Showing 102001 words to 105000 words out of 119225 words
Chapter 35 - TSUTSAR NAMA BOOK 2 By Bilyn Abdul.txt
ya zauna Hayatu ya maida ƙofar ya rufe sannan kowa ya zabura ya shiga mazauninsa. Hayatu da TJ na gaba kamar koyaushe. Securitys ɗin sa na'a wata motar kamar ko yaushe suma. Da dasu uku ma kawai zaiyi fitar. TJ na ƙoƙarin tada mota ta fito da ɗan saurinta. Kamar kullum tana a cikin kwalliya dake ƙara fidda mata ƙyawunta da bayyana wayewarta. Hayatu ne yay ma TJ nuni daya dakata, dan haka ya tsaya ɗin harta ƙaraso, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, dan direct bayan ta nufa saitin inda Maash da bai san ma da fitowar tata ba yake. Dan hankalinsa nakan takardun daya ɗauka a gefensa da Hayatu ne ya ajiye masa su dan ya duba. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata data haɗe da gayu ta furta, “My bro.. please zan bika, nasan dai club zaka je”.
Idan kujerar motar nan ta motsa shima ya motsa duk da kuwa muryar tata tazo masa a bazata tunda shi bai san da fitowar tasu ba. Ƙara narke murya tayi cikin nuna damuwa da shirun nasa ta sake cewa, “Please mana Yaya Awwab na shigo?”.
“Kai kana jiran miye?!”.
Ya faɗa cikin yanayin fusata batare daya ɗago ba. Ai jikin Tj har rawa yake wajen murzama motar key dan ko kallonsu ogansu yayi sun san mi yake nufi balle magana da baki. Da wani kalar mayen kallo Azizat tabi motar, ga wani irin sanyi ƙalau da jikinta ke komawa kamar an zubama bread ruwa. Dai-dai motocin na isa katafaren golden an black gate ɗin gidan da aka wangale musu wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen sakkowa saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Bata motsasu ba, bata kuma yi yinƙurin barin wajen ba. Ashe turaren da Mammah ta bata duk na ƙarya ne tunda gashi tazo gabansa amma bai kulatan ba. Arwa dake ta bayansu ce laɓe ta tako zuwa inda take bayan ta gama cin dariya, dan tun fitowar Azizat daga ɗaki tabiyo bayanta, dama kuma itace ta ɗauke turaren da Mammah ɗin bama Azizat ɗin dan a kunnenta komai ya faru sanda take bata batare da su sun sani ba. Hannunta ta kama kawai tare da janyota ta faɗa jikinta. Rungumeta tayi cikin sigar nuna lallashi batare da tace mata komai ba, sai dai shafa bayanta kawai da takeyi dan babu wani abu da zata faɗa mata kuma wanda ita bata sanshi ba. Sai dai kawai taƙi yarda ne kamar yanda kowa ya sani. Dan tunda yayansu yaface bayayi tofa babu ubanda ya isa cewa yayin sai Umminesa, itako batama da cikakkiyar lafiyar hankalin fahimtar abinda ake a gidan, a shi kansa ma bata masa kallo irin na mutum face ojujun dake sake hargitse lissafin brain ɗinta. Bata ganin laifin Azizat wani lokacin, dan wlhy ko ita da suke kamar uba ɗaya da Yaa Awwab ɗin a lokuta da dama takan ji inama-inama. Amma yanda tasan yana mata kallon ƙawa uba ɗaya yasa take dannewa kawai. Sun ɗan jima a wajen kafin ta kama hannunta su koma ciki...
🌜❤️🌛
A yanayin da ya shigo duk yanda Dad ke ɗauke kansa akan al'amarin nan sai da ya zuba masa ido cikin tashin hankali. Hakama Attahir da ke zaune jigum zaram ya miƙe akan Mansoor. Sai dai yana kamo hannunsa da ya dafe kansa da shi Mansoor ɗin ya kaɓe. Sai kuma ya zube cikin kujera. Amamkinsu ji kawai sukai ya fashe musu da kuka. Dole Dad ya miƙe shima. Su duka biyun sukai kansa da tambaya. Bai iya ya amsa musu ba, face kukan da yake yi da sambatun faɗin, “Shike nan na rasata. Ta auri wani bani ba. Kun cutar dani. Da kunsan irin son da nake mata da baku aitaka abinda kuka aikata ba”.
Hannu Dad ya sanya a bakinsa ya rufe, kafin cikin kulawa da tausayawa da lallashi ya shafa kansa. “Please Mansoor cool down. Nasan an maka badaidai ba. Nima kuma ina ji a raina mun cuta maka. Amma yanzu in sha ALLAHU a shirye nake na gyara kuskurenmu”.
“Taya zaku iya gyarashi Dad? Ta yaya? Bayan wadda kuka rabani da ita ta min nisa?. Iyayenta sun mata aure Dad, Samraah tayi aure, ta auri wani bani ba. Wlhy Dad ina sonta so na gaskiya da ban taɓa kwatanta yima wata ɗiya mace irinsa ba”.
Gaba ɗaya jikin Dad sanyi ya ƙara yi, sai ma ya rasa abinda zai sake faɗa. Kusan mintuna biyu kowa yay shiru a falon sai kai-kawon zuciyoyi kawai sukaji an faɗo musu babu ko sallama balle excuses. Hajiya Sakeena ce ke faman huci da cika da batsewa. Ta watsa musu wani mummunan kallo su duka sannan ta dire idanun nata akan Mansoor. “To mara mutunci haƙarka bata cimma ruwa ba. ALLAH bai karɓi rayuwar Husnah ba kamar yanda kaso kayi fata. Kaje ka gaggaya min magana son ranka har gidan mijin aurena. To yanzu ko zakaji amsa...”
Kamar an jeho Mamy itama sai gata. Kai tsaye kan Hajiya Sakina tayi. Cikin tashin hankali da mamaki ta zube a gabanta tana kuka da roƙonta ta rufa mata asiri. In sha ALLAHU indai batun auren Husnah ne zata saka Attahir ya aureta. Wata shegiyar dariyar rainin hankali Hajiya Sakina ta sanya. Kafin ta tafa hannaye da faɗin, “Iye nanaye caras-cass. Ai daga baya kenan, kema kin sanni bana manta bashin gaba ai Aunty. Ɗanki yaci zarafina ga ɗiyata ɗaya can tilo kwance a asibiti rai a hannun ALLAH. Dama na faɗa miki, in har Mansoor ya saki Husnah wlhy kema sai kin rasa naki igiyar auren dan sai na fallasa abinda kike binnewa”.
“K!! Sakeena!!”.
Attahiru daya gama kaiwa maƙoshi da abinda ke faruwa ya dakama Hajiya Sakina tsawa tare da yunƙurowa kamar zai mareta. Cike da rainin wayo tai wani irin ja baya tana ɗaga duka hannayenta sama alamar surrender. Sai kuma ta kwashe da dariya tana tafasu. Tsitt falon yayi kowa na kallonta har Mamy. Sai da tai Mai isarta kafin ta nuna Attahir ɗin tana haɗe fuska. “Oh lallai ashe kaima ka girma Attahiru? Ai ban sani. Sai ka saurara bada kai nake yi ba yanzu da tsoffinku nake”. Ta wani ɗauke kanta ta maida kan Dad da ya zuba mata ido kawai. Sai kuma takai zaune zama irin na ƙasaita da ƙularwa.
“Kayi haƙuri Yaya idan kaga an ɗaure alƙali a kotu tofa ɗaurowa tayi. Nasan zaka so sanin yanda akayi matarka ta dage dan hana yiwuwar aure tsakanin ɗan ka da budurwarsa. Da kuma ƙullawa tsakanin Husnah da ɗanka.”
Cikin ɓacin rai Dad ya tareta da faɗin, “Sakeena ki tafi maganarki kai tsaye kin san bana son shashanci”.
“Uhhm hakane Yaya kayi hakuri”. Ta faɗa tana maida kanta kan Mansoor da Attahir da suka gama cika da batsewa. Kamar bataga a yanayin da suke ba ta fara bayaninta. “Idan Mansoor da Attahir basu manta ba a ranar da matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ya shahara a ƙasar nan dama duniya yay bikin buɗe Companynsa a garin kano wato *_Awwab El-Mu'azz Adams_* da akafi sani da *_MAASH_* kun tattauna wani batu akansa da daddare daya shafi video recording da budurwar Mansoor tai masa”.
Da wani irin sauri Mansoor ya ɗago yana kallon Attahir. Saurin girgiza kai shima Attahir ɗin yayi zai fara rantsuwa Hajiya Sakina ta dakatar da shi. “Kwantar da hankalinka Mansoor ba Attahir bane ba. A sanda kuke tattauna batun wannan video Aunty ta shigo sashen naku saboda damuwar rashin cin abincin kirki da Mansoor yayi. Ta kawo masa kunun tsamiya data dama masa akan ko zai sha tunda tasan yana sonshi sosai. Sai dai tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar ta tsinkayi Mansoor yana sanar ma Attahiru batun video tare da nuna masa shi, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH ya rufe wannan sirrin har sai sun gano gaskiya. Ya kuma taimaka musu akan tabbatar da gaskiyar saboda shi yana da abokai ƴaƴan manyan ƙasar nan da sukayi karatu tare a us masu alaƙa da Maash. Cikin jimami Attahir yay masa alƙawarin bincikawa. Sai dai ya tabbatar masa da sam baya jin Maash zai aikata wannan al'amari da gangan in ma harfa ya aikata ɗin. Dan ya ɗan san Maash ɗin shima sama-sama duk da ba wata mu'amala mai ƙarfi bace ta haɗasu face zaman makaranta ɗaya a us. Ya kuma gargaɗi Mansoor ɗin akan ya gargaɗi budurwarsa ta adana video ɗin da ƙyau gudun kada wani ya gansa har yayi tunanin yin wani abu na cutarwa ga Maash. Dan yanzu mutane sun lalace. Ganin Maash mutum mai tarin dukiya za'a iya amfani da video dan yimishi barazana. Ɗari bisa ɗari Mansoor yaji wannan shawara ta ɗan uwansa, ya kuma tabbatar masa da zai nema itama Samraah ya gargaɗeta a daren nan ma basai gari ya waye ba.
Da baya da baya Aunty ta bari sashen, ta samu kai kanta falon, ta samu ka shige sai su Amal kawai na kallo, dan haka ta samu damar shigewa ɗakinta da sauri itama. Kai kawo ta shiga yi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa akan abinda ta jiyo. Kaima dai Yaya kasan aunty akan batun kuɗi. Mace ce mai son ace ita itace. Shiyyasa ko'a sutura bata saka ƙarama. Koda bazaka saya mata ba tasan buga-bugar da zatayi ta samarwa kanta. Hakan yasa ma kuke yawan samun matsala da ita. Dan idan ban manta ba har ƙararta kasha kaiwa gida akan wannan halin nata na idan taga abu a wajen wane sai da tayisa itama hankalinta ke kwanciya tun ma baka da komai. To awannan gaɓar ma bikin Mansoor take hari. Ta riga ta gayyato ƙawayenta ƴan ƙarya irinta da matan oganninka na wajen aiki, gashi kai kuma ka kwafsa mata kaƙi yarda da duk tsare-tsaren sharholiyar da muka tsara, ka kuma ce bazaka bata ko sisi ba. Haka shima Mansoor yaƙi. Attahir ne ma ya ɗan biye mata ya bata 1mil yace ta ƙara dana wajenta tayi haƙuri. Dan haka jin wannan batun video da maganar Attahir ta kawo mata wuta a cikin kai.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_
.......A ranar daƙyar ta iya barci kamar yanda ta faɗa min, washe gari tunda farar safiya tai kirana. Da farko kwana-kwana nima ta dinga min, sai da na nuna mata ta fito kawai a mutum muyi magana tasan dai ni mai rufa mata asiri ce sannan ta buɗe min komai. Koni zancen nata ya girgizani gaskiya. Bakomai yasa hakan ba sai jin batun Maash. Dan ni nasan wani abu kaɗan daga Maash ɗin sakamakon mijina yaronsa ne. Saboda a Companynin sa na Abayoyi dake anan Dubai yake aiki. Na buƙaci nima ta ɗan bani lokaci nayi tunani, ta roƙeni karna wuce yinin yau to.
Banko wuce yinin ba, dan ta hanyar mijina na ɗan ƙara bincika halin Maash da ƙarfin ikonsa. Amsar daya bani akan cewa Maash mutum ne murɗaɗɗe, sannan yana da zafi sosai. Amma da wahala ka masa abu a farko ya maida hankali a kanka. Sai idan ka cigaba da aikatawar ne, idan har fa ya maka gargaɗi na farko baya sake na biyu sai hukunci. Wannan amsa tashi ta bani ƙwarin gwiwa, dan koba komai dai mu ai bama fata bayan na farko mu sake, yo inama zamu sake ganinsa. Wannan ɗin ma rabonmu ne ALLAH ya kawo mana har gida. Husnah ta jima tana son Mansoor amma yaƙi saurarenta, aunty kuma taƙi ƙarfafa al'amarin duk da ta sani, dan haka kawai naga ai wannan wata hanya ce ta samun cikar burina, sannan nima dai dani za'a ci kuɗin. Kai tsaye nai kiran aunty muka tattauna da tsara yanda komai ya kamata ya tafi, tare da bada sharaɗin in fa har akaci nasara a 500mil inada kaso biyu. Ma'ana inada 200mil kenan. Aunty ta nuna min bazai yiwu ba, sai dai na amshi 100mil nayi haƙuri, tunda nasan abinda ke gabanta ai. Kai tsaye na fito mata a mutum. (Aunty ke tayaya kike tunanin auren Mansoor da yarinyar nan zai kuma kasance? Mufa zamu amshi kuɗin nan ne a hannun Maash da sunanta, idan ma har ya bibiya ita zai saka a kama. Sai dai auren Mansoor ya koma kan Husnah tunda dama ba'ayi invetion ba wai ko baki gane ba). Da sauri ta amsa min da hakane fa Sakeena. Wlhy kaina duk ya cure. Yanzu dai a daren nan zan samo video daga wayar Mansoor. Ke kuma sai ki samo mana Number Maash a wayarki. Na amsa mata da karta damu, kafin ma na samar da Number zan saka a fara aika masa saƙon barazana gidansa dan akwai wani yaron mijina dake tare da Maash ɗin kuma ya san sabon gidan nasa...
🌛❤️🌜
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso guesthouse ɗinsa. Gidane daya amsa suna gida sai dai bashi da girma sosai. Amma a ƙyau da tsaruwa ba'a magana. Dan yanda akai kusan rabin gidan da gilashi dolene ya ɗauki hankalin mai kallo. Ga wata green ciyawa da aka malala a harabar gidan aka ratsa lafiyayyen baƙin kwalta da mota zata iya bi kawai kota tsaya. Sai furanni da ƙamshinsu ya cika gidan da kukan tsuntsaye. Babu wani hayaniya, dan anguwar ma shiru ce sai uban karunuka ata waje duk da kuwa akwai securitys da baka isa ka shigoba sai da izininsu. Cikin girmamawa security ɗin daya wangale musu gate da remote ke ɗaga musu hannu, koda ya maida ya rufe motocin ya biyo. Dai-dai Hayatu na buɗema Maash mota ya iso wajen. Sannu da zuwa da gaisuwar girmamawa yake jerama ubangidan nasa. Maash dake ƙoƙarin fitowa hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan ya gama fitowa a motar a taƙaice ya furta, “How are you Semuel?”.
“I am fine Sir”. Samuel ya faɗa cike da zumuɗi. Ga bakinsa washe kamar gonar auduga. Dan ya jima baiga boss ɗin ba kasancewar kwana biyu bai shigo nan ɗin ba. Tamkar wani mai mulki haka yake tafe cikin takun mazantaka da rashin hayaniya guards ɗin nasa da su Hayatu harma da TJ da Samuel biye da shi. Hayatu ne ta ɗan gefensa amma ya zartashi a taku ke masa magana ƙasa-ƙasa. Shiko yana tafiya tamkar bada shi ɗin yake ba. Dan inda yake ajiye ƙafa kawai yake kallo. Da sauri wanda ke tsaye a bakin ƙofar shiga wajen ya wangale musu ƙofar shima tare da risinawa kwasar gaisuwa wajen boss. Hannu shima kawai ya ɗaga masa. Babu alamar damuwa a tare da shi alamar dai duk wanda ke tare da shi yasan ɗabi'unsa, da girmamawa ya cigaba da faɗin, “Sir ya iso tun kusan awa ɗaya. Kamar yanda ka bada umarni securitys basu barshi ya shigo da mota ba. Kuma da yaronsa biyu aka barshi ya shigo kawai.”
“Good job” ya faɗa a taƙaice yana tura kai ciki. Dan shima tun shigowarsu anguwar yaga motocin Minister ɗin tare da yaransa da aka dinkare a waje. Da ga shi sai Hayatu da TJ sai amintaccen guard ɗinsa Shu'aibu suka shiga. Kallo ɗaya yayima Minister da ya gama cika da takaici ya ɗauke kansa. Babu wani alamun damuwa ko nadamar shanyasa da yayi ya ƙarasa kujera ɗaya tal data banbanta da duk kujerun dake a haɗaɗɗen falon ya zauna. Wani shegen zaman ƙasaita da gadara yayi, yayinda Shu'aibu ya koma bayansa ya tsaya kamar saƙago. TJ ya ajiye kayan dake hannunsa a stool ɗin gefen kujerar na sashen damarsa. Hayatu kuma yakai zaune a ɗaya daga kujerun falon ta gefen kusa da shi. Bakin Minister daya miƙe domin girmamawa a washe kamar bashine ke faman tsinema Maash ɗin ba a zuciya. Amma kuma dama birgar ta bayan idoce kawai. A kallon ido cikin ido ko ganawar fuska da fuska Maash tamkar lu'u-lu'un narkakken ɗanyen zinare yake a cikin idanunsu. Duk da ƙarancin shekarun nan nasa shi fa takalmin ƙarfe ne baya takuwa a yanda kaso. To kaɗan daga aikinsa yace bazaiyi business ɗin da kai ba. Kuma babu ubanda ya isa yace komai, idan kuma kace zaka kona wajen wani saboda ka saɓa da Maash, to ka tabbata kuwa babu mai saurarenka kuma koda a ƙetaren ƙasar ne. Sai da ya tabbatar Maash ɗin ya gama zama sannan ya miƙa masa hannu cikin murmushi. Amma mi, sai Maash ɗin yaƙi bashi nasa, a maimakon hakan ma sai ya haɗe hannayensa biyu a daƙile alamar ya amsa masa. Shiko minister sai faman murmushin yaƙe yake dan abinda Maash ɗin yayi ya baƙanta masa zuciya, dan gaisuwar ma shine yayi Maash ya amsa a taƙaice. Bai nuna ya damu ba, dan lallaɓawa yake kasancewar ya jima yana neman alfarmar wannan zaman amma abin ya gagara, dan kusan wata biyu kenan. Yanzun ma da ƙyar sai da ya biyo ta wasu hanyoyin yaran Maash ɗin sannan ya dace. “Ranka ya daɗe ai kusan 1hour kenan da isowarmu”. Ya faɗa cikin son nuna an shanyasu a wayance. Kamar Maash ɗin bazai tanka ba dan hankalinsa nakan wayar hannunsa da yake daƙila, kusan minti ɗaya har ma Minister ya fidda rai da