Showing 3001 words to 6000 words out of 30994 words
Chapter 2 - YANCIN MATA Hausa Novels Complete by Maman khairat .txt
haka nadaure,nazubo abincin taci ko sallah batayi ba dan mahaifiya ta sallah bai dameta ba adashe da yawan yawo shine yadameta nasan bata duba mahaifina ba dan wataran sai yayi k'wana biyu basuga juna ba dan mahaifina shine kezuwa sugaisa batare da ya ji shine a sama da,ita ba.muddin mamace zata koyamun yadda zanyi biyayya tabbas wuta zanshiga
Ko bacci nagagara yi sai kusan asuba bacci yayi awun gaba dani namakara sallah dan naji dad'in alluran da,akayi mun Sosai .
K'arfe bakwai 7am Mama tafitoh tanemamun abunda zanci har kunu tasiyomun nasha amma ina tina me mahaifina yaci yanzu "Rabi,atu kishirya yaufa sau biyu zakifita talle dan inason in fara zubin wani adashen ." Mama kibari infitah da yamma kinga zaifi babu wannan zancen "zanyi wanki a Babane kiji wani shisshigi meyasa zakice zakiyi mishi wanki shi kuturu ne ? haba mama .
Duk yadda naso kar,inje Talle amma mama takafe .
Baba kabari inna dawo sai inyi maka wankin tunda mama tace bazatayi ba komeye dalili " Rabi,atu karki damu kinji kije Tallenki sai kindawo ki,kula da tarbiyarki karfa ki yadda jama,a suyi miki wayo kinji Toh nagode Abba .
Amma !Amma!! Amma !!
"Karkice komai kinji kije nima zanfita ana kawo kaya zamuje musauk'ar zanfita Allah yamuku jagora Amin ya rabbi ..
FAUZIYYA
Shiru nayi hawaye masu zafine suka fitoh daga k'wayar ido na "wai mahaifina ya kawoni in daza,a salwantar min da rayuwata ya ruguzamun Farin cikina shine sanadin fyade'n da a,kayimun amma yanuna kud'i da a bun duniya sunfi ,ni mahaimmanci agareshi rayuwa kenan .
Awa biyu tsakani naga yafara motsi har yabud'e ido " ki lalumomin wayata kibani in kira likitana dake kusa dan zan,iya mutuwa sannan ga key kisamu ki fice daga gidan nan dan y'an sanda karsuyi zarginki " mungu banida fargaban koya yasan halin danake ciki dan wani daraja nake karewa yanzu "bamuda lokaci kinji amma dan Allah kitaimakeni kibani wayata sannan kid'an kimtsa wajen banason a samu matsala.
Zuciya ta tabushe bandamu da duk wani abunda zai fad'aba ko Tausayi banjiba na nemi key nabude na fice nadawo gida .
Anty Halima " ina Abbana ?,zaki tambaye ni kinbani ajiyan shine kiduba yana d'aki "Abba gacen Alhaji Gali nafasa mushi kai yana cikin jini ko motsi bayayi kaje ka ,taimakeshi amma komai zai,iya komawa kanka.
" na shiga uku yanzu Fauziyya shine zaki kashe mutum amma ko,imani babu "a she nima zaki,iya kasheni wannan yarinyan Allah yamiki abunda kikeyimun
Duk yarikice samun Anty Halima yayi " kiduba yarinyan nan takashe Alhaji Gali.
Wani Alhaji Gali? "Ke Halima banason maganan banza ,inaganin Abbana yazube ,a k'asa saboda takaicin da yafaru ..✍🏿
Ina matuk'ar Alfahari da marubuta
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
*Y'ANCIN MATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
*Kibiya kud'i kisha karatu a kan d'ari biyu kacal* *zakibiya kudi tawannan* *Asusun Amina maaji*
*Acc no 4271914014* *Fcmb ko katin mtn ta wannan Number 08968748984*
Paid book 200
🅿️9️⃣⏭️1️⃣0️⃣
"Akwai kunu da taliya muje kizubamun " nifa gaskiya Fauziyya kincenza jiya kad'ai a yadda nasanki nasan kinsan darajan manya dasanin danamiki kenan .ko kulata banyiba nawuce cikin gida muka gaisa da ummin ta nashige d'akin da,a kaware dan Saudat ina zaune ina tinanin yadda Alhaji Gali yamurdeni ya aikata alfasha a kaina wannan rayuwar abun dubawane inason inyi maganin mahaifina ko tahalin yayane dan yazama,izina ga masu sa,yaransu su,aikata ba dai dai ba.
Har Saudat takawomun komai naci nak'oshi nadad'e inata tinani har bacci ya kwasheni sai kusan sha biyun rana natashi daga bacci ganin babu Saudat a d'akin nafice da sauri "ummin Fauziyya " har kintashi eh natashi ummi "daman inaso muyi magana tsugunawa nayi "
Fauziyya inason kigayamun dalilin dayasa ,lokacin da y'an sanda sukazo tafiya da mahaifinki bake nan ina kikaje? Karki boyemun komai dakeda Saudat duk d'aya ne nasan yadda muke qawance da Nafisa watoh mahaifiyarki bazata tab'a barin yarana batare da ta tsawatar musu ba ,kigayamun "kuyi hak'uri Ummi bansan meyayiba nidai ina shigowa anguwarnan a kacemun y'an sanda suntafi dashi kinji kenan " karkiyimun k'arya dan jiya naje zanshiga gidanku naji Abbanki yana ,cewa kibar mishi gidanshi anyi haka "eh anyi haka Sosai makuwa matsala mukasamu kinsan halin Anty Halima .kigayamun babu Wanda zaiji babu komai toh Allah dai yarufa asiri amin ,in har kinada damuwa kidinga zuwa kina gayamun kinji kitsaya kici abinci kodai in angama Saudat takawo miki eh takawomun karkuma in dad'e tad'auka dawani manufa .
Ina fitoh wa Iliya ne yamun magana " Fauziyya akwai abunda yakefaruwa duk dabanason kisan kome yake faruwa amma yanada kyau kigayamun ko da shawara ce sai in baki koya kikagani babu komai karfa kasaka komai a ranka "zansaka da Abbanki yana karb'an gaisuwana amma yanzu nagaishe shi yaki amsawa ko kulani baiyi ba karkadamu kaci gaba da gaishe shi haka nabarshi a gun nayi tafiyata ko k'ara jin muryanshi banaso nagama kamar sauri yakeyi zaiwuce sabon tasha yasaro Rake .
*Anty Halima*
Ina shiga tahau bala,i" ke zonan inakikaje tund'azu nake nemanki wato tunda Alhaji Gali yamaidaki mutum shiyasa kikafara bin maza kodai yauma cend'in kikaje dan nasan abun da uwa tatafiyi kenan
Dan Allah kidaina aibata mahaifiyata da wannan k'azamin hanya wallahi batada masaniya sannan bakisan kotana raye kobatanan ba yakamata kisan da wannan in sha Allahu zankare Y'ancin mata ,a ko,ina babu abunda zai sameni Sharri kuma zaikoma gareki .wataran sai nagayawa Anty Halima magana nakesamun Sauk'i d'akinmu d'aya da ita ciki da parlour ne bandamu da duk wani abunda zatafad'aba .
Alhaji Gali
Malam zakar naji kace kana nemana meyafaru "Fauziyya ce takai k'arana wai kacemata kabada sadakin ta eh nine nagaya mata dan nagaji da irin abubuwan da kaketa wani k'unbiya k'unbiya " kace mubari takai shekara a shirin "nafasa sannan in kaga dama kace tatare dan komai inadashi basai kakawota da komai ba " zanbaka abunda za,adafa tatare bakomai amma sai nagayayi wuri da maganan auren Fauziyya "nidai nagama magana shine kawai abunda zancemaka kasani " menayi y'an sanda suke nemana "daman akan maganan ne sunyi mata gwaji sunce fyade akayi mata " tayazakace haka aurenta nayifa kaida kanka a gidan nan ka auramun ita har da shedu amma suce fyade ka amince "kayi hakuri bansan ranka ya baciba " bakomai jeka sannan katuromun ita zamuyi magana jiki a sanyaye Abba yabar gidan yara sukabishi da buhun shin kafa inaganin Abbana yashigo ko mun magana baiyi ba dadane zaicemun "Fauziyya baki ga Abbanki bane yanzukuwa ko kallon banza ban ,ishe shiba" ki shirya Alhaji Gali yana kiranki in kuwa bazakije ba,ga Antyn ki tarakaki "haba Abba mekazamar dani sokake naje ya k'ara aikata abunda yaga dama dani kenan babu inda zanje " nikike gayawa haka ko shikenan tashi muwuce fuskar Abba ko fara,a babu yakama hannuna mukaje ina shiga na zafgamishi harara ina tsaye "zaka,iya tafiya malam zakar Abba ko tausayina baijiba ko d'igon imani babu baya tinanin za,aci zarafina yatafi zuciyarshi fari yanafita Alhaji Gali ya matso " haba bebyna meyasa kikakai k'arana meyafaru "mungu azzalumi macuci k'arshenka bazai tab'a kyau ba tunda kazamar min da uba *kawali* kasani zakayi nadama ko kunya baiji ba yakamoni ya wargani kan gado nanne nayi ido hudu dawata kwalba na fasamishi a kai har sau biyu sai ganin jini nayi yanata malala ,ko ajikina dan nasan banyi nadaman hakan ba gashi duk k'ofofin a rufe komawa gefenayi na zauna dan duk duniya in kace in nuna makiyina Abbana zanfara nunawa kafun Alhaji Gali..
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
Ku tuntub'eni ta wannan Number 08068748984
Paid book 200
🅿️1️⃣3️⃣⏭️1️⃣4️⃣
Fauziyya kinkasheni da raina yazakiyi mun haka ,akan wani dalili "Halima tun farko nace kibani abu in mangare yarinyan nan kinki .
" ni yanzu ba surutu zakayiba katashi kaje kaduba koyaya ne in kuwa kasheshi tayi wallahi guduwa zanyi in barku karku shafamun kashin kaza. "Halima kitayar dani in dubo, kokizo kirakani dan Allah ,taya zakace in rakaka haka zakaje kaduba ,inaganin ya mik'e yada'u hulanshi yatafi kodamuwa banyi ba,shigewa d'aki nayi cen nafitoh nawuce gidan Su Saudat " Fauziya meyasa yanzu bake yawan zama ,a gida naje Anty Halima tace kinje yawon dandi mekenan ",kekuwa ina zansan wannan abun amma bari na tambayi ummi ko tasani ", ummi menene dandi ?" Iskanci oh yanzu daman abunda Anty Halima tafad'a kenan gaskiya "Ummi zamuyi magana amma inason kuzamemun sheda toh muna jinki Fauziyya meke tafe dake" akwai wani attajiri a anguwan nan sunan shi Alhaji gali wajen kantudu yake duk abunda yafaru nagaya mata har k'aranshi danakai komai nagaya mata ,hawaye masu, zafi ne suke zubamun a idona har nagama basu labarin "
Kinga jarabawa a rayuwarki yanzu duk wannan abun mahaifinki ne yajefaki cikin uku ba ya tarwatsa duk wani farin cikinki ya rabaki da martabar ki, lalle biri yayi kama da mutum .
Amma yanzu ina Abban naki yake yafita "kiyi hak'uri karki kuskura kice zakiji tsoron su harsu nemi d'auraki a kan keken b'era kinji sannan gobe kizo muje Asibiti a duba lafiyanki kar kuma ciki yashiga bamu sani ba " Ummi wani ciki kuma bayan sau d'aya ne ,koma yaya ne
Alhaji Gali
Malam Zakar meyafaru naga kadawo "nazone in baka hak'uri Fauziyya bata kyauta munba ko kad'an " metace maka? aa karka damu yanzu natashi na kimtsa wajen kar likita yazo ,amma batada laifi fad'uwa nayi shiyasa "amma wannan wani zafin fad'uwa ne sai jin sallamar Doctor khamal bayan sungaisa " lafiya kuwa?
"Babu komai Fad'uwa nayi yanzu " kai sannu dole zamuyi d'inki gashi banzo da abun d'inkin ba "karka damu bari malam zakar yasuyoma, na ,karubuta mishi . da sauri a karubutawa Abba yaje yasiyo d'inki akayi mishi mai kyau ya sallami Doctor khamal " malam Zakar kaje gida babu komai nima yanzu zanfita amma ga wannan kayan kaje kawanke kata, sawa dan jini ya b'atashi nikuwa basake sawa zanyi ba. karka damu a gaishe da Fauziyya ..
RABI,ATU
Nafita talle nabiya shagon allurana a kayimun nak'ara shan magani Abdul nagani yanata biyoni Rabi,atu ya jikin da Sauk'i ya Abdul "nata jiranki baki fitoh ba nace lafiya kuwa " yanzu nafitoh "karki damu wannan agun mahaifiyarki kike nikuma da nawa mahaifiyar tunda tahaifeni tarasu ,Allah sarki Allah yamata rahama Amin ya rabbi " zankoma gida dan karta nemeni tace kar,in kai mangari ba ,"kije kigaishe da mutanan gida ga wannan "ya Abdul nagode Sosai baka gajiya,ya zangaji kefa ta dabance dubu biyu nayi Dan wani yasiyi gyada sannan akwai sauran cenjinshi d'ari yace yabar mun nahad'a da d'ari biyar din nasaka a bakin zanina ,lokacin da na,iso ganin mota ne a tsaye a k'ofar gidan mu naci burki " gaisawa mukayi mawuce , "ga yartawa wannan ce eh itace yanzu kishigemun gaba ina sonta dubu talatin yabawa mama amma tadawo tanamun tijara
Fauziyya kinyi kusan daina tellen ma," saboda me mama? wannan mutumin sonki yakeyi shiyasa amma wannan Rusheshen mutumin ina zankai shi ne, yadda yacemun aurenki zaiyi "aure kuma gaskiya ban yadda ba taya daga had'u wanku zakice kinbada ni haba mama," ki matsamun yanzu yan adashe zasuzo nikuma wanna dubu talatin din zanje Yau muci dad'i gyalen ta tadauka tawuce cen naganta da kaya dayawa,anshigo dashi,murhu bibbiyu tahad'a cikin minti kadan tayi komai cen sai ga Babana "sannu da dawowa baba yauwa Rabi,atu Rabi,u yana gaisheki munyi waya,
Inaganin mama tazubawa Baba abinci yaci tare da santi" kodai Yau and'au a dashe "kai dai bakaci arziki ba kajira kawai.
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji maman Khairat
Zakibiya dari biyu ta wannan acc din Amina maaji 4271914014 FCMB ko katin mtn 08068748984
Paid book 200
🅿️1️⃣5️⃣⏭️1️⃣6️⃣
"Taya zakice inci zan tambaya tunda ban nemoba yazama dole in tambaya "kabari zuwa gobe zangaya maka. " kigaya mun zaifi banason cin kayan daba ta hanyar arziki a kasame shi ba .
"Yanzu zargi nakakeyi ?" Taya zan zargeki bayan tun farko ba zargi ne yahad'amu ba .bake d'auka na a matsayin miji ,agareki nida bola duk d'aya muke agareki kiji tsoron mahaliccin ki shi talauci ba wasa bane sanin kanki, ba,a haka nataso ba kinsan koni waye a cikin dangi ne.
Meyakawa zancen nan da duk lokacin da zakayi magana sai kanemi ka takuramun kodai kayimun gori ?"banayi miki gori saboda haramun ne ,bazan gaji da sanin inda kikasamu kud'i ba yanzu dubu goma Rabi,u yaturama na zanfita inyi mana cefene saboda muhuta k'wana biyu"lalle yaron nan wato shine nibazai turamun ba sai ubanshi ko ,kinyi gaggawa "bayan kudin siyan abinci yabaki dubu uku nawama haka na Rabi,atu dubu d'aya yabata gasunan anciromun zanbaku " garakam bani in k'ara jari zaifimun dubu ukun yabata tabar wajen ina bacci Mama tatasheni
"Ke Rabi,atu kitashi kinsan wannan Alhaji Yusuf d'in dakika ganmu tare? bansan shiba toh yazo neman auren kine yace sunrabu da matarshi, shikuma yaci alwashi bazai tab'a auren y'ar boko ba gara yanemi y'ar datasan darajan mutane yace a gunki yakesiyan goro " nikuma mama toh sai mekenan ? auren kizaiyi a NASARAWA yake yamun bayani yaransa uku matansa Biyar biyu basu haihuba suka rabu "amma shine yazagayo in zama tashida kenan? eh kizama tashida ..
Nikuma nace na amince har yabani dubu talatin yanzu gashi naje, nayi cefene ga dubu uku kisayi hoda da abinda bakida shi ,juyawa nayi nayi bacci na, inaji tana magana " in mutuwa zakiyi keda mahaifinki sai dai Ku mutu amma aure yace nan da sati biyu za,ayi shi banzaye kawai tun farko nace muku keba matar talaka bane baki yadda bako ,
Ina tashi gidan su Binta nawuce mungaisa da Innar ta tace mun gatacen a kitchen "lafiya Rabi,atu da sassafe ?" Kibari Bintu kinsan Mama ce abunda mama tagayamun shina gayawa Bintu Jan hannuna tayi "kitashi muje gun Inna tabaki shawara dan ita uwa ce agaremu duk kan mu .
Tsugunawa duk kanmu mukayi " meyafaru Inna kinji Mama ce keson aurar dani ga wani gardin mutum dan taga yanada kud'i matansa biyar duk yasakesu "tab babban magana " kiyi hak'uri kici gaba dagayawa Allah dan lamarin Mamanki sai addu,a dalilin gayamata gaskiya yanzu bata huld'a dani "kiyi mata biyayya karki kuskura ki d'aga murya har tamiki mummunan addu,a kinji ko kiyi hak'uri" Babanki yasani ne? "bansani ba tunda Inna tafara magana hawaye kezuba daga ido na nafisan karatu da aure inna zama wani abu sai inyi auren amma primary nagama banci gababa saboda talauci shekaruna sha bakwai ko sha takwas ban kaiba " kiyi hak'uri kije kita gayawa Allah zai yimiki maganin komai har bakin k'ofa Bintu tarakoni ,ina zuwa naga motar Alhaji Yusuf a k'ofar gidan mu dan haushi bansan baya cikin motar bama hararan motar, nayi ,ashe yanacen gun Baba sai jin Baba nayi yana cewa "nifa bazanbaka Rabi,atu ba dan batakai inyi mata aure ba shekarunta sha bakwai ne a duniya sannan matanka biyar kibi kadawo da biyu amma Rabi,atu bazan tab'a mai da,ita k'aramar bazaura ba kasani da kyau.
" Baba kayi hak'uri zan rik'eta da mahimmanci bazan yimata komai ba har sai takai shekara ashirin kafun ko sha tara "koma meye ne nagama magana duk da inacikin talauci amma bazan tab'a sai da d'iyar dana Haifa ba .
Mama
" bari kaji musa bazan lamunci irin wannan ba aure ne koda zanyi yawo tsirara sai nayima Rabi,atu aure da Alhaji Yusuf in ba mugunta irin nakaba ka,kafe wanna y'ar taka kakeyiwa bak'in ciki kayi asara ,tashi Alhaji muje mugama maganar mu zaifi mana.
Ina ganin suka fita ko kallon arziki basu samu daga gareni ba ikon Allah wannan wani irin jarabawa ne ..
FAUZIYYA
Ganin Abbana dakaya,a hannu yashigo "Halima ga kayannan ki wanke mun kinga yadda yarinyan nan tafasawa Alhaji Gali kai kuwa ,in bamai sonka ba waye zaice a bar wannan maganan kiduba buhun shinkafa daya bamu sannan duk wani hidima yimana yakeyi yarinya sai ,hassada batada wani aiki"batun farko Kaine kake goye mata baya ba ,in bahaka ba taya yarinya ka haifeta tafi k'arfin ka " kibarta zanyi maganin ta tunda mutane ne suke zugata da shegen yaron nan mai sai da rake sai da sukayi bacci naje na debi abinci naci dayawa shinkafar da taliyan shima nad'iba kwana biyu naje na boye, .
Washe gari
Policetetion nanufa ina zuwa sajen Saifullah yagane ni "Fauziyya kece? eh mekuma yafaru?" Alhaji Gali yadawo banji kunkirani ba inatasa,ido "yazo nan yanuna ya aureki yabada sadaki sannan sunbada sheda ankawo mutane uku da suka halicci d'aura auren sunzo sunbada sheda"karya ne babu Wanda ya d'aura mun aure sunyi abun son ransu sunbada cin hanci an cutar dani anzalince li Allah yabimun hakkina.
Na dauka kai na Allah ne kanagun aka cutar dani na d'auka nasamu yaya a she kaima d'an sanda bogi ne macuci wallahi kuji tsoron Allah .
Jana gefe yayi " kiyi hak'uri duk yadda kika d'auka ba haka bane lokacin da sukazo dan zalinci aike na akayi waje mai nisa bandawo ba sai da suka kusan gamawa na tabbata akwai abu, a k'asa karki damu nasaka wayata k'arama acikin rigar sanyina na kunna recording nasan na,ajiye komai sannan nayi saved amma bantab'a sauraro ba Ranan asabar zan kwatanta miki gidana kizo muji tare harda matana da mamana dan suzama sheda.
Yanzu kitafi zanrubuta sai in fitoh in baki a rubuce kin,iya karatu ?eh na,iya jirani ina,zuwa...
[8/28, 19:49] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
Y'ANCIN MATA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
Ku tuntub'eni ta wannan Number 08068748984
1️⃣7️⃣⏭️1️⃣8️⃣
POTISKUM LOKAL GOVERNMENT
Da sauri sajen saifullah yaje ya rubuta yakawo mun nayi godiya Sosai nawuce har da Number waya a jikin takaddan ,a hanya nata mamakin mutane daya wa, basuda amana kokad'an .
Ina isowa nahad'u da Iliya"ina kikaje naganki haka ?"naje anguwa ne "meke faruwa ne duk kinwani lalacewa ko fara,ar dana sanki dashi babu kodai akwai wani abu ne?
" babu komai Iliya taya zan manta dakai kawai banajin dad'in garin ne shiyasa sannan ina cikin rud'ani dayawa gaskiya ina buk'atan addu,ar ka dan Allah .
"Babu komai Fauziyya nidaman kullum in ganki cikin fara,a shine damuwa ta,kinyi mun alkawarin aure kirfa ki cenza ra,ayi
Muyita addu,a Allah yamana zab"in abunda yafi zama alkairi amin " kitsaya kitafi da rake tunda na yanka karkuma kik'i karb'a dan Allah "daka barshi zaifi komai amma kawo nagode,duk yadda nakeson Iliya saboda nutsuwar shi tun, lokacin da Alhaji Gali yarabani da Marta ba na sai naji komai yafice mun ,daman abunda mace ke tattalin shi kenan natsaya