Showing 21001 words to 24000 words out of 49729 words
Chapter 8 - BINTU Book Complete Document by Rufaida Umar .txt
wata buk'atar ba ki k'i amincewa. Bakisan fa dad'ina ba Bintu, Yaya Fatima ita ta yayeki, itace komai na gatanki. Tana sonki fiye da son da na nunamiki, a tunaninki, Yaya Fatima zatayi abinda zai cutar da ke da rayuwarki?"
Inna ta k'arashe cikin sanyin murya. Ta ja majina
"Tun kafin na 6ata miki rai nayi abinda ban ta6a yi gareki ba, ki tashi ki koma inda kika fito, idan kuma na isa da ke, ki amince da auren dan uwanki."
Bintu ta mik'e jikinta a sanyaye, da alamu dai maganganun na Innarta sun shigeta. Har ta sanya kai zata fice, Inna ta kirawota ta mik'a mata dubu biyu akan ta k'ara kud'in mota. Ta k'ara da fad'in.
"Ma'aruf yaro ne da yasan abinda yakeyi, yasan daraja da girman d'an adam. Miji ne wanda zakiyi alfahari da shi. In sha Allah ba zaki koka ba da kasancewarsa miji gareki. Ki koma ki yi biyayya ga uwarki mai k'aunarki. Kada ki sake ki sanarmata kinzo garinnan. Kije, Allah Yayi albarka ga rayuwarku, Ya shiga lamuranku. Ina miki murnar samun miji abin alfahari ga dukkan wacce ta sameshi."
Bintu ta dubi innarta cikin zubar hawaye. Sai kuma ta juya a sanyaye ta gyara zaman jakar hannunta wacce ta fito da zummar zuwa makaranta ta yo Rano. Ta fice daga d'akin bata bi ko ta kan k'annenta ba dake yi mata magana ba ta bar gidan da sauri-saurinta.
Don tayi sauri yasa ta hawan k'aramar mota peagout. A motar ma hawaye kawai takeyi. Gaba d'aya ta tsinci kanta cikin jin kunyar abinda ta so aikatawa Maminta mai k'aunarta da zuciya d'aya. Lallai ta kusa tafka kuskure babba, dad'in magabata kenan. Duk wanda a duniya ya rasa mai fad'a masa gaskiya shakka babu yana cikin garari na rayuwa. Tayi alk'awarin yin biyayya ga Abba da Mami, zata auri d'ansu ba wai don halinsa ba, saidai domin Allah.
"To so fa? Kina sonsa?"
Wata zuciyar ta jefomata tambayar da ta hautsina cikinta. Ai ita batasan ma soyayyar ba ballantana ta fahimci komai. Kodayake, a zamanin k'uruciyarta, Aisha ta ta6a shaida mata kad'an daga yanda kake gane ka fad'a son mutum. Fad'uwar gaba, da wani kallon kwayar idanu.
Ta ja k'aramin tsaki. Shirme kenan. Tsoro ke kawo fad'uwar gaba kawai, shi kuma kallo, kawai idan mutum yana da kwarjini zaisa ka ji bazaka iya duban kwayar idanunsa sosai ba. Banda wannan, sauran kawai tunani ne na marasa aikin yi da suka yarda suka amince da soyayya har ma suke wahalar da rayuwarsu.
A haka tayita tunane-tunanenta har dai suka shigo Kano, kai tsaye tashar unguwa uku suka isa. Mintuna arba'in ne suka kawosu. Ta duba agogon dake d'aure a fatar hannunta. K'arfe uku na rana har da mintuna.
Ta fito ta nemi abin hawa tayi mishi kwatance.
Adaidai junction na titin Zoo road, wajejan Oasis Bakery motarsu ta tsaya cikin go-slow.
Ma'aruf yana daga gefensu batare da zato ko tsammani ba, a gefensa abokinsa ne Hashim suna ta6a hira. Juyowar da zaiyi ya hangeta cikin adaidaita, fuskarta babu walwala, hankalinta gaba d'aya yana ga kallon gabanta, yayi daidai da basu hannu da akayi wanda ya janyo rabuwarsu. Mamaki kwarai ya kamashi. Daga ina take? Wajen wa ta zo a wannan unguwar? Abin mamakin kenan, sam bata da k'awaye ballantana yayi zargin ko wajensu ta zo. Haka ya 6oye mamakinsa ya maida hankali ga abokinsa da ya dage ba shi shawarar yanda zai tafiyar da zaman aurensa da Bintu har ma ya ladabtar da ita.
Shi dai Ma'aruf baice uffan ba. Tunaninsa gaba d'aya ya tafi ne ga ganin da ya yiwa Bintun yanzu daga hanyar da zata sadata da unguwa uku. To ko dai Rano ta je? Yayi kwafa a ransa kawai.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<26>>
Rufa'i ya dubi Maminsu.
"Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne."
Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi.
Maganar Mami ta katse tunaninsa.
"Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?"
Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami kirata. Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba.
"Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya.
Nan Rufa'i ya hau bata hakuri.
"Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce."
Da ire-iren haka ya samo kanta.
Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba.
Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa.
"Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar."
Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in?
"Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace.
"Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama."
Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa.
"Allah Ya huci zuciyar..."
Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe.
"Matar Yayanmu."
Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa.
"Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana."
"Ayi hakuri Maminmu."
Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha.
* * *
Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan.
Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya.
"Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?"
Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki.
"Waya gayamaku zan je gidan Uncle?"
"Daddy."
Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen.
Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa
Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace.
Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba.
Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa.
Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya.
"Ina Atine ne?"
Ciki-ciki ta amsa.
"Ta je kicin dafa fidar Hanif."
Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata.
"Ke zo nan."
Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi.
Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana.
"Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?"
Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta.
"Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?"
Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa.
"Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..."
Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta.
"Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?"
Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo.
"Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba."
Sai kuma ya d'an ja tsaki.
"Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata."
Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon.
"Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..."
Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa.
Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta.
"Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado.
"Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?"
Aisha ta ja tsaki.
"Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba."
Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki.
"D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba."
"Bani aron naki nayi kiransa."
Ta harareta "Kud'ina bana banza bane."
Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya."
Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita.
Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta.
Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane!
* * *
Bayan Wata d'aya da sati biyu....!!
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<25>>
Ko da ta isa gidan babu wanda ya d'ago wani abu. Bayan ta idar da Azhar ta dawo falon. Mami ta dubeta, ta sakarwa Mami murmushi kafin ta kwanta saman cinyarta.
"Wash! Wallahi nagaji Mami."
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Mamin ganin Bintu bata sanya komai a ranta ba. Ta dafa kanta.
"Sannu 'yar gidan Mami, amma yau baku jima ba."
Ta lumshe ido tana mai jin dad'in susar kan da Mamin keyi mata. A haka Aisha ta shigo gidan daga gidan amarya Hafsa. Ganin Bintu tayi turus.
"Har kin dawo?"
Ta harareta.
"Menene?"
Aisha na dariya ta zauna.
"A'a mamaki nayi dai. Haba Mami, kinason biyewa yarinyar nan wallahi. K'atuwa da ita sai shegen shagwa6a, wannan dai mijinki yana da aiki wallahi."
Ta ta6e baki ta muskuta.
"Wallahi A'i kin fiye sanye ido, dad'in abin ba ke zakiyi aikin ba. Mijina kuwa..."
Shaf, ta mance da wani batunta da Ma'aruf harma take batun miji. Sai kuma ta ji nauyi, ta maze ta share batun ta hanyar sanyo wata hirar.
"Ke ni bamu labarin gidan amarya."
Nan fa ta soma zuba, tuni Bintu ta ware ta mik'e zaune. Har Mami suka had'u akayita hira, a k'arshe suka shige d'akinsu sukayi la'asar.
Tana zaune saman darduma tana sauraron bayanin da Aisha ke faman zubawa yayinda take sauya kayan jikinta.
"Ke ni har na soma tunanin anya ba zan ce Ashir d'ina ya fito ba, irin wannan soyayyar da na tarar a gidan Hafsa da Bashir ai hum."
Ta yi shiru tana dariya. Bintu ta ja tsaki.
"Ke kuma babu soyayyar da ta burgeka sai ta wad'annan? Kwata kwata basu burgeni ba balle suyi abinda zai burgeni."
Hafsa ta zauna gefen gado da d'aura k'irji tana murmushi mai bayyana hak'ora.
"Bakisan so ba, amma zan d'agamiki k'afa wuyarta dai mu mik'a ki d'akin Yaya."
Ran Bintu ya 6aci ta danne saidai duk da hakan saida fa aikamata harara.
"Dad'in abin ni soyayyar ba damuna tayi ba, ina bawa lokutana muhimmanci. Da soyayyar gwara a siyomin rake nayita 6alla ina shan abina."
Hafsa ta kyalkyale da dariya, ta kai mata duka a kafad'a alokaci guda kuma ta mik'e.
"Lallai akwai aiki awajen mata."
Da haka ta shige band'aki, Bintu ta bita da kallon baki da matsala. Ta kwantar da kanta ta yi shiru. Wai daman damuwa tana kashe jiki har haka? Iko sai Allah, gashinan ayau sanadin wannan rikitaccen al'amari ta zama wata mai sanyi. Wayarta da tayi k'ara yasa ta d'aukowa, Innarta ce, bayan gaisuwa ta tambayeta ko sun isa lafiya. Ta tabbatar mata lafiya kalau. Ta k'ara binta da nasiha akan ta maida komai ga Allah, in sha Allah ta na ji a jikinta akwai alheri a aureta da d'an uwanta. Bintu tayi na'am da hakan kafin daga bisani suyi sallama.
Ma'aruf a 6angarensa yaso ya yiwa Bintu tambaya game da inda ta je saidai kuma zuwa yanzun bayason shiga dukkan lamuranta. Ai ya damu da ita kenan ma idan ya shiga.
Kwana ukun da Mami ta d'ibar mata na cika, Mami ta ji daddad'ar magana bayan ta kirayeta don jjn abinda ta yanke. Dad'i yasa Mami ta rugumeta a jiki.
"Alhamdulillah, Allah Yayi muku albarka."
Bintu ta lumshe ido kawai ranta na k'una. Ita fa tasan rayuwarta zata yi babu dad'i ne muddin ta auri Ma'aruf.
Abin ya bata mamaki ganin Mami har da 'yar kwallar farinciki. Lallai sai yanzu take k'ara gaskata maganar Innarta. Ta kuma hak'ik'ance Mami dagaske tana son wannan had'in.
Kafin sati biyu magana fa ta zagaya dangi. Tuni Abba da k'aninsa Mahaifin Ma'u wanda suke kira Alhaji, suka sun je har Rano sunga mahaifin Bintu an tsaida magana. Abun fa ya yiwa manyannan dadi. Nan suka yanke nan zuwa watanni biyu kacal.
Haka suka dawo cike da tsantsar farin ciki. Ai Bintu tun daga ranar bata k'ara bari koda wasa sun had'u da Ma'aruf ba, hakanan shima tunda ya fahimci ta sani ya rage shigowa falon Mami ya yi dogon zama. Saidai idan Mamin ce ta nemeshi game da shawarar wani abun na biki.
* * *
Wani yammaci ya kama lahadi, gaba d'aya gidan sun had'u a falon Mami suna hira har Rufa'i wanda ya zo da d'ansa, shima gogan yana zaune ya gama had'ewa cikin riga da wando farare tas, sunata hirar siyasa. Abba ne kawai