Showing 21001 words to 24000 words out of 38049 words
Chapter 8 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
yanzu kika samu ta yadda kika cutar min da ɗan'uwa? To kin taɓa mutuwar ki da kanki."
Ta na gama faɗin haka ta rufe idanu cikin wata kalar murya ta soma faɗin mai haɗe da kuka-kuka ta taƙarkare ta soma magana.
"Baba! Baba! Baba!"
Dajin ne ya ɗauki girgiza tamkar zai kifa cikin ƙasa; ita kuwa aljana Janu na tsaye kan wata bishiya ta na dariya, so take ta ga wanda zai zo...
Wata irin iska ce ta mamaye dajin mai ƙarfi; babu wanda yake jin ƙarfin iskar sai Suhaima data cure a guri ɗaya ta na karanto duk addu'ar da ta zo bakinta, har da su addu'a shiga banɗaki, da addu'ar gama cin abinci take karanto wa cikin fitar haiyaci...
Sai da iskar ta lafa Suhaima ta ji dirar wani abu a gabansu; ta ɗago da sauri idanun a waje tamkar za su faɗo ƙasa.
Tsaye ta gansa rufe da fuskarsa sanye da fararen tufafi takobinsa mai harshe biyu riƙe a hannunsa..
A razane take kallon sa; Iman na ganinsa soma magana cikin tsananin ɓaci rai da kaiwa maƙura a kan abin da Janu ta musu...
_*MAMAN NUSAIBA CE*_
[3/11 22:35] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
1️⃣0️⃣
"Baba ina so yau ka yi maganin wannan azzalumar; ta hana Mama ta zauna cikin salama duk ta addabe ta, ka kashe ta kamar yadda take kashe bil'adama da aljanu. Baba kaga Mama ta na zubar da jini ka yi wani abu kar Janu ta zuƙe mata jini yanzu."
Cikin ɓacin rai take magana har muryarta na canja wa; shi kansa Baban nasu kallon ta kawai yake.
"Hahaha! Hahaha! Wa ya isa ya ja da ƙarfin ikona? Ku har kun isa ku fara arangama da Janu; na bar ku ne dan ba ku isheni kallo ba amma tun da kuka za ku iya zan kashe ku gabaɗaya har Maman taku. Kai Sayyid kake ko Sayi ma? To daga kai har 'ya'yan naka duk kun kawo kanku inda za a kashe ku.
"Janu ce ke maganar ta na daga kan bishiya sarƙar hannunta na wani irin hasken wuta ja; Suhaima tuni ta yi sumar tsaye sai da Iman ta dafe ta sannan ta zabura, a firgice ta nuna Baban su Iman ta ce.
"Yaya Sayyid!"
Kallon kasa kallon ta ya yi kansa a ƙasa; wani irin hayaƙi ne ke fita a fuskarsa shi kuma baya so Suhaima ta gansa a asalin suffarsa, dan haka ya daure ya rikide ya dawo suffar mutane yadda ta san shi sannan ya ɗago.
Fashe wa da kuka ta yi ta soma ƙoƙarin motsa ƙafarta amma ba ta kuzari iya sarrafa gangar jikinta; kallon shi ta yi a rauna ce ta kuma faɗin.
"Sayyid ɗina!
Ta faɗa cikin wata kalar murya ta na masa wani irin kallo; kallo ne irin na kewar masoyi wanda haka ya haifar mata da rashin kuzari a jikin ga kuma tashin hankalin da take gani, ita har ma ta manta da Janu da kuma Ayan da ya koma haske.
Murmushin gefe baki ya mata ya gyara tsayuwar sa tare da miƙa hannu ya janyo ta ta dawo kusa da shi; kallon Ayan ya yi wanda yake tsakanin mutuwa da rayuwa; ya miƙa hannu ya ɗago gasken yana kallon Janu kamar yadda itama take kallon su da jajan idanunta.
"Ummu!
Ya faɗa a hankali yana matso da hasken kusa da su; kamar ƙiftawar ido sai ga Ayan ya dawo yadda yake, amma idanunsa a lumshe suke.
Ita dai Aljana Janu na gefe ta na dariya sai juya sarƙarta take.
Ayan na buɗe idanu ya yi ido huɗu da babansa; da sauri ya ce.
"Baba ina Mama?"
Nuna masa ita ya yi da hannu ya matso kusa da ita ganin yadda take kallon baban nasu ya kuma faɗin.
"Mama ki kwantar da hankalinki komai ya zo ƙarshen tun da har Baba ya zo; ki daina kuka Mama."
Haɗiye kukan ta yi tasa hannu ta goge hawayen ya tayata goge wa, kallon Ayan ta yi fuskarta fauke da alamar tambaya; shi kuma ya yi murmishi ya ce.
"Mama nasan mai kike tunani; ki bari duk Baba zai miki bayani."
Ba dan ta so ba ta yi shuru ta na ƙara koma wa bayansa , so take ta sake kallon fuskarsa dan ta tabbatar da shi ɗin ne, amma kuma tsoro ya hana ta yi hakan...
"Idan kun gama ku miƙo mini ita nan; na faɗa muku ba na son raina ya ɓaci fa. "Janu ke faɗa ta na sauko wa daga kan bishiyar ta ja ta tsaya.
Ayan da Iman suka shiga gaba suka tsaya, Iman na aiko mata wani irin kallo ta ɗaga hannu ta nuna ta da ta soma magana.
"Ke har kin isa muna gani ke kashe mana Mamanmu? Wace ce ke? Dama Baba ke hanani aika ɗanyan aiki a kanki nake haƙura, amma yau kin kai haƙuri ƙarshe mu da ke za a ga wanda zai kashe wani."
Wata kalar figitacciyar dariya Janu ta yi; wanda hakan yasa Suhaima maƙale wa a bayan Sayyid ta na faɗin.
"Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Sayyid ka taimakeni kar ta kasheni Wallahi muguwa ce ajin farko."
Sunbatu ta dinga yi jin yadda sautin dariyar Janu ke hautsina mata hantar ciki; gashi kuma shi Sayyid ɗin ko motsi bai yi ba ta maƙale a bayansa.
"Mama ki nutsu mana. "Iman ta faɗa a sanyaye fuskarta na nuna ɓacin ran dake cikin zuciyarta.
Hannu Sayyid ya buɗe ya saka yatsunsa biyu a kan gishinta ya ce.
"Ummu yi shuru."
Ɗif ta tsayar da kukan kamar ba ta wajan ma; Iman ta juyo ga Janu ta ce.
"Idan har kin cika ke mai ƙarfi ce ki zo mu kara."
"To! Yarinyar nan naga alama kina son na aika ki inda ba'a dawowa. Ke ko wanda ya haifeki yasan ko ni wace ce ballantana ke ƴar ƙarama dake ki ce za ki ja da ƙarfin ikona..
A harzuƙe Ayan ya ce.
"Karfin ikon banza da wofi; muguwa azzaluma."
Wannan kalma ba ƙaramar ɓata wa Janu rai ta yi dan haka ta yi girgiza ta na kwarara ihu; sai gata ta dawo wani darkekiyar Damisa ta nufo kansu a sukwane..
Ganin haka yasa Ayan da Iman suka koma Giwaye manya-manya; bakinsu na feshin wuta suka tsaya ƙyam suna jiran zuwan ta. Kafin ta iso suka kuma rikide wa zuwa wata kalar halittar ta da ban, suna haɗe wa aka dinga kaiwa juna sara da suka ta ko'ina.
Yaƙi suke ba kakkauta wa , har zuwa lokacin ba wanda ya yi nasarar kai ɗan'uwansa ƙasa sai fafatawa ake ba ji ba gani..
Janu ta shammaci Iman ta shaƙo ta da ɓakar sarƙar dake hannunta; ita ko Iman rintse idanu ta yi duk da azabar ciwon da yake shiga cikin rubuta amma saŕa take kaiwa iya bakin ƙoƙarin ta.
Sayyid na tsaye yana kallon su ko motsaw bai yi ba; ganin Janu na neman shaƙo Ayan ya yi wani irin huci da babbar murya ya ce.
"Ayan! Maza ka kashe ta kar ku raga mata, riƙe nan "Ya ƙarshe maganar yana cilla ɗaga takobinsa sama."
Saurin buɗe hannunsa Ayan ya yi sai ga takobin ta bayyana a hannunsa; Janu na ganin wannan takobin ta dakka tsalle irin nasu na aljannu ta daki hannun Ayan takobin ta faɗi.
"Hahaha! Hahaha! Riba uku kenan ga takobin da na ɗauki shekaru ina neman ta, ga kuma jinin da zan sha na ƙara ƙarfi da ƙarfin dake jikinku idan na kashe ku" Ta faɗa ta na nufar takobin da wani irin sauri."
Murmushi Sayyid ya yi ya juyo ya kalli Suhaima wadda ya mayar da ita kamar gunki a tsak cak take, kan Janu ya yi yana jiran ta isa ga takobin.
Hannu ta kai za ta ɗauka aka yi sama da ita aka sako ta tim! Ta faɗo;cikin mamaki ta kalli takobin ta kuma murza hannunta ta miƙa za ta ɗauka. Wannan karon tsananin haske ne ya fito a jikin takobin ya nufi jikin Janu; ihu ta kurma ta na faɗuwa ƙasa, wani irin azaba ce take huta mata ruhi ba'a iya ganin komai na jikinta duk hasken ya mamaye ta hakan yasa ta ɓace ɓat a gurin..
Ayan ya duƙa ya ɗauki takobin yana murmishi ya ce.
"Baba ka bari na bi bayanta na kashe muguwa ko an huta da zalincin ta."
Ita kuwa Iman sai ɗaure fuska take dan ba ta so Janu ta gudu ba a karo na barkatai; kallon Sayyid ta yi cikin fushi ta ce.
"Baba ka bari mu bita mana."
"A a kada ku bita za ta dawo ai; dama takobin nan take nema da jimawa amma ba ta san a ina take ba, to yau ta ganta kunga kuwa ai za ta kuma dawowa."
"Mama!
Iman ta faɗa a firgice ganin Janu ta soka mata wata ƴar wuƙa a gefen cikinta; Wani kalar tsalle Ayan ya daka sai gashi a gaban su, bai tsaya yin komai ba ya farmaki Janu cikin sa'a ya yanke ta a fuska...
Wasu irin kalamai ta dinga yi kamar ƙiftawa da bismillah sai ga dajin ya cika da wasu irin halittu masu firgitar wa; wuta na fito wa daga bakinsu, bayansu wuta ce ke ci ta kewaye dajin. Wata mahaukaciyar dariya Janu ta dinga yi ganin sun kewaye su; ta kalli Sayyid ta ce.
"Ka bani takobin nan ko kuwa yanzu waɗannan dakarun nawa su lamushe ku."
Sai yanzu Sayyid ya juyo suka haɗa idanu da Janu; babu shiri taja da baya sai kuma ta tsaya cak ta na ɗaure fuskar, shi ko gyara tsayuwarsa ya yi hankali kwance ya ce.
"Idan na ce ba zan bayar ba fa?"
"Sai na amsa da ƙarfin ikona.
"To ki kwata mu gani azzaluma; yau duk inda kika gudu sai na kamo ki na miki kisan gilla a dajin nan, ko kina tunanin wannan ƙudajen da kika zo da su za su bamu tsoro ne? To kin yi ƙarya."
Ya faɗa yana zaro wata takobin daga bayansa ya kamo Suhaima ya miƙa ta gurin Iman wadda ta canja halitta zuwa wata ƙatuwar mata.
Ganin haka Janu ta dubi wannan tawagar tata ta ce da su.
"Ku kashe mini shi; sannan ku kwace duk wani ƙarfi da yake da shi, yau zan kawo ƙarshen ka dama ka hanani sukoni."
A haukace suka dinga sa kibiyoyi a jikin kwari da baka mai ɗauke da wuta suka dinga yi wa Sayyid ruwan ta; Ayan ya murza zoben hannunsa kafin kibiyoyi su iso hasken ya musu rufa, suna isowa sai kawai suak tsaya cak ba su iso kansu ba...
Janu ta cika da ɓakin ciki ta ɗaga hannu saba sai ha takobi ta bayyana a hannunta; nuna Sayyid ta yi ta ce.
"Idan ka isa ka fito mu gwabza ni da kai ba tare da yaranka ba ko wasu tawaga."
Murmushi ya mata ya juya takobin hannunsa ya ce.
"Dama ke kika ɓata wa kanki lokaci; ni nafi ƙarfi wannan ƙananun yaran naki "
Wani irin kallo ta masa ya fito fili itama ta fita ; a tare suak yo kan juna kowa da haushin ɗan'uwansa suka haɗe a guri ɗaya. Yaƙi suke ba ji ba gani kafin wani lokaci tuni Sayyid ya soma jikatar da Janu da ƙyar take kare kanta; Iman ba huci ganin Baban nasu yaƙi kashe Janu ta rufe idanunta, wani irin ɓakin hayaƙi ne ya bayyana a cikin idanunta ta na buɗe wa suka fita zuwa kan janu. Yana isa ya shige jikinta ta yi wata irin kururuwa ta zube a ƙasa, Iyan ya fito ya iso inda suke ya ɗaga takobin ya sara mata ta kuma kurma ihu azaba, a fusa ce ya ce.
"Shin za ki rabu da Mamana ko sai na aika ki can ne?"
Duk da raɗaɗin azabar da take ji hakan bai hana ta mayar wa da Ayan martani ba.
"Yaro koma baya da ubanka nake yi ba kai ba."
Sake kai mata suka ya yi ta kuma yin kururuwa dajin na amsa-koyawar muryarta, ta na wani irin huci ta ce.
"Kar ka kasheni Ayan ita ɗin fa an sadaukar mini da jininta, dan haka ka rabu dani ku yi rayuwarku ni ku bani ita na rabu daku; ina son shan jininta dan yana da garɗi sosai. Idan za ka bar mini ita zan kirkiro maka wata sabuwar uwar mai kama da ita sak sai ka bani ita z..
Ba ta ƙarasa maganar ba Iman ta daka tsalle ta fille mata dogon hannunta; cikin azaba da zafi ta juyo ta kalli Iman ta na numfashi da ƙyar ta ce.
"Karki kasheni zan baki ƙarfin tsafina ki ƙara ƙarfi, wannan uwar taki an bani ita."
Wani irin juyi Iman ta yi ta watsa hannun ta a kan Janu sai ga sarƙar dake hannun Janu ta daure Janu gam-gam...
"Na haƙura da ita ku rabu da ni zan tafi na barta har abada ba zan, zan baku komai nawa ni duka yankin ma zan bar muku na koma yankin da ba kowa na zauna. "Janu ta faɗa a gakabaice ta na roƙon Iman dake murza zoben hannunta ta na ƙara matse Janu, duk inda sarƙar ta kwance sai ta zuba mata wata irin azaba mai raɗaɗi."
"Kin yi ƙarya wallahi ki tafi ba tare da kin warware sihirin da kika yi wa Mama ba; kuma shi wanda ya sadaukar miki da itan ba kin kashe shi ba? Saboda zalinci irin naki iyayenta sun sadaukar da kansu dan ki bar musu ɗiyarsu ta rayu; sai kika yarda amma daga baya kika dinga bin ta kina shan jinin jikinta ke muguwa, to yau ƙarshen ki ya zo Ayan ka fille mata hannun ɗaya "Ta ƙarashe maganar ta na mai bai wa Ayan umarni da ya aiwatar da abin ta saka shi ya yi."
Kafin ta juyo ga Ayan buɗe bakinsa wani irin hayaƙi Green ya fito daga bakinsa ya sauka a kan hannun sai ga shi a ƙasa...
"Waiyo! Waiyo! Ku rabu dani ba zan sake ba kar ki kasheni ku taimaka.
Haka take faɗa jin yadda ake yankar ko'ina na jikinta.
Sake kai mata suka ya yi ta kurma wata irin kururuwa; birgima ta dinga yi ta na kiran wani suna tak ai ta na ƙoƙarin tashi. Cikin mugun sauri Ayan ya caka mata takobi; ta dinga juyi ta na wuliliya zuwa can dajin ya ɗauki girgiza, wuta ce ta kama dajin gabaɗaya har da jikin Janu wutar na ci amma ana jin sautin muryar ta ta na roƙon su Ayan...
Sai da suka ji ta daina maganar sannan Sayyid ya janyo Suhaima ya sa hannu ya zare mata wuƙar da Janu ya caka mata; kama su ya yi gabaɗaya suka ɓace a dajin..
Basu bayyana a ko'ina fa sai a cikin wani daji mai cike da furanni ga kukan tsintsaye; kan wani gado mai mugun kyau ya kwantar da ita. Ayan ya matso kusa da ita ganin yadda jini ke zuba ya dafe gurin yaan rufe idanunsa, can ya buɗe ya jikin ya raga zuba amma bai tsaya duka ba..
Tattaba jikinta ya yi yaji a sake ya rufe idanu ya ɗaura hannunsa akan saitin zuciyarta yaji ba ta bugawa, a tsorace ya buɗe idanunsa wanda suka koma ja ya dubi Sayyid ya ce.
"Baba ta kashe Mama."
Saurin ɗauko ta Sayyid ya yi yana tattaba amma sam ba ta motsi..
Wani irin ƙara Ayan ya yi ya kwanta a kan Suhaima cikin tashin hankali ya ce.
"Mama kada ki mutu ki barmu muna sonki, Mama!
Ya faɗa cikin tashin hankali...
*mai ke faruwa da Suhaimar Sayyid?😢*
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/14 22:54] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
1️⃣1️⃣
Lumshe idanu Sayyid ya yi tare da kai hannunsa saitin zuciyarta; danna ƙirjinta ya yi da ƙarfi amma shuru, Iman da ta yi lamo kamar marayan da bai ci komai ta dubi Sayyid ta soma magana..
"Baba ka tashi Mama mana."
Kafin ya yi magana ta ja dogon numfashi sai tari ya biyo baya; saurin canja suffarsu suka su duka suka dawo suffar mutane kamar yadda ta san su, gabaɗaya kan ta suka yo Ayan ya yi saurin kiran sunanta.
"Mama ki tashi kasa ki tafi ki bar mu."
Buɗe idanunta ta soma yi a hankali har ta buɗe tarr; ta juyo jin hannunta a cikin wani lallausan hannu ta kalli hannun sai ta ga nashi ne, yunƙurin tashi ya soma yi Sayyid ya ɗago da ita ya zaunar duk sai jera mata sannu suke. Hannu ta kai kan gefen cikinta wanda zuwa yanzu jinin ya daina zuba, da sauri ta kalle su ta ce.
"Dama ba ciwo naji ba yanzu?"
Ta faɗi maganar ta na kallon su kamar ta samu TV; gyara mata zaman ya yi sannan ya ce.
"Kin warke ne yanzu nasan bakya jin ciwon komai ko? "Cewar Sayyid yana shafa summar kanta; ita kuwa shuru ta yi jin wani sanyi na ratsa mata sassa jikinta, tunano abin da ya faru ta yi ba shiri ya zabura za ta tashi ya kalle ta.
"Ya dai?"
"Wannan muguwar tana raye kuwa?"
Iman ta yi murmishi sannan ta cè.
"Mama ai yau mun shafe tarihin rayuwarta, daga yau kin daina jin tsoron yin bacci ko fita wani guri."
Sororo take kallon Iman har za ta yi magana sai kuma ta fasa mata ta juyo kan Sayyid.
"Sayyid wai dama kaine baban su Ayan shi ya sa suke ce mini Mama?"
Gyaɗa mata kai ya yi yana murmishi; ita kuwa ta ƙura masa idanu tuna matsayin su Iman yasa ta kuma faɗin.
"To dama ka yi aure ne? Kuma ina mahaifiyar su Ayan take ne?"
Kallon ta ya yi da kyau sannan ya ce.
"To ai 'ya'yanmu ne ni da ke."
A zabure ta kalleshi jin amsar da ya ba ta, cike da mamaki