Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 38049 words

Chapter 2 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

407

Ads at the middle of Article

Suhaima! Me Uncle ya yi suka kashe shi?"
Ta tambayi kanta tambayar da tasan babu mai ba ta amsa sai wannan aljanar yarinyar, goge hawaye ta yi ta rausayar da kai gefe ta kalli maman Sani a sanyaye ta kuma cewa.
"Allah sarki Mommy ai kuwa za ku shekara dubu ba ku gano komai ba game da kisan Uncle ɗina, duk wahalar banza ce kuke. To amma me yasa suka kashe shi?"
Ta kuma tambayar kanta a karo na biyu duk da tasan ba mai ba ta amsa..


Cikin ƙanƙanin lokaci su Abba suka wanki gawar Alhaji Abdullah shi da wasu malamai, ana gamawa aka suturta gawar suka sakata a makara motar malam. Matarsa aka kira ta zo ta amsa addu'a ta na kuka da ƙyar Sani ya janye ta daga kan gawar, bayan ta fita 'yan'uwansa suka shigo kowa ya masa addu'a sannan suka fito da shi daga ɗakin zuwa waje inda za a masa Sallah.
Firgita Suhaima ta yi ganin gawar Uncle ɗin nata ana fita da ita, ba ta san lokacin data ɗaura hannu biyu a ka ba ta fashe da kuka ta na kiran Uncle. Mutanen palon suka dinga rarrashin ta da ƙyar ta kyale..


Bayan an dawo daga jana'izar Alhaji Abdullah da Yamma su Suhaima suka koma gida.
Shaf-shaf suka shiga kitchen suka ɗaura abincin dare, Suhaima ta yi lamo da ta soma wani abu sai kawai ta yi shuru ta na kallon gefe, idan Umma na mata magana sai ta maimaita iusan sau 5 kafin ta fahimci mai take faɗa.
Ita kuwa Umma a tunaninta jimamin mutuwar Uncle ɗinta ne yasa duk ta koma haka, shi ya sa ba ta matsa da tambayarta a kan tunanin mai take.. Suna ɗaura abincin ana kiran sallar Magariba, fitowa suka yi Suhaima ta bi bayan Umma har sun kusa shiga sai kuma ta yo ribas ta nufi ɗakinta. Aro jarumta ta yi ta yafa ta yi bismillah ta sa kai ɗakin ta na muzurai, ba komai a ɗakin kamar yadda ta barsa jiya da dare haka yake, hamdala ya yi ta nufi toilet ta ɗauro alwala. Bayan ta fito ta riƙe baki fuskarta na bayyana mamakin dake cikin zuciyarta ta ce.
"To wai ya ma aka yi na manta da ambaton sunan Allah ne lokacin da na yi mafarki? "
Ta tambayi kanta ta na sa yatsu biyu ta ɗaura a gefen kan ta murza tare da faɗin.
"Da alama fa Na'im maganarsa gaskiya ce ƙila na fara zarewa ne."
Sauke hannun ta yi ta gabatar da sallar cikin sauri wacce Hausawa ke cewa shaf-shaf, minti uku ma ba ta yi ba ta gama Sallar. Koda ta salamce miƙewa ta yi ba salatin Annabi(s.a.w) ba addu'ar komai ta fice a ɗakin...


Bayan sallar Isha'i Abba ya shigo suka ci abinci aka taɓa hira zuwa ƙarfe goma suka soma sallama kasancewar gobe Monday .
Suhaima ta yi tsuru ta tsaya a bakin ƙofar ɗakinta, ganin dai ba sarki sai Allah ta wakkala ta faɗa ɗakin, kan gado ta faɗa ko minti ɗaya ba ta kara ba bacci ya shureta...


"Barka da zuwa Suhaima."
Muryar wani garjejan ƙato ta ziyarta majiyarta, a zabure ta ɗago ta ganta a tsakiyar ƙungurmin daji, gefe ta kalla ta ganta a gaf da wani ƙaton ƙabari. Kukan da take juyowa ne ya ƙara firgitar da ita, tun da take ba ta taɓa jin sautin kuka mai tsorararwa da saka firgici ba irin wanda take ji ya karaɗe dajin gabaɗaya.
Shuu!
Ta ji ƙaran wucewar wani abu daga samar kanta, kafin ta yi ƙwaƙƙwaran motsi wannan abin dake samar kanta mai kama da tsuntsuwa ya shureta sama ya illata cikin maƙabartar......






#share
#commets






_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[2/27 22:36] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_










Daga Alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_






_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*




بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣3️⃣


Tim! Aka watsar da ita a kan wani ƙabari babba, daskarewa ta yi a gurin tamkar gunki numfashinta na barazanar rabuwa da gangar jikinta.


"Suhaima! Suhaima! Suhaima!
Ta ji sautukan muryoyi daban-daban suna kiran sunanta a haɗe, ƙara ta ƙwalla ta na rufe kunnuwanta jin yadda sautukan muryoyin ke ratsa mata kunne har cikin ƙwaƙwalwarta.
"Buɗe idanunki na ce!" Aka faɗa cikin tsawa, babu shiri Suhaima ta buɗe idanunta ta sauke su akan yarinyar nan ta fashe da kuka ta na ja da baya yarinyar na biyota. Juyi aka yi da ita sai gata a gaban wani halitta mai sanye da kaya jajaye, baki ya buɗe mata yana dariya.
"Hahaha! Hahaha! Hahaha barka da zuwa Suhaima."
Zuwa wannan lokacin idanun Suhaima sun ƙafe babu alamar hawaye sai zaro su da take, a firgice ta kalli halittar nan jin an daka mata tsawa jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari ba ta san lokacin da ta dinga taune lips ɗinta na ƙasa ba..
"Wai ni me na muku ne?
Ta faɗa bakinta na zubar da jini sakamakon taune lip ɗinta da ta yi."
"Har kin manta abin da kika kika mana ne? Aka ba ta amsa daga gefenta; juyowa ta yi ta dubi yarinyar dan yanzu ta na son jin lefin data aikata musu har suke kawo ta maƙabarta, da sauri ta ce.
"Wani abu na muku ki faɗa mini sai na baku haƙuri, ku rabu dani na zauna lafiya cikin salama ."
Ta yi magana jikinta na rawa, hannu ta kuma haɗewa ta dubi yarinyar ta ce. "Baiwar Allah ki sanar dani lefina a gareku na miki alƙawarin zan gyara halaiyata na nemi yafiyarku. Ni dai a iya sanina ban yi komai ba."
Ta faɗa ta na sauke hannayenta. Wani firgitaccen kallo ta aiko mata, nan da nan tsoro ya ƙara shiga jikin Suhaima, ta sadda kanta ƙasa, a fusace ta ce.
"Au har ma kin manta abin da kuka aikata mana? Tambayata ma kike na faɗa miki lefinki a garemu? To yanzu kuwa za ki sani sai kin gwammace ba ki tambayeni ba. Yarinyar ta faɗa ta na damƙar gashin kan Suhaima ta mayar da ita cikin maƙabartar ta jefar." Kuka Suhaima ta shiga yi ta na haɗa hannaye ta na roƙon yarinyar amma ta juya mata baya ta yi kamar ba ta san mai take yi ba, wata irin guguwa ce ta mamaye cikin maƙabartar mai tsanani duhu haɗi da ciyayi Suhaima ta ƙanƙame jikinta jin yadda ƙasa ke shiga hancinta da idanunta. Sake damƙar gashinta ta yi ta janyota ƙiii sai gasu a bakin wani ƙaton rami mai zufi, macizai ne a cikin ramin suna ɗaga baki kowanne yana neman abin da zai sara.
Kwalalo idanu Suhaima ta yi ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri karki sakani a cikin bala'in wannan, zan yi duk abin da kuke so ki taimaki rayuwata kinji."
Ta ƙarashe maganar hankalinta a matuƙar tashe ganin masifar da take tunkaro ta; Tashi sama yarinyar ta yi tamkar tsuntsuwa ta tsaya a samar ramin ta na kallon Suhaima da jikinta yake rawa ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi saboda firgici ta tashin hankalin da take ciki. Dariya ta yi cikin hargowa ta soma magana.
"Karki sake haɗani da Allah ki cuceni, ina so na yi ramuwar gaiya dan ba zan taɓa yafe abin da kuka yi wa rayuwata ba Suhaima. Idan kuma ki na so na rabu da ke to sai kin sadaukar mini da wani abu wanda kika fi so fiye da komai a rayuwar duniya, idan kuma ba za ki iya ba to zan ɗaura daga inda na tsaya sai kin zaɓi mutuwa fiye da rayuwarki. Ni sunana Janu idan na sake ji kin kirani da wannan sunan sai na yanke miki harshe."
Ta ƙarashe maganar ta na dawowa gaf da Suhaima; shuru Suhaima ta yi ta na tunanin wannan sunan da yarinyar ta ambata ta ce sunanta kenan, sosai ta lula duniyar tunani ta na son sanin inda ta san mai sunan amma ta kasa tuno komai..


"Shin za ki yi sadaukarwar ne ko yaya? "Ta kuma faɗa ta na ɗaga Suhaima sama ta kawo ta samar ramin, kwalalo idanu ta yi ganin wata ƙatuwar macijiya na ƙoƙarin kawo mata hari, baki na rawa ta ce. "Zan yi Janu ko mai kake so na sadaukar miki zan miki matsawar za ki rabu da rayuwata. Amma nima ina da tambaya idan kin bani dama, sannan ki taimaka ki mayar dani ƙasa amma ba cikin maƙabarta ba waje sai mu yi maganar."
Ta faɗa ta na fatan kar taƙi amincewa; Wani irin gurnani Janu ta yi sai ga fuskarta ta juyo ta bayanta ai kuwa Suhaima ta runtse idanu tare da rufe bakinta dan kar ta yi abin da zai sa ta fusata ta afka ta cikin wannan ramin.
Dariya ta kuma yi ta daɓi kan Suhaima, kanta ne ya shiga juya mata jin zafin ya kawo wa ƙwaƙwalwarta ziyara ta ɗaure ba ta ce uffan ba .
A dajin da ta fara ganin kanta ta gansu sun dawo cikinsa, shuru ta yi ta na sauraron Janu ta ji me take so, hannu Janu ta daga sama sai ga wani haske ya bayyana a gaban Suhaima.. Cikin tsoro ta kalli hasken kamar jira ake ta kalla sai ga wasu mace da namiji sun bayyana fuskokinsu na ɗauke da damuwa, idanunsu na zubar da hawaye hannayensu sarƙe da na juna suka ƙurawa Suhaima idanu.
Zunbur Suhaima ta miƙe tsaye ta na nuna su da hannu ta soma ƙoƙarin yi musu magana amma hakan ya cittura sai bakinta da take buɗewa ta na nuna su da hannu, durƙushewa ta yi ta fashe da kuka marar sauti dan muryarta ta kasa fitowa; Janu kuwa na gefe ta na dariyar ƙeta tare da ƙara matso mata da wannan mutanen su kuma suna zubar da hawaye a tare suka ce.
"Shin kin tuna mu ne."


Da sauri Suhaima ta ɗago kai bakinta na rawa ta yi ƙoƙarin yin magana amma sautin muryar yaƙi fitowa, ganin hakan yasa Janu ta kuma fashewa da dariya dajin na amsa kowar muryarta, su kuma sun ƙura mata idanu suna jiran ta basu amsa amma shuru. Janu ta dubesu ta ce.
"Wannan ta na ƙarƙashin ikona ne ba za ta taɓa iya muku magana ba sai na ba ta izinin yin hakan, na kira ku ne don ku sheda sadaukarwar da za ta yi ta fanshi rayuwarta, idan maye ya manta mai ɗa ba za ta taɓa mantawa ba ina fatan kun gane ko?"
Ta ƙarashe maganar ta na kuma yin wata dariya ta ɗago Suhaima kamar wata jaririya sai kawai ta yi sama da ita ta sako ta ƙasa tim! Da sauri suka kalli Janu matar ta ce.
"Kar mu yi haka dake Janu ki faɗi sharaɗin ki."
Ta ƙarashe maganar ta na haɗe rai ganin yadda Janu ke yi ko a jikinta .


Ita kuwa Suhaima ta na yashe a ƙasa sai numfashi take saukewa, a galabaice ta ce. "Ki faɗi me kike so na miki."
Ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya Janu ta yi ta ce. "Ina so ki sadaukar mini da jinin iyayenki da na 'yan'uwanki, idan ki ka yi haka zan rabu da ke na yi sabgar gabana."
Kwalalo idanu waje Suhaima ta yi jin wannan ƙatoton tashin hankali da Janu ke son sakata ciki, to idan ta sadaukar da jinin Abba da Umma da Na'im da Suhaila ita meye amfanin zaman ta a duniya? Shin me na aikata a gareki Janu da kike bibiyar rayuwata har kike neman rabani da ahalina gabaɗaya?
Ta faɗa a cikin zuciyarta ba ta san maganar ta fito fili ba sai da ta tsinkawo muryar Janu cikin fushi na cewa.
"A MAƘABARTA NE lamarin ya fara, ke kika taɓo abin dan haka ke za ki rufe shi in ba haka ba masifa da bala'i sun yi ta bibiyar rayuwarki kenan. Ina ba ki lokaci ne shi ya sa ma ban kasheki ba kamar yadda na kashe wannan mugun Uncle ɗin naki, amma dai ki ci gaba da yi mini gardama ke ba fille kai ba ma zan miki farke ki zan yi na feɗe neman jikinki na gasa na cinye na shanye jinin. Ba ki san wace ce Janu ba zan nuna miki asalin kalata."
Ta ƙarashe maganar ta na miƙa hannunta sai ga takobi fara sol mai baki biyu ta bayyana a hannunta, cikin zafin nawa irin nasu na aljannu ta kai wa Suhaima suka a ciki, wani mahaukacin ihu Suhaima ta kurma wanda har sai da su Umma suka fito a guje suna banka ƙofar ɗakinta jin ihun da ta yi..


A matuƙar firgice take kallon jikinta ta na laluma cikinta, kalle-kalle ta soma nan idanunta ya kai kan su Umma dake tsaye sun zuba mata idanu.
"Wai yarinyar nan anya kuwa ciwon hauka bai kama ki ba?"
Umma ta faɗa ranta a matuƙar ɓace ta na kallonta; Zufa ta jiƙa inda take zaune ta miƙe a hankali ta sauko daga kan gadon ta iso garesu, da kallon tsoro take binsu ta soma magana.
"Umma ba dai abin da ya sameku ko? Anty Suhaila ta na lafiya kuwa? Abba wai me yake son faruwa dani ne? Kullum fa sai na ganta ta yi ta kaini Maƙabarta ta na firgitani yau kuma ta ce wai A MAƘABARTA NE lamarin ya fara ni na buɗe dan haka ni zan rufe da kaina. Abba Shin wai me ya faru A MAƘABARTAR da kullum nake ganin kaina a ciki? Ku bani amsa don Allah me kuke ɓoye mini wanda na kasa sani? A kan idona fa aka fille wa Uncle kai kuma ina tashi ya rasu, yau kuma ni aka soka da wuƙa Abba yanzu kenan mutuwa zan yi?"
Ta faɗa ta na ƙarawa kukanta sauti, sannan ta ci gaba da cewa.
"Don Allah ku fitar dani daga cikin duhu A MAƘABARTA NE wani al'amari ya faru wanda ku kun sani amma ni ban san komai ba, gashi ana ta firgitani shin me ya faru A MAƘABARTAR Abba? "Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka tare da riƙe ƙafar Umma ta kuma faɗin.
"Umma ke ki faɗa mini me kuka sani game da mafarkina A MAƘABARTA da nake yi? Ku faɗa mini kar Janu ta kashe ku."
Ta faɗa cikin ƙaraji;
Abba ya kamo hannunta fuskarsa ɗauke da tashin hankali har jikinsa ya ɗauki rawa ya soma magana a firgice.


"Suhaima..










_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/1 22:03] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_
















Daga Alƙalamin


Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_






SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO(Malam)*






0️⃣4️⃣




"Suhaima babu abin da ya faru A MAƘABARTA kawai dai mugayen mafarkan da kike ne kike gani kamar da gaske A MAƘABARTA NE wani abu ya faru; ki kwantar da hankalinki zan samu Liman na masa bayanin irin mafarkan da kike sai a taimaka miki da addu'a. Kar naji kin faɗi maganar nan a wani guri, saboda za a miki kallon mahaukaciya sabon kamu."
Ya ƙarasa maganar yana addu'ar kar ta kuma jefo masa tambayar da bashi sa amsar ta; ita kuwa Suhaima ƙurawa Abba idanu ta yi ta na son gaskata maganarsa amma sam zuciyarta taƙi yarda da maganar ta Abba, dawo da kallonta ta yi kan Umma sai kawai ta miƙe tsaye ta goge hawayen dake zarya kan kuncinta cikin raunatacciyar murya ta soma yi wa Umma magana.
"Umma idan na gano wani abu wanda bai mini ba to tabbas zan bar gidan nan na shiga duniya."
Ta faɗa kai tsaye ta na hura hanci;
Kwalalo idanu Umma da Abba suka yi cike da mamakin kalamanta, dukkansu nanata kalmar shiga duniya suke kamar ɗalibin da aka daurawa sabuwa aya yana bitar ta. Komawa ta yi bakin gado ta zauna ta haɗa kai da guiwa ta dinga rera kuka mai tsuma zuciya, ita kan taga ta kanta ba dama ta kwanta sai ta haɗu da wannan muguwar aljanar wai ita Janu kamar wani danƙo, waye zai faɗa mata gaskiyar da aka ɓoye mata? Shin mene ne ya faru A MAƘABARTA da har ake ƙoƙarin ɗaukar rayuwarta?
Ajiyar zuciya ta sauke tare da tsagaita kukan nata, cike da mamaki take kallon su Umma dan ita a tunaninta tun tuni sun bar mata ɗakin sai ta gani suna nan sun yi jugum-jugum suna kallon ta, kanta ta kuma mayarwa ta ci gaba da kuka yadda zuciyarta ke ba ta shawara ta aiwatar da abin da take so, amma wani sashe na zuciyarta na gargaɗar ta sai ta kuma ƙarawa kukanta sauti ta yi baya ta zube a kan gadon..
Zuwa yanzu ta ji ba ta jin tsoro dayawa ba kamar da ba, sai da ta gaji da kukan dan kanta ta bari Umma ta iso gareta ta zauna tare da ɗago da ita suka yi facing ɗin juna.
"Suhaima ki daina saka wa kanki damuwa game da mafarkin da kike, kin san dai mafarki ba gaskiya ba ne duk ƙarya ce ko?, Sheɗanu ne ke son rikita miki lissafi ki dawo haiyacinki."
Tsayar da kuka ta yi ta ce.
"Umma tabbas akwai abin da kuka ɓoye mini, kuma da mafarkin da nake ƙarya ne to da zai kasance ba kullum zan ke yi ba, amma ko gyangyaɗi na yi sai na ganta ta na azabtar da ni ya zan yi Umma?"
Ta faɗa hawaye na zirya kan kuncinta zarr³; Shuru Umma ta yi dan ta rasa ma da wata kalma za ta yi amfani dan ta gusar da tunanin mafarkin nata, zuwa can ta ruƙo duka hannayenta cikin kulawa tare da tausayin ganin halin da take ciki ta fara magana.
"Ƴata ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same ki sai alkhairi."
Ba dan Suhaima ta yarda da maganar Umman nata ba ta gyaɗa mata kai tare da goge hawayen da ke kan kuncinta wanda har sun gaji da zirya , a sanyaye ta ce. "To Umma."
Murmushin yaƙe Umma ta sakar mata, ita kanta lamarin ya tsaya mata a rai, tsoro da tashin hankali sun mamaye zuciyarta har sai da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads