Header Ads
Showing 96001 words to 99000 words out of 198763 words

Chapter 33 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt

Ads the beginning of article before Image

30 Jun 2024

2386

Ads at the middle of Article

ɗan sunkuyar da kai ta ce "Barka da yamma yaya umar"


Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ƙare mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa.






Ayshercool
08081012143
What's app only please, ban da kira please 🙏.
₦500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank.
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels


Susbcribe my YouTube channel please 🙏






Jin shirun ya yi yawa, sai da ta yi zaton, ko wayar ya katse, ta sake ɗaga kanta, ta ce "Ina wuni yaya umar?".


Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Lafiya ƙalau, ya mutan gidan?".


Cikin jin daɗi ta ce "Suna nan lafiya, ya mama da su Yaya Aliyu"


"Lafiya ƙalau, na ga message ɗin wannan Yarinyar ne, na mijinta ba shi da lafiya". Yayi maganar yana sake fatan iman ta ɗago kanta ya kalleta, ko ya cigaba da jin nutsuwa a zuciyarsa.


Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta ce "Eh, ba shi da lafiya, su na gida ita da shi".


"Za su koma gidansu yau ne, ko su na nan?"


"Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi".


"No ƙyaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir".


Murmushi ta yi ta ɗan ɗago ta ce "To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai".


"Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi".


"To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya"


Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faɗar sunan.


Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so.


Girgiza kansa ya yi ya ce "Ya salam, why? Why? Abun da ban taɓa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni" ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene.


A ƙasan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman.


Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction ɗin ta, ta ƙarasa wurinsa ta ce masa "Wai dama ka tashi, ina ammin?".


"Ta fita ita da Nusaiba" ya bata amsa.


Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce "To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?"


"To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba".


"Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo" ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa.


Murmushi ya yi, da sai da haƙoransa suka bayyana, ya ce "Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma".


"Wane irin wulaƙanci ne, ina magana da ɗan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?"


Rumaisa ta kalli Samha ta ce "Au dama ɗan uwanku ne? To ni kuma ƙarewar ƴan uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me ɗan uwa?"


"Shut up" yayi maganar yana matse mata baki.


"To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?" Kallonta kawai yake yi.


"To ina ruwana. ka ci abinci ne?"


Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni".


Ɗan shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ƙarya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar shaƙuwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taɓa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.


Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sauƙi jikin?"


"Eh, Alhamdilillah"


"To sannu, ka tashi mu tafi gida"


Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba"


Miƙewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.


"Kuma duk mai kula mijin wata, ɗan wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin ɗaga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ƙwafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta ɗora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.


Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.


"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani"


Bai ce uffan ba, ya ƙara lafewa, yana sauke numfashi.


Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.


"Ita ma haka ka yi mata ko?"


"Ita wa?"


"Wannan matar da ta fita yanzu".


"Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai.


Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa"


Yayi ƴar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi".


Ya kalleta ya ce "Wani alƙawarin ki ka yi wa fulani?"


Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faɗa ba. Kuma gaskiya ka ɗagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini ɗazu, ƙasusuwana sai ciwo suke yi".


Bai ɗagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.


***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana ɓata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ƴar uwata, ni da a tunanina, na lallaɓata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?"


Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ƙi magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi".


"Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?"


Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi"


"Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma shaƙe mutane yake yi".


Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.


Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.


Can kuma ta ce "Tashi, in ɗauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki".


Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba"


"Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami".


"Mimi"


"Na'am basarake"


"Meyasa ki ka faɗi maganar ɗazu?"


Ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Wacce?".


"A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?".


Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ƙarya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba ɗaya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....."


Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta ɗaure ni tamau da sarƙa, ko ta din ga dukana da sarƙar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taɓa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?"


Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya ɓaci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da ɗan kirki kaɗan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo"


Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?".


"Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ƙara girma na auri Yaya Mahmud" ƙuri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.


Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri ɗaya.


Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faɗa na ƙarshe bai yi masa daɗi ba.


***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ƙasan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.


Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karɓo masa, sai dai ta bar shi ya ɗan farfaɗo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.


Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.


Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.


Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci"


Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.


"Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya ɗan tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah"


Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaɓe baki.


Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message ɗin mai sunan baba.


Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ƙanan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.


Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.


Unexpectedly ya ɗaga kai ya ga Iman, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Sannu da zuwa yaya umar".


"Yauwwa sannunki" daga nan ta yi masa jagora, har ciki.


Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya ɗauki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu.


"Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?" Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir.


Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haɗe rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba.


Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta.


Ammi ta ce "Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sauƙi.


Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama.


Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ƙi yarda ya ajiye shi ya maƙalƙale shi.


Ya fita da shi a kafaɗarsa ya na murmushi, murmushin ba ƙaramin kyau ya yi masa ba.


Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba.


Ya ɗan kalleta sannan ya ce wa Sabir "Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?"


Iman ta yi murmushi ta ce "Baban mai sunan baba"


Murmushi ya yi, ya miƙa mata sabir da yake ta ihu, ya na sake miƙawa umar hannu.


"Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun ɗazu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani" Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata.


"Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa".


"Shut up malama" yayi maganar cikin fushi da kishi.


"Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?" rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir.


Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ƙura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana.


Rai a ɓace ta wuce, ba ƙaramin haushi ta ji ba, dan tuni ta fara kuka.


Ruma ta ce "Mai sunan baba, bari na raka ka"


"No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su" ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ƙaramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa"


A harabar gidan mai sunan baba suka haɗu da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba.


Mahmud ya ce "Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da alaƙa da rumaisa ko?".


Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce "Eh ƙanwata ce".


"Kamannin na gani ai, sunana Mahmud"


Mai sunan baba ya ce "Babban suna, ni kuma umar"


Mahmud ya ce "Masha Allah, ka gaida gida, a gaida mama, duk ina jin sunanku a bakin ƴa ta, bari na zo na sauke ka a hanya, fita zan yi" Umar ya jinjina kai, dan gaba ɗaya ya ji Mahmud ya burge shi, mussaman yadda ya yi masa magana kamar sun saba.


A ɗaki rumaisa ta tarar da iman, ta na kuka.


Ruma ta ce "Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir ɗin nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?".


Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raɗau, kamar shi ya raɗa mata.


Ruma ta ce "Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy"


Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba".


Ruma ta ce "Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wulaƙanci ba, amma cika mini alƙawarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ƴar tsintuwa?".


Iman ta ɗan yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata.


***
ASALIN LABARI.....
1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi.


Masarautar kano na ɗaya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta.


Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al'ummarsa.


Ya na da tarin dukiya, ƴaƴa, barori da sauran hadimai.
Yana da tarin ƴaƴa, daga matansa da kuma ƙwarƙwarorin sa.


A wannan lokacin, ya na kimanin ƴaƴa goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ƙaunar ɗan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya ɓoyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran.


A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu.


Galibi ƴaƴan sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ƙallafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su.


Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban ɗaki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban ɗaki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya ɗauketa ita ma.


Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ƙasar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da ɗan sa, Sharif ya ƙallafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban ɗaki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince.
Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ƙanƙanin yaro kamar Sharif a wannan lokacin.


Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daɗin zaman ƙasar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaɗaici, a cewarsa.


Da ƙyar mai martaba ya saka aka dawo masa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads