Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 119225 words

Chapter 34 - TSUTSAR NAMA BOOK 2 By Bilyn Abdul.txt

Ads the beginning of article before Image

27 Jun 2024

5257

Ads at the middle of Article

ɗin.
“Barka da dare Maa”.
Ya faɗa cikin girmamawa kamar yanda yake min yanzu musamman idan babu kowa a waje. Harara na ɗago na balla masa ina mai jan sirrin tsaki. Shiko yay ƙasa da kansa. Ƙafa na ɗaga zan bar wajen da sauri ya ce, “Dan ALLAH kiyi haƙuri. Ki kai masa bedroom inba hakaba bazai shasa anan ba. Dan muna uzirin fitane, Ummie kuma bata ƙaunar zamansa da yunwa duk yau babu abinda yaci kuma sai chocolate.”
Wata hararar na sake balla masa. Shiko ya sake marairaicewa da faɗin, “Dan ALLAH dan ƙaunar da kike ma Ummie”.
Idanuna na rumtse da ƙarfi. Kamar kar nayin sai kuma dai na ɗauka dan ni shaidace, duk randa Ummie ta cika fitina a gidan to dan gudan jinin nata ne. Sai dai kuma daya raɓeta babu sauran zaman lafiya musamman ace ya shiga ɗakin da take ko yazo kusa da ita sosai. Sai dai ya kasance a nesa da itane yanzu zata fa zuba masa ido kamar mai son tuna wani abu a kansa kosan sanin wanene shi har hotonsa haka take masa. Cikin ƴar fusatar da Hayatun ya sake saka min nai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa da ƙaddara tasa zan masa shiga ta biyu. Nasan latsin rainin wayonsa. Zai ma iya kasancewa yana jina yay shiru, niko ina son komawa na kaima Ummie madararta tasha magani. Agadarance na murɗa ƙofar na shiga ina mai sake tsuke fuskasta da haɗa baƙar maganar dazan gasa masa da nake fatan ta hanashi barci. Wayam babu kowa a ɗakin, sai dai anan ɗin ma hasken akwai ƙaranci, sai dai yafi na falon dan anan ana iya ganin komai. Kayansa daya watsar a kan lallausan milk carpet ɗin dake a gaban gadon na ballama harara da taɓe baki. A bayyane na furta, “Ƙazami kawai sai iyayi da feleƙe, amma ba'a iya yima kai komai.” a saman bed side drawer na nufi ajiye tray ɗin, sai idona ya sauka akan bindiga. Sosai na waro idanu, jikina har tsuma yake wajen ajiye tray ɗin hannuna kaɗan ya rage ban zubar da shi ba na dai gyara masa zama ina ɗaukar bindigar. (Ta tabbata dai guy ɗin nan ɗan ta'addane. Yo anya ma ba ɗan fashi da makami bane? Kambu aiko yau zan tona asiri, zai ko tabbatar ya kawo ƴar jarida gidan nan) na ƙare zancen a zuciyata ina sakin ƙwafa a fili. Ƙofa na zabura zan nufa ina ƙoƙarin soke bindigar a cikin jikina. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar bathroom. Naji firgici, dan yanayina ma ya nuna hakan sakamakon a yanda na jiyo na kalla wajen. Ganin shine ɗaure da towel iya ƙugu zuwa gwiwa yana riƙe da ƙarami a hannunsa zai kai shi fuskarsa amma ya tsaya yana kallona nai saurin ɗauke idanun nawa tare da zaburar son nabar ɗakin kafin ya farga da abinda na ɗauka. Sai dai me ina isa jikin ƙofar naji ta bada ƙitt alamar rufewa, duk da kuwa a rufen take dama. Ban fasa kai hannuna jikin handle ɗin ba, na murɗa na murɗa amma ko gezau tabbacin dai an kulle. (To ta yaya?) Zuciyata ta tambaya, rashin amsa da makama ya sani juyowa, sai ko idanunsu suka sauka akan ƙaramin black & golden remote dake hannunsa alamar da shi ya kulle ƙofar. Dan yanda ya ɗauke kansa tamkar baiyi komai ba ya sake tabbatar min da hakan. A ɗan zamana gidan na fara haddace mugayen halayensa a cikin kaina. Dan babu ubanda yake ragamawa da wannan murɗaɗɗen halin nasa na rashin mutunci. Ko kallona bai sake yi ba ya nufi gaban mirror ɗinsa hankali kwance. Saurin kauda idona nayi daga kansa dan dama dai a gaba ɗaya cikin sakanni da baifi goma bane komai ya faru, ban kuma iya masa ko kallon sakan ɗaya cikakke ba saboda yanayin da yake ciki, dan ma babu yawaitar haske a ɗakin ne shiyyasa.
A bazata cikin dakewarsa da daƙilallen yanayi irin na mugayen muskilan mutane a silent voice ɗin nan nashi ya furta, “K idonki bazai daina gane-gane ba ko?”.
Sam da farko bammayi zaton shine yay maganar ba. Sai da nai ɗan jimmm sannan na fahimta. Baki na murguɗa batare dana kallesa ba cike da tsiwa nima na furta, “In dai masu mugun halin ta'addanci na a inda nake gane-gane ma yanzu ya fara ai. Kuma in kere na yawo zabo na yawo wataran za'a gamu. Adai juri zuwa rafi. Saboda wataran tulu zai fashe a tsakkiyar kasuwa. Dan in ma an binne wani abun wani bazai binnu ba. Musamman ma Samraah Abdul-wahab Gwarzo”.
Shiru bai tanka min ba. Ni kuma na kasa iya ɗaga ido na kallesa saboda a yanda yake samandagari guda babu riga ƙaton kawai. A bazata matuƙar bazata naji tsaiwar mutum a kaina daf, ai bamma san sanda na ɗago ba a harmutse. Ƙamshin turarensa ne yay mugun rige-rigen shiga min hanci saboda iskar razana dana shaƙa da ƙarfi. Kusancin namu yayi yawa dan haka nai matuƙar zabura baya ina ƙyaƙyƙyafta idanu uwa ya na namijin biranya. Hannu ya miƙomin alamar na bashi. Nasan bindigarsa yake nufi, amma sai na balla masa harara na ɗauke kaina. Dan ya kafeni da muggan idanunsan nan na maguna. Sai dai yanda nake a tsorace yasa a ankare nake karya shammaceni. Ina kuwa ganin ya motsa na sake zabura baya. Ganin kaina yayo na ɗage zan falla da gudu koda cikin bathroom ɗinsa ne tunda ya kulle nan mugun yasa ƙafa ya taɗoni, sai gani zube a saman gadonsa.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_




......Da wani kalar sauri da rawar jiki na motsa zan tashi, zuciyata na wani kalar masifaffen gudu a cikin ƙirjina tamkar zata fito ta baki ya hana hakan ta hanyar ɗora ƙafarsa ɗaya a saman gadon ɗaya a ƙasa ya ranƙwafo yay mun rumfa. Hakan ya saka kammu gwaruwa waje ɗaya saboda na riga na ɗago. Wani azabane ya ratsa min goshina, da sauri na koma tare da dafewa da hannayena duka biyun ina faɗin “Wayyo ALLAH mai kan rodi ya fasan kai na”. Nayi kusan minti ɗaya a haka raɗaɗi na ratsani dan da gaske naji zafi kafin na janye hannun ina ƙoƙarin hana hawayen da suka cika min ido zubowa, bindigar na ciro daga hijjab ɗin na nunasa da ita, cike da masifa na buɗe baki zanyi magana amma a mamakina sai naji bakin ya gagara motsawa, sai rawa lips ɗina kemun kar-kar da motsi a hankali. Dan wani irin masifar jinai ya cika min ko'ina. Hatta ɗakin jina nake a matse matuƙa a cikinsa. Idanuna na rumtse da ƙarfi ina sake wayancewa na maida hannuna saman goshin na dafe, ɗayan kuma dai na nunasa da bindigar. A cikin zuciyata nake jera masa ALLAH ya isa. Jin kamar ana ƙoƙarin saka min abu a jikin tsintsiyar hannuna ya sani saurin ƙoƙarin janye hannun. Bamma san sanda na sake zaburowar ba ganin ya saka min handcuffs. Hannun nai ƙoƙarin fisga shi kuma ya cire key ɗin daya kulle handcuffs ɗin dai-dai nan. Bindigar hannuna ce ta faɗi.
“Malam minene haka kayi?”.
Na faɗa cikin gigita da ruɗewa. Bai tanka min ba, sai ma ƙoƙarin sauke ƙafarsa yake yi, cikin ƙunar rai da rufewar ido na sake buɗe baki zan yi magana tare da kai ɗayan hannuna zan damƙoshi batare dana san mi nake shirin yi ba ya wani kalar juyowa. Farin yatsarsa mai ɗauke da dogon farin farce ƙal-ƙal masu sheƙi ya ɗaura saman pink ɗan ƙaramin lips ɗinsa. “Shiii!!!” ya faɗa yana wani waro min cat eyes ɗinsa masu girma da cikar gashi. A take tsigar jikina tai bala'in tashi. Bamma san sanda nai saurin kauda kaina ba bakin nawa na rufewa bamm batare dana iya furta ko a ba. Ga hannuna da nakai zan riƙosa na tsaye ƙyam, ban sauke ba ban kuma ƙarasa kaisa jikinsa ba, dan sai yanzu nama fahimci taɓargazar da naso yi...
Maash dake bin fuskarta da wani ɗan iskan kallo zuciyarsa na wani masifar hanƙoron mamakinta a cikin ƙirjinsa ya janye idanun ya saukesu akan hannunta. Sake tsuke fuskar yayi, a kausashe ya furta, “Idan wannan small hand ɗin ya sauka jikina You will regret it har wayewar garin yau”. Ya ƙare maganar yana kaɓar da hannun tare da ƙoƙarin ɗaukar bindigar nai saurin ɗaukewa kafin ya kai nasa hannun na tura cikin skirt ɗina.
“Humm” ya faɗa yana wani shanye girman idanunsa da jan sirrin tsaki da yay matukar zafata. Sake rumtse idanuna nayi ina mai sake tsuke fuskata nima, cikin nuna alamar ɓacin rai, batare dana buɗe idanuna ba cike da tsiwa na furta, “ALLAH ma ya tsari ɗiyar Abdul-wahab da taɓa trash body irin naka, jiki duk ta'addanci da jinin mutane ma. Sannan ma ni ba ƴar iska bace dazan taɓa jikin maza. Kuma wlhy ka tashi min a kai tun kafin kai na saka kai regretting ɗin yanzun nan terror kawai an saba bin na hotels”.
Ban gama rufe baki ba naji saukar yatsunsa a saman lips ɗina. Wata irin masifar azaba ce ta ratsani saboda yanda ya haɗesu ya matse a waje guda, tsabar iya mugunta da baƙin hali ya dinga murzawa. Kusan sakan talatin sannan ya daina murzawar tuni idanuna sun cika da ƙwalla. Yayinda ɗayan hannuna ya shiga kai masa duka akan ƙatoton damtsen hannunsa amma mugun ko gezau. A wata sabuwar bazatar da ruɗani da tashin hankali na sake jin saukar hannunsa a saman cikina. Ihu nake son ƙwalawa amma babu dama ya riƙe bakin. Da bala'i-bala'in ƙarfi na gimtse idanuna da ƙanƙame jikina saboda yanda ya damƙi bindigarsa dana tura a wajen tare da fatar shafaffen cikina. Ai da azabar ƙarfi na dunƙule hannuna na buga masa a damtsensa ina fisge kaina amma yaƙi sakin lips ɗin nawa saima sake matsesu yake. Ɗayan hannuna kuma dana dakesa da shi ya sake zuramin wata handcuffs ɗin itama ya ratayo jikin ƙarfen net ɗin da akai kwalliyar gadon da shi, dan ƙarfene a wajen. Fisge-fisge na farayi, amma ko'a jikinsa saima ya ɗakko salataf ya nane min bakin da shi bam. Tashi yay tsaye sosai akan ƙafafunsa, na fahimci hakan ne a dalilin jin iskar ac na ratsani dan rankwafowar da yay ɗazun a kaina koma jinta banayi sam. Idanuna a rumtse suke dan bazan iya kallonsa ba. Fisge-fisgen na cigaba da yi ina uhum-uhum! Na ƙoƙarin yin magana amma ko uhum banji yayi ba. Hakan ya sakani buɗe idanuna kadan, sai na hangosa can ya nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton closet ɗinsa ne saboda labulen da aka saka a wajen fari ne shara-shara kuma ƙofar wajen an yita da girma sosai. Hawaye naji suna ƙoƙarin sakko min, amma nayi ƙoƙarin hana hakan dan bazan taɓa yarda yaga gazawata ba. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito. Cikin ƙananun kaya baƙaƙe yana ƙoƙarin ɗora baƙar jacket milk mai ƙyalli a samansu. Ko kallon inda nake baiyi ba, ya ƙarasa gaban mirror ya fesa turare da ƙara kwantar da kwantaccen gashin fuskarsa dama nakan nasa da ya ɗaure waje guda. Boot takalman daya fiddo baƙaƙe masu ƙyau daga sama ya zauna bakin gadon ta kusa dani ya saka. Matsar da jikina nayi baya ina ƙunƙunin da ba'a ji tunda bakin a rufe yake. Sai da ya gama saka takalminsa batare da ya kallan ba ya miƙa hannu ya ɗauka tray ɗin dana shigo da shi, ƙaramin stool yaja gabansa ya ɗora, hankalinsa kwance ya fara kai fruit ɗin bakinsa a nutse tamkar baya so. Ɗauke idanuna nai daga kansa ina ƙwafar da ba'a ji sosai, amma nasan zai iya yajin shi. Sai dai mugun ko a jikinsa yama ƙi nuna yasan dani. Baifi cokali biyar yayi ba ya ture gefe, tissue ya ɗiba ya goge bakinsa yana miƙewa. Yanzun ma ko kallona baiyi ba ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fita duk da buge-bugen da nake uhhhum-uhhhum ɗin dai bai kulanin ba. Fitarsa da minti baifi biyu ba har na fara hawaye sai gashi an sake buɗe ƙofar. Shegen karen nan nasa ne ya shigo. Shi kuma biye da shi, ya tsaya daga bakin ƙofa idonsa akan karen cikin bada umari yay masa nuni da ni yana faɗin, “Ko yinƙurin cire abinda ke bakinta tayi Laalah ka gutsire lips ɗin na bar maka su ƙyauta”.
Shegen karen kuwa kamar wani mutum ya wani kaɗa bindi yana nufo ta gefen gadon ta inda zai iya ganina ya kwanta ya zubamin ido. Yanzun kama rawa jikina ke min, dan wlhy tsoron makirin karen nan nake ji over. Ya riga ya masa wani azzalumin training da in akace maka yay wani abun saika ɗauka ma ƙarya ne. Wlhy da ace bakina a buɗe yake haƙuri zan bashi, amma ina zalumin ya rufeshi.
A hankali ya tako cike da ƙasaita inda nake, ya ɗan hawo gadon tare da kwanciya yana facing ɗina. Fuskata na kauda. Amma sai ya saka hannunsa ya maidota ta inda yake. Gira ɗaya ya ɗage cikin ƙanƙance idanun da ƙara maida muryarsa low ya furta, “Kwantar da hankalinki kema yau zaki samu abinda nake bama na hotels ɗin, Ba sai kin nuna jealous ba, ke dai kawai jirani na dawo”.
Baki na cije da matuƙar ƙarfi ina jin kamar na shaƙosa amma babu dama. Haka ina ji ina gani ya tashi bayan ya sumbaci gefen fuskata cike da shaƙiyanci ya rufe ƙofar ya fice abinsa. Sai kawai na sake fashewa da kuka dan bani da zaɓin daya wuce hakan.


Hayatu da ƙin fitowar Samraah ta sakashi yawaita kallon ƙofar jin motsi ya sashi ɗagowa. Akan ogan nasa da sam bama shi yake kalloba shi ya zuba su. Sai dai kwarjininsa da cikar haiba ta cika masa idanun, janyewa yay tare da miƙewa cikin nuna girmamawa ya furta, “Barka da fitowa Yaya”.
Kai kawai Maash ɗin ya jinjina masa yana mai cigaba da kalle-kallensa, can kuwa idanun nasa suka sauka akan abinda yake nema wato Laalah. A can ƙasan maƙoshi da silent voice ɗin nan nasa mai fita a daƙile lips ɗin na motsawa da ƙyar ya furta, “Laalah!”. Azabure karen ya miƙe da ga inda yake ya nufosa da gudu-gudu. Bai masa magana ba yay gaba shiko ya bisa. Da kallo Hayatu ya bisu da ga shi har karen ta ƙasan ido. Yana nan tsaye cikin mamaki sai gashi ya sake fitowa dan bai wuce mintuna biyu da wasu sakanni ba. Yanzun ma bai kallesa ba face nufar ƙofa da yay yana faɗin, “Let's go”.
Da sauri Hayatu ya kwashi kayan daya zube a Centre table wanda duk takardu ne yabi bayansa. A maimakon ƙofar baya da sukafi bi yau ta babban falo suka bi. Duk da abin ya ɗan bama Hayatu mamaki sai baice komai ba, dan yasan ogan nasa yakan iya haɗa shekara ma baibi ta babban falon ba da sunan fita a gidan. Sai dai in zaije duba Ummie, ita ɗin ma sashenta na a jikin nashi ne shiyyasa akwai ƙofar da yake bi basai ya fito tanan ɗin ba, dan wannan kullum ne safe da yamma, idan ma ya yini a gidan zai iya zuwa biyar bai gaji ba.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_




.......Babu kowa a falon sai television dake aiki kasancewar dare ya fara duk al'ummar gidan sun shige ciki, hatta uwar dabar gidan Hajiya Mammah da alama yau bata kusa. Dan dama dai itace zaka zo ka iske a falon koda yaushe saboda sa idon masifa da son nuna ita a dole boss ce. Tuni guards ɗinsa da TJ sun gama shirya motocin fita. Fitowar tasa ta sakasu duk miƙewa da barin abinda suke yi. Gaishesa suka shiga yi da girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan yau sosai ƴan miskilancin ne a kusa, ga abinda ya faru tsakaninsa da Samraah yanzu. Da sauri Hayatu ya buɗe masa bayan farar zananniyar motar da TJ ya fiddo, wadda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kuɗi yay aiki wajen sayen ta. Dan sai wani irin sheƙi take da ƙyalli mai ɗaukar ido. Gata nan wata ƴar ƙumbula bata cika hayaniya ba, ba kuma ta cika mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa da ke gara kan kuɗi ta yanda suke so saboda amincewar UBANGIJI garesu. Sai da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads