓarawo ya tafi ashe yana laɓe a bakin ƙofa. Dan kuwa a wani dare labari ya koma baya. Jikin Ummie ya sake hargitsewar da yafi na baya muni da tashin hankali. A wannan lokacin ma dai Awwab sake tattara komai da komai yayi ya dawo da gaba ɗaya hankalinsa da ƙarfinsa akan mahaifiyarsa. Anyi-anyi ya koma kan harkokinsa yayi biris da kowa da komai. Bashi da aiki sai addu'oi da karatun Alqur'ani ga mahaifiyarsa. Da farko lafiya lau yake mata komai, sai dai zuwa wani lokaci matsalar baya ta sake dawowa ta rashin jituwa a tsakaninsu. Ya matuƙar tada hankalinsa akan hakan amma an rasa mafita. Manyan likitocin babu irin waɗanda ba'a gani, hakama masu maganin gargajiya dana Islamic duk inda aka jisu sai an kawasu. Shima na ƙasar Togon anje nemansa aka samu babu shi, wai dama zuwaune a wajen ba'a san takamaimai ɗan wane yanki bane ba. Shekara guda ana cikin wannan zaune tsaye aka bama Paah shawarar yin aure. Amma yaƙi firr sai da aka tsaya a kansa sannan da ƙyar ya amince. Sai dai kuma babu wacce zai aura kamar yanda ya faɗa. Yawan kulawa da Hajiya Lawusa (Hajiya Ƙarama) ke bama Ummie yasa Baba prof.. bada shawarar aurenta. Dan itama a lokacin mijinta ya rasu tanada ƴa ƙarama wadda ita kaɗai ta haifa.
Sosai akasha fama kafin Hajiya ƙarama ta amince. Sai dai duk abinda ake Awwab bai sani ba sai daga baya. Sosai ya nuna ɓacin ransa da kishin mahaifiyarsa. Hakanne dalilin tada wannan ginin gidan ya cigaba da yinsa. Abinka da maganar kuɗi, cikin abinda baifi watanni uku ba komai an kammala. Shine ya dawo da mahaifiyarsa nan acewarsa ya bama Paah spiece da matar tasa su ƙarata, duk kuwa da can ɗin ma gidan mallakin Ummie ne. Dan gidan da mahaifinta ya gina da guminsa ya kuma rayu a cikinsa. Hakan yayima Paah zafi, dan Awwab ya tattara kowansu ya watsar, baya shiga sabgar Hajiya ƙarama duk da kuwa a baya kowa yasan aminiyar mahaifiyarsa ce, harma da mahaifin nasa ya tattarashi ya ajiyesa gefe.
A ƙalla mun kusa shekara guda a gidan nan da dawowa muketa ɗawainiya da Ummie, dan Awwab dai ya ajiye zancen kasuwanci gaba ɗaya sai kula da mahaifiyarsa. Kullum cikin jimasa ciwo take amma hakan baya hanashi zuwa gareta. Baba prof.. ne akoda yaushe baya gajiya da kawo masu magani, zuwan wani da ga Niger ya bada shawarar Awwab ya rage zaman gidan, dan in har suna a muhalli guda da mahaifiyarsa to lallai lafiyarta zatayi wahalar samuwa. Dan an riga an saka rashin jituwa a tsakaninsu. A samar da masu kula da ita har ALLAH ya bata lafiya. Sam Awwab yaƙi aminta da wannan shawara. Kowa ya buga sai yace babu inda zaije. Hatta da mahaifinsa da basa jituwa a yanzu sai da yazo yana bashi haƙuri da lallashinsa amma ina firr yaƙi amincewa. Mu kammu duk yanda yake girmamamu da jin kunyarmu yaƙi sauraren mu. Hakama Baba prof da kakarsa ta wajen uba matar Baba prof... Ɗin. Ana cikin haka ɗan uwansa Fahad ya dawo ya kammala karatun, ana murnar dawowarsa sai kuma murna ta koma ciki. Dan kuwa sam babu jituwa tsakaninsa da Awwab. Sosai suke nunama juna tsana. Zama inuwa ɗaya ya gagaresu. Akwai randa babu wanda yasan abinda ya haɗosu kawai Awwab ya kama zanesa. Da ƙyar aka amshi yaron a hannunsa sai da ya kwanta asibiti kuwa saboda jigata. Yana samun sauƙi ko hanyar gidan nan bai dawo ba ya tattara inasa inasa ya koma inda ya fito. Daga ranar bai sake leƙo ƙasar nan ba har yanzu. Shima kuma Awwab ɗin bana jin ya sake waiwayar inda yake. Sai su Baba prof.. da Paah.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


....Abinda ya fara dai-daita tsakanin Awwab da Hajiya ƙarama kulawar da take bama Ummie. Wanda dama tun kan ta auri Paah tanayin hakan, shima kuma Awwab ɗin ya sani, shi dai auren ne yake ganin kamar akwai cin amanar mahaifiyarsa sai kuma kishi da yake tayata. Amma daga baya daya fahimci Hajiya ƙaramar bata canja daga duk abinda takema ummien ba sai ya sakko. Wannan dalili na shiryawarsu ya saka Hajiya Ƙarama da Paah dawowa gidan nan. Basufi watanni uku ba Hajiya Nafisa da suke kira (Hajiya Mammah) a yanzu yayar Paah da akai aurenta bayan haihuwar Awwab dan ta jima batai aure ba mijinta suka samu saɓani. A Niger take auren, koda tazo sai Ba prof.. yace bazata zauna masa gida ba, dan a yanda muke jin labari fitinarta ta hanata zama lafiya da mutane kamar yanda ta hanata aure da farko, ba kuma a wannan karon bane ta fara tahowa gida yaji, sai dai na wannan karon yayi tsamari sosai dan harda dukanta mijin yayi. Koda Baba prof.. ya bibiyi al'amarin sai ya gano itace bata da gaskiya, shine ya hanata zaman gidansa. Kakarsu Awwab ɗin ce tace ta dawo nan gidan ta zauna. Itama da farko Awwab yaso borema zamanta, sai dai bamusan yaya akayi ba kuma daga baya yayi shiru. Dawowarta gidan nan komai ya fara canjawa. Ta maidani sashen masu aiki ni da iyayen Hayatu wai matsayin data sammu da shi kenan. Bayan hakan bata sammu a cikin danginsu kona Ummie ba. Ba muji komai ba muka koma. Sai dai muna ji muna gani kulawa da Ummie ya fara gagararmu, an kawo sabbin masu aiki, tare da saka Awwab komawa kan kasuwancinsa. Yaranta biyu ƴammata sun baro Niger sun dawo nan suma. Gasu basu da tarbiyya sam, basa shakkar taka kowa da wulaƙanta kowa. Gasu malalata basu iya komai ba. Dan dalilin zaman nasu yasa Awwab saka a samo masu aiki ganin suna neman ƙazanta gidan. Hajiya Mammah bata wuce wata biyar a gidan ba ALLAH yay ma mahaifiyar Hayatu rasuwa, sosai na shiga kiɗimuwa hakama mahaifinsa da shi kansa Hayatun. Shima Awwab rasuwar ta girgizashi sosai. A dalilin wannan zaman gaisuwa Alhaji Abdullahi ƙanin Paah ya dawo gidan nan da zama shi da iyalinsa, matarsa ɗaya da yara biyu Malika da Muhsin. Dan koda aka gama komai sai suka ƙi komawa nasu gidan suma. Abin nan ya bani mamaki ya kuma ɗauremin kai, sai dai banda tacewa. Ashe basu kaɗai bane, sai ga mahaifiyarsu itama (Kakar su Awwab ɗin matar Baba prof..) wai itama ta dawo nan saboda sun samu saɓani da Baba prof ɗin akan ƙin komawar Hajiya Mammah gidan mijinta. Shikenan duk sun dawo, Baba prof.. da autarta Mashi'a ne kawai babu, dan ita ba'a Nigeria take aure ba. Sai dai duk ƙarshen shekara tana zuwa bikin ƙara shekara na Ummie da Paah ke shiryawa.
Da farko su dukansu kulawa suke bama Ummie. Dan ko sashenta kaje sai ka san ita ɗin ƴar gatan dangi ce. Komai tsaff kamar ba wadda ke'a halin ciwo ba. Idan ba abin ne ya motsa ba ma bazaka taɓa cewa ga lalurar dake damun nata ba. Sosai Awwab ya samu nutsuwa a ɗan tsakanin. Hankalinsa ya kwanta har wata ƙiba yayi ya ƙara haske. Mu kammamu mun samu nutsuwa. Dan a lokacinne akai auren Hayatu da Falak ɗina. Bayan bikin shima Awwab ya bamu shawarar yin aure ni da mahaifin Hayatun. Da farko munso turjewa, amma suka dage shi da Hayatu dole muka amince. Watanni biyu zuwa uku tsakani kakarsu Awwab ta kwanta jiyya. Bata wani jima ba ALLAH yay mata rasuwa a ƙasar Egypt Cairo. Rasuwar ta girgiza kowa na family ɗin, musamman ma Baba prof.. da sai ya baka tausayi. Bayan gama jimami komai ya koma normal. ALLAH ya cigaba da riƙo da hannayen Awwab komai ya taɓa na kasuwanci sai yayi albarka. A cikin abinda bai wuce shekara ɗaya ba ya sake zama wani mahaukacin mai arziƙi da sunansa ke yawo tako ina ama duniya ba ƙasarsa kawai ba. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai ƙarancin shekarunsa da mutane ke gani amma ya tara irin wannan dukiya. Sannan mahaifinsa ba wani shahararren mai arziki bane balle ace ya gada ne. Sanda kakansa da mahaifiyarsa sukai nasu tashen basu ko kama ƙafar nashi arziƙin ba, ansan sunansu ne a iya wani yanki na garin Lagos, shiko duniya ce ke kallonsa a yanzu.
Tun Awwab na ƙarami dama ba mutum bane mai yawan magana sai idan shi yaso. Sai dai akwai tausayi da girmama duk wanda ya girme masa. Bai san wulaƙanta mutane ba koda kuwa ƴan aikine wannan tarbiyyar mahaifiyarsa ce da kakansa Abbie. Babu abinda ya damesa da sabgar kowa tashi kawai yake yi. Tun bayan rasuwar Abbie Baba prof.. ne kawai amininsa. Dan da shi kawai zakaga yana dogon hira. Sai ko mu idan yaso wani lokacin zakiga yazo har nan sashen ya zauna koda ba zaiyi magana ba. Dan alokacin da mahaifiyata ta tarasu zaki ɗauka yanada alaƙar zuminci mai ƙarfine da ita. Sosai ya nuna damuwarsa.
Tunda ayyuka da harkokinsa suka sha masa kai sai abubuwan gidan suka fara canjawa. Kulawar da ake bama Ummie ta fara ja baya. Ciwonta ya sake tsananta. Idan kinga ana kula da al'amarinta ya shigo gari ne, kuma a lokacin zakiga ciwonta ya tsananta. Duk yanda muka so mu kula da ita mu an hanamu, sashenta ma an mana iyaka da shi, duk randa kuma na shiga koda a sace ne al'amarin baya daɗi tsakanina da Hajiya Mammah. Hajiya ƙarama ce kawai ke nata ƙoƙarin bata taɓa fasawa ba dan hargagin Hajiya Mammah baya damunta. Sau biyu ana korarmu ni da Abban Hayatu saboda nacewa akan kulawa da Ummie, Awwab ne ke dawo damu. Dole muka tsaya matsayinmu na masu aiki dan mu zauna lafiya. Amma neman hanyar kuɓutar da Ummie da son gano bakin zaren kullum cikin yi muke. Masu aiki kullum cikin kawowa ake domin kulawa da Ummie, sai dai basa zarta wata ɗaya suke guduwa. Kowa ɗauka yake saboda ciwon Ummien suke guduwa. Ni kuma a raina inajin ba hakan bane ba akwai abinda ke korarsu.
“Wannan shine tarihin wannan gida a taƙaice Kandala. Dan na yanke miki abubuwa da yawa ne a cikinsa saboda wasu dalilai. Sannan ina fata ki fahimci wasu da kanki kuma”.
Hawayen da suka kasa tsaya min tun ɗazun na ƙara sharcewa. Cikin rawar murya data gama dasashewa na ce, “Amma mama miyyasa duk kika faɗa min wannan? Bayan baki sanni ba? Baki san koni muguwa bace, ko nama shigo gidan ne dan wata manufa”.
Ɗan murmushi tayi itama tana share hawayenta. Kafin ta kamo hannuna cikin nata. “Nasan ke ba muguwa bace Kandala. Duk da dai da farko haka kawai naji ƙaunarki a cikin zuciyata. Sai kuma wata fuska da nake gani akan fuskarki da bansan dalilin hakan ba. Da ga baya Hayatu ya sanar mana alaƙar dake tsakaninki da Awwab....”
Wani mugun zaro idanu nayi ina zabura gefe da fincike hannayena dake a cikin nata. Magana nake son yi amma na kasa. Sai lips ɗina dake rawa kawai. Murmushi ta saki tare da sake kamo hannun nawa ta ce, “Kwantar fa hankalinki Samraah. Kar kuma ki fasa aikin ladar da kika fara. Daga Ummie har Awwab da ɗan uwansa abin tausayi ne, suna buƙatar mai tallafama rayuwarsu. Mu kuma da muke da damar yin hakan bamu da wani ƙarfin iko. Dama fatan da muke masa yay aure ya samu mace ta gari da zata juya mulki da tsarin wannan gida ta inda kowa baiyi zato ba. Alhamdullah kuma muna fatan an samu, dan ko yanzu Awwab yaso nunama duniya matsayinki a gurinsa dole kowa ya girgiza, duk da ina tsoron kar su cutar dake dan mutanen nan hatsabiban kansu ne suma, dan ma taurin kan Awwab na rage musu tasiri a wasu lokuta. Sai dai duk abinka baka isa gane wanene na kirkin ba idan kika cire Baba prof.. Dan kowa da tasa illar da manufa da kike gani. Amma ke yarinya ce mai wayo da ilimin addini, dan har na zamani na fahimci kina da shi, ɓoyewa kawai kike kamar yadda kika ɓoye mana ainahin kanki da sunanki. Dan ALLAH ki daure ki taimaki waɗan nan bayin ALLAHn. Awwab mutumin kirki ne, yana iya ƙoƙarin sa wajen tsare mutuncin kansa ta hanyoyi da dama da samarin zamanin nan sukan kasa musamman idan kudaɗe na yawo a hannayensu. Kisa a ranki aikin lada kike yi sakamakon ki naga UBANGIJI. Kisa a ranki ceto zakiyi na Uwa da yaƴanta a cikin gobarar da bata da iyaka. Nasan bake zaki bama Ummie lafiya ba, amma zaki zama wani tsanin taimakawa mukai ga samuwar lafiyar tata. Dan in har kina a tare da ita duk maganin da mu kuma zamu nemo mun san zaki bata. Za ki kuma dinga mata addu'a har shi Awwab ɗin dan bana raba ɗayan biyu akwai sihiri mai ƙarfi shima a jikinsa. Fatanmu shima Fahad ya dawo gida su dai-daita da ɗan uwansa. Sannan waɗan nan mutanen da suka cika gidan nan kowa ya koma inda ya fito..”
Karo na farko na saki murmushi mai ciwo. Sai kuma na girgiza kaina. “Mama zan iya tsayawa dai akan samun lafiyar Ummie in sha ALLAHU da kuma batun dawowar ɗan uwansa gida. Amma shi babu abinda ya shafeni da shi ko halin da yake a ciki. Yaje can ya nemo mai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads