Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 38049 words

Chapter 1 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

405

Ads at the middle of Article

Ummu Amjad
MAƘABARTA NE
Daga Alƙalamin
Sarat Alƙasum
(Maman Nusaiba)




JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION




Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Yadda na fara lafiya Ubangiji kasa na gama lafiya. Gaisuwa a gareka dukkan masoya🤗






0️⃣1️⃣




Misalin ƙarfe 3:am na dare gudu take yi a kan titi sai waigen banyata take, wayar dake hannunta ta yi ringing, a hanzarce ta danna za ta yi magana ta ji an yi sama da ita shuu. Ihu take kurmawa ta na faɗin.
"Waiyo Umma ku taimakeni za a saceni."
Wani irin ɓakin duhu ne ya mamaye idanunta abin da ya ƙara kaɗa hantar cikinta, idanunta tamkar za su fito waje saboda firgici da tsananin tsoron da take ji.
Idanunta ta runtse bakinta na rawa zuwa wannan lokacin ta kasa furta koda kalma ɗaya, ji ta yi an dire ta a kan wani abu mai ɗan tudu ta yi saurin buɗe idanunta, ƙara ta ƙwalla ta na ƙanƙame jikinta sakamakon ganin wani zabgegen abu wanda ta kasa ganin tsayinsa, baƙi ne sosai ba ta iya ganin wani kalar abu ne, shi dai gashi nan kamar mutum kamar doguwar bishiyar giginya..


"Hahaha!


Ta ji wata dariya mai sa zuciya firgici ta ziyarci dodon kunnenta.
Sake ɗago kai ta yi ta juya gefenta ai da sauri ta zaro idanu ta na ja da baya sai ji ta yi ta bugi wani abu, jiki na rawa ta juyo cike da zullimin mai idanunta za su gane mata ta yi arba da ƴar ƙaramar yarinya wacce ba za ya wuce shekaru 7 ba. Bakin yarinyar jini ne ke fita haka zalika kanta yana ɗauke da ƙahuna guda uku, hannayenta har jan ƙasa suke masu dauke da baƙaƙen faracuna masu tsayi da kaifi, kannuwanta tamkar na tunkiya jajaye sai juyawa suke kamar yadda dabbobi ke yi da nasu, ƙafarta sak irin ta biri.


Baki na rawa ta ce.
"Baiwar Allah ku su waye wai?"
Wata mahaukaciyar dariya yarinyar ta yi cikin muryarta irin na ƙananun yara ta soma magana.
"Karki sake tambayata mu su waye, idan ba haka ba "Ta ƙarashe maganar ta na zaro mata manya-manyan idanunta baƙaƙe tamkar gawayi ne a kwayar idanun."
Muƙut! Ta haɗiye yawu ba shiri, dafata ta ji an yi ta baya ta zabura ta juyo, arba ta yi da wannan dogon ɓakin abin. Saboda tsananin tsoro futsari ta saki cikinta ya murda ta saki zawo ganin wannan shirgegiyar halitta. Runtse idanu ta yi ta ƙasa furta komai in banda futsari babu abin da take saki.


"Hahaha! Hahaha! Hahaha!"


Sautin dariyarsu suka shiga gigita ta, zuwa can ta ji tsit hakan yasa ta buɗe idanunta.
"Waiyo na shiga uku!
Ta faɗa ta na kallon ƙasan inda take. Tsalle ta yi ta koma gefe ta na kallon wajan a firgice ta soma magana.


"Waiyo ni! A MAƘABARTA NE nake kuma a kan kabari?"
"Kwarai kuwa a MAƘABARTA NE kike."
Ta ji an ba ta amsa daga gefenta.
Juyowa ta yi cike da tsoro ta sake arba da yarinyar nan, baki na rawa ta kuma cewa.
"Wai me kuke nufi da ni ne? Me na muku kuke bibiyar rayuwata? Z..
Tsawa aka daka mata ta kasa ƙarasa maganar.
"Mu ba'a tambayar mu."


Shuru ta yi sai kallon ƙaburburan dake kusa da ita take.
Tim! Ta ji ƙaran faɗuwar wani abu, da sauri ta kalli inda abun ya faɗo, baki ta buɗe ta na son yi magana ta ji an manne mata bakin kawai ta zazzaro idanu ta na kallon mutumin da yake ɗan nesa da ita.
Kamar kiftawa da bismillah ta ga an fille kan wannan mutumin, zubewa ta yi a ƙasa ta na son yin magana ba hali ta rarrafa ta nufi gangar jikin mutumin idanunta waje. Jini kawai ke ta malala a jikinsa ta ɗaura hannu a ka ta kurma ihu ta ce.
"Uncleeeee!"
Firgigit ta farka daga baccin da take jikinta ya yi sharkaf kamar an zuba mata ruwa, numfashi take fitarwa ta na jinjina kai sai kuma ta fashe da kuka wiwi ta soma surutai.
"Allah ka tseratar da ni daga wannan mugayen mafarkan da nake, wannan abun biyu su waye su da kodayaushe suke kaini maƙabarta?"
Zabura ta yi jin ana shafa bayanta ta juyo, ihu ta sa ta na sauka daga kan gadon ganin jarirai guda biyu kwance a kan gadon, kallon fuskarsu ma abin firgita ne. Kafin ta yi ƙwaƙƙwaran motsi sai ganin ɗaya daga cikin jariran ta yi ta tashi tsaye ta na tafiya ta doso ta, ai a zabure ta nufi ƙofar fita ta na kiran sunan duk wanda ya zo bakinta, sai dai ta na zuwa bakin ƙofar ta kasa buɗewa ga wannan jaririyar na doso ta ta na zaro mata ido. Fuskar jaririyar ƙofa-kofa ce wani ɓakin ruwa mai yauki yana fitowa haɗi da wasu irin tsutsoyi suna fitowa suna shiga cikin idanunta.


"Waiyo Allah Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Umma! Ku taimakeni aljana za ta kamani Umma, Abba! Abba! Ku ceceni kar ta ƙaraso gurina."
Haka take faɗa ta na buga ƙofar da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar, juyowa ta yi taga jaririyar ta kusa isowa inda take ta taƙarkare ta kurma ihun da ya fito da dukkan 'yan gidan suka yo ɗakinta.


"Suhaima! Suhaima! Buɗe ƙofar mana.
Ta jiyo muryar mahaifiyarta na kiran sunanta, sai yanzu ta tuna ƙofar a kulle take, cikin rawar jiki ta murda makullin ƙofar ta buɗe. Ƙoƙarin tareta suke ganin ta na neman gudu, mahaifinta ya kamo hannunta ya ce.
"Suhaima wai anya lafiya kike."
Kasa magana ta yi sai cikin ɗakin da take nuna musu ta na ƙara ƙanƙame mamanta, mamaki ne ya kamasu suka kalli ɗakin ba su ga wani abu ba.. A tsorace ta ce. "Abba aljannu ne a ɗakin nan ni dai ba zan sake kwana a ɗakin nan ba, yanzu fa ja..
Ba ta ƙarasa maganar ba sakamakon arba da ta yi da wannan jaririyar ta na girgiza mata kai fushi ya baiyana a kan fuskarta. Sororo duk suka tsaya suna kallon Suhaima da zazzaro idanu ta na musu nuni da ɗakin, ƙanenta ya shiga ɗakin ya duba bai ga komai ba ya fito. Tsaki ya ja ya ce. "Dalla can Wallahi Anty kin soma samun ciwon hauka tsakanin jiya da yau" Ya faɗa yana wucewa.".


Fama aka dunga yi da Suhaima ta shiga ɗakin amma ta ce ita fa ba za ta kwanta a ɗakin nan ba, Umma ta jata ta kaita ɗakin yayarta ta kwanta. Ganin ita ɗaya ce za ta kwanta ta ce. "Umma don Allah ki zo mu kwanta Wallahi sake ganinsu zan yi ki taimakeni."
Ta faɗa ta na zare idanu tare da ƙanƙame hannun Umma. Ganin da gaske tsoro take ji Umma ta ja ta suka kwanta ta maƙale a jikin Umma ta na runtse idanunta. Sosai mamaki ya kama Umma jin yadda zuciyarta ke bugawa, addu'a ta dinga tofa mata ta na shafa kanta har bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita..


Washe gari bayan an fito daga Sallah Abba ya dawo gida, a palo ya yada zango ganin Suhaima a palon sai ƙifƙifta idanu take kamar barawon da dubunsa ta cika.
Ganin Abba yasa ta dan sunkuyar da kai ta ce. "Go..good morning Abba." Tsuru ya mata da ido yana amsa gaisuwar da ta masa, wayarsa ce ta soma ruri ya fito da ita daga aljihu, ganin mai kiran sai abin ya bashi mamaki har sai da fuskarsa ta nuna. Yana ɗaga kiran da sallama cike da mamaki ya ce. "Sani ina shi Abdullah yake naji wayarsa a hannunka da safiyar nan?"
Kuka ya ji Sani yasa ya soma koro masa jawabi.
"Uncle Daddy ya mutu."
What! Ban gane me kake nufi ba da gaske ya mutu?"
Amsa ya basa da.
"E muma sai da muka tashi muka gansa an masa yankan rago."
"Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Sai ya yi baya rajaf ya zube a kan kujera ya saki wayar ta faɗi ƙasa.
Umma da ta fito daga kitchen jin maganar Abba ta ce. "Lafiya dai? Me ya faru naji kana sallallami?"


Suhaima kuwa kwalalo idanu waje ta yi ta na jiran taji mai Abba zai faɗa, dafe kai Abba ya yi da ƙyar ya iya cewa.
"Abdullah ya wasu."
Zabura Suhaima ta yi za ta fankaya da gudu Umma ta yi saurin kamo hannunta , a ruɗe ta kalli Abba ta ce. "Abba Wallahi sune suka kashe Uncle na gansu a gaban idona suka cire masa kai, Abba Wallahi n..
Ba ta ƙarasa ba ta zube a ƙasan carpet a sume.....








# comments
#share
#noting




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[2/25 23:18] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_






Daga Alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_




SADAUKARWA GA MUTANE BIYU.


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO( Malam)*






بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣2️⃣




Hankalin Abba da Umma a tashe suka ɗago da Suhaima, da sauri Umma ta nufi kitchen ta ɗauko ruwa har ta na haɗawa da gudu ta miƙawa Abba, ya amsa ya shafa mata a fuskar amma shuru. Umma ta durƙusa ta ɗauki ruwan ta kurɓa ta fesa mata a fuska, numfashi ta ja kamar wadda aka tsikara ta miƙe zunbur ta na zare ido, ganin su Abba a zaune yasa ta matso kusa da Abba ta ce.
"Wallahi Abba na gani sun fille masa kai."
Kallan kallo Umma da Abba suka dinga yi a tsakaninsu, tunani suke ko dai Suhaima ta samu taɓin hankali ne basu sani ba. Dafata Umma ta yi cikin tashin murya ta ce.
"Suhaima wai me ke damunki ne? Shi Baban Sanin ne kika gani an fille masa kai? To in haka ne a ina kika ga an masa hakan?" Fashewa ta yi da kuka ta na riƙe hannayensu ta ce.
"Jiya na yi mafarki naga an fille wa Uncle kai a gaban idona, sai gashi yanzu kuma an ce an kashe sa. Ina jin fa abin da shi Yaya Sanin ya faɗa ya ce yankan rago aka yi wa Uncle."
Ta ƙarashe maganar ta na kallonsu, sosai take jin wani baƙon al'amari na ziyarar zuciyarta. Ta runtse idanu hawaye suka gangaro Umma ta goge mata ta na ba ta baki har ta yi shuru...


"To waye ya kashe shi Suhaima?"
Abba da Umma suka tambayeta a tare, dan ba ƙaramin al'ajabi suka shiga ba.


"Nima ban ga wanda ya kashe shi ba, amma dai ina gani aka fille masa kai jiya a cikin baccina."
Ta faɗa ta na sake fashewa da kuka.
Abba ya ce. "Yo wa ya ce miki mafarki gaskiya ne? Kar ma na ji kin faɗawa wani wannan maganar shashancin."
Sai da ya gargadi Suhaima sannan ya wuce ya nufi gidan Alhaji Abdallah.




Hankalin Suhaima har yanzu ya kasa kwanciya ta kasa tsaye ta kasa zaune, ƙaguwa ta yi da jiran Umma data shiga ɗaki zata shirya su tafi jana'izar Abdullah. Miƙewa ta yi ta shige ɗakin data kwana, a hankali ta shiga tamkar ɓarauniya sai lalleƙa ko'ina take, ganin ba komai ta ja gwauron numfashi ta zauna a kan gado ta na dafe ƙirji. Ko minti ɗaya cikakke ba ta yi a ɗakin ba wani ɓakin duhu ya mamaye ɗakin, hankalinta ne ya tashi ta ƙanƙame jikinta ta na rufe ido. Wata irin zirgiza ɗakin ya ɗauka tamkar zai kifa cikin ƙasa, Suhaima ta ƙarawa kukanta sauti ta na kiran Umma.
"Suhaima! Suhaima!
Ta ji ana kiran sunanta daga samar ɗakin, hakan yasa ta ɗago kai bakinta na rawa ta kalli samar. Saurin sadda kai ta yi ƙasa ganin yarinyar da ta gani a cikin mafarkinta ita da wannan jariran ta ruƙo su a hannu ɗaya ta na miƙo mata su.
Saukowa yarinyar ta yi tare da yaran ta iso gaban Suhaima wutar ɗakin ta ɗan haska kaɗan ta yadda za kaga wanda yake kusa da kai, dariya Yarinya ta yi ta haɗe fuska ta ce.
"Suhaima shin kin taɓa ganin inda aka raba hanta da jini?"
Girgiza kai Suhaima ta yi ta ƙi yarda su haɗa ido da yarinyar, tsawa ta daka mata cikin fushi ta kuma faɗin.
"Ke! Idan kika kuskura na sake yin magana kika girgiza mini kai sai na mayar dake Mage ko Ɓera."
Da sauri Suhaima ta ce.
"A'a don Allah ki taimakeni ki rufa mini asiri karki mayar dani Mage, ni hasali ma tsoron Mage da Ɓera nake z.. Kafin ma ta ƙarasa maganar su duka ukun suka zama Maguna manya-manyan da su, ɗaya fara, ɗaya baƙa, ɗaya blue duk suka zubo mata idanu tare da yin kukan maguna. Tsalle Suhaima ta yi ta koma ƙuryar gado ta na ƙanƙame jikinta, ganin haka yasa suka kwashe da dariya suka dawo yadda suke .
"Za mu tafi amma ki sani muna nan dawowa gareki dan dole ne ku girbi abin da kuka shuka, yanzu wasan zai fara." Waro idanu Suhaima ta yi cike da rashin sanin inda maganarta ta dosa ta ce. "Baiwar Allah to ni mai na muku da har kike cewa zan girbi abin da na shuga? Ni fa ko zagin babba ban taɓa yi ba ballantana kuma yaro kamar ke. Ga kuma wasu jarirai sai firgitani kuke don Allah ku yi haƙuri ku rabu da rayuwata."
Wani mugun kallo jariran suka mata wanda yasa ta ji cikin ya bada sautin ƙululuu!
"Zan iya taimakon ki amma sai na gama aiwatar da aikina akan sauran bil'adama da nake son gama shi nan da wani lokaci, wannan jariran kuma bani da hurumin faɗa miki su waye su da kansu za su fada miki komai. Rakosu na yi sun ce suna son ganinki shi ya sa na rakosu, amma in ba haka ba ba za ki ganni ba sai a mafarkin ki mu haɗu a maƙabarta, inaso zan yi ramuwar gaiya wadda tafi ta gaiya ciwo."
Baki buɗe Suhaima ke kallon Yarinyar har ta dasa aya a maganarta ba ta san ta gama ba, haushi ne ya kama Yarinyar nan ta zabga mata mari a fusace ta ce.
"Idan ina magana ba'a tafiya duniyar tunani."
Wani irin raɗaɗi da zafi ne suka ziyarci kuncin Suhaima, sosai taji marin har cikin ƙwaƙwalwarta ta dafe kuncin ta ce.
"Y..Yi haƙuri Anty."
"In kika sake ce mini Anty sai na mayar dake duniyar aljannu."
Ta faɗa ta na sauka a gadon, yaran ta rungume kafin Suhaima ta yi magana ta kuma juyowa ta na zaro mata idanu ta ce.
"Idan na sake ji kin faɗi wani abu game da mafarki kin san gabar."
Ta faɗa ta na ɓacewa daga ɗakin, Suhaima na ganin ta tafi ta miƙe jiki ba ƙwari ta faɗa toilet da sauri, kafin ta tsugunna tuni ta saki futsari a jikin dole tasa ta cire kayan ta nufi bahon wanka.. Ta na murda famfo idanunta na rufewa ta miƙa hannu ta taro ta kai fuskarta, ƙarni ta ji ruwan na yi ta yi saurin buɗe idanunta ta kalli hannunta, zabura ta yi ta na zubar da na hannunsa sakamakon ganin ruwan ya zama jini.. Ta na gefe tsaye sai ta ga famfon ya kunna kansa ta zuba ido ta na kallon ikon Allah, ganin babu jinin ta matsa a tsorace ta tari ruwan zuciyarta na bugawa, a hannunta ta zuba ta ga bai canja ba hakan yasa ta yi sauri ta wanke hannu da ƙafa da kuma fuska gudu-gudu ta fito daga toilet ɗin.. Babu abin da ta yi data fito riga doguwa kawai ta zura ta janyo hijabinta ta sa, da yake a ruɗe take ƙasar kan hijabin shi ne a sama, samar kuma a ƙasa haka ta fito ta na buga sauri kamar za ta tashi sama..
Galala Umma ta saki baki ta na kallon Suhaima ganin yadda ta saka hijabin, sai da ta iso Na'im ya dube ta yana riƙe baki ya ce.
"Anty Suhaima da alama sai mun kaiki Kano Dawanau, dan naga alama kin soma abu irin na masu lalurar ƙwaƙwalwa."
Harara ta watsa masa tare da jan tsaki ta ce.
"To fitsararre maza ka zageni kaji daɗi, ni ban san me ya sa ka raina ni ba. Kodayake ai ban soma kai maka hannu ba ne shi ya sa, wuce dalla can malam ka kaimu lokaci na tafiya."
Ta faɗa ta na kuma jan wani tsakin tare da amsar makullin motar dake hannun Umma ta cilla masa ya cafe.
Umma ta ce.
"To sai ki gyara hijabin ko."
Ta ji muryar Umma ta daki dodon kunnenta, hannu ta kai ta laluma hijabin ta ji ba daidai yake ba sai ta juya ya dawo nomal sannan suka wuce a gidan...


Kasancewar gidan Alhaji Abdullah ba shi da nisa da nasu gidan basu ɗauki lokaci ba suka iso bakin get ɗin gidan, hon Na'im ya yi Maigadi ya buɗe masa ya shigo ciki.


A harabar gidan Abba ne tsaye tare da jami'an tsaro da wasu mutane biyar suna magana a kan kisan, Suhaima ta miƙo kafarta waje ta ɗago ɗayar za ta fito da ita wata irin iska ta bigi inda take ta wuntsila za ta faɗo Umma ta yi saurin tareta.
"Ke ki bi a hankali mana saurin mai kike yi?"
Ta faɗa ta na sakin ta, dafe ƙirji ta yi jin gabanta na faɗuwa a haka dai ta lallaɓa ta fito.


Daret ciki suka wuce Umma da Suhaima, tun daga ƙofar shiga palon suke jin sautin kukan matar Alhaji Abdallah. Cike suka tarar da palon suka nufi inda matarsa take suka zauna Umma na ba ta haƙuri.


"Haba Umman Suhaima ku barni na yi kuka, taya za mu kwanta da mijina lafiya lau amma a samu wani ya shigo har ɗakinsa ya masa yankan rago kuma ku ce kar na yi kuka? Shi kenan an mayar da yarana marayu ni kuma na tashi daga matar aure na koma bazawara? Wallahi ko wane ne ya kashe mini miji ba zan taɓa yafe masa ba ko ƙabarinsa yana cin wuta."
Matar Alhaji Abdallah ta faɗa ta na kallon 'yan falon idanunta sun yi jajur fuskarta ta kumbura saboda kukan da take.
Su Suhaima masu ruwan ido a kusa tuni ta dinga zubar da hawaye, tsoro da firgici sun ƙara samun mazauni a cikin zuciyarta da ma gangar jikinta. Tagumi ta rafka ta na magana murya ƙasa-ƙasa ta ce.
"Waiyo Allah ni

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads