Showing 42001 words to 45000 words out of 198763 words
Chapter 15 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt
tafi gidansu Hauwwaliya.
Ko a unguwar su rumaisa, babu wanda ya san da batun kawo kuɗin rumaisa.
Gaba ɗaya yayyen rumaisa sun haɗu a falon mama, ga ƙanin mahaifinsu na kano, sai kuma yaya ɗan lami, da ya wakilci dangin mahaifinsu na katsina.
Baba lawalli ya dire kuɗi ya ce "To ga kuɗin aure nan, naira dubu ɗari biyar, kuma sun saka wata ɗaya rak, na ce su ƙara mana, mu samu mu shirya a tsanake, sun ce su basa buƙatar komai daga garemu sai rumaisa kawai"
Mai sunan baba ya ce "A'a ba zai yiwu ba, dole zamu yi mata kayan ɗaki, ba zai yiwu daga baya azo ana yi da ita ba, son zuciyar sai yayi yawa ai".
Abubakar ya amsa da "wannan gaskiya ne"
Mama kuwa a ɗan tsorace dubu ɗari biyar, sai da yarinyar zan yi? Ina laifin ko dubu hamsin ma"
Usman ya ce "Haba mama, ko bazawara ai ba a bata dubu hamsin ba, sai ka ce a ƙauye? Yarinya falleliya, son kowa ƙin wanda ya rasa, ki ce dubu hamsin".
Abubakar ya ce "Wai kai usman duk maganar kirki sai ka sako wasa, a mayar da hankali a yi magana sosai".
Yaya ɗan lami ya ce "Kamar yadda muka fara magana, an riga an saka gonar nan a kasuwa, kuma an fara tayawa, tun da ita ba a yankinmu take ba, wurin da take da tsaro"
Baba lawalli ya ce "A'a ba sai an kai ga sayar da gonarku ba, in sha Allah zamu iya, zamu fitar da rumaisa kunya"
Mama ta ce "Duk da haka, ɗawainiyar aure, ba nan kusa bace ba, kuma da amincewar ƴan uwanta za a sayar". Haka suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda abubuwa zasu wakana.
Bayan sun watse, mama ta kira ammi a waya, ta yi godiya, sannan ta ɗora da ƙorafin kuɗin nan sun yi yawa.
Ammi ta ce "Ni dai babu ruwana, babanta turaki ne ya bayar da kuɗin, kin ga babu mai ikon cewa a rage yayi yawa, kuma duk abun da zamu baku, ai bai yi yawa ba, mutum guda fa zaku bamu, ina musu fatan alkhairi sannan ina sake yi muku godiya da karamci. Sanan dan Allah kar ku ce zaku takurawa kanku, babu abun da zai gagara, komai za ayi in sha Allah, rumaisa kawai za a kawo mana".
Mama ta ce "Babu abun da zai gagara ma in sha Allah, Allah Ya sanya alkhairi"
"Amin ya Allah, zuwa jibi in Allah ya kaimu ma zai shigo wurinta, idan da abun da take buƙata na shirye-shirye sai su shirya"
Mama ta ce "To babu laifi, Allah ya saka da alkhairi" da haka suka yi sallama.
Mahmud kuwa, haka nan ya ji zaman garin duk ya ishe shi, Alla-Alla yake kawai ya koma, saboda haka ya haɗa kayansa ya tattara ya koma.
Iman ma, haka nan ta fara ciwon kai a tsaitsaye, abu kamar wasa, sai dai ta sha magani ta basar, amma ko sauka baya yi, yau da aka kai kuɗin auren nan tana murna, sai dai a gefe guda kuma tana fargabar abun da Samha zata iya aikatawa.
Da sallama ta shigo, hannunta riƙe da jarkar lemo, mama ta kalleta ta ce "Sannu, sai yanzu ki ka dawo? Haka muka yi da ke dama?"
"Dan Allah mama kiyi haƙuri, wasa muke yi ne"
"Wane irin wasa?"
"Wasan ƴar carafke, ƴar gala-gala sai kuma na koya Habiba yadda ake faten tsaki"
Mama ta ce "Ko kuma zuwa ki ka yi kina gaya mata zaki yi aure?"
Ware ido rumaisa ta yi ta ce "Wallahi ni ban gayawa kowa ba, kawai wasa muka yi"
Aliyu ne ya janyo hannunta yana cewa "Ke, kin kusa zama matar aure, dole ki daina wannan yawon,tun da an kawo kuɗin auren nan"
Sororo ta kalleshi ta ce "Wai dama da gaske ne?"
"Au, da da wasa ne? Dubu ɗari biyar aka kawo"
Ta buɗe baki ta ce "Haba duka nawa ne? A sai mini keke a ciki, da akuya in din ga kiwonta"
Abdallah ya tunsture da dariya ya ce "Ke tafi can, gado za a saya miki ƙato, da wardrobe da kayan kitchen"
Ta ɗan yi shiru sanan ta ce "To duk a gidan nan za a zuba su? Shikenan sai mu din ga kwana da ni da mama a kai"
Usman da yayi alwala zai fice masallaci ya ce "Gado bana mama bane ba, naki ne da mijinki, a gidan da zaki zauna za a saka miki"
Kamar adam yana wurin ta ce "Taɓ, ai wallahi ba zai hau mini kan gadona ba, ta yaya mace da namiji zasu din ga amfani da gado ɗaya"
Usman bai kuma cewa komai ba ya fice, gaba ɗaya suka watse suka bar tsakar gidan, jin zata fara rashin hankalin nata.
Har bayan sallar magariba, zancen yadda biki zai gudana suke yi, ita kuwa ƙasan zuciyarta ta kasa manta, abun da take gani a game da Adam.
Tashi ta yi kamar mara gaskiya, ta je kusa da mai sunan baba ta zauna, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Mai sunan baba, dan Allah ka ara mini wayarka zan yi waya, na duba ta mama babu kuɗi a ciki"
Sai da ta fitar da rai zai yi magana, sannan ya miƙa mata wayar, ta saka hannu ta karɓa, ta yi masa godiya, ta tashi ta je in da ta kwafi lambar iman ta kirata.
Duk da iman tana jin jiki, amma ta dake jin muryar rumaisa ta ce "Amaryar takawa, takawarki lafiya"
"Anty iman, baki da lafiya ne?"
"A'a lafiyata ƙalau, ashe an kawo to Allah ya sanya alkhairi ya Kaimu lafiya"
Rumaisa ba ta amsa addu'ar ba ta ce "Ina rabin ran, dama kira na yi ki saka masa wayar a kunnensa na yi masa magana"
Iman ta yi murmushi ta ce "Bacci yake yi, amma idan ya farka kan ki yi barci zan kiraki in sha Allah, dan na san idan ya ji muryarki zai yi miki gwaranci"
Rumaisa ta yi dariya ta ce "Ke kuwa Muryar mamansa fa, ki gaishe mini da ammi, ba zan barci da wuri ba".
"To shikenan, yauwwa ki na ji na?"
Rumaisa ta ce "Eh"
"Dan Allah anty rumaisa ki dage da addu'a, akwai ƙalubale a wannan auren naku, kin san duk wani abun alkhairi zai fuskanci suka, ki yi ta addu'a, wannan familyn da kike shirin shigowa, akwai tarin ƙalubale da rikici, wanda su ke taka rawa wurin damuwowin da baban sabir yake ciki. Dan Allah idan kin aure shi ki din ga tausaya masa, maraya ne da ƙalubalen rayuwa ya sanya zuciyarsa yin rauni, ki yi ta yi muku Addu'a mu ma zamu tayaku in sha Allah".
"Ni ma marainiyar ce ai, kuma shi ƙato ne, ni yarinya ce ni zai tausayawa, ya daina hantarata da hararata ai" tayi maganar iyakar gaskiyarta.
Iman ta yi dariya ta ce "Zai tausya miki in sha Allah, sai mun yi wayar, kar ki yi bacci da wuri, na san dole zai farka da wuri"
"To shikenan ina jira" sai da aka fara yi mata warning ta cinye masa kati, sannan ta mayar masa da wayar
Wayar da tsoron mai ita bai sa kowa ya raɓeta, amma rumaisa ta je ta kwantar da kai ta karɓa.
Gaba ɗaya batun auren nan baya kan rumaisa, ta haƙura da rigimar ba ta so, tun da mai sunan baba ya sanya baki, sai dai tana tsoron kar ta je Adam aljani ne.
Mama da murnarta ta sanar da takawa, duk yadda su turaki suka yi a wurin kai kuɗin auren, da yadda ya din ga yaba dattaku da kuma kimar dangin rumaisa da yadda aka karramasu cikin mutuntawa.
Ba dan Adam yana jin daɗin hirar ba ya cewa ammi "To Allah ya yi mana jagora"
"Amin, ko kai fa, dan Allah ka saki ranka a kan auren nan, ba zan yi maka zaɓen tumun dare ba, in sha Allah rumaisa alkhairi ce a gareka da yaronka"
Ya jinjina kai ya ce "Yauwwa, Allah ya sa"
"Amin ya Allah, yauwwa ka san dama wata ɗaya aka saka, bana son ku zauna a gidanka da kuka zauna da aisha, bana son ka din ga wani abu da zai ɓata mata rai, na san ba zan hanaka tunanin matarka ba da ka rasa, amma idan kana son samu cikakkiyar dama zama cikin kwanciyar hankali da iyalinka, ka yi iya ƙoƙarin ka, ka din ga danne tunanin aisha a gabanta, sabon gidan nan na jambulo, a sake yi masa fenti, tun da dama sabo ne sai ta zauna a ciki".
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mhmm, bai yi mata girma ba?"
Ammi ta ce "To ai gidanka na tudun yola, ya fishi girma, kuma nan gaba iyali zaku tara, kuma tana matarka dole a yalwata mata mazauninta".
Ya ce "To" dan jin batun tara iyalin yayi wani banbarakwai, zuwa yaushe kenan, ta gama girman da zata tara iyali?.
"Sannan jibi in Allah ya kaimu, zaka je ku tattauna, idan da wani abu da take buƙata, ko take son ka yi mata, a harkar auren. Ba ina nufin na manta da mutuwar aisha bane ba, saboda abu ne da ba zamu manta da shi ba, musamman a yadda ya zo mana, amma rumaisa yarinya ce, aure abu ne da ake fatan ya zo wa mace sau ɗaya a rayuwarta, bai kamata a tauye mata hakkinta ba, ayi aurenta kamar mara galihu ba"
Baya son yi wa ammi musu, amma gaba ɗaya ba jin daɗin maganar yake yi ba, shiyasa kawai yake bin ta da to.
Sai da ammi ta gama magana, sannan ya tashi ya tafi, dan gaba ɗaya yau ba a gidan yake son kwana ba.
Yayi nafilfilinsa na dare, yana addu'a, ya idar zai miƙe aka kira shi a waya.
Sunan Bashir ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da faɗin "Malam bashir"
"Yallaɓai, ya gida ya aiki?"
"Alhamdilillah, ya naka aikin"
"Lafiya ƙalau, dama na kira ne na ji, ko zaka shigo ɗin?"
Adam ya ɗan yamutsa fuska ya ce "Bana jin daɗi ne, sai wani lokacin kawai"
Bashir ya ce "To shikenan, Allah ya ƙara afuwa, lambar nan da aka fara kiranka da ita, bayan sace madam, Sidi yayi bincike a kanta, ya turo mini bayanan wanda yayi register da layin".
Da sauri Adam ya gyara zama ya ce "Tom ina jinka, ya aka yi, kun gano shi?"
"Eh to, babu wata nasara dai, a gombe aka yi register da layin, na tura wakilai har wurin, abun da dai muka gano, mai wayar wani bafulatani ne, daga bisani ya bar gombe, irin fulanin nan ne na tashi, ya koma katsina, sai dai a katsinan ma da na je, na tarar an kai musu hari a rigarsu, an ƙona musu dabbobi, dan haka bana zaton shi mamallakin layin shi ne wanda yake da alhakin garkuwa da ita, akwai dai yadda aka yi".
Adam ya yi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki ya ce "To shikenan Bashir, na gode da ƙoƙarinka sosai"
Bashir ya ce "Adam, dan Allah kar ka damu ko ka karaya, ba zamu daina ba in sha Allah, sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi, ni dai jikina ya gama bani garkuwa da Aisha plan ne kawai, amma zamu cigaba da addu'a da kuma bincike"
Adam ya ce "To Allah ya iya mana".
"Amin ya Allah, ina boy, da rigimammiyar babarsa?"
Sai a yanzu Adam ya tuna an saka masa rana da shi da rumaisa.
Haka nan ya tsinci kansa da cewa Bashir "Yana nan ƙalau, an saka mana ranar aure ni da ita"
Waro ido bashir ya yi ya ce "Rumaisan?"
"Mmmm" ya amsa a taƙaice.
Wata dariya ce ta ƙwacewa Bashir ya ce "What a perfect match, amma kamar ta yi ƙarama da yawa fa"
"To ya zan yi, biyayya ne ga umarnin ammi".
"Kuma in sha Allah ba zaka taɓe ba, ni nayi maka murnar hakan wallahi, zamanku wuri guda zai sanya idan da wani abu da zai taimakawa bincikenmu da ta sani ta gaya maka"
Adam kawai ya girgiza kai, dan ya san azabar taurin kai irin na rumaisa kan a kai ga faruwar hakan, aiki ne ja.
"Na gode bashir, bari na ɗan kwanta"
"To shikenan ango, Allah ya tashemu lafiya" Adam ya ajiye wayar, ya lumshe idanunsa, abubuwa daban daban, suka cigaba da karakaina a cikin kansa.
Mai sunan baba kuwa wanka yayo, ya zo ya yi shirin kwanciya, lokacin ƙarfe goma da mintuna ashirin, har ya kwnata wayarsa ta fara haske, alamar ana kiransa.
Ya kalli wayar babu suna, dan haka ya gyara kwanciyarsa, sai dai har kusan sau uku ana kiran wayar. Ya saka hannu ya ɗau wayar, ya kara a kunnensa.
Ƴar siriryar muryarta, mai cike da shagwaɓa ya ji ta ce "Anty rumaisa, Allah ya sa baki yi bacci ba, gashi ya tashi"
Zirrrr ya ji wani abu ya tsirga masa, tun daga kansa har ƙafafuwansa, yayi shiru bai ce komai ba.
"Anty rumaisa, ko kin yi bacci ne? Ki yi magana mana".
"Ta yi barci" ya faɗa a taƙaice.
Babu tsammani ta ji muryar ta sa, a rikice ta ce "Innalillahi, yi haƙuri" ta kashe wayar ƙirjinta yana bugawa da sauri-sauri.
Ajiye wayar yayi yana jan guntun tsaki, ya juya bayansa yana mamakin, yadda take shaƙe muryarta a iya wuyanta tana magana, wata ƴar murya kamar ƴar tsanar roba.
Da asubar fari, rumaisa ta tashi ta fito, zata shiga banɗaki ta tarar da mutum a ciki, ta zuba ruwa a buta, ta zauna a gefe tana hamma.
Gajiya ta yi da zama, ta ce "Wai dan Allah waye a banɗakin nan, zan yi a tsakar gida fa".
Shiru aka yi ba a bata amsa ba, waɗanda suka yi alwala suka fara tafiya masallaci.
Usman ne ya buɗe ƙofar ya fito, yana hararta.
"Yaya usy wai dama kai ne a ciki? Wai dan Allah kai kullum sai ka yi wanka da asuba? Wankan me ka ke yi, ka yi da asuba, ka yi da safe zaka tafi makaranta, idan ka dawo da yamma ko da daddare sai ka yi, wanka da asuba ko sanyi baka...."
Buɗe baki yayi ya ce "Zan ci ubanki, saka mini ido ki ke yi ina ruwanki da ni".
Aliyu ne ya fito yana dariya, ya ce "Malam ka yi mata bayanin wankan uwar me kake yi da asuba?"
Tsuke fuska Usman ya yi ya ce "Ba na so"
"Meye ba ka so, tun da ba zai gaya miki ba, in anjima idan ya zo ɗakin mama ki tambayeta, wankan me yake yi da asuba?"
"Ai ba sai ta tambaya ba, ita da zata yi aure kwanan nan, za ta yi ita ma".
"Aliyu ya ce "Kai fa ba ka da hankali".
"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan wanka da asuba ba, sau ɗaya zan din ga yi a rana, lokacin sanyi ma wataran ba zan yi ba"
Usman "ke dalla tashi ki bar wurin nan, munafuka cctv Camera, wuce ki je ki yi abun da zaki yi ko na karya miki wuya" tashi ta yi ta ja butar ta sum-sum ta tafi banɗaki.
Yau asabar ce, dan haka bayan sallar asuba, mai sunan baba ya dawo ya kwanta barci, sai dai wajen ƙarfe takwas na safe, wayarsa ta ishe shi da vibration a ƙasan pillow.
Cikin bacci ya ɗau wayar, ya saka a kunne yana lumshe ido.
"Anty rumaisa, barka da safiya jiya ki ka yi bacci na kira kin yi barci".
"Ke! Ba wayarta bace kar ki sake kirana wayata ce ba tata ba" a wannan karon ma ba ƙaramar razana ta yi ba, cikin rawar murya ta ce "Yi haƙuri, na zata wayar mama ce".
"To ta umar ce, ki ka sake kirana ni da ke ne, an hana mutane barci tun jiya, ki yi ta wani yenyen, ba zaki buɗe baki ki yi magana ba" ya ƙarasa mitar yana kashe wayar.
Nusaiba da take gefenta ta ce "Wannan wane bala'e'en ne haka?" Iman ta girgiza kai ta ce "Ba kowa, ga Sabir nan bari na je na kwanta"
Nusaiba ta karɓi Sabir, ita kuma ta tashi ta tafi ɗakinta tana tunanin yadda mai sunan baba ya faɗa haka take magana.
Sunansa da ya faɗa umar ta sake maimaitawa, dole yayi masifa, ta faɗa a ranta.
Tana shiga ɗakinta ta ji tamkar an shaƙeta, kuma ta kasa gaba ta kasa baya, hannu ta saka tana riƙe wuyan nata, amma ta ji numfashinta yana neman ɗaukewa. Cikin fita hayyaci ta sulale Jikinta ta faɗi ƙasa.
Can katsina kuwa, Gwaggo har da taka rawa saboda murna, tana faɗin Allah ya dubi ƴar marainiyarta, za ta yi a gidan daraja, gidan sarauta gidan masu abun hannu.
Nan da nan ta ce ba zama, azo a kama wasu daga cikin dabbobinta a sayar, ta fara saye-sayen kayan da za a kai wa rumaisa.
Iman kuwa ba a tashi sanin halin da take ciki ba, sai bayan wasu awanni, da nusaiba ta ji ta shiru, ta shiga ɗakin ta tarar da ita a ƙasa a sume.
A kiɗime ta je ta sanar da ammi halin da ake ciki, ranga-ranga aka ɗauki Iman zuwa asibiti, ba tare da ta san waye a kanta ba ma.
***
Gidansu ruma kuwa, mama ma ta fara shirin tafiya kasuwa, domin fara saye-sayen da za a buƙata, dan ba ta taɓa kawo wa rumaisa aure yanzu ba, amma cikin ikon Allah, sai gashi ba tare da wani shiri ba, dan ko ƴan kwanuka ba ta fara saya ba.
Rumaisa na uwar ɗakan mama, tana ta zane-zanenta, mama sai mita take ba ta son zane-zanen nan, wataƙila ma zanen ne yake sanyata firgita cikin dare.
Rumaisa ta yi dariya ta ce "Haba mama, zanen ne zai tsortani, kin ganni nan kin san bana tsoron kowa sai Allah, balle wani zane".
"Kya ji da shi dai" ta yi maganar tana fita falo.
Yaya Abubakar ya yi sallama a falon mama, mama ta amsa masa ta ce "Garbatina ya aka yi ne?"
"Fita zaki yi ne?"
Mama ta ce "Eh, kasuwa zan shiga na fara saye-saye".
"To da magana nake son mu yi, amma idan kin dawo ma yi"
"A'a, zauna ka gaya mini sai na fita"
Suka zauna, Abubakar ya kalli mama ya ce "Mama, kamar yadda muka yi da ke, na je na ɗan zazzaga unguwar ina tambayar ya yanayin gidansu yake, da kuma shi kansa mu'amalarsa da mutane, to sai dai sakamakon baki ya rabu biyu. Wasu suk ce mutumin kirki ne, mai yawan kyauta, da girmama mutane kuma miskili ne, wasu kuma sun ce ba shi da kirki, yana da faɗa da zafin rai wai kwanan nan ya taka ƙaninsa da mota, ba wannan ne ya fi ɗaga mini hankali ba, wai ana kyautata zaton maye ne, kuma yana da taɓin hankali!!!
Ayshercool
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION,