Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 198763 words

Chapter 23 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt

Ads the beginning of article before Image

30 Jun 2024

2363

Ads at the middle of Article

da aka faɗa tana da amsar bayarwa..


Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta.


Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen.


Iman ta shigo ta ce "Yaya ku fito".


Ya ce "To, muna zuwa"


Ya sake kallon rumaisa ya ce "Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself"


Ta yi ƙuri da ido tana kallonsa. "Am talking to you" yayi maganar a ɗan kausashe.


"To" ta amsa a hankali.


Miƙa hannu yayi zai riƙo nata, ta janye a ɗan razane.


Ta girgiza kai ta ce "Ka daina taɓani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka riƙe mini hannu".


Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ikon Allah, to mu je" da ƙyar ta yadda suka jera, suka fita.


Suna fita aka din ga rafsa guɗa, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura.


Suka ƙarasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu'a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ƙuri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar.


Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta miƙawa adam hannu ta ce "Ban ga ka fito da ƙyalle ba, dan mu tabattar da me ka aura".


Ya ce "Haba jakadiya, wannan al'adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?" Yayi maganar yana kallon rumaisa.


Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?.


"To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka buƙaci gani, kar mu je saura aka kawo mana".


Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi.


Sai da ƙirjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce "Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan"


Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga ɗakin, na kwana a ƙasa, meye wani abun alfahari.


Ƴan uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce "Dama ɗaki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida".


Da sauri rumaisa ta ce "Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama".


Adam ya ce "Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a ɗan tayata zama"


Gwaggo ta ce "A'a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga saƙonki nan babarki tana gaishe ki"


Tashi rumaisa ke ƙoƙarin yi, amma ya riƙeta, ya hanata tashi.


"Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?" Ta yi maganar tana kuka.


Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo.


Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya"


Ta ce "Babu komai, Allah ya sanya alkhairi"


Ya ji daɗin tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba.




Ɗago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faɗin "Is ok, yi haƙuri kukan ya isa haka"


Ƙoƙarin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ƙyaleshi.




Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koɗa yadda gida yayi kyau.


Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce "Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taɓa zaton zaka auri ƙaramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ƙaramar yarinyar ce ta kuɓuta da Sabir, daga hannun 'yan bindiga"


"Ai babu mamaki a ikon Allah, ƙanƙantarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saɓawa shari'a ba".


Ta kalli rumaisa ta ce "Sannu ƴar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan ɗauka"


Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama.


Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara.


Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faɗe-faɗen maganganun su, da yada habaici.


Da azahar ɗin kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana.


Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi.




Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata ɗakinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe ɗin ta, ga su iman nan, su tayata a haɗa mata ɗakin.


Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi.




Tana ƙoƙarin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce "Bar shi, zan yi da kaina"


Kallonta suka yi gaba ɗaya,Nusaiba ta ce "Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so"


Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi".




Nusaiba ta ce "To shikenan, baba uwani ƙyale mata".




Adam ya shigo ɗakin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan.


Nusaiba ta ce "A'a ta ce a ƙyale mata, za ta yi abun ta da kanta".


"Shikenan, ku ƙyale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la'asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba".


"A'a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?".


Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce "Do as i said"




Baba uwani ta yi mamakin yadda ƙiri-ƙiri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa taƙi. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo.




Sannan ta yi mamakin yadda suka haɗu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara ɓoye mata wasu abubuwan.


Kan su ƙarasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ƙarasa gida.




Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce "Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi".


"Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru".


Iman ta ce "Ammi kin san me?"


"A'a sai kin faɗa".


"Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ƙyalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun 'yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama"


Ammi ta yi shiru ta ce "Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam da rumaisa, sai ya bawa mara ɗa kunya in sha Allah".


Nusaiba ta ce "Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wataƙila Mummy ce zata saka su, ai daɗinta maman Sabir ɗin ma ba kanwar lasa ba ce".








Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faɗa sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa'a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya.


Mummy ta kalleta ta ce "Ya aka yi?".


"Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ƙyalle, ya ce wannan tsohuwar al'ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya....


Samha ta ce "Dakata, ƙarya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ƙarya yake babu abun da ya faru"
Mummy ta ce "Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace".


Ta risuna ta ce "In sha Allah uwar ɗakina".




Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window ɗakinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo.




A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ƙasan bene bata taɓa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ƴan gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta ɗan rage damuwa, da yin la'asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta.




A kwana na huɗu ya lura, tana gujewa haɗuwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai.


Bayan sallar magariba ya shiga ɗakinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru.


Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya.


Ƙasan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ƙasan benen.


Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buɗe gaban motar ya ce ta shiga.


Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar.


Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huɗu, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan.


Security light duk ta haske ko ina a gidan.


Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.


Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.


Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita"


"Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta"


Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.


Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki"


Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman".


"Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai"


"To ni kaɗai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka"


Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga ɗebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta".


Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, ɗauke da Sabir a hannunta.


Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman"


Rumaisa ta ce "Mata ina wuni"


Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa"


Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu.
Adam ya ce "Kai, kwana huɗu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki ɗauke shi"


Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.


Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir.


Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haɗo mini kayansa, na tafi da shi ko?"


Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a ɗauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata".


Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faɗi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.








Ayshercool
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*




Rumaisa kasa cewa komai ta yi sai jinjinawa ammi kai, baba uwani kuwa har da shewa tana juyi, tana yi wa ammi godiya da karamcin da ta yi mata, a matsayin wadda za ta je ta yi guiding ɗin ma'aikatan gidan takawa.


Ammi ta yi wa Adam alamar ya bi ta, ya tashi ya bi bayanta ɗakinta, ta kalleshi ta ce "Takawa, na san auren nan ba son ka bane, zaɓina ne amma dan Allah ina sake roƙon alfarmarka, ka yi haƙuri da yarinyar nan, komai zai wuce zaka yi alfahari da auren nan, ka ga yarinya ce ƙarama, dole za ta yi ta koke-koke na rabata da gida da ka yi, dan Allah ka yi haƙuri da ita. Ko dai wani abun ka yi mata?"


Ware ido ya yi ya ce "Ba abun da na yi mata wallahi".


"A'a takawa, dan Allah ayi haƙuri a bata lokaci, yarinya ce sosai sai ka yi haƙuri"


Adam wata irin kunya ce ta kama shi, ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya nutse don kunya, ya girgiza kai ya ce "Ban yi mata komai ba"


"Na ji ba wai ina son jin sirrin aurenku ba ne, amma dan Allah ka kula da ita, next week idan Allah ya kai mu za a koma makaranta ko?"


Ya ce "Eh, na biya komai ma, ana komawa zan kaita sai kuma na samo direban da zai din ga ɗaukota idan bana nan"


Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya ƙara buɗi"


Suka fito, Ammi ta ce a zubawa su takawa abinci su tafi da shi.


Ammi dai ta lura gaba ɗaya jikin rumaisa a sanyaye yake, har ta fara tunanin ko takawa dai yayi mata wani abun ne.


Ammi ta zauna a kusa da ita, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Rumaisa, ko akwai wata matsala ne?"


Ruma ta girgiza kai alamar a'a.


"To ki yi haƙuri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi haƙuri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi haƙuri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ƙalubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ƙaunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ƙannensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi haƙuri kin ji rumaisana".


Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah "


Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi.


Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taɓata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba ɗaukar ki zan yi ba" da haka suka ƙarasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta.


Washegari da safe, ta tashi tana ɗan goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles ɗin.


Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ƙuri da ido, ba ta yi magana ba.


"Baki iya gaisuwa bane?"


Ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba"


"Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki.
Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina buƙatar wani abu?"


Ta girgiza masa kai alamar a'a.


"To ki zauna wuri ɗaya, banda taɓe-taɓen abun da ban saka ki ba".


"To sai yaushe zaka dawo?".


"Lokacin da Allah ya yi".


"Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji"


***
Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan.


Kasancewar bayan mai hoton da ɓangaren su Adam suka ɗauko, Abdallah ma ya ɗauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura su group ɗin su, na ƴan gidan.


Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan ɗan shiga kasuwa, hotunan suka shigo.
Suna da yawa ya sauke su, ya fara buɗewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ƙanwarsa.
Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman ɗin, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman.
Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu.


***
"Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya ɓoye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads