Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 49729 words

Chapter 6 - BINTU Book Complete Document by Rufaida Umar .txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

714

Ads at the middle of Article

maida kyauren ya rufe.
Bayan ya kammala sha ya ajiye kofin gami
da duban Matarsa da murmushi d'auke
saman fuskarsa....
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶


©Rufaida Omar
(July...2016)


<<18>>
"Yaranki ne suka ban sha'awa."
Cikin rashin fahimta Mami ta tambaya.
"Wai Bintu da d'anka?"
Ya jinjina kai.
"Kwarai na ji musu sha'awar kasancewa tare k'ark'ashin inuwar aure, duba da abubuwa da yawa. Saidai ke d'ince bansani ba ko zaki iya bamu 'yar ta ki."
Mami tayi shiru, ita kanta ta jima tana wannan tunanin, saidai sanin halin Bintu da Ma'aruf ne yasa ta danne sha'awarta, ta tabbatar da kamar wuya su amince da hakan. Musamman na ita Bintun.
Tunaninta ya katse sakamakon rik'o hannunta da Abban ya yi.
"Lallai idan hakan ya tabbata, ba mu ba, har su yaran zasuyi farinciki Fatima. Baki lura da yanda yarinyar ke tsananin k'aunar Hanif ba? Ki sanyawa lamarin albarka. Sauran ki barwa Allah, ni kuma zanyi k'ok'arin fahimtar da yaronnan."
Ta dubi mijinta, annurin da ta gani kwance saman fuskarsa ya tabbatar mata lallai da gasken gaske ya d'auki lamarin har gashinan ya gaza 6oye farincikinsa. Batasan irin wannan k'auna da Abba ke yiwa Ma'aruf ba, tamkar shi kad'ai ne d'a a wajensa. Ta numfasa gami da zare hannunta cikin nashi
"Zan fi kowa farincikin k'ulluwar wannan al'amari, saidai karatun Bintu fa? A ganinka ita zata amince ta aureshi?"
Abba yayi shiru kafin ya dubeta.
"Bana nufin tursasa musu, saidai yara mu muke da iko akansu ba su keda iko kanmu ba. Ballantana kuma na yiwa yarannan kyakkyawar shaida Fatima. Ina ji a jikina, in sha Allah, ba zasu bamu kunya ba. Batun karatu, ai aure bazai hanata karatunta ba. Ki bar komai a hannun Allah, in sha Allah zasu fimu jin dad'in wannan had'in."
Mami dai hankalinta ya rabu gida biyu, a gefe guda tana mai jin dad'i idan ta misalta yau gashinan Ma'aruf da Bintu sun amince da auren juna wane irin farinciki zatayi? A gefe idan ta tunano rashin jituwarsu duk sai zuciyarta ta karye, bata hangen yiwuwar lamarin ko kad'an, abin ne da kamar wuya.
* * *
A can kuwa, Ma'aruf da Bintu babu mai cewa wani uffan tun soma tafiyarsu. Motar tayi shiru ko rediyo bai kunna musu ba. Abinda sam Bintu bazata jura ba kenan, idan baza'ayi biyu ba to ayi d'aya. Ko suyi hirar ko ya kunna rediyo. Batason tafiyar kurame, hakan yasa ta fiddo wayarra ta hau k'ok'arin sanyawa kunnuwanta (Earpiece).
"Ke baki iya hira ba?"
Ta tsaya jin abinda yace, ta dubeshi hankalinsa na ga titi. Ta kauda idanunta.
"To ai bansan abinda zance ba."
"Bani labarin Banki da Sarkin Nanaye."
Ya k'arashe da murmushi. Itama sai ta d'anyi dariya. Ya dubeta.
"Ko ba sunayen nasu kenan ba?"
Ta tsuke baki, to ta samu abinda take so.
"Yaya ai sune suka fiye naci, na nunamusu bana sonsu amma wallahi sun addabeni. Ai Banki aure ma zaiyi yanzu, Sarkin Nanaye kuma ya gaji ya hak'ura."
Ma'aruf na murmushi lokacin da ya sha kwanar da zata kaisu gidan su Hafsa sannan marigayiyar matarsa.
"Kina da matsala Bintu, mijinki yana da aiki babba."
Ta ta6e baki
"Ni bana sha'awar aure fa a yanzu."
"Sai me? Keda ga shi har soyayya kin iya kina yi."
Tayi dariya.
"Wannan sai A'i, ni bana soyayya. Na d'auketa 6ata lokaci wallahi. Shiyasa nake k'ara godewa Allah da bai ta6a sanyamin son wani namiji a rayuwata ba, son aure."
Shiru ya biyo baya, can kuma Ma'aruf ya dubeta kad'an ya d'auke kai.
"Ai nayi zaton bazaki k'ara shekara ba zakiyi aure. Kodayake banga namijin da zai iya da shiriritarki ba."
Ta 6ata fuska.
"Kuma a hakan fa wallahi sona ake..."
Sai kuma ta fasa maganar ganin kallon da yayi mata. Ta muskuta.
"To ai gaskiya ne."
"Eh, irinsu Ukasha ba, amma sanin kanki maza ire-irenmu, munfi k'arfin ki."
Ta dubeshi kad'an, wai me yake d'aukar kansa ne?
Shi kuwa sam bai fad'a da wasa ba, ya fad'i iyakar gaskiyar abinda ke zuciyarsa ne. Baisani ba, furucinsa ya yiwa Bintu zafi matuk'a.
Ya faka a k'ofar k'aton kyauren gidan.
"Bismillah, jeki."
Ta dubeshi lokacin da ta murd'a k'ofa. Kamar ta gasa mishi bak'a sai kuma ta fasa ta fita a fusace gami da banko k'ofar da k'arfi. Har saida ya firgita.
Sai lokacin ya tunano furucin lallai zai iya 6ata ran mace mai ji da gayu irin Bintu. Yayi 'yar dariya kafin ya ja motarsa. Ai kam da wuya, su had'u wuri d'aya da Bintu ayi rabuwar arzik'i.
Ita kuwa haka tayi ta yiwa Aisha mitar abinda yace. Tun Aisha na sauraro har ta gaji.
"Ke wai magana bata wucewa a wajenki? Menene abin jin haushi anan? Ni banga abin damun kai ba, kin mance da bakinki kin sha fad'a babu abinda zakiyi da kamar Yaya Ma'aruf?"
Bintu ta numfasa cikin yanayin fushi.
"To ai ni a nufina na fi k'arfinsa ne, ba wai yafi k'arfina ba."
Aisha tayi dariya kawai, lallai ma Bintu, ta yaya zata had'a kanta da Yaya Ma'aruf? Kodayake ance mace ta fi namiji kyau watakil da wannan furucin na bahaushe take tutiya.
Har aka tashi walimar bata saki ranta ba, ta ji haushin abinda yace mata, ta kuma ci alwashin ramawa.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶


©Rufaida Omar
(July...2016)


<<19>>
Duk yanda Aisha ta so ta zauna ta kwana, amma fafur fa k'i. Dole haka suka rakota titi suka koma. Tana daf da kaiwa bakin babban titi inda anan take saka ran samun abin hawa, ta ji hon a bayanta. Ko tsayuwa batayi ba ballantana ta juyo ta dubi mai shi.
Banda murmushi babu abinda yakeyi, bai so biyowa d'aukarta ba saidai babu yanda ya iya tunda Mami ta kira ta shaida mishi ya biya d'in sanin da tayi Bintu ba zata amincewa kwanan ba. Isarsa ne Aisha ke sanarmishi ko mintuna biyar batayi ba da tafiya, hakan ya sanyashi biyo titin sanin ana wuyar abin hawa a titin cikin unguwar ba lallai ne tayi sa'ar abin hawa ba.
Hon da ya cika kunnuwanta ne ya sanyata tsayuwa gami da juyowa a fusace da niyyar yiwa mai shi rashin mutunci. Saidai ganin motar yasa ta fahimtar Yaya Ma'aruf ne. Ya bud'e murfin mota ta fito yana dubanta.
"Ke bakyajin hon ne? Taho mu tafi." Ta dubi gefenta, wasu samari ne zaune suna dubansu.
"Alhamdulillah." Ta fad'i a ranta.
Cikin d'aga murya tayi magana.
"Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!"
A fusace ya nufota, tayi azamar d'aga hannu gami da ja baya a tsorace.
"Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!"
Daga haka ta ja tsaki ta juya, tana jin sa'adda samarin suka kwashe da dariya har da masu fito. Ma'aruf ya rasa abin cewa, gaba d'aya ta d'aureshi da jijiyoyin jikinsa. Ya gaji da binta da kallo kawai ya fad'a motarsa a fusace ya ja.
Cikin matsanancin gudu ya wuceta har yana tayar da k'aramar guguwa.
"Yau naga ta kaina." Ta fad'a a fili. Anya zata koma gida? Kai babu batun kome, ta gwammace tayi kwanan gidansu Hafsa idan yaso gobe Mami ta tahomata da kayan buk'ata ko ta bayar a kawomata. Amma ai ta riga da tayi musu sallama. Kawai sai ta hau mota, kai tsaye gidan yayanta Rufa'i ta je. Suna zaune da Hajara sai ganinta sukayi kamar an jefota.
"Ke kuma lafiya?"
Ta zauna, hannu ta kai ta ja ruwan dake ajiye saman faranti akan center table ta kur6a.
"Anan zan kwana."
Rufa'i da Hajara suka dubi juna. Kafin su tambayi komai, ta kwashe abinda ya faru ta sanarmusu. Rufa'i mamaki ya haneshi cewa uffan, Hajara kuwa banda salati mai had'e da dariya babu abinda takeyi.
"Wai Bintu baki da aljanu kuwa?"
Bintu ta turo baki.
"Lafiyata lau, ai shine ya ja. Cewa yayi fa wai maza ire-irensu sunfi k'arfin ajina."
Rufa'i yayi wani murmushi tunano maganar da Mami ta gayamishi d'azun. Lallai akwai badak'ala.
"Banda abinki, kema kinsan broda ba shi da rufa-rufa. Idan ya fad'i abu iyakar gaskiyarsa yake nufi. Amma ni kaina ban ji dad'in abinda yace ba. Ai kinfi k'arfin ma ire-irensa."
Hajara ta tuntsire da dariya.
"Yanzu kin sanarwa Mami kina gidana?"
Ta girgiza kai. Ya dauki waya ya kira Mami ya shaidamata. Mami tace babu wani abu. Da kansa bayan ya fita da dare ya biya ya kar6o mata kayan amfaninta. Bai ko had'u da Ma'aruf ba ballantana ya ba shi hak'uri kan abinda Bintun ta yi.
* * *
Ma'aruf fa???
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶


©Rufaida Omar
(July...2016)


<<20>>


Maimakon ya nufi gida, sai ya zarce zuwa gidansa. A fusace ya shiga falon gani da zama kan kujera ta zaman mutum uku wacce batayi k'ura ba sakamakon yana zuwa lokaci-lokaci yasa d'an dolo ya gyara ko'ina.
Ya runtse ido yana huci, a sannu kuma abinda ya faru ya shiga dawowa kwanyarsa. Ba shakka Bintu tayi masifar rainashi. Kasa zaman gidan ya yi ya fito. Iyakar tsawon rayuwarsa, babu macen da ta ta6a yi mishi wannan wulak'ancin sai ita. Wai k'anwarsa, wacce ya d'auketa wata yarinya da batasan komai ba sai shirme da shiririta. Lallai idonsa idon Bintu, hum!
Koda ya isa gidan, bai zarce ko'ina ba sai d'akinsa. Har wayewar gari Mami da Abba basu sanyashi a ido ba.
Safiyar washegari, bai fito ba sai wajejan goma na safe.
Mami na zaune a falon Abba suna hira sai gashinan. Ya shigo da sallama, duk suka dubeshi suna masu amsawa. Ya had'e cikin jeans blue marar nauyi, sai farar shirt, kansa babu hula gashinan nan yayi luf-luf. Zama yayi ya gaishesu har lokacin 6acin ran nan da Bintu ta jaza mishi yana nan mak'ale cikin ransa har ma ya shafi walwalarsa.
"Ya akayi dai kakana? Akwai abinda ke damunka?"
Maganar Abba ta sanyashi sakin fuska kad'an, ya zauna ya tankwashe kafafunsa.
"Babu komai Abbana."
Abba ya gyad'a kanshi. Zaiso a yanzu ya ji ta bakinsa, saidai rashin walwalar da ya gani tattare da shi yasa shi yin shiru.
"To, Allah Ya rufa asiri, acigaba da hak'uri da rayuwa."
"Amin. Nagode Abbana, addu'arku muke buk'ata koyaushe."
Abba ya gyad'a kai cikin jin sanyi a ransa.
"Kuna tare da shi a koyaushe in sha Allah."
Haka suka cigaba da hirar duniya har Mami ta fita ta barsu. Saida Ma'aruf ya sake sosai sannan Abba ya numfasa.
"Kakana, akwai maganar da nakeson muyi."


Gaban Ma'aruf ya fad'i, ya soma ambaton Allah.
"Ina saurarenka Abbana."
D'akin ya d'anyi shiru kafin kuma Abba ya soma magana. Saida ya soma na nasihohi masu nuni da muhimmancin yarda da k'addara kafin ya gangaro zuwa ga abinda yakeson fad'a.
"Madallah, a matsayina na mahaifinka, ina mai neman amincewarka wajen had'aka aure da 'yar uwarka Fatima Bintu matuk'ar hakan bazai zamto cutarwa ba ga rayuwar d'ayanku. Ka sani, bani da burin tursasaka, ko a farkon aurenku ma kaida d'an uwanka ban tursasa d'ayanku ba, saidai kowannenki da kansa ya za6i matar aure. A wannan karon ma, ba hakan nakeson ayi ba. Na baka nan da kwanaki uku, kayi tunani ka yanke abinda kaga ya dace. Idan baka k'aunarta, to lallai ka sani, ba zan tursasa maka aurenta ba, hakanan itama Fatima Bintu, dukkan abinda tace akan lamarin, to fa bazan takura mata ba. Daman zumunci na so had'awa."
Abba ya d'anyi shiru yana duban Ma'aruf wanda gaba d'aya ya gama shiga hali na rikita.
"Kana iya tafiya."
Ya mik'e jiki kamar ba nashi ba, haka ya bar d'akin a daddafe. Bai iya k'arasawa falon Mami ba, zama yayi a kujerar dake a barandar Abba ya zubawa farfajiyar gidan ido kawai. Bintu? Bintu fa?!! Ita kuma Abba ya hango mishi matsayin abokiyar rayuwa? Ya Ilahi!
Saida ya kwashi mintoci kusan uku kafin ya mik'e ya bar wajen. Abba ya sauke labule ya koma saman dardumarsa ya zauna gami da d'aga hannu ya yi addu'ar neman abinda yafi alheri. Fatansa ya ga wannan aure ya tabbata.
A can kuwa, Ma'aruf fa ya shiga tara ba uku ba, kansa ya d'aure matuk'a. Meya kawowa iyayensa wannan tunanin? Su rasa wanda zasu hasko a matsayin matarsa sai Bintu? Yarinyar da kunya bata isheta ba?
Ya runtse idanu sannan ta bud'esu, nan da nan suka kad'a. A yau mutuwar Ma'unsa ta dawo mishi sabuwa fil! Ba don mutuwa ta mishi YANKAR KAUNA ba, yaushe iyayensa zasuyi tunanin aura mishi wata Bintu? A yau ya k'ara jin kewa mai d'umbin yawa na Ma'unsa. A gefe guda wani iri tsanar Bintu yake ji.

("Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!")


( "Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!")


Ya runtse ido ya bud'e duk a lokaci guda. Cikin zafin nama ya mik'e ya nufi firij, ruwa ya ciro ya soma kwankwad'a kafin wani sanyi ya ziyarci ruhinsa. Lallai zai koyawa yarinyar hankali, zai tabbatar mata cewar ita d'in marar kunyar k'arya ce.
Alokaci guda ya saki wani guntun murmushi.
* * *
A gidan Rufa'i kuwa Bintu ta sake sai hada-hadar tafiya gidan yini sukeyi tare da Hajara wacce itama zata je. A ranar ne kuma za'ayi Dinner Party, ta kama dole da yamma ta koma gida don kwata-kwata Mami bata had'o mata da ankonsu na Dinner ba.
Bayan sun kammala, Rufa'i da kanshi ya saukesu wajejan uku na rana. A can suka iske Mami itama da Atine har da Hanif. Nan ta hau tambayar Binti dalilinta na k'in komawa gida, dariya kawai Bintu tayi bata ce mata komai ba. Ganin bata da niyyar maganar ta kyaleta. Aisha kawai ta sanarwa, saidai alokacin ta fahimci jini d'aya ba wasa ba, don kuwa da gaske Aisha ta ji babu dad'in abinda ta yiwa Yayanta. Bintu ganin haka itama ta watsar da ita, saidai basu ci ko rabin awa ba, Aisha ta sauke fushinta, ita d'in ko kusa bata da rik'o.
Da yamma Mami ta had'a Bintu da direba domin zuwa d'auko kayanta na dinner. A karshe Bintun tace zata fito kawai daga nan gidan. Yana sauketa, ya juya wajen Mami don su d'inma zasu halarci Dinner, kasancewar har da iyaye.
Ta dubi farfajiyar gidan, wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ganin babu motar Ma'aruf wannan ya bata tabbacin baya gidan. Hankalinta kwance ta shiga.
Wanka ta soma yi sannan ta d'ora alwala. Saida ta idar da Magrib sannan tayi zaman gaban madubi ta shiga fente fuskarnan nata da kwalliya. A fili take fad'in.
"Yau zan kece raini."
Ta kammala shafe-shafenta sannan ta fiddo orange lace d'in da sukayi na 'yanmata, d'inkin doguwar riga(fitet gown) ta zura. Nan ta k'ara zaman tafkeken ribbons dinta sannan ta d'ora nad'in da sukayo akanta.
Ta saki baki tana duban kanta a madubi, iyakar had'uwa ta had'u. Wayarta dake k'ara tun d'azu tana yankewa, sai lokacin tayi niyyar d'agawa.
"A'i ya dai?"
K'arar da ta ji ya bata tabbacin sun kama hanya.
"Kin fito? Mami tace ki tsaya ga Yaya Ma'aruf zai taho ku fito tare."
"Tab!"
Da sauri ta katse wayar, ta jera da wa? Ita kuwa me ya kaita wannan gangancin. Da sauri-sauri ta had'a 'yar jakarta ta zura takalminta tana magana a fili.
"Hauka nakeyi zan fita da Yaya Ma'aruf? Kasheni kawai zaiyi "
Saidai me?




[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶


©Rufaida Omar
(July...2016)


<<21>>
Bata kai ga bud'e k'ofar d'akin nasu ba ta ji hon d'in motarsa.
Ai take hanjin cikinta suka kad'a. Da sauri ta fito daga d'akinsu tana lek'ensa ta windon falon Mami. Tana kallo ya kashe motar ya kwashi wayoyinsa, akan idanunta sukayi magana da baba maigadi, batasan abinda suke tattaunawa ba, k'arshe ya yo ciki. Da sauri ta saki labule, kirjinta kamar ana lugude tsabar bugun da yakeyi. Shikenan kashinta ya bushe. Ta fito tana sand'a har ta iso farfajiyar gidan.
"Ke!"
Ta ji an dakamata tsawa, a firgice ta juyo, yana tsaye jikin windon falonsa yana hangenta.
Ta zaro idanunta taba dubansa kafin kuma tayi narai-narai da fuska kamar mai shirin kuka.
"Zo nan!"
"Shikenan na gama yawo." Tayi furucin a fili.
Daga haka ya sauke labule. Dole ta taka ta nufi d'akin, a ranta banda addu'o'i babu abinda takeyi.
Ta shiga da sallamarta. Ya amsa a ciki, yana tsaye a tsakar falon. Yayi mata kallon tsanake tun daga fuska zuwa yatsun k'afafunta daga inda yake tsaye. Fuskarsa sai ka rantse bai ta6a dariya ba. Batasan ya akayi ba ta ji ta tsugunna.
"Yaya barka da dare."
Bai amsa ba.
"Ina zaki?"
"Di..di..nar Hafsa."
Ya d'anyi shiru.
"Mami bata ce kiyi jirana bane?"
Ya fad'a cikin tsananin zafin rai, gaba d'aya yarinyar haushi take ba shi, ya tsani a rainashi. Abin ban haushin ma, wai ita akeson ba shi matsayin mata, wannan abu da me yayi kama?
"Ta fad'a."
"Ok, itama kin rainata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads