Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 28227 words

Chapter 1 - Matar Bahaushe by Mrs.Basakkwace.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

414

Ads at the middle of Article

MATAR BAHAUSHE
Writing by
MRS Basakkwace




















*NA MARUBUCIYAR*
*SAMHA*
*KISHIYA CE*
*ƳAR MACE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
*ND KNOW*
*SURUKAR ZAMANI ND* *MATAR BAHAUSHE*








GMAILS
*KHADEE241@GMAIL.COM*
OR
*MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*






*SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU*:-
*HAJIYA HAFSAT MUNNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO(MOMYN IMAN ƊAN IYA)*




DEDICATED TO *KHADEEJATOU S DOGARI*








*SHAFI NA ƊAYA*




*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI*








A gajiye yake tafiya kallo ɗaya zaka mai ka tabbatar da cewa ba ƙaramin talaka bane saide ƙarfin imani da ƙarfin zuciya yahana shi ciwon zuciya ko hawan jini ya kama shi dattijo ne ɗan kimanin shekara saba'in da wani abu zuwa tamanin dogo ne bai da jiki da kagan shi kaga ƙiran fulani yana da farin gemu saida yayi tafiya mai nisa kafin ya iso wani ɗan ra kwarkwaɓaɓɓen gida a dai dai ƙofar gidan gaban shi ya yanke ya faɗi sai da ya tsaya yaja dogon numfashi ,don yasan yau ko shakka babu in Talatu ta fara mai masifa baisan inda zai sa kan shi ba don biyar bashi maganin ta yayi yawo bai samu dakon da zai samu abin kashewa ba ƙarfin zuciyar shi da kullum bata karaya ita tasa ya faɗa gidan bakin shi ɗauke da sallama(HAKAN YASANI SAURIN BINSHI INGA WACE WAINAR ZA'A TOYA A GIDAN),wata dattijuwa na hango zaune wacce bazata gaza shekara hamsin ba fara je mai ɗan jiki mai matsaikacin tsawo kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar ƙazama ce na ƙarshe duk ta kwaye cinyoyi daga ita sai ɗaurin ƙirji ga zanin ya dafe tsananin dauɗa kan nan tujaja bako kitso ya danƙare ƙunba fato-fato duk dauɗa ya cika ta tana gantsar rake ta washe jajayen hauru ta tace," waalaikussalam(waalaikumusalam)sannu da zuwa,da uhum kawai ya amsa ya nufi ɗaka,mai makon tabishi ɗakan zaman ta taci gaba da yi tana shan rake kamar mayya sai da ta gama kafin ta miƙe tashiga ɗakin mai ciki da tar kace uwar ɗaki ta nufa ta ganshi kwance kan tabar ma tace,"Alhaji kuɗin cefanan?, yunwa nike ji".





Gyara kwanciya yayi yace,"Talatu kiyi haƙuri ki ɗauki hatsinki ayi tuwo dashi inna samu za.......!
Saurin katse shi tayi ta hanyar faɗin da kata Alhaji yau ma baka samo ba,wai kai kullum talauci akan ka yake,inna bada hatsi ina kuɗin niƙa,ina na ice,ina na kayan miya mikake nufi Alhaji?,yace," Talatu duk ki ranta kiyi zan biya", tace,'aa Alhaji akan mi,kaga ina sanaa ne sata nike ko biyan maza da zakace nacida kaina da kai da ƴaƴan ka iye?,shiru yayi bai ƙara cewa kanzil ba don yasan Talatu tu yanda bata sa kanta yi ba bazata yi ba,tace au ƙyaleni kayi Alhaji wato kama maidani ƴar iska ba laifin ka bane nawane da na zauna a wannan mugun auran ƙaddara wanda ban tsinana komi a cikinsa sai wahala haka ta rinƙa masifar fa wunin rana baiko ce mata ci kanki ba,da dare yayi ko garin kwaki da sugar ta aika aka siyo mata tajiƙa daga ita sai ƴar autanta suka sha.
*TOH WANNAN KENAN*








******
"Waike Hanifa bakiga nashigo bane bako ɗan sannu da zuwa sallama na fa baki amsa balle in samu tarba mai kyawu kinsan yunwa nikeji tun safe da nafita banci komi ba har yanzun",wani matashin saurayine ke wannan maganan bazai gaza shekara ashirin da takwas ba zuwa da tara,turo baki wanda aka kira da Hanefan tayi tace,sannu da zuwa ga abinci can a kitchen in ka tashi ci tana gama faɗar haka ta ciga ba da danna wayarta tana taunan cingam,girgiza kanshi yayi yana mai mamakin halin Haneefa da sukai auran soyayya biyayya da tattalin juna dududu auran su baifi wata guda ba amma mi muggan halayanta duk sun gama bayyana gareshi bedroom ɗinsu kai tsaye ya nufa tundaga ƙofa yaji wani wari dauɗan kayan wanki ya bugeshi saurin toshe hanci yayi ya shiga ɗakin da kwalaye da ledojin biskit ya fara karo a ƙasa girgiza kai yayi yace,wato Haneefa haka tabar ɗakin nan kaca-kaca ta gama ciye-ciye ta kasa gyarawa aje breif case ɗinshi yayi gefe ya fara tattara kayan da tacire ta watsar harta pants ɗin ta da bra ɗinta suna tsakar ɗaki suma sunyi duƙun-duƙun da dauɗa ga basket ɗin kayan wanki da ta kawo shi bedroom ɗin ta aje yacika famm da kayan ta har ƙin rufuwa yayi ranshi ne ya ɓaci ya nufi toilet don yayi alwala yayi sallah magriba don yana hanya aka idar tozali da yayi da wani bokiti da Haneefa ta jiƙa panties ɗin ta tun randa aka kawo ta har yau bata wanke suba har sun fara canja kala a ruwa yasa ranshi ƙara ɓaci ,duk ƙoƙarin shi ya danne ya kasa haka yasa shi saurin fitowa yana ƙwala mata kira,amma mi in dutse ya tanka ta tanka ba abinda take sai chart abinta hankali kwance,wafce wayar yayi ta miƙe ranta ɓace tana wani watsa masa kallo tana miƙa hannu alaman ya bata wayar ta ,harara ya galla mata ya ƙara haɗe rai tare da fincikar ta sai bedroom ɗin ya wurgata kan gado yace," Haneefa miye wannan ɗakin mijinki ne haka inda mijinki zai kwanta kenan ba gyara balle ƙamshi ga uban kayan wanki ga kwalaye da ledoji kamar ɗakin mahaukata ko almajirai ?,ƙara fincikan ta yayi sai ban ɗaki yace," wannan fa Haneefa dama tsaftar ki ta banza ne ƙyaleƙyale ne a waje cikin ko ba komi illa dattin shara kamar bola Haneefa dama farin cikin da kike faɗa zakiban kenan kafin aure,abin mamaki ko a jikin Haneefa abinda yakeyi tace," Saleem gidan yamin girma ne bazan iya gyarashi ba sammm wallahi asamo min ƴar aiki",shiru yayi haɗi da buɗe baki mamaki ne fal a zuciyar shi game da canjin halin Haneefa baice mata ƙala ba ya nufi ɗayan ɗakin shima still duk datti kakkaɓe ƙuran ɗakin yayi ya feshe shi da freshner kafin yashiga toilet ɗin ya wanke shi tasss,fitowa yayi ya ganta kwance kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ta kaɗa su kallo ɗaya ya mata ya kauda kai don wani irin haushin take bashi,ɗakin su ya shiga ya buɗe wardrobe ya rinƙa kwasan kayan shi yana kaiwa can ɗakin da ya gyara har yaga kwashe komi nashi tana kallon shi tana jan tsaki kamar halshen ta zai tsinke,
shi ko yi yayi kamar baisan da halittan taba,jera kayan yayi a wadrobe ɗin ɗakin kafin ya fito ya shiga kitchen anan ranshi ya ƙara ɓaci ba wani abu na gari duk ta ɓata su duk tarin kayan da iyayen ta sukai mata ta gama ɓata su hatta da cokali ba wankakke wasu plates ɗin har tsutsotsi suke fitar wa girgiza kai kawai yayi yafito zuciyar sa na masa wani irin zafi ɗakin shi da yakoma ta shiga ya ɗauko key ɗin motor shi ya fita a gidan don neman abinda zaici.






Kai tsaye Hadiza Balangu dake sultan road unguwan sarki ya nufa ya sai abinci da shayi yasha yafito a daidai bakin motor shi yaga wata ƴar budurwan yarinya tsaye ta rafka tagumi kallo ɗaya zakai ma yarinyan kasan tana cikin matsanan cin hali cikin sanyin muryanshi mai daɗi yace,"Malama ɗan matsa",ahankali ta ɗago ta kalle shi kallo ɗaya ta kauda kai don ya mata kwarjini tace,"dan Allah Alhaji ka temaka mana da abinci nida ƙanne na wallahi tun safe bamuci ba yunwa zata kashe mu", ƙara ware idon shi yayi akanta cike da mamakin budurwa haka ina iyayenta mahaifi da mahaifiyar ta tafito biɗan abin da zasuci a wannan daran kusan tara da rabi da ƙyar bakin shi ya buɗe yace," baki da iyaye ne?,tace,"ina da shi",yace ,"toh miyasa sai ke zakizo biɗa?,murmushi tayi da saida kuma tunta ya lotsa azuciyar ta ko kamar zai fashe sabida baƙin ciki tace,karka damu da sani ko ni waye ka temake ni in kana da hali ƙanina Mahafuz yana can yana kuka Munnayah ko baccin dole tayi sabida yunwa,tausayin yarinyar yaji ta kama shi ga wata can cikin niima tana wulaƙanta niiman uban giji,juyawa yayi yaje ya anso musu abinci ya miƙa mata,jiki na rawa ta amsa tace,Allah yasaka da alkhairi Allah ya baka abinda kakeso Allah yabaka ƴaƴa na gari da mata ta gari Allah ua albarkace rayuwan ka na gode,kasa motsawa yayi yana ƙare ma fuskanta kallo don shi bai taɓa ji Haneefa tayi addua ba koma waye ma amma ƙaramar yarinya da iya kwararo addua,ahankali ya buɗe baki yace," ina zakine yanzun in sauke ki?,tace,"hakan ma na gode gwani mukthar muke by attahiru road malali",gwalalo ido ya ƙara yi cike da mamakin gwanin mukhtar da ta kira akwai talakawa ne irin wannan almajirar ƴa.....................!








MORE COMMENTS
MORE TYPING




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*






NA *MRS BASAKKWACE*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*










*SHAFI NA BIYU DANA UKU 2&3*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*








___________📖Gwala-lo ido ya ƙara yi cike da ma-makin gwani mukhthar da ta kira akwai talakawa ne irin wannan almajirar ƴar.






Murmushi tayi harsai da suɓu-suɓun kumatun ta suka lotsa tace,"na gode matuƙar godiya,Allah ya baka abinda ka-keso Alhaji",bata jira abinda zaice ba tafara tafiya duk da iskan hadarin da ya taso samma bata da mu ba Allah-Allah take ta fito wajen wurin tasamu abin hawa da kuɗin da ya bata,don tasan MAHAFUZ in baici ba kuka zai tayi saide bacci ɓarawo ya sa sace shi.








Dasauri yashiga motor shi ya tayar yazo daf da ita yace,"dan Allah ki shigo nan ana wiyan samun abin hawa".






Jin ya ambaci sunan ubangiji kuma tabbas gaskiya ne ana wiyan samun abin hawa yasa ta buɗe gambon (ƙofar motor) ta shiga bakin ta ɗauke da sallama,amsawa yayi cike da ma-makin ƴar kafin yaja motor ya ɗau hanyar malali.








Wani tangamemen falo ne da yasha kayan more rayuwa,in kashige shi sai kai tinanin ba acikin nigeria bane sabida tsananin haɗuwan sa,haɗuwan sa yakai waɗuwan da baki bazai iya faɗa ba hannu bazai iya rubutawa ba,wani dattijo ne wankan tarwaɗa mai matsakaici tsawo saikai da komowa yake,yayi da wata hamshaƙiyar Hajiya ke gefe tana zaune kan kujera mai mazaunin mutum biyu sai girgiza ƙafa take tana taɓa baki tace,"Alhaji ai kullum sai na faɗa ma MAIMUNATU ta raina abincin gidan nan duk dare sai ta biya maza yau wannan yazo gobe wancan ne ,bata ganina da gashi ko kaɗan yaune asirinta ya tonu a wajenka da tabar yaranan suna kuka na lallashe su sunƙi shiru na basu abinci da yake ta zuga su ko ansa ba suyi ba".






Ranshi ƙara tunzura yayi sosai kamar ya faɗo ƙasa sabida abinda ƴar iskan yarinyar nan tayi mashi Allah a baki fir'auna a zuci fita yayi fuuuuu ya nufi mai gadi ya tambaye shi ko yaga wucewar MAIMUNATU,yace,bata wuce ba,zama yayi a gefen mai gadi yana jiran dawo-wan ta,maigadi ko girgiza kai yayi cike da tausayin yaran Alhaji yanda Uwar gidan shi ta maidasu kaman almajirai,gashi taja masa kunne bai isa ya faɗa ma.








Itako tana gani ya fita tawani bushe da dariya tace,"Allah yasa daganan ya koresu kamar yanda uwarsu tabar gidan nan dan dukiyar Alhaji dagani sai ƴan uwana ya dace muci tunda ban haihu ba".










Alhaji bai jima da zama ba motor SALEEM yai parking a ƙofar tan gamemen get ɗin gidan su MAIMUNA,SALEEM ganin gidan da ta nuna saida ya ƙara kallon ta ya kuma kallon ta sabida duk unguwan babu gida mai kyawunshi ƙila ƴar aiki ne zuciyar shi ta faɗa masa.,murmushi tayi tace,"nagode sosai",asanyaye yace,"karki damu".








Alhaji da jikinsa har rawa yake da yaga motor ƙofar gidan shi ya wani miƙe ya doshi motor daga SALEEM har MAIMUNA basu ankara dashi ba ,buɗe mazaunin driver yayi yana huci,yayin da MAIMUNA taga mahaifinta tsaye yana huci take hanjin cikinta suka kaɗa ,SALEEM ko binshi yayi da kallo yayinda Alhaji ya lailayo ashar ya watsa ma SALEEM.








SALEEM yace,"lafiya Alhaji daga zuwanka sai zagi?




Yace,"nazage ka dan ubanka kun gama tambaɗewa da yarinya ka kawo ta gida,tou wallahi dole ka aure ta,inko baka aure taba dole a daran nan ta barmin gida ita da shaggun ƙannan ta".








MAIMUNA gabanta ya tsanan ta faɗuwa ta gwalalo ido jin yace ta aure wanda bata sani ba ko ta barmai gida cikin rawa murya tace,"Daddddy".










Cikin tsawa yace," dakata munafukar banza munafukar wofi ba abinda zaki faɗa min in ɗauka".








SALEEM shiru yayi yana tinanin yaushe ye aure anya baza'a zargeshi ba,yasan baida matsala da mahaifiyar shi tana da fahimta asali ma bata son auran HANEEFA dashi sabida tafi ƙaunan farincikin shi da nata yasa ta amince amma tace,duk mai ya biyo baya ba ruwanta don idon yarinyar a buɗe shike,wanda shi bai fahimta ba sai yanzun.








Alhaji ƙwala ma maigadi kira yayi yace,jeka fito min da ƙannan MAIMUNA kawa tso su waje su san inda dare ya musu.










Jin ya ambaci haka MAIMUNAH batasan sanda ta ɓalle murfin motor ba ta fito ta zagayo inda yake ta zube a ƙasa tare da ƙan-ƙam masa ƙafa-fuwa ,wani shureta da tayi saida ta mirgina so uku.








SALEEM tausayin yarinyar ya kamashi matuƙa fitowa yayi yaje inda take ya ɗago ta ya rumgume ta a jikin sa,take suka ji wani shock ,yayin da MAIMUNA baƙon alamari ya shigeta don na miji bai taɓa mata haka ba sai yau ƙarfin ta ta tattaro ta tureshi ta ƙara komawa ga Alhaji zata ruƙo shi ya ƙara kasheta da marin da saida ta kife jini ya fara fita ta hancin ta,SALEEM da sauri yazo gaban Alhaji ya haɗa hannayen sa biyu yace,"Alhaji a ɗaura yanzun' nawane sadakin?.










Alhaji yace,"dubu goma ma ya isa tunda kun gama zubar da mutunci a titi".










Zubewa ƙasa tayi tana kuka jin tausayin kansu bawan Allah daga temako an masa sharri an kuma liƙa masa auran ta baiji ba bai gani ba.










Mai gadi ne ya fito ɗauke da da MAHAFUZ da MUNAYYA ko wannen su kuka yake fuska biji-biji da majina yazo har gaban MAIMUNA ya ajesu take suka ƙara faɗawa jikinta suka fashe da kuka,ƙan-ƙame su tayi itama ta ƙara fashewa da kuka.








Alhaji yace,muje ciki a ɗaura,bin bayan sa SALEEM yayi yana tafiya yana waigen su MAIMUNA da suke kuka cikin ciyayi zaune tausayin su ya kamashi sosai dakewa kawai yake don in yaci gaba da magana shima kukan zaiyi.










MORE COMMENT
MORE TYPING🖌️




*TOFA SHIN ZAA ƊAURA AUREN SALEEM DA MAIMUNA,YA MAKOMAR HANEEFA,YA MAHAIFIYAR SHI ZATA ƊAU BAƘON ALAMARIN*




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*






NA *MRS BASAKKWACE*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*










*SHAFI NA BIYU DANA UKU 4&5*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*










__________📖Dakewa kawai yakr don in yaci gaba da magana kuka zaiyi,shiga gidan sukai Alhaji yasa aka tattaro mai duk ƴan aikin gidan maza,shine waliyin amarya yayinda Baba mai gadi ya zama waliyin SALEEM,miƙa ma sa sadakin MAIMUNATU yayi tare da faɗa masa cikak-ken sunan sa take aka ɗaura aure akan sadaki dubu goma kamar yanda Dad ɗin Maimunatu ya buƙata ana gama ɗaura auran ya kuma danƙa ma Salim kuɗin yace,ga sadakin matan ka,kuma daga yau kar in ƙara ganin su gidana daga ita har shaggun ƙannan ta na bar muku su,SALEEM kaman ye kuka jikin shi duk ye sanyi da cin mutuncin da wannan mutumin yake ma ƴar sa tou anya ma ɗiyar sa ce da ya haifa da cikin sa ansa yayi jiki ba ƙwari ba tare da ya ce uffan ba yabar haraban gidan a inda ya barsu anan ya iske su suna ta kuka sun rungume juna,a hankali ya furta kutashi mutafi duƙawa yayi ya sa hannu ya ɗauke MAHAFUZ ya rungume shi a jikin sa yanajin ƙaunan yaro ya shige shi lokaci guda,ahankali ta miƙe tare da riƙo hannun MUNNAYA suka ƙarasa inda motor gidan baya ya yasa MAHAFUZ ya zaunar dashi haka ma MAIMUNATOU abaya ta shigar da MUNAYYAH ta zaunar dasu takoma gidan gaba ta zauna ta rafka tagumi,shiga shima yayi ba wanda yace ma kowa uffan kowa da tunanin da yake saƙawa a zuciya.










Kai tsaye unguwan da mahaifiyar shi take ya nufa dasu duk s zuciyar shi namasa bugu kar MOM ɗin sa taƙi yarda amma haka ya dake a dai-dai bakin get ye horn maigadi ya wangale get ɗin ya danna motor sa haraban gida parking yayi a inda aka tanada don aje motoci ya fito ya zagaya gidan baya ya ɗauko MAHFUZ sai alokacin yace,"bissimillah kufito mushiga ciki",duk da jikin shi yayi sanyi,buɗe murfin motor sukai suka fito suka nufi cikin gidan falon ba kowa illa ƙaran AC dayake kunne cewa yayi su jirashi anan yana zuwa kitchen yanufa ya ɗebo musu abinci yazo ya aje musu kafin yace,suci yana zuwa bari ya kira MOM ɗinshi,ajiyan zuciya MAIMUMATU ta sauke jin gidan MOM ɗinshi ne bana aunty shiba.,haurawa sama yayi kai tsaye ɗakin MOM ɗinshi ya nufa a hankali ya tura ƙofar bedroom ɗin yashiga tana zaune tana jera kaya a wardrobe da akai mata guga taji shigowa juyowan da zatai suka haɗa ido yanayin shi kaɗai ya ƙara tabbatar masa da cewa tabas ɗanta nacikin damuwa amma inta tambaye shi sai yace babu,faɗaɗa murmushi tayi tace,"a'a my boy kaine a daran nan lafiya de ko?,murmushi yayi wanda iyakanta fuska batare da yace,komi ba ya ƙaraso ya rungumeta gam ajikin sa,MOM tace,"sake tou karka ɓalla ni",cikin sanyin murya yace,"MOM kiyafe min nayi babban laifi kafin in faɗa miki MOM dan Allah ki alƙawari bazaki fushi ba zaki ɗauke shi a matsayin ƙaddara ta MOM kuma ƙaddaran ki",shafa kan tilon ɗanta tayi cike da kulawa tace,my boy komi nene zan riƙe shi da daraja hannu bibbiyu kaji faɗamin farin cikin ka shine nawa




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*






NA *MRS BASAKKWACE*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ƊAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ƊAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*










*SHAFI NA 6&7*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*










__________📖MOM murmushi tayi tace,"baƙin ta taka ba amma Allah yabaka ikon riƙo Allah yasa shine mafi alkhairi muje wajen su","ameen MOM nagode da kika

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads