Showing 27001 words to 30000 words out of 38049 words
Chapter 10 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
na ɗauke ki na kawo ki inda nake mu yi ta wasa, wani lokacin na zama yara mata kamar ke wani lokacin kuma na zama namiji.. Ana haka Janu ta gano kina a raye zuwan ki na farko Makaranta na haɗu dake muka ƙulla soyayya duk da kina yarinya ne ba ki san mai ake nufi da so ba; haka na tafi zuwa yankinmu sai kawai naga Janu ta jaki zuwa Maƙabarta na yi sautin tarwatsa hanyar na ɗauke ki, na koma mace na kaiki gida na baki abinci na kaiki wajan wasa, ganin iyayen naki na neman ki sai na aje ki a bakin maƙabartar hanyar da suke wuce wa suka ganki..
Tun daga ranar nake baki kariya, kina jaririya na ɗaura miki wannan ɓakin zare wanda da shi nake iya sarrafa tunaninki,sai na ɗauke ki mu bar yankin kar Janu ta kashe ki..
Kwalalo idanu Suhaima ta yi jin yadda yake bata wannan rikitaccan ahali nata masu zama da aljannu; kuka ta sa masa ta na ƙoƙarin kwace ruƙon da ya mata amma ta kasa, a ruɗe take faɗin ..
"To amma me ya sa na daina ganin ka na tsayin shekaru tun ina da shekaru 14 na fasa haɗu wa da kai, zuwa yanzu kuwa ina da shekara 24 ko ma fi?"
Ɗago da ita ya yi ya ce.
"Janu ce ta yi nasara a kaina shi ya sa na kwanta jinya, nahiyar ma gabaɗaya na bari, lokacin da kike shekaru 12 to a lokacin har mun haifi Ayan da Iman su 'yan biyu ne na ɗauke su muka bar yankin. Sai bayan kin ƙara girma na fara basu izinin su zo su ganki saboda sun takura suna son ganin ki, ranar farko tsorats ki suka yi hakan yasa na musu faɗa sosai na ce musu suke zuwa a suffar mutane ba irin tamu suffar ba. Bayan na gama dawowa nan yankin duk na ga abin ya dinga faruwa dake, da kaina na taso ruhin iyayenki na haɗa ku a mafarki."
Da sauri ta ce.
"E ai na gansu sau uku ne, sai kuma shi Kakana na gansa sau biyu."
"Wannan dai shi ne asalin ki kuma dama can Boka iyayensa sun jima da mutuwa sai shi kaɗai, dangin mahafiyarki kuwa sun tashi sun koma Kasar su Ethiopia can inda suke. Sai wannan lokutan ina yawo na gano inda suke kuma har yau suna son ganin ƴarsu."
Shuru Suhaima ta yi sai kuma ta kalli Sayyid ta ce.
"Kana nufin ka ce ni na haifi yaran nan? Kuma har yanzu ba ka musulunta ba?"
Gyaɗa mata kai ya yi ya miƙe tsaye ya juya mata baya; cikin nuna tabbatar da maganar tasa ya ce.
"E ban musulunta ba, kuma ina matuƙar ƙaunar ki fiye da tunanin kowa. Shi ya sa ma na kawo ki nan dan mu ci gaba da rayuwarmu mai daɗi kamar yadda muka saba a shekarun baya."
Jiki na rawa ta kuma cewa.
"To amma me ya sa ka sawa kanka sunan musulmai har da yaranka?"
"Saboda ina son sunayen ne, ki saki jikin ki mu yi zaman mu a nan ki ci gaba da haifa mana yara mu tara su, sannan zan kaiki ki ga dangi mahaifiyarki."
Jin abin da yake faɗa ta fashe da matsanancin kuka; sai kawai ji ta yi ya rungume ta yana shafa bayanta nan da nan jikinta ya yi sanyi amma ba ta daina kukan ba..
"Ni fa ban ga wani abin kuka ba a nan, nine dai mijinki kuma zan iya komai a kanki wadda take addabar rayuwarki na kawar da ita ni da yaranki, dan haka ki daina damuwa. Kuma na miki alƙawarin ba zan taɓa futo miki a suffar aljannu ba sai ta mutane, idan kina so ma zan je na nemi auren ki a inda aka riƙe ki a mana aure sai na saya miki gida a cikin gari mu zauna mu da yaranmu."
Saboda tsabar tashin hankali ba ta ma san hular dake kanta ta faɗi ba sai da taji ya mayar mata yana lallaɓa ta, kalamai yake mata kunne yana saukar mata da hucin bakinsa.
Ita kan taga ta kanta miji aljani yara aljannu, sai ka ce a garin gaɓa-gaba, taya ma tana mutum za ta auri aljani wannan ai haramun ne ko ita ba musulma ba ce ba za ta iya auren aljani ba; wani sabon kukan ta saki ta ce.
"Sayyid ni dai ka rabu dani ka mayar dani gida, mu a addinin mu rahamun ne ka auri jinsin aljannu kana mutum; kai ko ba musulma ba ce ba za ta auri aljani ba ta na matsayin mutum.. Ka yi haƙuri ka rabu da rayuwata na zauna a cikin mutane ba zan iya rayuwa a nan ba."
Ta faɗa cikin wani mugun tashin hankalin da yafi na baya, taya ma za ta Kubota daga hannun Sayyid da yake ikirarin ita matarsa ce wai har ma da yara?
"Ba zan taɓa rabuwa dake ba, ke tawa ce ba mai rabamu muna tare.
Ta tsinkayo muryarsa ta ziyarci dodon kunnenta; ta yi hanzarin tashi ya hana ta, duka take kai masa a ƙoƙarin ta na ya rabu da ita sai taji ya ce.
"Wannan ai dukan soyayya ne kike min, hakan ya ƙara tabbatar mun kina matuƙar so na."
Wani sabon kukan ta saki sai ya haɗa hannayensa ya tashi ta zauna; murmishi ya yi ya hura mata cikar bakinsa a fuska. Kallon shi ta yi ta na kuka suna haɗa idanu ta ji masifar son shi ta mamaye ta ,ji take kamar ta tsaga jikinsa ta shiga saboda yadda take ji, hannu ya buɗe mata ai kafin ya gama buɗe wa ma ta faɗa kansa ya mayar ya rufe yana wani kalar murmishi..
Murmishi Ayan ya yi duk da bai ji daɗin kalaman maman nasu ba da ta ce za ta barsu; amma ya ji daɗin yadda Baban nasa ya yi wa maman nasu, kallon su ya yi ya ce.
"Baba ka rabu da Mama ta koma inda take so mana; za mu ke kai mata ziyara ai; tun da ta ce ba za ta iya zama a nan ba."
Ɗaure fuska Sayyid ya yi ya kalli Ayan ya ce.
Am so sorry my fans kwana biyu van yi post ba duk na yi busy ne, yau dai na fanshe muku two fage na muku a ɗaya. Ina matuƙar godiya da ƙaunar ku a gareni masoya Allah ya bar zumunci💞💞😘
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/16 23:22] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
1️⃣2️⃣
"Babu inda zan sake bari ta tafi ba tare dani ba; in har kaga Ummu ta bar nan to ni da ita da ku be muka tafi wata nahiyar dan ci gaba da gudanar da rayuwarmu. Ba zan kuma yin sake Ummu ta ƙara tafiya ta barni ba, dama ba son zaman inda take nake yi ba duk da babu abin da suke mata na ɓacin rai."
Tun da ya fara magana Ayan yake kallon shi cike da mamaki; ganin ran Baban nasu ya ɓaci a kan kalamansa sai ya sunkuyar da kai tare da ita gabansa ya soma basa haƙuri.
"Ka yi haƙuri Baba kada ranka ya ɓaci a kan wannan ƴar maganar; naga Mama ta ce ba ta son zama a nan sai mu barta ta zaɓi inda take son zama indai muna so mu faranta mata rai Baba. Nasan kuma ta na sonka Baba ka yi haƙuri ka bar Mama ta koma inda aka riƙe ta."
Jinjina kai ya yi bai ce komai ba; ganin haka yasa Iman matsowa ta tashi Ayan ta na murmishi ta ce.
"Kaga ka rabu da su tun da dai Mama ta dawo garemu ai bamu da wata damuwa kuma; kawai dai mu yi ƙoƙarin faranta mata rai."
Kallon ta Sayyid ya yi yana jinjina kai dan ba ƙaramin faranta masa rai ta yi ba da kalaman ta.
"Iman ku tafi ku tono wannan kwalbar A MAƘABARTA wadda Janu ta binne ita da ɓakin aljani; in ba'a tone ba ko da Janu ta mutu to fa ku sani ruhinta ba zai taba barin mu , maza yanzu ku yi abin da na umarce ku."
Ya yi magana yana nuna musu hanya; da sauri suka kalli juna Iman ta kama hannun Ayan suka ɓace a gurin. Dawo da kallon shi ya yi kanta ta yi luf a jikinsa idanunta a lumshe ka.ar mai bacci.
"Ummuu...!
Ya kira sunanta cikin wata kalar murya wadda ta sa Suhaima buɗe idanu ta kalle shi; murmishi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, magana ta fara cikin kasalalliyar murya.
"Sayyid ɗina..!
Ta ja sunan ta na yi masa wani irin kallon; ji take kamar ta shiga cikin jikina saboda wata zazzafar ƙaunar sa da ta mamaye kowacce kusurwa ta jikinta. Ajiyar ta sauke sannan ta ce.
"Zan ci abinci."
Fuskarta ya kamo cikin hannayensa masu matukar laushi; ya sumbaci kumatunta tare da mayar da ita jikinsa sannan ya ce.
"Wani kala kike so?"
Murya can ƙasa ta ce.
"Tuwon shinkafa da miya nake so."
Hannu ya ɗaga sama ya haɗe yatsunsa guda biyu ya ɓala su sai ga abinci ya bayyana a kan trey; tashin ta ya yi ya ce.
"To gashi ki ci ki ƙoshi."
Da sauri ta gyara zama ta sa hannu ta ɗauko loma ba bismillah ta soma cin abinci da sauri-sauri; shi kuwa sai wani kalar murmishi yake yana kallon yadda ɗan ƙaramin bakin bakinta yake motsawa wajan tauna abincin..
Tana gama wa ya nuna mata waya kyakyawar roba a gefen kular abinci ta kalle shi; gira ɗaya ya ɗage mata yana mata nuni da ta sa hannu.
Ba muso ta sa hannun da kansa ya wanke mata hannu da baki duk ta na kallon shi ta na lumshe idanunta kamar wata ƴar ƙwaya; ganin bai ci ba ta ce.
"Sayyid kai ba ka ci ba."
"A'a ni na ƙoshi ai muje ki kwanta ki huta.
Ya yi maganar yana miƙar da ita tsaye; kafin ta yi wani yunƙuri ya kai hannu ya rufe mata idanu. Ita dai ji kawai ta yi an ɗauke ta an rungume can kuma ta tsinkawo muryarsa yana magana.
"Ummu to kwanta a nan."
Ya yi maganar yana nuna mata wani makeken gado mai mugun kyau; tarr ta buɗe idanunta ta kalli gadon baki buɗe saboda mamaki ta ce.
"Sayyid nan ɗin ina ne ka kawoni kuma? Ni fa ka mayar dani wajan su Umma inaso na zauna a can, ka taimaka ka mayar dani idan kuna son ganina sai ku zo ku ganni a kodayaushe ka ji."
Ta yi maganar wasu zafafan hawaye zarya kan kuncinta ; ta ci gaba da magana.
"Indai har da gaske sona ka barni na tafi gida; yanzu haka hankalin su Umma a tashe yake duk da an aje mai kama dani a ɗakin."
Tun da ta fara magana yake kallon ta, ganin yadda take kuka da gaske sai ya ji zauna yana kallon ta fuskarsa cike da damuwa, hannunta ya kamo ta yi saurin buge nashi ta ƙudundune nata ta na faɗin.
"Ni ka mayar dani wajan su Umma ba na son zama a nan; idan kuna so ku ganni ai ba sài kun kawoni nan ba."
Murmishi ya yi ya shafa hannunsa duk da ba wani zafin dukan yaji ba ya ce.
"Haba Ummu me ya sa kike gudun mu wai?"
"Saboda babu aure a tsakanin mutum da aljan, sannan Addinin Musulunci ya haramta yin mu'amala ta aure tsakanin mutum da aljani, ina mai baka haƙuri da ka rabu da rayuwata ka samu wata a jinsin ku na aljanu ka aura, na san za ka samu wadda ma ta fini komai. Ni ma ka barni na zauna a cikin jinsi na, yaran kuma da muka haifa ni dai ban dauki cikìn kowa ba, amma na yarda ana haihuwa da jinsin ku. Kuna aurar jinsin bil'adama ku sadu da shi ta hanyar mafarki, wani lokacin ma zai ji kamar da gaske ne yana mu'amalar aurataiya da wani; amma da ya buɗe idanu sai yaga ba kowa kaima kuma nasan ta haka ka zo min har na samu ciki na haifa ma yaran nan. Ka daure ka sadaukar da soyayyar da kake mini Sayyid ka mayar dani cikin yan'uwana mutane na zauna, kuma ina fatan ko ba yanzu ba ka musulunta kafin mutuwar ka ta zo gareka.."
Wani irin ƙyarma jikin Sayyid ya ɗauka, idan ta furta kalmar ya rabu da ita sai ya ji tamkar ana zare masa zuciyarsa ne, lumshe idanu ya yi jin yadda jikinsa yake ƙoƙarin canza wa zuwa asalinsa na aljani; ya yi saurin saita nutsuwar shi ya kalle ta cikin tsananin tashin hankalin rabuwar da take cewa ya yi da ita..
"Ummu!.. Yanzu in na rabu da ke wa zan samu wadda zan so ta kamar yadda nake matuƙar son ki?"
Da sauri ta ce.
"Za ka samu kai dai ka yi haƙuri ka rabu da rayuwata, idan su Ayan sun so ganina sai su zo. Ni kan rahamun ne a gareni na zauna da kai,naso ace ka fito a jinsin matane amma kuma ba yadda na iya dole mu rabu...
Mamaki sosai ya kama Sayyid ganin fa da gaske Suhaima ta dawo cikin haiyacinta, ya rasa ma taya aka yi abin da ya mata ya sake ta cikin ƙanƙanin lokaci haka? Girgiza kai ya yi yana tunanin in har yana so ta yi farinciki to gara ya barta kawai ta koma inda ta taso..
"Ummu naji zan rabu da ke amma ba dan na so hakan ba, ina sonki fiye da komai na duniya."
Da sauri ta kalle shi baki na rawa ta ce.
"D.. Da gaske Sayyid ka haƙura za ka barni na yi rayuwata ba tare da ka takura mini ba?"
Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa ya ce da ita.
"E na barki ki yi rayuwarki a cikin jinsin ki saboda son da nake miki zan sadaukar da ke miƙo min hannunki na cire miki wannan zaren da na ɗaura miki."
Ya yi maganar yana miƙa mata nasa hannun; ba ta musa ba ta miƙa masa ranta fes. Tsintsiyar hannunta ya dan danna sai ga zaren ya bayyana, sosai Suhaima ta cika da al'ajabin wannan zare, tana cewa ashe dama tun tana jaririya zaren nan na cikin jikinta ba ta sani? Tab lalle aljannu lamarin ku na daban ne.
Ta na wannan tunanin ya cire zaren yana kallon cikin idanunta ya ce.
"Ga su Ayan nan za su mayar dake su dawo min da mai hidima na."
Jinjina masa kai ta yi ransa ya yi sanyi haka ma jikinta, ta na jinjina irin son da Sayyid ɗin yake mata sai yanzu ta tabbatar da gasken-gaske yake son ta ba dan ya cutar da ita ba, inda wani ne da har abada ita da ta ga jinsin mutane har ƙarshen rayuwarta zai aje ta a nan ya tsafe ta, ƙila ma ƙarshe ya mayar da ita rabi mutum rabi aljana, amma gashi shi yaji tausayin ta ya ce zai mayar da ita gida..
A sanyaye ta ce.
"Sayyid ka yi haƙuri na so ace a mutum ka zo da babu abin da zai hana na aure ka, in kaga ba mu yi aure ba to wani ikon Allah ne ya hana mu zama ma'aurata."
"Babu komai ai na fahimce ki, sannan da kin shirya zan kaiki ki ga dangin mahaifiyarki. Ga wannan da kin shirya ki murza ta za ki ga Ayan da Iman sun zo gareki."
Ya yi maganar tare da miƙa mata zobe ruwan gwal; amsa ta yi ta sa ta na murmishi ta masa godiya sannan ta ce.
"Ina ƙara jadadda maka in har kaji kana son shiga addinin musulunci kai da yaran nan to zan fi kowa jin daɗin hakan."
"Ummu zan yi tunaniin gani ko zan shiga.
Ya ba ta amsa a sanyaye kamar wani mutum.
Murmishi ta yi ta na kallon zoben ta ce.
"Sayyid shi addinin Musulunci ba a shigarsa ba tare da an ji ana son za a shiga ba, ka shiga addinin Musulunci bisa raɗin kanka ba wai dan na maka maganar sa ba. Ka ji a ranka cewa ka yi imani da Allah ka kuma ji ƙaunar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam sai ka amshi kalmar shahada, amma in ba ka wannan shauƙin guda biyu to kada ka shiga; ka bari har sai lokacin da ka ji zuciyarka ta aminta da su imani ya shige ka sannan ka amshi kalmar shahada."
"To Ummu yanzu dai ba na jin hakan; amma Ayan ya soma jin hakan dan yana son ya ga musulmai suna ibada ya yi ta kallon su suna birgeshi; musamman idan suna karanta littafin nan."
Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce.
"Shi ma ya bari ya yarda da wannan abubuwan sai ya amshi kalmar shahada, yanzu su zo su mayar dani gida."
Bayyana Ayan da Iman suka yi yana riƙe da ita; kallon su Sayyid ya yi ya ce.
"Ya ya dai? Ko kun samu matsala a hanya ne?"
Rai a matuƙar ɓace Ayan ya ce.
"Mun je za mu tone sai kawai tawagar Janu suka zo, shi ne muka yi ta faɗa karshe muka kashe su muka tone muka ƙona. Shi ne Iman ta jikata ɓakin aljani ya tare ta."
A zafafe Sayyid ya ce.
"Ina fatan dai kun kashe shi?"
"Tun tuni ni na kashe mugu Baba yanzu itama za ta warke."
Ya yi maganar yana ciro zoben hannunta ya ɗago da ita Suhaima ta yi saurin kamo ta ta riƙe ya ɗaura zoben a kan gurin sarar ya kawo haske. Nan da nan ya ɓace ciwon suka kira sunanta ta buɗe idanunta a kan Suhaima, kafin