Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 198763 words

Chapter 14 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt

Ads the beginning of article before Image

30 Jun 2024

2357

Ads at the middle of Article

ta ce "Da wuri haka?"


"Kar ki ce haka maman rumaisa, jinkirin ba shi da wani amfani, kin san mu masaurata ba sa son jira, ayi musu addu'a dan Allah, in sha Allah za a kawo kuɗin aure"


Har mama da ammi da suka gama tattaunawar su, babu wani ƙwarin gwiwar cewa wani abu, a tsakanin adam da rumaisa, kowannensu shi ya san halin da suke ciki.


Bayan sun gama magana, suna fita rumaisa ta tubure da kuka ta ce ita fa ba ta so, ba zata aure shi ba, da fari mama ta fara rarrashin ta, ta zaci abun na ta na hankali ne, amma ta ga ba ta da niyyar nutsuwa, ita dai ba ta gaya wa mama, me take gani ba, amma ta ce ba zata aure shi ba.


Shihowar mai sunan baba ce, ta sanya ta ɗan nutsu, Aikuwa tambayar da ya fara yi, shi ne meya sameta take kuka.
Mama ta sanar masa da duk abun da ya faru, rumaisa ta zaci yanzu ma zai turje, sai ji ta yi ya ce "Allah ya tabattar mana da alkhairi, nan kano zasu kai, ko can katsina?"


Mama ta ce "Wai da su kai wa kawunku na mandawari, ba sai an wahalr da su ba"


Mai sunan baba ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu"


Cikin kuka rumaisa ta ce "Mai sunan baba ni fa na fasa bana son shi".


Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Suwa zaki mayar ƴan iska, ko yau suka ce a ɗaura, sai an ɗaura, ki bari na fita na dawo na tarar kina wannan kukan, ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa da ke".


Haka nan rumaisa ta tsinci kanta da kasa gaya musu abun da take gani a tare da adam, da alamu suka nuna mata su basa gani, ita kaɗai kawai take gani.


Usman kuwa cewa yake "Wallahi ba zaki yi mana baƙin ciki ba dan ubanki, haka kurum ke fa ki ke son auren mai kuɗi, kuma Allah ya kawo, ki ce ke ba kya so, kin yi kaɗan yarinya, dole ayi auren nan, ko ba komai ma hau doki, kina kallo albarkacinsa aka fito da Aliyu, yanzu malam shamsu har gaisheni yake, saboda yadda ya kankaro mana mutunci, sai kin je".


Cikin kuka ta ce "To ni bana son shi"


"Uban da ya sanya, ki ka amince tun da fari, shi zai sa ki haƙura ma a yanzu" gaba ɗaya aka ƙi goya mata baya, ta din ga surutai da koke-koke suka ƙi kulata.


Ammi da suka tafi gida, jikinta sanyi yayi, da ganin yadda rumaisa duk ta rikice lokaci ɗaya, kuma ta ga bai kamata ta ɓoye musu wasu abubuwan a kan Adam ba, amma tana ji a jikinta rashin lafiyar ta sa abu ne da ya shafe shi, da shi da ita rumaisan, ta din ga fatan Allah ya sanya hakan ba zai zama cutarwa ga rumaisa ba.
Nusaiba ta din ga tambayar ammi yadda suka yi.


Ammi ta ce "Sun amince, rumaisa ce dai take nema ta ce ta fasa, amma ina ganin rigima ce kawai irin ta ta, kuma kai takawa, kamar yadda na gaya maka a baya, dole ka sassauta ka mayar da kanka dai-dai da ƙuriciyarta, bana son ayi auren nan ya zaman tana jin tsoronka, ko tana ganin kamar ba ka da imani"


Adam bai iya fahimtar abun da ammi take faɗa sosai, ya kwanta a kan 3seater, ya lumshe tabbas.


Iman kuwa tausayinsa da na ita kanta rumaisan ya kamata, mussaman da ta ji cewar nan kurkusa sosai za ayi auren.


Har dare yayi, ko abincin kirki rumaisa ta ƙi ci, sai koke-koke, suka shareta suka cigaba da harkokinsa, usman sai tsara yadda abubuwa za su kasance yake yi.


Mama ta kira yaya Abubakar a waya, ta sanar masa da batun, ya ce zai shigo kano, Yakamata tun wuri su san me suke ciki, su san mai yakamata a fara tanada na auren rumaisa.
Jin abun da yaya Abubakar ya faɗa, ya sanya rumaisa jin kome za ayi mata ba zata iya barin gidan nan ba, sai dai idan an yi auren ya dawo gidan ya zauna, ko ya barta a gida ya bata sabir kamar yadda aka yi mata alƙawari.


Tashi ta yi ta nemi wuri ta yi kwanciyarta, saboda hirarrakin ɓata mata rai suke yi.


Daga nesa take hango shi cikin hayaƙi, a hankali hayaƙin yake bajewa, yana ƙara kusantota, ganinsa ta yi cikin sarƙa hannu da ƙafa, ga idonsa na ci da wuta a wannan karon ba hayaƙi kawai yake yi ba, fiƙarsa duk ta fito daga bakinsa, ga faratansa sun yi zaƙo-zaƙo. Tunkarota yake yi, yayin da ita kuma take ja da baya, cikin tsoro da razani.


Duk iya ƙoƙarin ta na addu'a, ta kasa dan ji ta yi tamkar an danne mata masarrafar tunaninta, zuwa maƙoshinta, ta kasa Addu'a.


Tun tana ja da baya, har ta kai bango, fizgota yayi da ƙarfi, ya danna mata faratansa a maƙoshinta.


"Wayyo Allahana mama na shiga uku, Innalillahi wa Innalillahi raji'un"


Ko sallame sallar da take mama ba ta yi ba, ta yo kan rumaisa jin tana ihu, kamar wadda za a kashe.


Mama ta fizge net ɗin rumaisa, ta riƙota tana tambayarta "Lafiyarki kuwa? Menene?"


Rirriƙe mama ta yi tana mayar da numfashi, hannu ɗaya kuma ta riƙe wuyanta, da take jin kamar yana yi mata zafi.


Tuni Aliyu da mai sunan Baba suka taso da gudu suka yo ɗakin mama, saboda yadda kururwar rumaisa ta cika gidan.


Mama ta jijjigata ta ce "Rumaisa menene ki yi magana mana"


"Mama baban Sabir ne, shine"


"Me yayi miki?" Numfashi take saukwa, amma ta kasa gayawa mama abun da ta gani.


A fusace mai sunan baba ya ce "Wulaƙancin naki da iskancin har ya kai ki din ga yi mana ihu cikin daren nan? Kar ki kuskura ki kaini bango, na kuma jin bakinki sai na zaneki, ki yi addu'a ki kwanta, idan ma kina yi ne saboda ba kya son auren, to kin yi kaɗan"


Mama gaba ɗaya jikinta yayi sanyi ta kuma cewa "Me ki gani ya razanaki haka?" Rumaisa ta yi shiru.


Mai sunan baba ya ce "Ba wani abu da ya razanata, shirmenta da take yi ne yake zuwar mata har a mafarki"


Aliyu ya yi tsaki ya ce "Rigimarki ba ta ƙarewa, har tausaya bawan Allah nan nake faman da zai sha" ya fice daga ɗakin, mai sunan baba ma ya fice.


Duk iya rarrashin mama, da lallaɓa yaro a matsayin ta na uwa, ta yi, amma rumaisa ta ƙi gayawa mama ainihin abun da ya faru, haka mama ta ƙyaleta ta sake tayar da salla.


Tsoro ya hana rumaisa ko rufe idonta, dan haka ta tashi ta je ta yi alwala, ta zo ta tayar da salla ita ma, sai dai tana yin raka'a biyu, wani nannauyan bacci ya ɗauke ta.
Mama tana jin yadda rumaisa ke ta surutai a baccin, kamar tana hannun ƴan bindiga.


Sai da mama ta sanyata a gaba tana ta tofa mata adduoi, har mama ta fara tunanin, ko rumaisa na da aljanu ne, maganar aure ta taso za su fara motsawa.
Dan haka ta ƙudurce a ranta, dole ta nema mata maganin sheɗanu.


Ta cigaba da sallolinta, tare da tsananta addu'a a kan lamarin auren nan da yake tunkarosu.


***


Mamaki Samha take ba ɗan kaɗan ba, ganin irin surƙuƙin ƙauyen da suke kurɗawa, ita da Mummy da kuma Hajiya Lubabatu.
Kasa ɓoye mamakin ta yi ta ce "Wai yanzu Mummy har nan ku ke zuwa? Ni fa ma fara jin tsoro"


Mummy ta yi murmushi ta ce "Yaro yaro ne, ke ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake, tafiya duk nisanta da surƙuƙinta, in dai da biyan buƙata ai shikenan, tafiya ɗazu ce".


Hajiya Lubabatu ta ce "Ke idan babu wannan ƴan biye-biyen mutum ya zauna lafiya, mussaman a irin gidajen sarautar nan, ai ni tun da Allah ya taimakeni, na kaɗa duk wata mata da ta raɓi gidana, na ga tsuguno ba ta ƙare mini ba, sai na dangana da mallakawa Jabir kujerar galadima,"


Samha ta ce "Takawan fa? Ba gidansu sarautar za ta koma ba".


Mummy ta zunguri Hajiya Lubabatu, sannan ta ɗora da cewa "Yauwwa, mun kusa ƙarasawa, daɗinta kowa yake gani, idan muka je sai ya katse ya sauraremu".


Samha ta ce "Ni fa idan za a kasheni, ban san hanyar komawa ainihin titi ba, gaba ɗaya kaina ya juye".


Hajiya Lubabatu ta ce "Zaki zama ƴar gari ne da zarar kin waye".


A cikin surƙuƙin ƙauye sosai mutumin yake, dan an fita daga gari sosai wurin kamar daji, a nan aka yi masa wani shinge, suka tarar da tarin mata da maza a wurin, da masu zubin hannu da shuni, da masu saffa-saffa, ga marasa lafiya kuma, wasu abun nasu ma dai ba kyawun gani.


Ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba, bayan an sallami na ciki, suka shiga, wurin duk an kafe ƙahuhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, ga wani irin wari da tsamin turaruka da magunguna da ɗakin yake yi. Mutumin yana zaune cikin wasu tsummokaran kaya, ga wasu irin kayan tsubbu a gabansa shi kansa duƙun-duƙun da shi, kamar ba ɗan Adam ba, ga idonsa ɗaya hakiya ta rufe, ɗayan kuma a juye ga idon jawur.
Sai da kan Samha ya sara, ta nemi faɗuwa, Hajiya Lubabatu ta riƙeta suka zauna.


Mummy ta ce "Barka da warhaka malam, ya aiki ya ƙoƙari"


"Lafiya ƙalau, kin yi nusau, ko buƙata ta biya ne, ko kuma dai kin fasa aikin da ki ka buƙata, tun da ki ka ce mana akawai maganin da ake masa amfani da shi, muke jiran ki kawo mana maganin mu yi aiki a kai, amma mun ji ki shiru".


"Ai malam maganin ne yaƙi samuwa, duk wata hanya da zan bi a samu, ba a dace ba, amma ba haƙura na yi ba, ina nan zan dawo. Gamu tare da baƙuwa, ƴar facalarmu ce, da ita da shi yaron Adam, duk iyayensu ƴan uwa ne, ta daɗe tana son shi, amma ya auri ƙanwarta, yanzu ƙanwar ta mutu, amma uwarsa na son aura masa wannan ƴar tsintuwar da na taɓa baka labari, kuma wannan ɗin ta kuma rasawa, shine muke son ayi wani abu a kai".


Yayi shiru, sannan ya ɗebi wata ƙasa ya zuba a wani fai-fai, ya dinga juya hannunsa, sannan ya kalli fai-fan ya ce "Tirƙashi, tabbas ga maganar aure nan, sai dai ita yarinyar tana tafe da wata irin guguwa mai ƙarfin gaske, sai kun tashi tsaye sosai"


Cikin sauri Samha ta ce "Malam so nake kar auren ya yiw....."


"Aure sai an yi shi, ma'aunin ƙaddarar yarinyar da zai aura ya rinjayi tasa, sai dai idan ɗayansu ne ya mutu"


Kamar Samha za ta yi kuka ta ce "Dan Allah malam a kasheta, ba zan iya jurewa ba a wannan karon"


Mummy ta ce "Malam, ka san yarinyar, wadda ka taɓa yi mini aiki a kanta ce shekarun baya, kawai ka yi wani abu a kai"


"To ya aka yi ƙasa ba ta nuna mini ita ce ba? Ban ga taurarinta sun fito a cikin nasa ba, amma duk da haka babu damuwa, ta jiramu a waje, zan bata abun da za ta yi"


Samha ta jinjina masa kai, ta yi godiya, sannan ta tashi ta fita ta bar su Mummy.


Hajiya Lubabatu ta ce "Malam, ya ake ciki ne? Haryanzu galadima yana nan a raye, ga lokaci yana ƙurewa, bana son wani dalili da zai gifta, da Jabir zai gaza mallakar zunzurutun dukiyar nan da sarauta".


"Allah ne mai kashewa da rayawa ba ni ba, dole ki cigaba da jira, ke kuma ya aka yi?" Yayi maganar yana kallon Mummy.


"Malam, kamar aikin da yake tsakanin yaran nan ya fara sanyi, kamar mahamud ya sassauta ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan, sannan malam yadda yake yinƙurin yin auren nan, a sake damalmala lamarinsa, bana ƙaunar ganin wani cigaba a tare da yaran nan".


Malamin ya ce "Ina iya ɓata aiki ne, ba sauya ƙaddarar bawa ba, zan yi abun da ya dace a kai, ku tafi ta kudu, ku ajiye abun sadaka a mararraba ta uku, sannan shekara ta kusa, za a shayar da ƴar baƙa ta arewa da jini, sai dai ta daina samun jinin da take sha, dan haka za ayi mata sadaukarwa da wani abun, na sallameku".


Da haka suka fita, Samha take ce musu bai faɗa mata mai za ta bashi na aiki ba, suka ce kar ta damu, suka yi abun da ya ce sannan suka tafi gida.


***
Abubakar ya dawo, sun kuma tattauna sosai a tsakaninsu, a kan auren rumaisa, suka yanke shawarar a sake jarraba sayar da gonarsu, domin a samu abun yi mata kayan ɗaki.
Ɓangaren rumaisa kuwa, sai koke-koke take a kan ita fa ba ta so, gashi har fargabar kwanciya bacci take yi, saboda munanan mafarkan da take yi, ta je ta samu malaminsu a islamiyya ta ce ya bata Addu'a, tana yawan yin mugun mafarki ya bata shawara da cewa "A duk lokacin da ki ka yi mummunan mafarki, ki nemi tsari sannan kar ki gayawa kowa, ki din ga kwanciya da alwala, sannan ki kwanta da ɓangaren dama, ya zamana kina Adduoi na safe da na maraice, sannan ki karanta na kwanciya barci, idan razana ki ake yi a mafarkin, ki daina tsorata, ba abun da yake samun bawa sai da iznin Ubangiji, kin riga kin yi azkar kin nemi tsari, babu abun da kuma zai cutar da ke".
Rumaisata riƙe maganar malaminsu, ta dage da addu'a da alwala, shine ta ɗan samu rangwame.


Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, tun da su ammi suka tafi, sai ana gobe kai kuɗi suka yi waya da mama, ranar juma'a bayan an saukko daga Masallacin juma'a, mai girma turaki da wasu manya a masarautar kano, suka kai kuɗin auren rumaisa gidan ƙanin mahaifinsu, naira dubu ɗari biyar, suka saka wata ɗaya rak.


Ƙanin mahaifin rumaisa ya nemi su ƙara musu lokaci, saboda shirin aure, ba abu ne mai sauƙi ba, amma suka ce basa buƙatar komai, rumaisa kawai suke son a kai musu, dan haka wata ɗaya suka saka.


Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*




Tun da aka ce za a kawo kuɗin rumaisa wasu daga dangi suka fara surutun, rumaisan guda nawa take da har mama za ta ce zata yi mata aure, mussaman da ta fi kowa sanin halin rumaisa na rashin nutsuwa.
Tun da aka kawo kuɗin nan, zance ya sake canza salo mussaman ganin manyan mutane da suka kai kuɗin, da kuma irin zunzurutun kuɗin da aka kai ɗin.


Bayan tafiyar su turaki, suka tafi ɗorayi, domin suje a tattauna abun da za ayi, na game da shirin aure.


Rumais kuwa ta manta da batun kuɗin aurenta aka kai, mama dai ta saka an yi soye-soye, suna ta faɗa da rumaisa tana dumbuza tana ci, dan da ta dawo daga makarantar boko, sai da ta ɗaure cin cin a leda fal, ta fita ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads