Showing 1 words to 3000 words out of 30994 words
Chapter 1 - YANCIN MATA Hausa Novels Complete by Maman khairat .txt
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
13/7/2023
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
Marubuciyar :
Namiji k'arin kunama
Zaman takewa
Akula damu
Nida haidar
D'an Adam butulu
Sakayya free book
Halacci ne paid book 200
Aminatu free book 200
Ina mafita paid book 200
Gidan marayu paid book 200
Yancin mata paid book 200
*Zakibiya kudinki ta wannan acc din Amina maaji 4271914014 fcmb**
*Ko katin *mtn ta wannan* *number* *08068748974*
*Jan hankali banyadda wani ko wata su cenzamun labari ko siyi suki buritsi a kan hakan ba wannan babban laifine .wannan labari true life story ne banyishi dan wani ko wataba in labarin yazo dai dai darayuwarki ki tintib'eni ta wannan number 08068748984*
Free page 1/8
Paid book 200
Page 1️⃣⏭️2️⃣
""""""""""""''Fauziyya,kifice mun,daganan tunda ke,a mahaifin nakima sai kinyiwa bak'in ciki dayake ke dangin matsayata ne masununa ,suwani ne.
Anty Halima "bazan tab'a aikata abunda kikeso kiga na aikatashi ba koyaya ne " wai hayaniyar menakeji ne kuwa meke faruwa" fauziyya ce "me fauziyyan tayi kenan gatanan tace inda katurata bazataje ba .
" saboda me? gakai ga,ita ka tambaye ta
Abbana kayafemun zina kukeso na aikata karkuyimun asaran shekarun dana bari a baya kutayani tattalin mallakan hankalina da kuma tinanina wayace miki zina zamuturaki wannan mutumin tunda yabigeki yaketa hidima damu, har aiki yabawa mahaifinki.
"Fauziyya kinsan Allah kiwuce kitafi gun Alhaji Gali dan tund'azu yake tafaman jiranki " ni gaskiya bazanje ba"toh kisani bakida matsuguni a gidan nan sannan abinci an daina baki kisani da kyau.
Inaji inagani Abbana da kanshi yakaini gun Alhaji Gali "Malam zakar Kaine? eh nine dakaina nagode Sosai kasan ba iya aikin zanyi ba kasan yanayin abunne sai a hankali ..
Tayaya kenan bangane batsai iya aikiba shi gurgune ko Mara hannu neda bazai iya aikin nan ba gida ko datti babu.
Ina tsaye Abba dakanshi yakawo mun tsintsiya yace kije kifara sharan ,inna tinada tunsafe banci komaiba har cikina murd'amun yakeyi sai inji duk raina yab'aci nida gidan ubana amma ace bazanyi rayuwa mai yanci ba haka natsaya tinani amma basharan mai kyau nakeyiba dan duk nashiga rud'ani inaganin akabawa Abbana kudin daban San konawa neba yasa,a aljihun riganshi duk abunnan da ,akeyi inata taya jikina karb'an y'ancin tane .
" fauziyya in kingama share d'ayan d'akin kizo kid'auki abun gogewa dan inason rintsawa, kingani tunda nasauk'o cikin garinnan bansamu sukuniba d'akuna ukune a gidan ga gida babba ne amma bashida daraja dan rashin mace ina ganin .
Alhaji Gali yashiga wanka danagama gyara d'aya d'akin nacigaba da gyara sauran bansan yanaciki ba nashiga a she yana band'aki sai jin fitoh warshi nayi yatura k',ofar yasaka key yarufe " dan Allah kabarni zanfita nafasa gyara d'akin daman Alhaji Gali babban mutum ne haka yatureni nafad'a dabaya a she a kan gado nafad'i inagani yamun runfa d'a k'irjin shi" dan Allah karka rabani da mutunci na inada shekara sha takwas kullum acikin kare martabana nake.
Tunbayau ba nakeson ki na zama banaji bana gani duk akanki surorin jikinki sunyimun kamun da sai mutuwa ne zatarabani da shi kiyimun agaji wajen mallakan wannan zumar.
A she kabada kud'i dan mahaifina yasiyar maka da mutuncina bansaniba wannan shine sharan?
Meyasa bakanemi almajiri ba kanemoni. meyasa baka nuna halinka ba a she kai ba,uban kirkibane ",banason musu fauziyya bakiyi kamada matar talaka ba nikadai nasan darajanki nadad'e inaso in kasance dake", ina matarka? Matana, tananan amma kamar karragone adafa babu komai aciki mezan samu " karkashiga gwonan da banaka ba katsaya a naka sai Allah yamaka zab'i irin Wanda yakeyiwa salihan bayi inaji ina gani duk wannan magiyar danayi mishi abun bai wani ratsa jikinshi ba sai da ya ketamun haddi yarabani da abunda nafi k'auna wato martabana magana nakeji sama,sama amma ko k'afata nagagara d'agawa daga inda nake watsa ruwa yaje yayi sannan inagani yajunamun ruwa yayi zafi "fauziyya gimbiya tashi keji kiyi wanka " wannan bashine zaihana auren muda keba "kisani niban aikata zinaba an d'aura mun aure dake tunba yauba nace kar,agaya miki har sai kinkai shekara ashirin a duniya " bazan iya jure kullum ina ganin abuba amma ,a tauyeni gaskiya bazan iyaba.
Ninasan komin k'iyayyar da mahaifina yakeyimun bazai aurar dani ga mutumin da baisan halinshi ba .
Sanin dakikayiwa mahaifinki bana yanzuba kinga yasan darajan aure shiyasa yakawomun ke "yayi kuskure da bai jira natayi mishi magiya ba a k'asar hausa bantab'a jiba yanata surutu amma abunda yadameni ya dameni inagani Yau nine fauziyya na aikata zina kaicu ni yazanyi da tarin zunubin da nad'auka Allah ya,isa tsakanina dakai .
Ficewa nayi daga gidan ina dosan k'ofar gidan mu,naga Abbana yana zaune wajen k'arfe hudu darabi da alamu ba,ajima dayin sallah ba haka nadaure nashiga ina shiga naga meimei tana yanka kayan miya d'aki nawuce nawuce toilet nayi wankan gaskiya nadad'e ina rok'on Allah
" Allah kayafemun kartasa nadiyar mahaifina kasani a wuta Allah natuba kayafeni kaji k'aina Allah ya,isa bazantab'a yafemaka ba mungu azzalumi macuci k'arshenka bazaitab'a zama mai kyau ba .
Duk abunda nakeyi har nakimtsa ko meimei ta lekwo ta,tambayeni haka nagama duk abunda zanyi hawaye sunjik'amun gaban hijabina inacikin kuka saudat tashigo .
"Ke fauziyya meyake damunki tund'azu nazo inata sallama shiru bakomai saudat kigayamun gaskiya meke damunki ?
Shikenan zantafi naje aikene nace barina dubaki dan d'azu nazo akacemun kinje anguwa Abba ya aikeki .eh kawai nacemata saudat tayi mamaki duk yadda mukeda ita amma nak'i fad'amata damuwata har Abba yashigo yanata kirana namik'e kamar in mutu saboda banajin dad'i ga yunwa ga rashin kuzari hmm
Sai ganin meimei nayi a kaina " ke fauziyya meke damunki ne? babu shine kinsameni ina aiki koki kulani? Kiyi hak'uri Anty Halima,wallahi banajin dad'ine shiyasa "kije Abbanki yana kiranki sai naji duk duniya babu Wanda natsana sama da mahaifina shine yajefani cikin garari dakanshi yakaini wuta mai uban zafi Wanda zanhallaka
Haka natashi nafita naje Abbana farine amma abunda yamun yazama gawayi yafishi haske agareni
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
*Jama,a kushaida nasadaukar da wannan littafin gaba d'ayanshi ga aminiyata Aisha Hussaini** jiyallen* *mamma* *Alkairin *Allah* *yakaimiki har inda kike* *ina matukar jidake koda* *mutane* *zasuk'iki* ni* inatare* dake halayyanki *yana burgeni*
*marubuciyar*
*Namiji k'arin kunama*
*Nida haidar*
*Akula damu*
*Sakayya*
*D'an Adam butulu*
*Halacci ne*
*Aminatu*
*Ina mafita*
*Gidan marayu*
*Y'ancin mata*
*Wannan labari zai zagaya ,ko,ina yatab'o kowani waje, dan zakudinga jin salon yana cenzawa kubiyo ni kusha karatu karkusake ayi babuku akwai tarin fad'akarwa da nishad'antarwa a cikin tafiyan*
Paid book 200
Free page 1/8
```A ranan danagama wannan littafi zankarb'i naira d'ari 100 in yawuce kwana biyu d'ari biyu 200 zaku biya kudinku ta wannan asusun Amina* maaji Acc no : 4271914014 Fcmb ,ko shedar biya ta wannan number 08068748984
Ina jinjina agareki qawar amana aminiya y'ar uwata Badi,at Ibrahim Mrs bukhari marubuciyar Gishirin zaman duniya* allah yahad'a fuskokin mu da amana cikin sauri najinjina miki matuk'ar gwargwadon iyawarki mun amince da shawaran juna ke tadabance y'ar gargajiya "jinjinan bangirma agareki .```
Page 3️⃣⏭️4️⃣
Anguwar Jankwano nan ne anguwar mu dake garin potiskum dan duk Wanda, akacemishi potiskum yasan garine daya tara mutane dayawa ga yaruka dayawa sarakai guda biyu na bolawa daban ngizim daban .
Sallama nayi ya amsa " fauziyya kindawo bakicemun komai ba ? Mezan gayamaka Abba sokake nacemaka kakaini inda aka ketamun martabana ko sokake nace maka katurani anyi mun asaran shekarun dana d'auka ina kare martabana .
Bantab'a ganin uba mara Tausayi ba sai kai meyabaka meyazugaka ina sonda kakemun ina, sunan mahaifiyarka dakake ikirari kafi sonta ,kacutar da rayuwata kazalince ni koda duniya zata taru a kaina bazan yafe makaba.
Tsawa yadakamun bansan lokacin danasamu waje nazauna ba."bakida hankali ne ko bakida tinani taya ina matsayin mahaifinki zakidinga jifana da wannan furucin ina iliminki yadosa.
Abba Kaine zanyi maka tambayan nan taya Alhaji Gali yasiyeka,ashe aikin da yasama,maka bada zuciya d'aya ba inkuwa hakane Allah yawadar wannan aikin yaro kamar d'an cikinka amma har yanemi yayi maka wayo "kasani muddin abu yafaru dani zakusha mamaki dan zansa a d'aureku .
Tashi yayi ya gauramun mari ga azabar ciwo ga mari da wanne zanji wannan wani kalan zamanine Wanda iyayen mu abun duniya yarufe musu ido .
Ficewa nayi nakama hanyar fita naji, yace" Fauziyya nikike jifana da kalamai Mara ma,ana kinsan a waye kike fad'an wannan kalman kinsan wannan shine kuskuren dazaki aikata mafi muni ,tunda dai haka kika zab'a muzuba mugani " babu abunda zangani tunda kafita daga sahun mahaifi ka koma mak'iyi na ko sauraron amsar da zaibani banyi ba nafice wajen shiga d'aki har mangaje Anty halima nakeyi .
A ranan ko bacci nagagara da safe haka nafitoh nagama duk abunda zanyi nafice babu Wanda nagayawa wannan maganan hanyar policestation nanufa dake kusa da gidan sarkin bolewa gefen gidan sarki daga b'angaren hannu dama tafiya kad'an zakayi yakaika kwaltan babban asibiti wajen *MADINA*
Nayi Kuwa sa,a wasu sunfitoh wani bawan Allah ne yadakamun tsawa "ke inazaki shiga?
" nakawo k'ara ne "meyafaru? K'aran wa duk a lokaci d'aya yakeyi mun tambayan " k'aran mahaifina nakawo .
Jana gefe yayi "yarinya shekarunki nawa shekarata sha takwas da watanni kingama makaranta ne? nagama a shekarannan k'aranwa kika kawo k'aran mahaifina ,meyayi miki?
" yakaini inda ,akaci zarafina "sajen saifullah yace muje kigaya mana abunda yafaru sannan kigaya mana wani anguwa kike binshi nayi har muka,isa wajen naga police dayawa a wajen bani wani kujera, sukayi nazauna, sai dasuka gama wasu abubuwa sukayimun magana .
" muna jinki daman mahaifina ne yakaini gun wani babban wani attajiri yaketa mun haddina "garin yaya kenan ?
Duk abunda yafaru nagaya musu take sukace inje zasu biyoni nak'i tafiya har sai dawani yace muje tare haka ko tsoro banjiba nakama hanya mukashiga mota .muna zuwa k'ofar gidan mu nanuna gidan nace wannan shine gidan mu take sukahau kwankwasa k'ofar Anty Halima ce tafitoh " lafiya kuwa ?"maigidan muke nema " meyafaru bawajen ki mukazo ba gunsa mukazo ,ganin mutane sunfara taruwa ne,sajen saifullah yahanani fitoh wa daga cikin motar ina gaba .
Anty halima cetayi cikin gida danta gayawa Abbana duk abunda yafaru "menayi yan sanda suke nemana ? Wannan ne sai kafita zakaji ,muje ransa a b'ace yafito daga cikin gidan kowani, tambayan shi basuyiba suka saka shi ,a mota mukawuce ina gaba yana baya yakifa kanshi dan bayason mutane Susan meke faruwa.
Mutane dayawa sunata surutu Iliya mai rake yagagara zuwa k'ofar gidan mu dan abun sai yaji babu dadi .
Saudat tashiga rud'ani gurin Iliya tayi" meyafaru naga antafi da Abban fauziyya ? "Saudat kezan tambaya banida masaniya nima ganinsu nayi ,toh ikon Allah amma bazan,iya zamaba dan Allah kijiremun wannan ko kuma kikira fahad k'anin ki zanbisu " amma bakasan wani station sukaje ba .
Karki damu saudat zanje akan fauziyya zan,iyayin komai dan in fitar da mahaifina kiduba irin soyayyar da sukeyiwa junan Ku ,ina fauziyyan take ?"ancemun tafita
Fita !kuma fita kuma!! eh tunsafe dan Anty Halima batasan inda tajeba kekensa, yad'auka yahau Wanda bashida masaniya akan inda akakai Abban fauziya .
A lokacin da muka,iso anhanani fita inagani a kasaka Abba agaba suka shige sai tambaya yake "menayi kuka kawoni babu wani bincike haka ake aikin ne?
Kabari muje zakaji komai ,saifullah ne yace muje nasauk'o nanufi cikin office d'in bayan Abba yazauna sai ganinan nashigo" daman kece kikakawo ninan lalle Fauziyya kinnuna mun ban,isa dakeba .
Tsawa akadaka mishi yayi shiru "yarka ce take k'aranka akan kakaita anyi mata fyade " nikuma "wannan ba gaskiya bane nadai kaita gun ubangidana akan tatayashi aiki dan bashida kowa anan garin " toh jiya yayi mata fyade kuma Kaine sila "ya tsakanin Ku dashi Allah ne yahad'amu" yataimakeni yabani aiki dan a lokacin dako nake a kasuwa nad'auki kayan wani shine buhun shinkafa yab'ata yace sai nabiya muna cikin haka shine yabiya shinkafar nikuma ya sallameni a she anguwarmu d'aya ...
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
*Y'ANCIN MATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
Paid book 200
Free page 1/8
🅿️4️⃣⏭️5️⃣
*Zakubiya kudinku ta asusun nan Amina maaji acc no 4271924014 Fcmb ko katin mtn ta wannan number 08068748984*
Bansaniba watarana nafitoh zanje masallaci a she yaganeni ya tsaya mukawuce sallah dashi har muka fitoh tare "a anguwan nan kakene? eh bamuda nisa da masallaci gacen gidana .
Nak'arayimishi godiya gameda taimakamun dayayi bakomai har dubu biyu yabani ,a lokacin banida komai yataimakemu Sosai" bawai muntambayeka ka dinga bamu wani labari ba ,abunda y'arka tafad'a gaskiya ne ?"banida masaniya da wannan abunda nasani"Alhaji Gali ba mazauni bane yacemun yanason in cewa fauziyya tayimishi shara ,nagayamata tak'izuwa shine nakaita nibansan yamata fyad'e ba .yamata fyade yanzu zamusa a je a bincika mana,ita dan abubuwan sutafi yadda akeso "ina hankalin ka yatafine.?
Mutumin da ba muharramin taba tayazakace sai taje tayi mishi shara, anhada nida wata police tarakani suntabbatar da fyade ne dan yanayina zaka gani kagane inacikin rud'ani har HIV sai dasuka gwada komai Abbana a gark'ame yake fitoh wa,dashi akayi lokacin da mukadawo ,ina isowa nacikaro da Iliya " fauziyya daman kema kunsamu labarin y'an sandan dasukazo kama Abba?
Banso Iliya yabiyoni ba danna san irin damuwa dani dayayi zai bar komai dan yafaranta mun .
"banida bakin yin shiru dole nace" mekazoyi ne ?
Haba Fauziyya yakikeyimun wani tambaya "sajen Saifullah neyace yabar wajen " mukuma nashige.
Anje neman Alhaji Gali bayanan yatafi Jos in katsare Abbana bazai, tab'a sanin inane garinsu ba kawai yadda ne irin na d'an Adam .
Babu komai a fuskan Abba na sai tsanata dan yanayin shi zakagani kasan zai iya kasheni ma akwai maganganu a bakinshi amma takaicin kawoshi policestation danayi yagagara magana sai hawaye danake zubarwa .
"Yanzu kai abunda zamuce maka munbaku nan da wata uku duk inda wannan mutumin yake muna buqatan shi sannan yace mata yabaka sadakin ta har andaura aurenta dashi amma yace sai tacika shekara ashirin a duniya ? " hakane ko inaso inga Abbana yayi magana amma yakasa sallamar mu,akayi tare dayimishi gargad'i
Duk abunnan Iliya yana kusa da wajen har mukafitoh yana tsaye "da sauri ya k'arisa gun Abbana " meyafaru ,sukayi maka cin mutuncin nan Abba?
Ko kallo bamu,isheshi ba"kisani karki yadda kitaka koda anguwan nan muddin kikataka toh nida hannuna zan kasheki.
Mashin yatare yahau sukawuce ambarni da Iliya dayaketa mamaki meyafaru.
Anty Halima
Tun lokacin da akazo akawuce da Abba mutane dayawa sunzo jajanta mata amma burinta taga Fauziyya suna cikin magana Abba yashigo bai tsaya ko,ina ba sai d'akin shi "lafiya kuwa? eh bakomai " karkusake kushigo mun da Fauziyya gidan nan muddin kunason lafiyan Ku"meyafaru"k'arata tayi wai naturata yamata fyade "fyade kuma!! Fyade!!
Tabbas haka ne" amma taya bazata bari mu shirya komai acikin hankali ko mukashe wannan magana ba "kad'auki son duniya kad'aurawa Fauziyya ga,irinta nan kad'an kagani .
Bandamu da gargad'in da Abbana yayimun ba haka nashige cikin d'aki Anty Halima sai kallona takeyi dan kitchen nanufa nad'ebi abinci naci inacikin ci naji anrufeni da duka ta,ko,ina yana dukana Anty Halima nayi
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji maman Khairat)
*Zakibiya kud'inki ta wannan acc no Amina maaji 4271914014 FCMB ko katin Mtn na dari biyu zakibiya kisha karatu*
*Kwana biyu tsakanin gama Free page zakibiya d'ari d'aya batare da kinsha wahala ba in yawuce kwana biyu yadawo d'ari biyu*
Paid book 200
Free page1/8
🅿️7️⃣⏭️8️⃣
Kificemun daganan yarinyar dabata kirkiba harke wuyanki yayi kaurin dazaki toh namun asiri "toh kisani bani bake " in banda asara ma,mezaiyi dake mutum duk kud'i ya zauna mishi asararriya duka ,da yakemun babu Wanda yakarb'eni dan tsakanin k'ofar gidan muda cikin gida da nisa Sosai kuwa "kinyi asara Fauziyya k'aran mahaifinki " dayake ba a y'arki akayiwa fyade bako karki manta yaranki suma suna wani wajen yadda kikahanani samun sukuni kema haka za,ayi wayaranki .
Dafe zuciyarshi Abba yayi zankai hannu in taimakeshi naji ya gauramun mari da sai danaga taurari "zanbarki ki zauna a gidan amma kisani abinci sai dai kiyi aikin k'arfi kisamu amma nikam badaniba kisani .
Innace dukan bai shigeni ba nayi k'arya r dan dukane irin namutanan da ko,ina duka akeyi
" Halima ki tattaromun kayan Fauziyya duka tabarmun gida "hak'uri zakayi yakike bani hak'uri sai kace bakida zuciya " karkayi haka duniya zata zagemu kaduba mutane dayawa basusan meyake faruwa ba karkayi kusan wauta mana .
Tinawa da wani saurayina nayi da Abbana yadauki yadda yabashi in yazo guna sai yakusan tab'a jikina ,a lokacin daya yaudari Abba ma,aikacin NEPA ne yacewa Abba zaibashi kudi yayi jari yasiyi magani har gun aikinsu nabishi yayiwa Abbana alkawari na dubu goma muna cikin haka yace inzo in huta a she d'akin wani abokinshi yakaini inata zama bayan yatab'a wasu abubuwa dake jikina aka,kirashi yace zaidawo dawowar da baiyiba inata zama cen abokinshi yashigo naga sai tab'amun jiki yakeyi so yake yayi fasikanci dani na kwad'a mishi mari nan ma nazo in gayamishi abunda yafaru ko,ajikin Abba da bashine yahaifeniba zance ni y'ar tsintuwace .
Ya Abba zaiyimun haka amma bakomai "kintsaya kinata kallona bazaki barmun gida bako,zanyi maganin ki " Halima kisani ko guntun tuwo kikabawa Fauziyya banyafemiki ba .
Babu ko tausayi gaskiya Anty Halima kamar ba mace ba ko kishi magana ake akan fyade amma son zuciyarsu yarufe musu ido amma bakomai tun tashina ban San waye mahaifiya taba. amma inason duk indatake tadinga tinawa dani tunda ance kurciya akayi mata amma bansan yaushe zanzama inada gata,a duniya ba gidan Su Saudat sunfimu wadata nesa bakusaba ban saniba ko zangaya mata musan meyene mafita.
Naci kukana dayawa Saboda takaici har dare yayi ko abinci babu Wanda yamun tayi ga yunwa kamar zanci babu fita nayi Iliya yanagun rakenshi nan wajen har kunu ake siyarwa "Fauziyya yadai ?" Inaso insha rakene bari in yanka miki zankuma sha kunu kasancewar daminace yunwa tana yawan damun jama,a kunu dayawa yasiyamun nasaka sugar har gyad'a yasiyamun ..
A zaure nashanye kunun nadawo"ke Fauziyya nafuskanci tunda kikasan maza shikenan mukuma munshiga uku,ina kikaje ne da dare takwas fa yayi "naje gidan Su Saudat ne " kinje gun masu kulli dai dai susuke zugaku bayan uwarki tsallakeki tayi tagudu karuwancin ta shine kikabiyo halinta ana hangamiki, abu mai kyau kekuma rake kike sokisha ko zakigane .
Duk wannan surutun ko jinshi banayi dan Iliya yafimun kowa a Anguwan in kacire Saudat.
Wucewa d'aki nayi nabarta washe gari bayan nagama aikina gidan Su Saudat nanufa "Fauziyya jiya ina kikaje akazo aka tafi da Abba " mubar maganan akwai abun karine ?dan yunwa nakeji ...
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji maman Khairat
Kai tsaye Ku tuntub'eni
08068748984
🅿️1️⃣1️⃣⏭️1️⃣2️⃣
"Rabi,atu kinyi bacci ne ? " nayi bacci mama kindawo ?nadawo kizubomun abincin inci kinkarb'i kudi' kinsiyo barkwano da maggi nasiyo bacci nakeji