Showing 144001 words to 147000 words out of 198763 words
Chapter 49 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt
yadda kayan nan suka yi miki kyau, rabon da na ga ko kwalli a idonki tun ranar biki, kamar na zuro baki nayi miki kiss"
Rufe baki tayi tana kallon anty laila, dan tana zaune a ƙasa.
"Daina juyawa kina kallonta, juyo sosai ni zaki kalla, so nake na tantance abun nan gaskiya ne, ko kuma yaudarata ake so ayi?"
"Wai me?" Rumaisa ta yi maganar cikin rashin fahimta, dan duk ba ta san akan me yake magana ba.
Ya ce "Zauna sosai, mana in ganki da kyau, juyo sosai".
"To ni ka daina yi mini wannan kallon mana, Allah zan kashe".
Sosai takawa yake dariya, ya ce "Laila you must explain this, you want scam me ba?".
Laila ta ce "Za ka ga scam ganin idonka, time off sai wani lokacin kuma".
Takawa ya ce "Wane time off kuma, laila zan kai ƙararki fa, ban gama ganinta ba, mimi look at me na" yayi maganar yana dariya.
"Papa ina ta so in ganka amma ka sakani a gaba sai dariya ka ke yi, kamar kaga comedy, shikenan ba zan ƙara video call ɗin da kai ba".
Ya ce "Haba little mimi, farinciki ne ya isheni na ganki, kar ki bar laila ta haɗamu, da na dawo zamu tafi honeymoon, mu yi spending so much time together, mu fanshe tsawon lokacin da muka yi bama tare, mu buga ball tare, mu yi gudu tare ko?"
"Eh kuma zaka goyani ma"
Dariya yake sosai ya ce "Ba zaki canza ba ai"
Ta ce "yauwwa meye honeymoon, zuma da kuma wata kenan?".
"Eh duniyar wata zamu je, mu sha zumar soyayya"
Ta buɗe baki ta ce "Innalillahi, soyayya har na ji kunya" laila ta kashe system ɗin ta ce "Sarkin shirme, sai kuma wani lokacin".
Adam kuwa dariya ya cigaba da yi ya ce "Daga tafiyata anya laila tana da gaskiya? Allah ya kaimu na dawo gidan. Mimi rigima".
***
Mai sunan baba ga damuwa ta addabe shi, amma ya rasa da wa zai yi sharing ɗin ta, ya kasa gayawa kowa, sai ƙumbiya-ƙumbiya yake yi.
Har gara Mahmud, ya ɗan saki jiki ya ce masa, da yana da hali da ya auri Iman.
Sai dai a hankali yake ƙara shaƙuwa da iman, yake kuma sake fuskantar ta, ita a rayuwarta sam ba ta ɗauki duniya da zafi ba, komai nata simple ne.
Waya yake yi da ita, zuciyarsa na azalzalarsa a kan yayi proposing ɗin ta, amma bai san yaya za ta kalli abun ba. Tana ta yi masa zancen shirin da suke yi a kan bikin saukar Alqur'ani da za ta yi.
"Yaya ake ciki game da maganar aurenki, kin samu wanda zaki aura nan da 3months ɗin ne? Na ga you are calm now".
Ta numfasa ta ce "A'a yaya umar, kamar yadda ka bani shawara ne, na barwa Allah komai ina ta addu'a, na san ya isar mini, na cigaba da gudanar da rayuwata"
"Duk cikin samarin naki, ba wanda zaki zaɓa ya fito?"
Iman ta ce "Ni bani da saurayi"
"Ban yadda ba".
"Yaya umar na daina soyayya, idan Allah ya kawo aure kawai zan yi, dama wasu wai an ce dan ina da kyau suke so na, idan suka ji bani da asali sai su fasa, wasu kuma dan ina gidan sarauta, idan suka ji bani da nasaba da sarauta sai su fasa".
"Mhmm ke baki yadda ki na da kyan ba? You are beautiful, ban taɓa cewa abu yayi kyau ba, amma na yadda Khadija mai kyau ce"
Iman ji tayi ya fasa mata kai, wani murmushi ya suɓuce mata, ba ta taɓa zaton mai sunan baba yana magana haka ba.
"Khadija"
"Na'am yaya umar"
"Ina son ganinki, zamu yi magana"
Kasa ɓoye farin cikinta tayi, ta ce "Yaya Umar yaushe zaka zo?"
"Zan zo in anjima da yamma, ina fatan ba zan janyo miki matsala ba?"
"A'a ba matsala, Allah ya kawo ka lafiya" bayan ya kashe wayar ta ce "Allah ya sa ya ce yana so na, am already in love with you yaya Umar".
Ammi ta samu a ɗaki, ta sanar da ita cewar za tayi baƙo, ammi ta ce "To shi kuma wanene?".
"Ammi wani ne"
"Iman, kar dan saboda wambai ya faɗi wannan maganar, ki je ki jajubo wanda ba mutumin kirki ba, dan ke ki ka ce ba zaki sake kulawa ba".
"Ba haka bane ammi, kawai dai na ji yakamata na sake bawa wani dama, ban sani ba ko za a dace"
Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya jishe mu alkhairi, na san dai za ayi surutu, ki kai muku kujera ta bayan sashin nan. Ni da kin gaya mini da wuri ma, da ba zan bari ki kawo shi gidan nan ba, kar aje a ɓata lamarin, Allah ya kawo shi lafiya. Ni dai ina sake gaya miki, ba a garaje a wurin zaɓar miji iman, kar takura da matsi, su sanya ki yi zaɓen tumun dare ".
"To ammi in sha Allah"
Kamar wannan ne karonta na farko da zata fara zance, murna da nishaɗi kawai take yi.
Nusaiba ta kalli yadda take ta shiga tana fita, tana haɗa masa abun da za ta karɓe shi "Lallai da gani wannan baƙon na musamman ne, yayi awon gaba da zuciyarki da yawa"
Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusy kenan".
"Iman kiyi haƙuri, a baya nayi ƙoƙarin goyon bayan uncle J, duk da ba kya son sa, sai daga baya na fuskanci lallai, akwai ƙalubale idan ki ka aure shi, na yadda da maganar rumaisa, wanda bai tausayawa mahaifinsa ba, yaushe zai tausaya miki. Kin san kodayaushe ni mai sonki ce, ban so ki da jabir, dan muzguna miki ba my Iman"
Iman ta tura baki ta ce "Gaskiya i feel bad, na ga kamar yayata ta daina so na, ba ta son abun da nake so"
Nusaiba ta dafata ta ce "Haba my iman, ke kin san ban da kamar ki, kawai dai wanda ki ke so ɗin ne, nake ganin kamar baku dace ba, ya fiye tsauri da jin kai. Kuma bana son mutane su yi miki dariya, ace duk wannan gwagwarmayar baki auri mutum na mussaman da zaki samu kwanciyar hankali ba, ba dan ina ƙyamar sa ba, amma kin san zaku fuskanci ƙalubale"
"Anty Nusaiba ba yadda ki ke tsammani bane, mutumin kirki ne, ba wulaƙanci ne da shi ba, miskili ne, ba jin kai ne da shi ba, kama mutunci ne da rashin son raini, amma mutum ne mai tausayi sosai. A yanzu ba dukiya nake nema ba anty nusaiba, kwanciyar hankali da soyayya.ki yi mini Addu'a, idan shi ne allhairina, Allah ya tabattar mini, amma kar ki gayawa ammi tukuna, sai yazo yau na ji me zai ce mini"
"Kar ki damu, ina yi miki fatan alkhairi ko yaushe ƙanwata".
"Na gode yayata ta kaina" Nusaiba ta yi murmushi ta fice daga kitchen ɗin.
Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daɗi, sai dai an rasa wanda zai yi magana, kasancewar shi wannan ne zuwansa na farko zance, ita kuma yayi mata kwarjinin da ya saba, ko ɗaga kai ta kasa, sai kallon wuri ɗaya kamar mara gaskiya.
"Ki yi tayi mini surutu a waya, har na rasa abun cewa, amma yanzu kin sakani a gaba kina sunkuyar da kai, kamar kinga dodo, daga gaisawa kin yi shiru".
Muryar nan ba ƙaramin narka mata zuciya take yi ba, murmushi ta kuma yi ta sunkuyar da kai.
"Shikenan, Khadija ɗago in gaya miki dalilin zuwana wurinki" da ƙyar ta ɗan ɗaga kai.
"Kallona zaki yi, bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ƙanwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taɓa gwadawa ba ma.
Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?"
'Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji' ta tambayi kanta.
"Ba kya son talaka ko?'
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Talk"
"A'a yaya umar" tayi maganar muryarta na rawa.
Umar ya ɗan tsura mata ido ya ce "Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faɗa, ba ta ji ne, but am good person ko?"
Ta ce "Yes you are".
"Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu"
Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daɗe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi baƙin tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba.
Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ƙamshin turaren mai sunan baba take ji.
Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku.
Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama.
Suna zaune a falon, suna kallo, suna taɓa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye baƙonta ya kuma suka yi da shi?.
Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama.
Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ƙarasa gaban iman, ya bata envelope ya ce "Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki"
Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar ɗin yake nufi ba.
Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce "Wanda ya zo wurinki ɗazu" sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope ɗin.
Laila ta ce "Iman, sai ɓoye-ɓoye ki ke yi, yakamata ayi mana ƙarin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki" tayi maganar cikin wasa.
Mahmud ya kalli Ammi ya ce "Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?"
Jiki na rawa ammi ta ce "Ni, eh mana Mahmud mai ze hana".
"Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?" Rumaisa ta faɗa lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi.
Bai ce komai ba ya ɗan murmusa, ruma ta ce "Waye ya kawo mana lemo?"
Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce "ko ciki zamu shiga ne?"
Ya ce "To"
Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin ɗaci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru.
A ɓangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ƙwace mata shi, ta ƙarfin tsiya.
A bedroom ɗin ta suka tsaya, ta ƙarasa ta saka hannunta, tana sake kaɗe masa makeken gadonta, da yake a ɗame da bedsheet fes da shi ta ce "Bismillah zo ka zauna"
Ya nemi wuri ya zauna a ƙasan carfet, ya ce "ki zauna, ni nan ya isa"
"To nima bari na zauna a nan ɗin, ai ba wani abu" ta zauna a ƙasa kusa da shi.
Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, farincikin ta ya kasa ɓuya, sai ƙoƙarin mayar da hawaye take yi.
Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce "Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma ɗan mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman ɗin zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaɗan ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo".
Ammi ta ce "In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wulaƙanta mini ita ba, ba damuwa, zan iya ɗaukar ɗawainiyar komai ni nayi masa".
"Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ƙoƙarin sa a kan kula da ita."
"Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haɗa mana kanku gaba ɗaya ƴaƴan galadima".
"Amin ammi na gode" ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshsheƙar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye.
Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi.
Ruma ta ce "Ammi, me yayi miki me ya ce miki? Ɓata miki rai yayi?"
Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta riƙe hannun ruma ta ce "Bayan tsawon shekaru, da fidda ran ɗa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, ɗa na ya kusa dawowa gareni, duk ƙoƙarin ki ne rumaisa na gode"
Rumaisa kasa riƙe hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce "Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi"
Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu'a, da ita da iyayenta.
"Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke ƴa ta".
Laila ta ce "To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani".
Nusaiba ta ce "Muna zaune ta yi mana wayo, ta ƙwace mana ammi ba".
Bisa kasada umar yayi proposing ɗin Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji.
Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan.
Ta ɗan numfasa ta ce "Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da baƙonta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa"
Laila ta ce "Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai"
Ammi ta ɗan waro ido ta ce "Mai sunan baba wai?"
"Eh ina ga shi ne"
Ammi ta ce "Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara'a baya son mutane, mamansa na yawan faɗar zafin ransa".
Laila ta ce "Ammi ki yi musu addu'a kawai, ke ba ga ɗanki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin "
Ammi ta ce "Haka ne, Allah ya sa kar a samu matsala daga baya, bari na ji ta bakin Iman ɗin, sai mu ga abun da yakamata ayi".
Laila ta ce "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya sa daga haka a samu ƙarshen wannan matsalar.
Ammi ta amsa da Amin.
Takawa na tsaye a valcony, hannunsa ɗaya riƙe da kofin tea, ɗaya kuma da takardar zanen da rumaisa ta saka masa a kayansa, sai dai kurman zane tayi, ba tare da bayanin komai ba, kuma da alama saƙo ne mai muhimmanci take son isar masa a zanen.
Kusan kullum sai ya kalli zanen nan, kuma kamar yadda ta ce kar ya tambaye ta, yasan da zarar ya matsa, ba lallai ta yi bayani.
Babban abun da ya fi ɗaukar hankalinsa, shi ne SMOKE, da ta rubuta da manyan baƙaƙe, sai daji da ta zana da dogayen bishiyu, sai aisha durƙushe a gefen bishiya ta riƙe ciki.
"Mimi what's the meaning of this?" Yayu maganar yana shafa zanen, hawayen sa na ɗiga a kan zanen.
***
Litattafai ne a gaban Iman, tana karatu, Ammi tayi sallama, Iman ta amsa.
"Sarki littafi, ina fatan kin gama karɓo komai, da za ayi amfani da shi na bikin saukar?".
"Eh ammina, everything is ready"
Ammi ta miƙa mata leda ta ce "Sidi ya kawo, ya ce a baki in ji umar"
Iman ta karɓa ta duba, keyholders ne, da jotter yayi mata na sauka.
"Auta haryanzu baki ce mini komai a kan yadda ake ciki ba, kin amince da mai sunan baban, kina ganin babu matsala?"
Iman ta ɗago da sauri, ba ta zaci ammi ta san waye ba.
"Ko da baki gaya mini, na gane waye, amma iman kina ganin babu matsala? Zaki iya zama da shi?"
Iman ta jinjina kai ta ce "Ammi yana da kirki"
Ammi ta yi murmushi ta ce "So hana ganin laifi, amma ya san halin da ake ciki, ya amince da hakan?"
"Eh ya sani".
"To Alhamdilillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" ammi ta tashi ta fita.
Iman ta bi Ammi da kallo har ta fice.
Mai sunan baba yana zaune a gaban mama, yana cin abinci, duk suna tare da su Aliyu, Abubakar yana kwance a gefen mama yana danna waya.
"Babana" mama ta kira sunansa.
A hankali ya ɗaga kai ya kalli mama.
"Ashe neman aure ka ke ban sani ba?"
Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon mai sunan baba.
"Mun yi waya da hajiya, ta ce sun baka dama ka fito, sai dai ban san zancen ba sai ɗazu da ta kirani a waya".
Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI