Showing 39001 words to 42000 words out of 49729 words
Chapter 14 - BINTU Book Complete Document by Rufaida Umar .txt
Shi kuwa mamaki ta ba shi ganin yanda take murna da tafiyarsa, wannan na nufin Bintu bata damu da shi ba? Ya tunano a baya idan wata 'yar tafiya ta sameshi yanda Ma'u ke damuwa har ta kai ga zubda ruwan hawaye na rashin son tafiyarsa. Amma yau ga Bintu ta zo matsayin matarsa, bata jin ko d'ar na tafiyar da zaiyi. Jikinsa ya d'anyi sanyi, haka kawai baiji dad'in yanda ta nuna d'in ba. Ya damu iyaka damuwa har saida ya gaza jurewa a ranar da zai tafi ya dubeta.
"Meyasa bakiyi bakinciki da tafiyata ba?"
Ta ji tambayar babu zato, sai kuma ta yi murmushi.
"To ai kaima zaka huta da ni, tunda kace ina matsawa rayuwarka. Kuma kace ni ba komai ka d'aukeni ba ko?"
Ya rasa kuma bakin magana. Ya watsamata wani kallo mai nuni da jin haushin kalamanta sannan ya sanya kai ya fita jaye da Trolley dinsa. Ta dafe bango da hannunta tana binsa da kallo gami da doka uban hamma. A hankali tace "Allah Ya kaika lafiya. Bari nayi baccina har na gaji ba takura."
Ta rufe k'ofar ta koma ciki, lokacin bakwai da mintuna na safe. Abin ya yi mata dadi don kuwa bata da paper.
[7/23, 11:59 AM] +249 99 715 2061: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<39>>
Zuwan Aisha gidan ya yi musu dadi. Haka zasu zauna suyita hirar duniya idan ba makaranta. A kokarin Bintu bai wuce koyaushe ta nunawa Aisha lafiya lau suke da mijinta ba. Har takan dauki waya tayi kiransa saidai har wayar ta gama rurinta baya ko kallonta. Saidai a wayance tayita zuba zance don burge Aisha.
Satinsa d'aya da tafiya, amma ko text bai ta6a yi mata ba, da zummar gaisuwa. A yanzu kuwa ta daina samun layinsa, saidai ta ji Aisha tace yayi kiranta ko kuma Mami. Jikinta yayi sanyi, haka kawai ta tsinci kanta da shiga damuwa. Kodai furucinta ya bawa Yaya Ma'aruf haushi? Ashe zai damu da ta nuna damuwa akanshi?
Ta kai dubanta ga Aisha wacce ke kwance rigingine a saman gado tana amsa wayar masoyinta Ashir, sai wani narke murya takeyi da murmushi. Daga inda take ta zubawa wayarta ido kawai amma kunnuwanta suna ga Aisha tana sauraronta.
Kawai sai ta ji abin ya burgeta, inama ita da Yaya Ma'aruf su dawo haka? Sai ta ji nauyi, kada dai ta kamu da son Ma'aruf ne? Ta girgiza kai, kokusa bata fahimtar abinda akeyi a group din nasu ta whatsapp ta tsinci kanta da komawa contact ta lalubo lambar Ma'aruf, har lokacin hotonnan ne akai bai chanja ba. Ta bud'o tana duba, a hankali takejin wani abu na yawo a zuciya da gangar jikinta. Tayi nisa a kallonsa ta ji Aisha ta makomata filo.
"To 'yar is me kikeyi kika wani nutsu?"
Bintu batajin wasa a yau, ta ajiye wayar ta dawo kusa da Aisha ta zauna.
"Tashi ki bani wasu amsoshi don Allah."
Aisha ta mik'e zaune ganin Bintu dagaske take ba wasa.
"Ina sauraronki."
Bintu ta muskuta tana fuskantarta.
"Ya mutum zai gane ya fad'a tarkon so?"
Me Aisha zatayi banda dariya. Ta d'aga hannu sama.
"Allah na godemaka da Ka bani tsawon ran ganin wannan rana. Cabd'i!"
Ta girgiza kai kad'an tana had'e rai cikin son kauda 'yar kunyar da ta ji.
"Malama banason haka, idan bazaki bani amsa ba ki bar yimin dariya."
Ganin Aisha bata da niyyar dainawa ya sanyata daukar wayarta a fusace ta shige d'aki. Kan gado ta fad'a tana murmushi, daman tasan hakan zata faru tunda ta riga ta gama cika baki a baya. Tana jin sadda Aisha ta shigo gami da zama gefenta, ta had'e rai. Aisha ta gimtse dariyarta ta soma magana duk kuwa da cewa Bintun ta juyamata baya.
"Idan ka soma son mutum, zaka tsinci kanka cikin yawan tunaninsa, haka kuma da zarar ka ganshi kun had'a ido zaka ji kamar wasu kibiyoyi ke fitowa daga idanunsa suna shiga naka har suna haddasa maka wani kasala, har ka kasa jure kallon ka sauke idanunka. Komai na mutum zai dawo yana burgeka, ko muryar mutum ka ji sai ka ji wani sanyi na dadi. Babban abinda ke tabbatarwa ka kamu da soyayyar mutum shine KISHI. Nan duniya zakaji baka kaunar abokin takara a zuciyarsa. Ba kuma ka kaunar wani ya ra6eshi da sunan so. Ko yaya kaga ya sakarwa wani fuska ya kula da shi fiye da yanda yake kula da kai sai ka ji tashin hankali sosai, da damuwa da bakin ciki a zuciya. Matukar kina jin wadannan abubuwan da na lissafa, shakka babu (You Are In Love)."
Bintu ta bud'e lumsassun idanunta tana duban fuskar gadonta, ta ji gabanta yana bugu da sauri-sauri. Ta kamu da son Ma'aruf yanzu? Kenan dukkan abinda takeji a ranta akansa soyayya ce?
"Kenan alamomin da nakeji akan Yaya Ma'aruf suna nuni da cewar inasonsa?"
Batasan sadda ta watsowa Aisha tambayar ba. Aisha ta rasa inda zata tsoma ranta don dad'i, don ta jima da gane cewar babu abinda ya ta6a shiga tsakaninsu kawai dai ta barta a yanda ta so ne.
"Idan har kina jin abubuwan da na lissafa akansa, to lallai kin fad'a cikin matsanancin soyayyarsa."
Sai kuma ta ji wata iriyar kunyar Aisha, lura da hakan ne yasa Aisha mik'ewa ta fita da zummar d'ora musu girki.
Ta sauke ajiyar zuciya ta mik'e zaune.
"Inason Yaya Ma'aruf." Shine abinda ta furta cikin siririyar murya.
* * *
"Ina sonki Fatima Bintu." Cewar Ma'aruf kenan a yayinda yake kwance cikin kujera idanuwa a lumshe yana tunanin Bintu wanda ya zame mishi jiki tun zuwansa Lagos. Gaba d'aya kewarta ta dameshi, baisan ya damu da yarinyar ba sai bayan da ya nisanta da ita. Yana fushi da ita akan ta nuna halin ko'in kula da tafiyar da zaiyi, wato dai bata damu da shi ba. A rayuwarsa yana so yaga an damu da shi. Sai ya kai zuciyarsa nesa yake k'in daukar kiranta, lallai shi yana son tilasatawa ransa ya fiddata. Yanaso yabar tunanin wani abu nata da ita kanta. Yana so ya yakiceta a ransa. Wannan yasa ya yanke shawarar yin wata d'ayan da ogansu yace yayi acan batare da ko sau d'aya ya dawo hutun karshen sati Kano ba. Sanin da yayi ma idan yazo ba wani abun zai samu awajenta ba.
Ya numfasa ya mik'e zaune. Kalmar nan ta "So" baiyi zaton zai k'ara furtata ba ballantana ya ji ta a ransa. Sai ga shi zuwa yanzu ya gama tabbatarwa ransa ya fad'a dumu-dumu cikin kogin son matarsa kuma 'yar uwarsa abokiyar fad'ansa Bintu.
Sai kuma yayi murmushi sadda ya tunano rashin jituwarsu tun afarkon zuwanta gidansu har zuwa girmanta.
Rufa'i ya dannawa kira, ya sanar dashi cewar wata d'aya zaiyi don haka ya dauki su Aisha ya maidasu gaban Mami. Daman ya kammala waya da Abba ya shaida mishi. Ya yiwa Bintu gajeran sak'o babu wani abin jan hankali ciki ya shaidamata su had'a kayansu Rufa'i zaizo ya tafi da su gidan Mami.
Ta yi kasak'e tana duban sak'on alokacin suna tare da Aisha tana k'ara koyar da ita yanda zata shawo kansa. Ta sanarwa Aisha kafin su soma shiri. Ranta duk babu dad'i jin zai cinye wata d'aya a garin da basu da wani addini sosai.
Haka suka kammala shiri suka nufi gidan Mami.
Saidai tana ganin Mami ta mance da batunsa ta hau murna. Ganin yanda ta d'an rame sai Mami tayi zaton ko ciki ne. Ta shiga nan nan da ita. Murmushi kawai sukayi ita da Aisha.
[7/24, 9:37 AM] +249 99 842 9948: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<40>>
A wannan wata d'ayan, wanda aka ci sati uku kenan da Bintu tayi a gidan Mami, ta yishi cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da cewar babu wata mu'amalar arziki dake shiga tsakaninta da Yaya Ma'aruf face gaisuwa da take mik'a mishi ta whatsapp, shima wani sa'in za'a nunamata ya je kuma ya gani amma babu amsa. Sai sadda ta ci sa'a ne yake amsa mata, daga amsa gaisuwar kuma bai k'ara cewa uffan.
Tun tana yi har ta soma gajiya, wani sa'in ta watsar.
Shi kuwa ya d'auki hakan kawai a matsayin rainin hankali, tunda gwana ce wajen hakan.
Ganin yana neman cutuwa sosai da bukatunsa, ya sanyashi farlantawa kansa azumin litinin da alhamis. Haka kuma da yawaita dauke hankalinsa da wani abu da ba zai jawo mishi motsuwarsa ba. Saidai iyakar dauriya yinsa kawai yake, akwai sadda Lawisa ta kusa cin galaba akanshi. Sukayi doguwar hira a waya mai ta6a sosai, a k'arshe suka yanke zata kawomishi ziyara har Lagos.
Koda zuwanta da soma gudanar da abubuwa, tun kafin lamura su 6aci, ya dawo nutsuwarsa inda wata kyakkyawar zuciyarsa tayi mishi tuni da "Bafa matarka bace." Da sauri ya fisgeta daga jikinta ya mik'e yana kiran innalillahi a fili kafin ya fad'a ya wanke jikinsa. Nan ya taddata tana hawaye, bai bi ta kanta ba ya kama hanyar fita sai kuma ya tsaya batare da ya juyo ba, cikin kakkausar murya yace. "Kiyi hanzarin barin gidannan tun kafin na dawo."
Yana shirin ficewa yaji ta rungumoshi ta baya, ya runtse ido, kafin ya juyo ya tureta.
"Karki k'ara kusantoni! Ki rabu da ni Lawisa, please daga yau ki fita hanyata."
Hannunsa ta rik'e a gigice. "Bazan fita ba, ka taimaki rayuwata Ma'aruf kada ka barni ha.."
"Ki kyaleni! Ki kyaleni nace!! Kafin na dawo ki tattara abinda kikasan mallakinki ne ki bar gidannan!!"
Ya fad'a a tsawance kafin ya sa kai ya fice.
Ranta ya 6aci sosai da wannan wulakancin da yayi mata, ita kuwa ko shine autan maza ba zata k'ara kallonsa ba. Ta dauki wayarta ta kira d'aya cikin mutanenta na Lagos. Nan tayi kwatancen inda take, a take kuwa Alhajin yasa direbansa zuwa d'aukarta. Ko wanka bata tsaya yi ba ta shirya tsaf ta bar gidan.
Ma'aruf bai jima sosai ba ya dawo, ya ji dad'in rashin ganinta a gidan, ya zauna ya rik'e kai. Idanunsa sunyi ja sun kumbura adalilin kukan da ya ci, yau ga shi ya kusa tafka kuskuren da da ace ya faru ba zai iya yafewa kansa ba. A gefe kuma ga soyayyar dake azabtar da shi, ya ji haushin yanda ta bar turomishi sak'on gaisuwa ko don baya kulata sosai ne? Batasan cewa yana jin dadin hakan ba?
Ajiyar zuciya ya saki, fatansa ya kammala aikinsa yaje ayi wacce za'ayi don ba zai zauna da cuta ba.
Acan kuwa, Bintu bata k'ara bi ta kansa ba, ta danne abinda takeji a ranta dangane da shi. Ta nemi zuwa Rano ganin iyayenta tunda sun samu hutu. Kasancewar shima Rufa'i zai kai Hajara ganin gida, yasa Abba bai hanata ba ya kira ya sanarwa Ma'aruf. Allah Ya tsare hanya, shine kawai abinda yace.
Farinciki ya rufe Bintu yau zata ga 'yan uwanta.
Suma can sun shirya tarbarta sosai. Tare suka je har Aisha.
Yan uwa sunyi murnar ganinsu. Inna ta shiga nan nan da su.
Kwanansu uku suka soma shirin tahowa don Rufa'i zaizo daukarsu. Inna ta k'ara yiwa Bintu nasiha sosai akan rik'e hakkokin mijinta da sauransu. Ta yaba kwarai ganin Bintun ta yi hankali, ta zama wata mai sanyi da nutsuwa, batasan cewa soyayya ke nukurkusarta ba har ta ladabtar da ita ladabin dole. Aisha ta samu abubuwa sosai a wajen 'yar Rano kasancewar bikinta baifi sati hud'u da kwanaki ba. Haka suka baro Rano cike da kewa.
A safiyar asabar ne ta koma gidanta kamar yanda Mami ta umarceta. Tare suka je da Aisha sai 'yar yarinyar da aka samo mata da bata wuce sha uku ba da zata tayata rainon Hanif, har da Hanif din wanda suna isa Bintu ta goyeshi a bayanta. Suka gyara komai don a ranar akesa ran dawowar Ma'aruf kamar yanda ya shaidawa Mamin.
Kicin suka fad'a suka hau girke-girke. Suna yi Aisha na k'ara bata shawara.
"Kwalliya fa zaki ci malama, irin wanda na gayamiki. Kada ki nunamishi fushinki Bintu. Kiyi hakuri, kece dole wajen yi mishi biyayya, amma fa ban hanaki jan aji kad'an ba, karkiyi yanda zai tsinke."
Sukayi dariya, Bintu ta dafa kirjinta.
"Bakiji yanda gabana ke bugu ba, a tsorace nake fa. Kinsan Yayanki akwai disgawa."
Aisha ta girgiza kai.
"Akanki ba, kuma kema kinsan abinda yasa yake miki hakan, kin nuna mishi baki da kunya."
Bintu ta harareta. Aisha ta dara kad'an.
"Allah kuwa rashin girmamashi sosai ne yasa yakemiki wasu abubuwan. Ki tuna keda kanki kin sha yabon yanda sukeyi da Anti Asma'u, yana sakarmata fuska, wasa da dariya duka, koda kuwa a gabanmu ne. Yana da mutunci wallahi ba wai kuma don Yayana bane. Ita gaskiya fa a fad'eta."
"Ya gasamin maganganu fa."
"Wannan kuma kinfini sanin ta sigar da zaki rama, saidai ina k'ara baki shawara, kada ki ja aji ta yanda zai tsinke wallahi."
Murmushi kawai tayi, suka cigaba da aiki suna hira, anan ne Bintu ke labarta mata yanda sukayi da Lawisa. Me Aisha zatayi banda dariya, har da rik'e ciki. Ta jima tana dariya da k'arawa.
"Kai wallahi kinyi daidai. Toh wallahi ko don saboda su ya dace ki bada kai bori ya hau kada kiyi sakiyar da ba ruwa."
Aisha ta k'arashe tana mai kwafa.
"Bakisan wacece Lawisa ba. Yar iska ce, idan ma nayi kiranta karuwa banyi k'arya ba wallahi. Ki tashi tsaye karki bari su samu k'ofa."
Bintu ta girgiza kai da gamsuwa da wani irin tsoro.
Bayan sun kammala, Aisha ta yiwa Hanif wanka, itama Bintun ta fad'a band'aki.
(Kuyi hakuri, ba da son raina na barku jiya ba.. Ba chaji ne)
[7/24, 12:57 PM] +249 99 715 2061: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<41>>
Mintuna ashirin da kammala shirinta da komai, ta fito falon inda Aisha da Sarah mai rainon Hanif suke zaune suna kallo. Ba Aisha ba, daidai da Sarah saida ta saki baki wajen kallonta.
Wani shegen siket ne bak'i mai shek'i amma ba shi da kyalkyali, tsaga gareshi tun daga gwuiwa har k'asa, sai wata riga ja mai igiyoyi wanda ya tafi X ko kirjinta bai rufu yanda akaso ba, bata da hannuwa sai na vest. Ta rufe kanta da jar hula mai wani laushi duk da hakan, tufkakkan gashinta bai kammala rufuwa ba.
Ta rik'e k'ugu ta karkace kai kad'an yayinda ta d'an tsuke baki.
"Ya?"
Aisha ta had'e yatsunta biyu.
"Wow! Kinyi kyau wallahi."
Ta k'araso tana mai yin farr da ido.
"Nasani."
Aisha ta d'aka mata duka a cinya sukayi dariya.
"Yau dai da wuya Yayanmu ya d'auke idanunsa akanki."
Sai kuma jikinta yayi sanyi. Fatanta kada ya gwatsaleta.
"I hope so."
"In sha Allah, kedai kada ki damu."
Cewar Aisha.
Angonnata basu shigo Kano ba sai bayan Magrib. Tuni Aisha ta tattara ta wuce. Duk yanda Bintu ta so zamanta har zuwa sadda zai shigo amma fir ta k'i.
Tana zaune ta rik'e Hanif tana mishi wasa ta jiyo tsayuwar mota. Ji tayi gabanta ya fad'i, ashe daman don batason Ma'aruf ne yasa batajin nauyin yin komai a gabansa?
Tayi saurin duban Sarah.
"Shiga d'aki."
Sarah ta mik'e da sauri ta fad'a d'akin Hanif.
Kwankwasa k'ofar da akayi yasa ta nufar k'ofar, Hanif yana rungume a jikinta bata ajiyeshi ba. A hankali take tafiya har ta isa k'ofar ta bud'e. Ido cikin ido suka dubi juna. Kowannensu yana kokarin isarwa d'an uwansa sak'o.
Sai kuma ya juya da sauri, Isa direban Mami ya tara gami da kar6ar akwatinsa.
"Nagode Malam Isa."
Ganin haka, yana shigowa ta sa hannu ta rik'o trolley din, shi kuma yayi amfani da hagunsa wajen amsar Hanif dake mak'ale a hannunta na dama.
Wani shock sukaji gaba d'ayansu, ya narkar da idanunsa wajen kallon abinda ya fi tafiya da imaninsa a wajenta. Ita kuwa ta dauke idanunta. Murya na rawa ta furta. "Yaya sannu da zuwa."
Baki amsa ba har ta juya ta nufi d'akinsa tana rausayar da batasan yanda akayi ta soma ba, wannan kam yafi (natural) tafiyarta had'uwa da tada hankali.
Baiyi k'asa a gwuiwa ba ya tura k'ofar da k'afarsa ya mara mata baya. A daidai k'ofa suka had'u, caraf ya rik'o hannunta ya ja zuwa ciki. Ta dubi yanda ya rik'e hannunnata gam kamar mai tsoron a rabasu, sannan ta dubeshi a tsorace, gabanta na bugu da k'arfi da kuma sauri-sauri. Ya ajiye Hanif a saman gado ya jawota gaba d'aya zuwa jikinsa gami da yi mata kyakkyawan rumfa ruf. Gaba d'ayansu sun ji a jikinsu kuwa. Daidai kunnenta ya yi magana.
"I'm in need of you Fati."
Yanda yayi maganar da irin muryar da yayi amfani da ita wajen yin ce ta sanya tsintar kanta cikin rawar jiki. Bata ankara ba ta jishi yana cigaba da abinda bazata iya jura ba.
"A'a! Bintu, not so fast!"
Da sauri ta daddage ta tureshi, bata bi takan Hanif ba ta fice a guje. Sai ma ta ba shi dariya, hakan ya sanyashi murmusawa.
[7/25, 12:04 PM] +249 99 842 9948: ¶°°BINTU°°¶