Header Ads
Showing 162001 words to 165000 words out of 198763 words

Chapter 55 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt

Ads the beginning of article before Image

30 Jun 2024

2561

Ads at the middle of Article

da suke ɗauka. Ka tambayi uncle bashir, a ina ya tsinto ni, ba zan ce takamaimai in da ya ganmu nan ne aka sace mu ba, amma daga nan zuwa in da aka ɗaukemu, kwana uku nayi ina tafiya, sannan duk wanda aka kama a wurin da ma'adanan nan suke, sun san suwaye SMOKE!"


Jiki a sanyaye ya ɗauki zanen yana dubawa, rumaisa ta sake cewa "Nayi maka wannan bayanin ne, saboda naga you are curious about it. Amma still SMOKE ɗin na da nasaba da sace anty aisha, dan ita ba dan a karɓi kuɗin fansa aka kawota ba, dan a koyawa mijinta darasin da har abada ba zai manta ba aka kawota, ku kula sosai wannan aikin SMOKE ne. Shi ne abun da aka ce lokacin da aka kawota.
Papa idan har babu wanda ya san anty aisha ta dawo daga kai sai ita, dole-dole akwai na kusa da ita da ya sani, aka haɗa baki da shi, ko ta gayawa wani kai baka sani ba, ko kuma ka ƙara tsananta bincike a kan yaronka da aka kashe wanda shi ya tafi kai ta garin nasu"


Tamkar rumaisa ta zare masa lakar jikinsa, gaba ɗaya in da ya dasa hasashen binciken sa daban, abun da rumaisa kuma ta gaya masa dabanz to meye manufar ƙin yi masa wannan bayanan tun da wuri?.


"Mimi meyasa duk baki yi mini wannan bayanin ba tuntuni, ki ka bari nake ta wahala?".


"Saboda baka buƙatarsa a lokacin da ka neme shi, yanzu ka mayar da hankali ka san suwaye SMOKE ɗin dai. Saura kuma ka je ka gayawa wannan abokan aikin naka, dan ka fiye yadda da mutane da yawa, yaya bashir kawai zaka gayawa, idan ba haka ba zan sake gaya maka komai ba"


Daga haka ta tashi ta bar shi da tufka da warwara.


Gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa da walwala, kwanyar rumaisa ba duk kai ba, rashin jin ta kawai mutane ke iya gani, amma ba kowa ke iya ganin baiwar da Allah ya yi mata ba.


Ita dai hankalinta kwance ta kwanta baccinta, amma adam bacci ya gagare shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya kasa kwanciya yayi bacci, yama rasa me zai yi.


Yayi alwala, ya tayar da salla, yayi ta addu'a.


Har ya hau kan gadon zai kwanta, ya buɗe ya shiga kallon hotunan aisha.


Ya kashe system ɗin ya kwanta, rumaisa duk tana kallonsa.


"Papa"


"Mimi".


"Ka kwantar da hankalinka dan Allah, zaka yi nasara, sai dai kar ka sanya ran ko komai ya bayyana zaka samu adalci yadda ka ke tsammani"


Bai ce komai ba, ya juya ya rungumeta sosai a jikinsa, yana ta jejjera numfashi.


"You are brave papa".


"Yanzu kin yadda ba sakaci ne ya sanya ina jami'in tsaro na kasa karɓo Aisha ba?".


Ta ce "Faɗa fa nake dan na baka haushi kawai, anty aisha ta gaya mini kai mutum ne mai yi wa iyalinsa hidima sosai"


Riƙe kunneta yayi ya ce "Daɗin me ki ke ji, idan kin ɓata mini rai ne?"


"Daɗin da ka ke ji idan kana tsokanata" ta bashi amsa.


Ya ce "Yauwwa kin tuna mini ma, bari in ɗora daga in da na tsaya, my mimi ƴan mata, budurwata ta kaina".


Ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikinsa, sai dai abu kamar wasa, Adam ya mayar da rumaisa cikakkiyar matarsa.


Wanda shi kansa abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, kenan matsalar ta sa a cikin gidansa take kenan?.


Bayan gama jero sunayen ƴan gidansu, har da kiran ƙawayenta, banda cizonsa da ta din ga yi, kamar ƴar damusa.


Bayan shuɗewar wani lokaci, ya laluba ya ɗau wayarsa, ya kunna fitila ya haska fuskar rumaisa, da ta haɗa yawu da majina, da hawaye sai jan majina take yi tana kuka.


"Amarsu ta ango, finally budurwata ta zama matata, wannan cizo kamar damusa mimi" ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka, tana wallahi sai na faɗa.


"Wa zaki gayawa? Ammi ko mama?".


"Kowa na duniyar nan, kuma sai na rubuta kowa ya gani, kamar yadda na taɓa yi maka"


Ya yi dariya mai isar sa, kashe murya yana kwaikwayon ta ya ce "Yaya usy, mai sunan baba. Ai ko shi mai sunan baban, bai isa hana ni karɓar sadakina ba. Inyee ni dakata ma, nawa na baki sadaki? Ciko zan yi ko wani abu zaki rago mini?"


Ta ɗora hannu a ka, tana cigaba da kuka har da ta shiga uku ta lalace, shi kuma ya sakata a gaba, yana ta tuntsira dariya, bai taɓa ganin karaya ƙarara da miƙa wuya a wurin rumaisa ba sai yau.


Ya ce "Dan Allah ki goge wannan majinar mana, ƙazama, kin bayar da mata gaskiya" ya janyo ta yana goge mata hawayen fuskarta.


Buge hannunsa tayi ta ce "Wallahi yaya usy ne ya janyo mini, ya ce duk abun da ka yi mini ba haram ba ne, idan ban yadda ba zaka yi mini kishiya da shi da anty laila, suka ɗorani a hanyar da bata kamata ba".


"Au zuwa ki ka yi ki ka gaya masa nayi miki wani abu?".


Ta ce "Eh, duk abun da ka yi mini faɗa nake yi, wallahi Allah ya....." Sai kuma tayi shiru.


"Allah ya isa, Usman ɗin ki ke yi wa Allah ya isa"


Ta girgiza kai. Ya ce "Ni?"


"Ni ban maka Allah ya isa ba"


Ya sake juyo da ita ya ce "Oyaa say thank you".


"Thank you for what?" Tayi maganar tana mamakin rainin hankalin da yake mata.


"Thank you for everything i did, faɗi"


"Wallahi ba zan faɗa ba"


"Ok, naga alamar bakin ki bai mutu ba, am equal to you".


"Na shiga uku, na gode Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata"


Yayi murmushi ya ce "Kowa ya tuba dan wuya ba lada, ya cikata" ya sauka ya nufi toilet.


Har ya fito tana zaune a takure, jikinta sai tsuma yake yi, tana ta tunanin ya ma za ta yi ne.
Abun gaba ɗaya ta rasa a wani muhallin za ta saka shi, anty laila dama tuntuni tayi mata bayani, usman ma duk da ba kai tsaye ya gaya mata ba, amma yayi mata bayani, amma ita dai sam abun ya zarce tunaninta.


Kamar zai tsayar da taxi ya ce "Sss" ta ɗago ta kalleshi.


"Zo"


Tayi shiru tana kallon sa.


"Magana fa nake" a hankali ta tashi tana raɓe-raɓe.


"Auren kenan mimi, ki daina hararata kamar zaki kai mini duka, ki shiga toilet ki yi wanka, kamar yadda ki ke na period, sai dai wannan akwai banbancin niyya".


Karatun ajin su yasir ne ya faɗo mata, sai yanzu ta gane ina karatun ya dosa, a wancan lokacin kanta a doɗe yake. To idan haramun ne ai ba za a koyar a makaranta ba, duk da haka ai mama ba ta ce mini haka ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.


A haka ta gama abun da za ta yi ta fito, sai dai still ba ta daina kuka ba.


"Haba mimi, hawayen zai ƙare fa, is ok ya isa haka, zo in canza miki kayan sai ki kwanata ki yi bacci".


Ta girgiza kai ta ce "Ni ba na so"


Ta canza kayanta, ta kwanta a ƙasa, wai ba zata sake kwana a kan gadon ba.


Ya tayar da salla, sai da tayi bacci, sannan ya ɗauke ta ya mayar kan gadon.


"Allah kai ka san dalilin da ya sanya ka ɗauki Aisha, ina tsaka da ƙaunarta, ka bani rumaisa, kuma ita ma ka sanya mini son ta, Ubangiji Allah ka jagorance ni a al'amarin nan, ya sanya ta zame mini sanyin idaniya, kuma ka bani ikon kula da ita" yayi Addu'a murya ƙasa ƙasa, ya shfa kanta yayi murmushi ya ce "Ni na cancanci in ƙara sadaki mimi"


Su da zasu yi kwanaki biyar, abu kamar wasa adam yayi burus da komawarsu, ya addabi rumaisa da sai da tayi dana sanin biyo shi, kuma ya hanata waya da kowa, ammi tana mita ta ce tana son ganin rumaisa suna shirin biki, ga sabir yana ta rigima shi mimi.
Adam yayi mursisi ya ce aiki ne ya riƙe shi zasu dawo.


Tayi kukan, tayi rashin kunyar, tayi tsiwar amma babu wadda tayi tasiri, adam yayi burus da ita.


Yau suna kwance da safe, tana jin yana waya da laila, laila tana tambayarsa rumaisa, ya ce bacci take.


"Wai takawa ba zaka dawo da yarinyar nan ba?"


"Honeymoon muke" ya bata amsa.


"Ni ka ke gayawa haka, lallai baka da kunya, dan Allah a dawo mana da ita, wallahi we are missing her".


Wata shida na barku tare da ita, dan haka a ƙyaleni.


"Anty laila" rumaisa ta yi maganar kamar za ta yi kuka.


"Na'am mimi, ya kike?"


"Dan Allah ki saka baki ya dawo da ni gida, na gaji" tayi maganar tana kuka.


Katse kiran yayi, ya harareta ya ce "Da gaske faɗa musun zaki yi abun da nake miki? Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana, kuma Allah ya tsinewa mai tona asirin aurensa, sirri ne mimi ba a faɗa".


"Ni wallahi a gida ba a ce mini haka ba"


"Amma laila ta gaya miki ai, kuma Usman ma haka, amma tun da haka ne shikenan, ina ga kawai wani auren zan yi"


Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*


*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels


Susbcribe my YouTube channel please 🙏


*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*


Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”


Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….


(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)




*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*












Tuni idonta ya cika da hawaye ta ce "Haba papa, duk abun da fa ka ce in yi ina yi, kuma duk da haka sai ka yi auren?".


Ya sake kashingiɗa ya ce "Yanzu ba gashi kina yi mini gardama ba".


Kawai ta kifa kai ta cigaba da kuka, maimakon ya rarrasheta, sai ya kwanta a bayanta ya ce "Rigimar ki ke so, ba kuma zan kula ki ba". Ta gama kukan ta hau bacci.


Da yamma ya ce ta shirya, ya kaita shan ice cream, tun da a satin za a koma makaranta, yakamata su tafi gida haka.


Tayi ta murna za su koma gida, duk da ta wani fannin zamansu a abuja yayi mata daɗi, ta wani fannin kuwa zata iya cewa, ba ta ji dadin sa ba.


Adam kuwa har fargabar komawa Kano yake yi gidansa, kar ya je su koma, matsalar nan ta sake dawo masa.


Ita kuwa baki yaƙi rufuwa, da suka koma, gidansu ya ɗan yi ƙura, ta gyara abun ta fes, ta karɓi wayar adam ta sanarwa da mama sun dawo, zata je gida a cikin satin, mama ta ce ba sai ta zo ba, ita zata kawo mata ziyara.


Rumaisa ta din ga murna kusan shekara da aurenta, sau ɗaya mama ta taɓa zuwa gidanta.


Ta cewa takawa, ya ɗaukko mata sabir, dama anty laila ta ce yana ta rigima, Adam ya ce sai dai su je ta ganshi su dawo gida.


Ta ce "Amma saboda me?"


"Ya fara wayo, ba zai kwana a tsakaninmu ba".


Cikin damuwa ta ce "Amma papa saboda me? A ɗakina zamu din ga kwana da shi".


"Saboda mun daina raba ɗaki daga yanzu, sai ya shekara biyu ko uku, ya isa shiga makaranta, kan lokacin kema kin kammala makaranta, zan ɗaukko shi gaba ɗaya ya dawo gidan nan, a gyara masa ɗakin sa"


Kai tsaye ta gane nufinsa, a tata wautar, da suka dawo gida, shikenan ta huta, amma taji ya kawo wata maganar daban.


Kamar da wasa, taga da gaske takawa yake yi, ba zasu sake raba wurin kwana ba, babban abun da ya ƙara sa shi farinciki da bashi mamaki, bai wuce jin ya koma normal ba har a gidan.


Sai washegari suka tafi gidan ammi, ana ta shirin bikin iman da mai sunan baba.


Suna mota kan su sauka takawa ya cewa ruma "Kalli can" ta ɗaga kai, ta hango mai sunan baba tare da iman, tana magana yana murmushi.


Ruma ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, su mai sunan baba an tafi duniyar love".


"Ina tausayawa iman zama da wannan yayan naki, dan dai ta nace ne kawai, amma gani nake kamar za ta sha wahala, mutum sai izza da jin kai".


Ta haɗe rai ta ce "Papa abun ma ba kara, yayana ne fa"


"Shi ɗin fa, kema ai kin san gaskiya, gashi dai ƙanwata yake so, amma ko zan wuce sau goma ko kallona ba zai yi ba".


"To ai kaima baka kula shi"


Ya ce "Oho muku dai, ki taho mini da key ɗina, kya je ku gaisa, ni ta baya zan shiga"


Ya buɗe motar ya fice, duk da murmushi yake yi, iman na masa zancen su saka kaya iri ɗaya ranar dinner, yana ce mata shi kunya yake ji, ba ya son taron mutane.
Tana yi masa magiya, tana ganin rumaisa ta nufeta tana murmushi suka rungume juna, ta ce "Mimi sannu da zuwa ya Abuja?"


Ruma ta ce "Abuja ba daɗi".


Iman ta ce "Haba dai? Baki ji daɗin garin ba ne ko yaya?"


"Ke dai a bar zancen kawai" ta risuna ta gaida mai sunan baba, tamkar ba shi ne yake murmushi ba, ya amsa cikin basarwa.


Sai da ya lura da yadda tayi ƙiba, ta ƙara kyau da haske, kuma daga yadda take

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads