Showing 72001 words to 75000 words out of 198763 words
Chapter 25 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt
da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin".
"Nima ban sani ba, cikina zai haɗe da ƙafata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku".
"Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu".
Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka buɗewa rumaisa file ya shiga da ita.
Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa.
Ta ce masa "Cikina ne da ƙafafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai".
Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?"
Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?".
Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?".
"Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa.
"Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne".
Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?"
Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban taɓa yi ba"
Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar? Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?".
"Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta.
Adam ya ce "Za ayi watanni takwas".
Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a.
Yayi counseling ɗin ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba.
Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya karɓa ya ja hannunta suka fita.
Ta bashi tausayi ba kaɗan ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba.
A durƙushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata.
Sai dai ta ce Allah karta ba za a buɗe mata jiki a ganta a gaban Adam ba.
Ga ciwo na cinta, ga zunzurutun wauta, in da Allah ya taimaka, nurse ɗin da take on duty mace ce.
Ƙarshe ta tsaya ayi allurar nan, ba ta tsaya ba, dai da adam ya fita, daga waje yana jiyo kukanta, sai ka ce ƴar shekara biyar, saboda an yi mata allura.
Sai dai ana gama yi mata allurar ta hau amai, kasancewar tun rana rabonta da abinci.
Aikuwa Adam ya din ga yi mata faɗa, na rashin cin abincin da ba ta yi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya tare da ita, ƙarshe sai da suka dangana da saka mata ruwa.
Haka Adam ya zauna da ita, har asuba a asibitin, aka gama yi mata abun da za ayi mata, na ƙarin ruwa da allaurai ya ɗauke ta zuwa gida.
Suna tafe a hanya ta samu barci, dama tun suna asibiti yayi sallar asuba.
Da ƙyar ya kaisu gida, saboda barccin da yake ji.
Sai da suka isa gida ya tasheta, ta fita daga motar tana takawa a hankali.
Baba uwani na jin tsayuwar motar, ta fito tana yi musu maraba, tana tambayar jikin rumaisa, Adam ya ce mata da sauƙi.
Suka nufi step ɗin bene, baba uwani ta sake cewa "Takawa ko zan zo na taimaka da wani abun ne?"
Ya ce "A'a ta warware, ciwon ciki ne dama, yanzu bacci za ta yi"
Ta ce "To shikenan babu laifi, Allah ya ƙara lafiya".
Ya amsa mata da Amin.
Sai da ya raka rumaisa har ɗakinta, sannan ya juya ya fita, sai dai yana fita ya ji kukanta ta na faɗin "Na shiga uku, zan mutu".
Da sauri ya koma yana tambayarta menene?.
Ta ɗage doguwar rigar jikinta, Jini na bin ƙafarta.
"Dan Allah ki yi wa mutane shiru da wannan koke-koken, maganin me zai yi miki?"
"Jinina ne zai ƙare, idan ya ƙare mutuwa zan yi".
"Ai gara ki mutun in huta, ki yi mini shiru ni, bari na yi wa baba uwani magana, ta zo ko da abun da zata taimaka miki da shi".
Da sauri ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka kirata, ka kirawo mini su Yaya usman a waya, dan Allah"
Kallonta yake, cike da mamakin wauta da rashin hankalinta.
"Ke wai ya ki ke so na yi ne?, shikenan ba zan huta ba saboda na aureki? Tun da ba za a kirata ba, sai ki wuce toilet ki gyara jikinki".
"Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin".
Guntun tsaki ya ja, ya wuce banɗakinta, ruwa ya haɗa mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banɗakin.
Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banɗakin, ya janyo akwatin lefenta, ya ɗauko mata pad, kasancewar lokacin da aka haɗa lefen har da ita a ciki.
Ya ɗauke bedsheet ɗin daga kan gadon.
Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banɗakin, tana ta raɓe-raɓe.
Ya kalleta ya ce "ƙazamar ina ce ke? Ba ta ɓaci da jini ba ki ka kuma sakawa?".
"To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.
Ajiye mata pad ɗin yayi, ya ɗauki bedsheet ɗin ya fice.
Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad ɗin na in da ya ajiyeta.
"Ba zaki saka bane?".
"Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani"
Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba.
Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad ɗin ta ɗaure a leda, ta canza phant ta canza wata.
Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata ɗakin.
Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haɗa da kayanta da ta cire suna banɗakinta.
Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice.
Ko da baba uwani ta ciro bedsheet ɗin, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya.
"Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ƴar tatsitsiyar ƴar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ƙarshenta ma na sha zagi".
Babban abun da ya yi wa rumaisa daɗi, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?"
Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daɗi, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka".
Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daɗin ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi"
"Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman".
Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karɓi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya.
Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai ɗaga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ƙaraci ringing ɗin ta, ta kaste yaƙi ɗagawa.
Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yayi sallama.
"Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma taƙi zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma"
"Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ƙorafi?".
"Mama taƙi ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya".
Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka? Meya sameki?".
"Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba".
Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ƙyaƙyace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo".
Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi"
Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?".
"Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa".
Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki".
"To ai ba wayata ba ce ba".
"Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ƙara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar ɗaukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar.
***
"Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves ɗin sa ne?".
"Ranka ya daɗe, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa".
"A'a fa, ka san yaron nan da wayon tsiya, kar in je lumbu-lumbu yake yi mini, yana wani binciken ta ƙarƙashin ƙasa, ko shirya wani abu da ban sani ba".
"Babu abun da yake aiwatarwa, ba tare da na san motsinsa ba, a yanzu dai haka babu ranka ya dade".
Ya juya ya kalli wakili ya ce "Khalifa, kai wurinka babu wani update ɗin".
Khalifa ya ɗan sauke numfashi ya ce "Babu Daddy, sai dai ina nan ina ta bin diddigin sa fiye da yadda ka ke tsammani, babu wani abu da yake yi s kanmu, sai dai wani ƙishin-ƙishin da nake ji, wai yarinyar da ya aura, ita ta tserato da ɗan sa daga wurin masu garkuwa da mutane, amma bani da tabbas, an ce in jira a samu tabbacin hakan".
Senator wakili ya jinjina kai ya ce "Duk yadda ake ciki ka sanar mini, idan har ita ɗin ce, ka samo mini tabbacin hakan, a kan lokaci".
"To shikenan, In sha Allah daddy"
***
A duk lokacin da rumaisa ta je canza pad, cikin ƙyanƙyami take yi, kuma a tsorace take da tunanin jininta zai ƙare, har sai da iman ta fuskanci wani abu, amms ba ta takura mata da son sanin menene ba, tun da ba ta gaya mata ba.
Mai sunan baba kuwa wuni yayi yana kallon missed call ɗin, iman a wayarsa, yana tunanin me za ta ce masa haka, da har ta yi masa 3missed calls, ko tana nufin ta ce Haryanzu ba ta san wayarsa ba ce ba?.
Gashi dai yana sane yayi ignoring kiran, amma yana son sanin dalilin kiran.
Yau sai da takawa ya dawo, sannan iman ta fara shirin tafiya gida, rumaisa ta din ga yi mata magiya a kan ta kwana, amma ta ce ba ta gaya wa ammi ba, direba ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita.
Takawa ya dubi ruma da ta haɗe rai saboda Iman ta tafi ya ce "Ya jikin naki?".
"Da sauƙi"
"Kin sha magungunan ko kuwa?".
"Na sha" ta amsa masa a taƙaice, bai sake kulata ba ya ƙyaleta, dan yanayin fuskarta ya nuna masa a fusace take, idan ya biye mata rashin kunya za ta yi masa.
Mai sunan baba kuwa, missed calls ɗin nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya ƙoƙarinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku.
Babban abun da ya ɓatawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira.
Iya ƙoƙarin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar.
Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi ɗakinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta ɗaga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama.
Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa.
"Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin ɗabi'arta ta iyayi.
"Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata.
Sai da ta ɗan ruɗe, amma ta yi iya yin ta, ta haɗa nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?".
"Lafiya ƙalau".
"Dama Anty Rumaisa ce ta karɓi aron wayata ta kiraka, kuma ba ka ɗaga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi haƙuri dan Allah" ta ƙarasa maganar kamar za ta saka masa kuka.
Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata ƴa da yake keɓewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin daɗin sauran muryarta.
Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?".
"Ɗazu ne na je gidanta, ba ta jin daɗi shi ne ta karɓi wayata, ta kira ka, amma ta ji sauƙi".
"Shikenan" ya katse wayar.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin daɗin kasancewa da shi ta waya. Wani guntun murmushi ta yi, tana ɗaga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo.
"Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale.
"Kamar yaya? Yayan Anty rumaisa ne".
"To meye alaƙarki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido.
Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai".
"Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata".
Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi ɗakinta.
Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sauƙi" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice.
***
Tun da Adam ya fara hawo wa step ɗin bene, yake jin ƙauri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnuƙe da hayaƙi, kuma hayaƙin daga kitchen yake fitowa.
A sukwane ya nufi kitchen ɗin, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ƙaurin manja.
"Ke meye haka? Me ki ke yi?"
Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"
Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin kashe gas ɗin, dan tuni suka haɗa baki da iman, direbanta ya ɗuro mata.
Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"
"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Buɗe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi saƙa mai kyau, sai ƙamshin attaruhu take.
Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".
Ta ce "Eh na yadda" ya gyaɗa kai ya fice.
Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya leƙa falo, ya hangota tana ta suɗar baki tana cin yaji.
Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.
Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving ɗin su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.
Tashi ya yi ya kunna fitilar ɗakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta ɓata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.
Bai ce mata uffan ba, ya ɗauki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.
A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ƴan kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ƙoƙarin tsafta.
Tea yake son haɗawa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.
Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka ɗauko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".
Ta taka kujera, ta buɗe wata drower, ta ɗauko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.
Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta ɗauki ƙaramin flask ta juye masa, ta haɗa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".
Kamar soko haka yake kallonta, ta ɗauki wani ɗan bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.
Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira ɗaya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne.
Ta karɓa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ƙyaleta su cigaba da kaiwa.
Ɗakinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banɗaki yana wanka, ta karkaɗe masa gadon, ta