Showing 78001 words to 81000 words out of 198763 words
Chapter 27 - Kanwar Maza 3&4 Original Book Complete writing by Aisha Cool .txt
aka lura ashe ni mace ce, ni na ce kar ka aureta da za a din ga zagina? to wallahi ba ruwana da wata masarauta, duk wanda ya yi mini, sai na rama, a wayance matar nan ita ma tana nufin, ni ƴar talakawa ce na aureka saboda kana da kuɗi fa take nufi, ba ta san taimaka wa na yi na aureka, saboda ammi ba da kuma Sabir" sosai take masifa, domin dama, dama take son ta samu ta amayar da abun da yake ranta.
Takowa ya yi zuwa gabanta, tana tsaye a gaban mudubi, sai iya shege take yi, tana masifa.
Sai kuma tsoro yakamata,ba yau ta saba ganin namiji ba riga ba, idan da sabo ta saba a gida, amma ganin adam a haka, ya sanya take jin, tamkar ta aikata wani jibgegen saɓo.
"Ke dama mace ce nan a haka?" Ai ba ta san lokacin da ta ɗago ta kalleshi ba.
Ya janyota gaban mudubin sosai ya, ya cire hular kanta, gashin nan na ta baƙi wuluk, ta yi parking ɗin sa. ya ce "Wannan ɗan gashin naki ne kawai zai sa a san ne ba namiji ba ce ba, kamar namijin haka ki ke ai, taimakawa na yi na aureki, dan ba yadda zan iya, amma kalleki fa sosai a mudubi" yayi maganar yana nunata a cikin mudubi.
Ɗaga kai ta yi tana kallonsa.
Ya ce "Eh mana, ke ba kwalliya ba, ke dai gaki nan, behaviors ɗinki ma na mazan ya rinjayi na matan. Wasiƙar da ki ka rubuta mini, ki ka ce na taɓa miki nono ni ban gansu ba ai.
Kawai da ma sharrinki ne, abun bai fi girman wake ba, wata ƙwaila da ke, ai ba ƙarya aka yi ba, dole kowa ya tausaya mini, look at you.
Da ma na ce nawa sun fi naki baki yadda ba, look at me, bai fi naki ba?" Yayi maganar yana shafa ƙirjinsa.
Rumaisa ji ta yi tamakar ƙasa ta tsage ta nutse, sai ta nemi duk wasu kalaman rashin kunya, da fitsararta, ta rasa, ta rasa me ma za ta yi, ta saka hannu ɗaya ta rufe ƙirjinta, ɗaya kuma ta rufe fuskarta.
"Meye a wurin da ki ke rufewa, abu fayau kamar filin ball, ni aure zan yi nan gaba kaɗan, dan da gaskiyarsu, ba mace ba ce ke, haryanzu dai namijin ce, ba a gama tantancewa ba, macen ce ko namiji, ga rashin kunya, ga fitsara da faɗan tsiya, duk ke kaɗai, ba zan iya ɗauka ba da wanne zan ji?".
Dummmm haka rumaisa ta ji maganar, jin ya ce wai zai ƙara aure, saboda ba ta da nono, idan ba batsa ba, meye haɗin sa da wannan abu?.
Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta ma rasaa wani muhallin, yakamata ta ajiye wannan maganganun da adam yake yi mata, ba tare da kunya ko tsoro ba.
Ya kuma haɗe rai ya ce "Wuce toilet ki haɗa mini ruwan wanka"
"Ruwan wanka kuma sai ka ce wata baiwa?".
"Ba zaki wuce ba kenan?"
Kamar ta saka ihu, haka ta tafi tana ƙunƙuni, ya bi bayanta, ta shiga banɗakin, sai dai ba ta san yana ƙofa a tsaye ba.
A Tsakiya banɗakin ta tsaya, ta riƙe ƙugu, cikin ƙwalla ta ce "Lallai ma, wai ni rumaisa ake yi wa wannan abubuwan, wallahi da sake". Idonta ya sauka a kan toothpaste ɗin da adam yake amfani da shi, a wani tube mai kyan gaske.
Ta ɗauka ta buɗe, ta lakata ta saka a bakinta. "Dan mugunta ni ya bani mai yaji, shi kuma nasa mai zaƙi, saboda ga wadda dauɗa ta kashewa haƙora, ban yafe ba duk abun da yake mini".
Da maganganun da take, da toothpaste ɗin da take sha, duk yana kallonta, ta ajiye ta nufi bath ɗin.
Nan ma wata mitar take yi "Wato ma kawai an kawo masa baiwa, na yi gyaran ɗaki, ya ci abinci na yi wanke-wanke, kuma wai ni zan haɗa masa ruwan wanka, ga shower ya kunna ya yi wankan, amma ba zai iya ba, ko da waye yake haɗa masa ruwan oho? Zai ga tsiya, wallahi ruwan zafi zan haɗa, idan ya ƙone gobe ba zai kuma sakani ba. Saboda tsabar wulaƙanci, mutumin nan ma bashi da kunya, kuma ammi ba ta san yana yin maganganun batsa ba, a haka kamar na Allah, kuma da alama ba ya yi wa kowa sai ni, to wallahi ni ina da tarbiyya ".
Ta din ga surutu a banɗaki, kuma ko da wasa ba ta waiwaya ba, balle ta ganshi, ta kunna ruwan zafi, fiye da rabin bath ɗin nan, sannan ta kunna na sanyi, ruwan sai tururi yake yi, ta ce "Allah ya sa yana zuwa kawai ya shiga, gobe ba ya kuma sakani aiki ba, bayan ya gama ci mini mutunci".
Ji ta yi an rufe ƙofar banɗakin, da sauri ta tashi ta waiwaya tana kallonsa.
Ya shigo kamar zai wuce ta, ya shammaceta, ya danƙota, ya shiga cikin bath ɗin da ita.
Ihu ta kurma, jin zafin ruwan, ga kayan jikinta nylon ne, ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhhhh, ai gara mu ƙone tare".
Kiciniyar tashi ta hau yi, amma ya riƙe ta sosai a jikinsa, ya din ga ɗibar ruwan, yana zuba mata a kanta.
Ayshercool.
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
"Na shiga uku, mama, dan Allah a taimakeni, ƙonewa nake yi fa"
"Ai da ni ki ka yi niyyar ƙonawa, sai dai mu ƙone tare" ya haɗa hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya, ya cigaba da zuba mata ruwan har a fuskarta.
Ta dinga mutsu-mutsu ta tashi, amma abu ya gagara, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa, sai ta hau kuka, tana yi masa magiya, a kan ya ƙyaleta.
"Har da sha mini toothpaste ko, saboda ke ƙazama ce".
"Ni ban sha ba".
"Ai ina jin duk abun da ki ke cewa, idan mu ka gama ƙonewar, sai mu yi jinya tare "
Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, fata ta zata kwashe, dan Allah ka yi haƙuri".
"Ai baki isa ba, ni zaki ƙona da ruwan zafi ki huta ko?".
"A'a ba haka nake nufi ba, dan Allah ka yi haƙuri ".
"Ni sharifi ne, ba abun da ruwan zai yi mini, ke da ki ka shirya ramin muguntarki, gashi kin faɗa".
Ganin ta na kuka wiwi, ya sanya ya cikata, ta tashi da sauri, ta fice daga bath ɗin, jikinta na tsuma ta tafi ɗakinta, ta tuɓe kayan a tsakar ɗakin, ta zura da gudu toilet, ta sakarwa kan ta shower, jikinta yayi ja, ta zauna a toilet ta cigaba da kuka tana faɗin "Wallahi ba zan yafe ba, wuta balbalin bala'i"
Sai da ta daina jin zafi, sannan ta fito ta ɗaura towel.
Duba jikinta take yi, tana duba wa ta ga, ko fatarta za ta kwashe, cikin ikon Allah ba abun da ta yi.
"Wato shi ba ma ya jin zafin ruwan, amma ni ya ƙona ni, zai gane ni ya taɓa, sai na rama, har da wani rungumeni saboda tsabar rashin sanin abun da ya dace, Innalillahi Allah ya sa kar a gane idan na fita, ya kuma riƙe mini hannu na kasa guduwa". Ta saka hannu ta toshe bakinta ta ce "Astagfirullah, Allah ka yafe mini".
Sai kuma ta tuna abun da ya yi mata na cewa, ba ta da nono.
Ta kalli jikinta a mudubi, ta ɗan bankaɗa towel ɗin ta kalli ƙirjinta, ta ce "Saboda tsabar saka ido, wai nonona ne bai fi wake ba, mutumin nan ya cuceni, wato kallona ma yake yi haka? To saboda ba ni da su ake cewa ni ba mace ba ce? To na ga ma ba sai mutum ya haihu ba suke da amfani? Amma bakomai, Allah ya sa su fito mini, na huta da gori. Kai Astagfirullah, in rasa mai zan roƙi Allah sai wannan abun, Allah na tuba ka yafe mini. Amma wallahi sai na faɗi abun da mutumin nan yake yi mini, tun wuri ayi mini tsakani da shi, a taka masa burki, kar ya sake rungume ni".
Sai da ta gama surutanta ita da mudubi, sannan ta tashi ta shafa mai ta saka kaya.
Ta daɗe a ɗakinta, sannan ta fita, ta tarar shi tuni ya fice, ta kwaso kayan gyaran ɗakin, ta ce yayi wa kansa dan ba za ta gyara ba.
Ba uwani ce zaune a ɗakin su, tana waya, ita da Samha.
"Wai haryanzu babu sani muhimmin bayani a kan in da zamansu ya dosa, ba kya bani wani update".
"Ranki ya daɗe, su suna saman bene, mu muna ƙasa, bana iya sanin me yake faruwa".
"Dole ki din ga bibiya ki sani, bamu saka kin yi faɗi tashi, ta amince ki je gidan ki zauna ba domin ki je ki miƙe ƙafa ba, biyanki zamu din ga yi, dole ki yi mana aiki yadda ya dace, ba kuma iya leƙen asiri ba, ki yi iya ƙoƙarin ki, wurin haɗa husuma a cikin gidan nan, ki nuna mata kin fita daɗewa a duniya, dole ta fito ta bar gidan nan".
"In sha Allah uwa ɗakina, za ayi yadda ki ka ce, kar ki damu".
"Ina saurarenki" Samha ta katse wayarta.
Rumaisa kuwa kitchen ɗin ƙasan ta shiga, Aisya da barira suna ta wanke-wanke.
Rumaisa ta ce "Ina kwananku"
Cikin sauri suka risuna suna gaisheta.
Rumaisa ta ce "Dan Allah ku daina gaisheni, wai ba ku ga ni ƙarama ba ce?".
Asiya ta ce "Ranki ya daɗe, ai Allah ya riga ya baki girma dole a biki, kuma ke matar basarake ce, dole a girmamaki".
Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Kunya ku ke bani ne"
"Ba wani abu, ko wani abun za ayi mikk?"
Ruma ta ce "A'a, girkin rana zan yi, kar ku dafa abinci da mu, ku yi daga naku, sai na sauran masu aikin".
Barira ta ce "To, amma ba abun da zamu tayaki?".
Rumaisa ta ce "Bakomai, Anty Asiya, dan Allah ɗauko mini mai, ki tayani na kai sama, bari na tafi da wannan kayan".
Asiya ta ce to.
Rumaisa na shirin fita, baba Uwani ta shigo tana tsuma, ta ce wa rumaisa "Amarya ba kya laifi, har mai gidan ya fita ne?".
"Eh, ya fita".
"Ina fatan dai ba wata matsala ko? Idan da wata matsalar zaki iya gaya mini, ni uwa ce a wurinki, kuma kin bar shi ya saukko shikaɗai, ai kamata ya yi ace ki na raka shi har mota"
Murmushin gefen baki rumaisa ta yi, ta wuce ta bar baba uwani.
A kitchen ɗin ta, Asiya ta sameta, ta ajiye mata man, har za ta tafi rumaisa ta ce "Anty Asiya, bari na baki hijjabi, da ke da Barira, a cikin kayan lefena suke, sun yi mini tsawo sosai".
Asiya ta buɗe baki ta ce "Wane mu ranki ya daɗe, kayan lefenki fa".
Ruma ta ce "menene a ciki, kyauta zan baku, sun yi mini tsawo". Ta tafi ɗakinta, ta ɗaukko hijjabai a akwati ta kawowa Asiya.
Asiya ta din ga godiya, ruma ta ce "Dan Allah ki daina yi mini godiya, har kin saka na ji kunya, ba fa ni na saya ba, nima bani aka yi".
Asiya ta ce "Haka ne, duk da haka dole na yi godiya, sannan dan Allah ranki ya daɗe, ki din ga ɗabi'ar matan sarakuna, girmanki ne dole a biki, kuma duk hukuncin da ki ka yanke a gidan nan dole a bi shi, amma wani abu nake son gaya miki, ban san ya zaki ji ba".
Rumaisa ta ce "Gaya mini bakomai".
"Ki yi hankali da taka tsantsan da baba uwani, amma kar ki ce na gaya miki dan Allah".
Ruma ta ce "Ai ni dama ba ruwana da ita, bana son dariyar da take yi mini, bakomai in sha Allah na gode" Asiya ta juya ta sauka tana murna, yarinya ƙarama mai halin manya, ta san ta yi kyauta.
***
"Amma Jabir kana ganin abun da Adam ya yi ya kyauta, idan Fulani matarsa ce, mu kuma ƴan uwanta ne, shi jami'in tsaro ne nima haka? Dan meyasa bai ɗauki wani mataki a kan ɓatanta ba, meyasa bai gaya ba? Daga yin garkuwa da ita ya aka yi ya ɓoye wa duniya? Ya yi wa kansa adalci kenan, idan yana da gaskiya, ai tuntuni yakamata ya bayyana Yarinyar nan, ayi bincike a kanta, ko za a samu wani information ɗin".
Jabir ya ce "Easy mana, haba Jamil, ina ga mun fi kowa sanin Adam, a ɓangaren taurin kai da zurfin ciki, duk familyn nan albarka, kowa ya san shi a kan haka, kai waye ya ce maka a zaune yake tun da ta ɓata? Adam ya shiga cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, tun bayan ɓatanta, kuma ba wai yana zaune ne kawai ba, da shi da gayen nan Bashir, da wasu daga ƴan sandan garin katsina, suka yi ta ƙoƙari a kan lamarin".
"Amma ya aka yi kai ka sani, ni ban sani ba? Ina yayanta kuma jami'in tsaro kamar shi?"
"Saboda na fi ka kusanci da shi, na san halinsa tsaf, dan haka na fika iya zama da shi, shiyasa nake sanin abun da ba ka sani ba, yanzu abun da ya kamata shi ne, kamar yadda ya ce ka tamabyai mai girma turaki, ka yi masa zancen ka ji mai zai ce?".
Jamil ya ce "Ai gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne ma, amma zan zurafafa bincike a kan lamarin nima".
Jabir ya ce "Better".
***
Ta window rumaisa ta leƙa, ta hango motar Adam, kusan biyar da rabi lokacin, Murmushin mugunta ta yi, ta koma ɗakinta ta yi zamanta, a sababbin litattafan da ya saya mata, na makaranta da za ta fara zuwa, ta ɗauki ɗaya da fensir, tana zane-zanenta.
A gajiye yake sosai, ya tarar da abincinsa a ɗakinsa, yanayin yadda aka ajiye abincin ya bashi mamaki, har da jug, jikinsa gaba ɗaya babu daɗi, dan haka ya yanke shawarar fara yin wanka, sannan ya ci Abincin.
Yayi wanka, ya sauya kaya, ya zo ya zauna, ya fara buɗe jug ɗin, yayi arba da ruwan famfo a ciki, shi da yake ajiye cartons na ruwa, da lemuka, ya buɗe abinci ya ga shinkafa fara ƙal, ga man ƙuli ga dunƙule da yaji.
Wani irin ƙululun takaici, ya ƙule masa wuya, ba ƙaramar yunwa yake ji ba, kuma ba ya cin abinci da mai da yaji. A fusace ya tashi ya fita, ya sauka ƙasa yana kiran baba uwani.
Ta fito a rikice tana tambayar ko lafiya?.
"Meyasa za a dafa mini abinci mai da yaji a gida? Idan akwai abun da babu, ba na ce a din ga gaya mini ba, dan me za a dafa mini mai da yaji?".
Ta shiga tafa hannu ta ce "Wallahi ranka ya daɗe laifin matarka ne, babu yadda ban yi da ita ba, ta ce ita za ta yi maka girki, na ce mata ba ka cin abinci da mai da yaji, amma yarinyar nan ta ƙi yarda".
Asiya ta kalli baba uwani, suna ƙasa basu san ma me ruma ta girka ba, balle baba uwani ta hanata, amma ta ce ta hanata ba ta hanu ba.
A fusace ya koma saman benen, baba uwani ta lallaɓa ta bi bayansa, tana cigaba da salallami.
A falo ya tarar da rumaisa ta fito, cikin fushi ya kalleta ya ce "Muzuru ne ni da zaki dafa abinci da mai da yaji ki ajiye mini?".
"Papa meye a ciki, abinci ne fa?".
"Shut up! Na yi kama da wanda zai ci abinci da mai da yaji ne?".
Baba uwani ta ce "Ayi haƙuri mai gida, ba za ta sake ba, rashin sani ne, in sha Allah zan nunnuna mata abubuwan da yakamata ta sani, duk laifina ne, yarinta ce take damunta"
"Ba wani yarinta baba uwani, ai na ce girki ba huruminta bane ba, ta bari a din ga yi amma kasancewar, kunnen ƙashi ne da ita, ba za ta ji ba".
Kuka rumaisa ta saka ta ce "Kuma sai na gaya wa ammi kana yi mini faɗa, idan na yi abu gwaleni ka ke yi".
Taski ya yi ya , tafi ɗakinsa, yana barin falon rumaisa ta yi wa bayansa gwalo.
Ya fito da mukullin motarsa, ruma ta ce "Papa ina zaka?" Banza yayi mata ya sauka, baba uwani sai bashi haƙuri take yi.
Bayan ya sauka baba Uwani ta kalli rumaisa ta ce "Ranki ya daɗe, ai ba a...."
Rumaisa ta kasteta ta hanyar cewa "Idan mun yi faɗa, ba sai kin nema mini afuwa ba, yarinya ce ni ba mahaukaciya ba, kuma ina sane na yi hakan, na san ba ya cin abinci da mai, an gaya mini" galala baba uwani ta bi rumaisa da kallo, dama baki ne da ita haka? Kamar ba daga bakinta maganganun suka fito ba.
"Amma ƴar nan idan ki ka fusata shi, yana da larura fa".
Rumaisa ta kalleta ta ce "Wace larurar?" Sai kuma ta tuna katoɓarar da ta yi ta ce "A'a bakomai".
"Shikenan tun da ba zaki gaya mini ba , idan ya dawo sai na tambaye shi wace larurar ce da shi?".
Baba uwani ta ce "Na shiga uku, da wasa nake yi miki, ba ya son ɓacin rai ne dai, dan Allah kar ki gaya masa".
Rumaisa ta ce "Aini duk abun da aka gaya mini sai na bi diddigi, bana mantuwa" ta wuce ta bar baba uwani tana gumi da dana sanin maganar da ta yi.
***
Ƙishirwar son ganin Umar faruk, ta din ga damun zuciyar iman, hotunan biki din ga shiga, tana kallon hotunan duk da ya fito a ciki. Cikakken namiji mai cikar zati kamala, duk da ba fara'a yake yi ba, son kowa ne ƙin wanda ya rasa, namiji mai matuƙar jan ajinsa da tsare gida.
'Na shigesu, me yake damuna ne?'
'son wanda bai san kina yi ba, wanda ba ki da damar ki nuna masa hakan, wands tsantseninss da kamewarsa, da matsanancin kwarjininsa ba za su bari ma ya gane hakan ba' wata zuciyar ta bata amsa.
Tashi zaune ta yi ta ajiye wayar, tare da furta 'Allah ka iya mini" ga gefe guda Jabir yana ta hura wuta, wanda har Ammi ta fara ganewa.
Ta sake ɗaukar wayar, ta shiga what's app ɗin ta, da ta yi saving number sa, da Yaya Omar, ta