Showing 63001 words to 66000 words out of 198763 words
Chapter 22 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt
da wannan maganar"
"Sorry sir"
Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya ɗaukar pose ɗin ta, ya buɗe, ga sababbin kuɗi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya riƙeta a hannun sa.
Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya.
A ƙofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ƙaraso, ya sauke glass ɗin motar, gaba ɗaya suka ƙaraso.
"Ta yi bacci fa" ya faɗa yana kallon Usman.
Usman ya ce "Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar ƴar kaza".
Adam ya ɗagata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi.
Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ƙanwarsa a kwance a jikin wani ƙato. Takawa ya ɗaga kai suka haɗa ido da shi, ya wani cukule fuska.
Aliyu ya zura hannunsa, ya ɗauko rumaisa gaba ɗaya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce "Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karɓa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai"
Aliyu ya ce "Tuba nake, zan kula sosai"
Juyawa mai sunan baba ya yi, ya shiga gida, ƙasan zuciyarsa istigfari, da tunanin meye nasa na jin haushi kuma, bayan komai daɗewa dole wataran ta zama matar wani.
Aliyu ya shimfiɗe rumaisa a katifar mama, Gwaggo cewa take "Wannan an yi shashasha amarya, haka take da wannan nauyin bacci haka, ta bar mutane da dakonta".
Mama ta ce a tasheta ta yi sallar isha'i, lawisa ta ce sun yi salla a gidan kwalliya, kafin su tafi.
Tana magagin, mama ta dafa ruwa, ta kaita banɗaki ta wanke mata fuska, ta yi mata wanka tas, ta lulluɓota ta kawota ɗaki, ƴan biki na ta yi mata dariya, sai dai har a cikin ranta ji take ruman ba ta wuce wankan ba, ƙaddarar aure zata rabata da ƴar da take matuƙar ƙauna.
Ɗakin samarin nan kuwa, kusan kwana suka yi babu bacci, suna ta ɗan tattaunawa, a kan biki, da kuma jajanta rabuwa da tilon ƙanwarsu, kuma kallabi a cikin rawunansu.
Mai sunan baba kuwa ya naɗe, ya lumshe idanunsa ya yi shiru, ba abun da yake ganowa sai kai wa da komowar iman a wurin nan, da yadda suke yawan haɗa ido. Tsaki ya ja ya nemi wuri ya kwanta, sai dai tunanin gobe dai-dai lokacin, rumaisa na gidan wani, ya hana shi bacci, ya din ga yi mata addu'ar shiga gidan miji a sa'a.
Bayan idar da sallar juma'a, aka ɗaura auren rumaisa da adam, ƴan unguwar da basu san waye mijin ba a ranar suka ji.
Unguwar ta cika da dawakai, da manyan motoci na alfarma, duk in da ka kalla, jami'an tsaro da kuma masu rawuna ne.
Sai dai tun da aka ɗaura auren nan, rumaisa jikinta yayi sanyi, take ta uban kuka, duk yadda aka so rarrashinta abun ya gagara.
Tuni hotunan biki suka zaga duniya, kowa da abun da yake tofawa, na alkhairi da akasin haka.
Samha kuwa kaiwa take ta yi tana komowa a ɗakinta, tana fatan aikin da ta bayar ayi mata, ya yiwu ba tare da samun wata matsala ko akasi ba, dan ta riga ta ƙudirce wa kan ta ɗaukar fansa, ko da tsiya ko da arziki.
Ammi a wani event center, ta shirya taron wunin bikin, sai dai abu ya so ya zama rigima, in da facalolinta da masu goya wa mummy baya, suka din ga ci mata mutunci, wai saboda Aisha ba ƴar ta ba ce, ta shirya irin wannan biki haka, kuma aka samo yarinya mara galihu ta aurawa mahaukacin ɗan ta.
Duk yadda ammi ta so jurewa sai da ta kusa zubar da hawaye, Nusaiba ba ta da hayaniya, balle iman, Laila ce masifaffiya dama, kuma ba ta ƙasar da ita kaɗai ta ishi duk wani mai bakin magana.
Da la'asar mama ta kira ammi, ta ce mata za a kawo rumaisa nan wurinta, ta gaisheta ta yi mata faɗa, sannan a wuce da ita gidanta, ammi ta ce ba sai an kawota ba, saboda wasu dalilai, zuwa magariba zata turo da waɗanda zasu ɗauki rumaisa.
A yammacin aka yi kilisar dawakai, takawa ya haɗe cikin kayan sarauta, rumaisa ma aka yi mata ado da alkyabba, aka yi ta musu hotuna.
Da magariba rumaisa ta yi wanka, ido duk ya kumbura saboda kuka, Yasir da ya shiga ya fita ya ga tana kuka, shi ma sai ya fashe da kuka, ta tashi ta saka kaya ma abu ya gagara mama sai daurewa take yi, amma hawaye ya cika mata ido.
Jiki a sanyaye mai sunan baba ya shiga ɗakin, ya tarar da ita a zaune, tana kuka mai taɓa zuciya.
"Rumaisa" ya kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleshi.
"Tashi ki saka kayanki, kar dare yayi sosai".
"Dan Allah mai sunan baba ku yi haƙuri, wallahi na fasa ni ba zan tafi na barku ba, mama dan Allah ku yafe mini ku barni na zauna a gida, ni ba zan iya rayuwa babu ku ba" tayi maganar cikin kuka.
"Tom, mun ji, amma fara saka kayan" da ƙyar ya saka kaya, ya ciro turare a aljihunsa ya fesheta da shi, mata sai rangaɗa guɗa ake yi.
Ta riƙe mama tana wani irin kuka.
Ya saka hannu ya cire nata daga jikin mama, ya ja hannunta yayi waje da ita.
Suna fita mama ta shiga ɗaki, ta fashe da kuka, dan an kai in da ba zata iya jurewa ba.
Suna tafe a mota tana kwamce a jikin mai sunan baba, tana ta kuka, kamar ta shiɗe.
"Am sorry, kiyi haƙuri haka lamarin aure yake, da haka kowace mace take tara nata iyalin, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, ya sanya alkhairi. Ban da rashin kunya da raina miji, mijinki ne ibada zaki je ki yi, ki nemi aljanna na san duk an gaya miki, ki girmama mahaifiyarsa, matar nan ina ganin mutuncinta saboda son da take yi miki. Sannan kuma Sabir ko Allah ya baki naki ɗan, kar ki canza soyayyar da ki ke yi masa, ki yi haƙuri ki saka a ranki, ƙofar sabon ƙalubale zaki buɗe ki shiga. Duk da ƙanƙantarki nauyin aure ya hau kanki sai haƙuri, kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, ki jure ki daure duk ƙalubalen da zaki fuskanta wataran sai labari, ina yi miki addu'a Allah ya sassauta miki jarrabawar gidan aure, don babu auren da babu jarrabawa"
Haka ya din ga yi mata nasiha, har suka je gidan, gida ya tsaru kamar ba na rumaisa ba, ko ina ya ji kaya.
Ana kai rumaisa wata ƙanwar ammi, ta sake saka mata alkyabba a kan kayanta, suka din ga yi mata guɗa a ka, amarya ƙanwar maza, dan su suka kawota ɗakin ma.
Sun daɗe tare da rumaisa, kowa da irin faɗan da yake yi mata. Sai da kowa ya watse, Tawagar angwaye suka ƙaraso, gida ba kowa sai tsirarin mutane da zabga-zabgan ƙarti.
Suna zuwa mai sunan baba ya tashi ya ce su tafi.
Rumaisa ta riƙe rigarsa ta tashi tana kuka "Dan Allah yaya umar, kar ku tafi ku barni, ku tafi da ni, ko ku zauna da ni a nan ɗin, dan Allah yaya. Yaya usy, yaya Abubakar, dan Allah duk ku zauna, Abdallah kar ku tafi, Yasir dan Allah" mai sunan baba duk ya kaɗa musu kai alamar su tafi.
Iman tana cikin waɗanda suka rage, gaba ɗaya tausayin rumaisa ya cika mata zuciya.
A hankali ya fincike rigarsa daga hannunta, ya juya, ta sake riƙo rigarsa.
Ya juya a kausashe ya ce "Wuce ki je ki zauna" a razane ta saki rigar ta sa tana kuka.
Yana juyawa sai hawaye, karo na farko da abu ya daki zuciyarsa ya saka shi kuka. Ya saka hanky ya goge, ya kalli Adam ya ce "Ga ta nan amana ce, marainiya ce, ko ka ci, ko kula da ita" yayi maganar wasu hawayen na cika masa ido.
Adam har mamaki yake, wace irin soyayya suke nuna wa rumaisa haka.
Bashir ya ce "Za a riƙe amana in sha Allah. Yallaɓai aje a rarrasheta dan Allah, tana cikin damuwa".
Adam ya ce "Sai ma ka faɗa? Ba daga ni sai ita zaku tafi ku bari, wannan kuma ya rage nawa" dariya abokansa suka yi, suka yi musu addu'a sannan suka watse.
Ya koma ya shiga ɗakin na ta, tana tsaye tana ta kuka, ya ƙare mata kallo sannan ya ce
"Yau sarki mai koriyar alkyabba, ya baki alkyabba saura ɗana ki a kan doki. Sannan ke kuma ki cika alƙawarin sanya shi durƙusa miki a kan gwiwoyinsa".
What's app only please 🙏
Ayshercool.
0808101214
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce "Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu".
"Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na ɗauko ki ba".
"Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba".
Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta riƙe hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji.
Ya sake kallonta ya ce "You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini ɗaki, wancan ɗakunan zaki ɗauki ɗaya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can" ya ƙarasa maganar yana sakar mata baki.
"Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki"
"Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ƙarata" ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom ɗin.
Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banɗaki.
Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka.
Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa.
Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ƙyam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauke shi.
Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa, ta duƙunƙune a cikin alkyabbar ta hau bacci.
Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin ɗaukar ta.
Haka ma ƴan mazan nan, Aliyu cewa yake "Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ƙarama wallahi".
Usman ya ce "To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?"
"A'a addu'a kawai nake yi"
Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faɗa da ya haɗa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faɗa ba, haka suka kai har wurin ƙarfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure.
Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam.
Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matuƙar tafasa da wani irin masifaffen kishi.
Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba.
Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banɗaki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a ɗaki.
Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faɗi, dan ya ɗauka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich ɗin ɗakin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke wai a nan ki ka kwana?" Yayi maganar yana taɓa ta.
Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi.
"Tashi, ki je ki yi salla" nan ma bata tashi ba.
Toilet ya shiga ya ɗebo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska.
A rikice ta tashi tana faɗin "Huzaifa meye haka wai?".
"Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini ɗaki ki tafi ga naki can ba"
Maimakon ta yi magana, sai ta haɗe rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba.
Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya riƙe hannunta ya yi waje da ita, ɗaya bedroom ɗin ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta.
Kallon ɗakin ta yi, wasu furnitures ɗin ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai.
Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma ɗakin da aka fara kai ta, wato ɗakin da Adam ya ce nasa ne, ta buɗe drower ya ɗau hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguɗa baki take ita kaɗai tana harare-harare.
Ta koma ɗakinta, ta yi salla, ta idar ko addu'a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli ɗakin sai ƙamshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba.
"Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su ɗauki ɗakin ƙasa, ko shi baban sabir ya koma ƙasa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu" ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta.
Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet ɗin.
Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi.
Shiru ta ɗan yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce "In sha Allah sai na fita na koma gida".
"Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan, baƙi sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ƙasa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba".
Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce "To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba".
Mamaki ne ya kama shi, baƙar magana rumaisa ta gaya masa.
Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce "Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je"
"To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?"
"Wuce mu je na ce" ya faɗa a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa ɗakinsa.
Ya nuna mata banɗaki ya ce "Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ƙasa suna jiranki".
Sai da ta gama kalle-kallenta a banɗaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a jiƙe, alamar yayi amfani da shi.
"Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba"
Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito.
Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buɗe wardrobe ya ɗauko, kaya ya tsaya ta gama shafa man.
Ya kalleta ya ce "Ga kaya nan ki canza".
Ta karɓa ta ce "To a gabanka zan canza kayan?".
"Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?"
Zare masa ido ta yi, ya ce "Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani"
Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta.
Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito.
Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta.
Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace ɗin yayi mata kyau sosai. Ba wani iya ɗauri ta yi ba, dan haka kawai ta ɗora ɗankwalin a kanta.
Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi.
Iman ta ce "Amaryar takawa, ina kwana"
Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta.
Ya kalli iman ya ce "Ta yi a haka?"
"Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a ɗan yi kwalliya sama-sama".
Rumaisa ta ce "Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a ɗaɗɗaure kamar ba ta wa ba".
Iman ta ce "Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya".
Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu.
Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daɗi, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta ɗaura mata ɗankwali.
Adam ya ce "Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi" Iman ta jinjina kai ta fita.
Ya kalli rumaisa ya ce "Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba".
"Kidnapping ɗina zaka yi kenan?" Ta yi maganar tana kallon sa.
"Eh" ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun