Showing 9001 words to 12000 words out of 38049 words
Chapter 4 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
an sa mata ruwa ɗaya an sa mata jini, fuskarta ta yi wani irin haske ta koɗe kamar ta kwashi watanni ta na cutar; bakinta ya bushe ƙayau kamar ta kwana ba ta sha ruwa ba.. Zama suka yi suka sa ta a gaba suna kallon ta cikin tausaya wa halin da take ciki.
Washegari wuraren ƙarfe goma na safe aka basu sallama, zuwa lokacin Suhaima taji sauƙi sosai sai dai rashin ƙwarin jiki haka suka dawo gida.
Suhaila ta haɗa mata ruwan wanka ta dawo ta taimaka mata ta shiga sannan ita ta dawo; shuru ta yi ta na tunanin jariran nan so take ta sake ganinsu su faɗa mata abin da zai fitar da ita daga wannan masifar da take ciki. Lumshe idanu ta yi kamannin yaran na mata zigo a idanun zuciya, ganin dai zaman ba zai fishe ta ba ta daure ta watsa ruwan ta ɗauro alwala ta fito.
A zaune ta samu Suhaila ta miƙa mata hijabi ta amsa ta na binta da kallo.
"Ya dai malama ko kin ga na canja ne kike mini kallon ƙurulla?" Murmishi Suhaima ta yi ta juya ta tayar da sallar da ake binta daga ta jiya har ta yau duk sai da ta rama sannan ta zauna; shayi mai kauri ta miƙa mata, ba muso ta amsa ta soma sha. Bayan ta shanye ta miƙe a hankali ta isa bakin gadon ta zauna ta kalli Suhaila ta na ƙaƙalo murmushin yaƙe ta ce.
"Anty Suhaila wai tun yaushe kike tare damu?"
Harara ta aika mata sai kuma ta mayar mata da murmishin ta ce.
"Ai tun jiya nake nan ke kina bacci shi ya sa ba ki san lokacin da na zo ba; yanzu ya jikin naki? Don Allah Suhaima ki daina saka damuwa a ranki kin ji kar ki ja wa kanki ciwo kuma, waye ya firgita ki wai jiyar?"
Kukan da take ƙoƙarin danne wa ne ya fito ta faɗa jikin Suhaila ta fashe da kuka wi-wi tamkar ana yankan naman jikinta; jikin Suhaila ya yi sanyi sosai ganin yadda Ƙanwar tata ke kuka bil'haƙƙi. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta ɗago da ita ta ce.
"Ƙanwata ki faɗa mini me ke damunki? Ko Abba ne ya takura a kan maganar fito da miji?"
Girgiza kai ta yi ta tsayar da kukan da take ta ce.
"Anty ya zan yi da rayuwata ne? Da na kwanta bacci ita nake gani ta na son kasheni."
Waro idanu Suhaila ta yi cike da al'ajabi ta ce.
"Wace ce ke son kasheki?"
"Ni ma ban san ta ba, haka kawai nake ganinta a mafarki na faɗa wa su Abba amma sun ce mafarki ba gaskiya ba ne, Anty ki taimakeni Wallahi tsoron ta nake ji."
Ta ƙarashe maganar ta na sakin wani sabon kukan ta shiga ba ta labarin aljana Janu da take gani a mafarkin ta, amma ba ta faɗa mata jariran nan ba.. Ajiyar zuciya Suhaila ta sauke ta ce. "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah da kin samu sauƙi zan ɗauke ki mu tafi Kaduna akwai wani babban Malamin addini zan kaiki wajansa mu gani ko zai gano abin da yake haɗa ki da ita wannan aljanar, yanzu kwanta ki huta Umma ta ce gobe Inna Laure za ta zo gurin sadakar uku na Uncle. Wai ashe basu ji mutuwar ba sai yau kin ji irin ɗibar albarkar da ta yi wa Abba kamar za ta fito daga waya ta dake shi, Inna Laure ba dai masifa ba Allah ya kawo ta."
Wani sanyi Suhaimata ji ya ratsa ta ko ba komai ƴar'uwarta ta fuskanci damuwarta, bugo da ƙari kuma ga Inna Laure za ta zo wadda ko kallon banza ba ta so a yiwa Suhaima lelenta take kamar Auta..
"Allah sarki Innata Allah ya kawo mini ita lafiya har na ƙagara ma na ji muryarta. " Dariya Suhaila ta yi ta ce.
"To ai shi kenan bari na ba ki guri ki huta nima baccin nake ji sai an jima." Jinjina mata kai ta yi ita kuma ta fita daga ɗakin ta rufo mata ƙofa...
Gyara kwanciyarta ta yi so take ta yi bacci ko ta haɗu da yaran su ci gaba da mata bayani, amma kuma wani ɓangaren na zuciyarta tsoro ya cika shi ba ta son ta sake ganin Janu. Ajiyar zuciya ta sauke ta rufe jikinta da bargo ta dinga karanta Ayatul kursuyu ta na addu'ar ko bacci ya shure ta kar ta haɗu da Janu da duniyar mafarkinta...
Zaune suke a tsakiyar ƙungurmin daji ita da wani tsoho da mata da mijin nan an ɗaure su da sarka; Janu ce ta bayyana a gabansu cikin mummunar suffa hannayenta riƙe da dalleliyar takofi mai kaifi da tsini sai walkiya take.. Idanu waje Suhaima ke kallon Janu ganin ta nufo gareta, wata irin dariya ta yi mai haɗe da kuka ta tashi sama ta tsaye a kan mata da mijin nan ta ce.
"Kina tunanin za ki iya kuɓuta daga tarkona ne? Kin yi kuskure da kike son sanin wani abu da ya shafeni, ke ɗin mallakina ce an mallaka mini ke tun ma kafin ki san ke wace ce. Zan maimaita abin da na yi shekarun baya idan har ba ki bani jininki na sha ba ko kuma ki bani na wasu ki ceci kanki."
Ƙirjin Suhaima ya shiga bugawa ta juyo da nufin da yi wa tsohon nan magana sai ta ga babu kowa daga ita sai Janu a tsakiyar dajin, jefen Janu ta juyo baki na rawa ta ce.
"Janu to ni taya aka yi na zama mallakinki. Sannan waye ya mallaka miki kaina da kike son kaini lahira?"
Wata gigitacciyar tsawa ta daka mata ta dawo gabanta ta ce.
"Ba zan faɗa miki ba indai har ba ki sani ba, to ki zauna a haka kasheki dai sai na yi na shanye jinin jikinki yanzu a nan ba'a ko'ina ba."
Takobin ta sa ta yanki hannun Suhaima sai ga jini yana ta zuba, ƙara Suhaima ta ƙwalla jin wata irin azaba ta karaɗe mata jiki, kafin ta motsa ta ga jinin jikinta na ƙara kwarara.
Ita kuwa Janu hannunta mai kama da na biri ta miƙa ta ba tarar jinin ta na shanye wa, ganin zubar jinin ya ragu ta kuma ɗaga takobin ta yanki ciyar Suhaima.
"Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Ta faɗa cikin tsananin azaba, ita kuma Aljana Janu ta dinga lashe jinin dake zuba ta na yin wata mahaukaciyar dariya.
Tashi ta yi ta soka takofin a ƙasa sai gasu a cikin maƙabarta, ta miƙa hannunta gefe sai ga sabon ginan ƙabari ya bayyana ta kwashe da dariya ta ce.
"Yau zan cika burina a kanki Suhaima, yanzu zan ci gaba da shan jinin ki idan na shanye tass sai na faɗeki ta cinye naman jikinki, idan na gama kuma na binne kasusuwanki a cikin ƙabarin nan."
Ta na gama faɗin haka ta kuma nufo Suhaima da numfashinta ya kai wa da komo wa, takobin ta ɗaga za ta soka mata sai ga haske ya bayyana ya musu tsakani..
A fusace Janu ta dubi hasken ta kai masa sara ya kauce sai ya bayyana a suffar mutane, namiji ne dogo sosai ya lulluɓe ko'ina na jikinsa idanunsa kawai ake iya hango wa; Suhaima ta ɗago ta na kallon yadda suke fafatawa tsakanin shi da Aljana Janu, matso wa ya yi kafin Janu ta ankara ya shuri Suhaima suka ɓace.. A ɓakin ƙofar gidansu ya sauke ta ya juyo ya hura mata iska, ji ta yi jikinta baya ciwon komai ya juya zai wuce ta ce.
"Bawan Allah!"
Juyo wa ya yi bai yarda sun haɗa idanu da ita ba kuma bai masa ba ya dai tsaya.
"Kai wane ne? Sannan ya sunanka don Allah? Ina so na ga fuskarka."
Kyakyawan hannunsa ya kai kan fuskarsa ya soma ƙoƙarin yaye lulluɓin da ya yi....
Allahu Akbar! Allahu Akbar!
Sautin muryar Ladanin Masallacin Unguwarsu ne ya farkar da ita daga baccin da take; hawaye sharr suka zubo mata a fili ta furta.
"Me ya sa ban ga fuskarka ba? Kai ɗin kuma waye?"
Rai ba daɗi ta miƙe ta yo alwala ta tayar da iƙama.
Wunin ranar haka Suhaima ta wuni ta na tunanin wannan wanda ya ceci rayuwarta, haka dai ta kwanta har dare ta na fatan in ta yi bacci ta gansa ya buɗe masa fuskarsa ta gani....
Washegari Inna Laure ta iso Kano, ta na dira daga mota ta dinga sababi tun daga harabar gidan har ta shiga cikin palon; bakinta har kunfa yake saboda masifa ta tsaya a tsaye.. Da gudu Suhaima ta fito suka rungumi juna cikin nuna farincikin ganin juna. Da ƙyar aka shayo kan Inna Laure ta daina faɗa sai dai ta ce baza ta ci abincin gidan ba Suhaima ta je ta sayo mata masa da miya a nan bayan layinsu, hijabi ta sa ta fita cikin sauri...
Tafiya take ta na sauri, ta iso jikin wata bishiya dake bakin hanya tsaya ta na gyara hijabint.
"Yarinya!"
Da sauri ta ɗago kai; idanu ta zaro baki na rawa ta ce.
*To fa masu karatu ga dai Suhaima a inuwar bishiya ko mai zai faru?*
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce )*_
[3/5 16:23] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣6️⃣
Baki na rawa ta ce.
"Baba." Kallon ta tsohon ya yi fuskarsa na dauke da damuwa bai ce da ita komai ba; ganin haka yasa Suhaima ƙaraso wa inda yake zaune ta durƙusa cikin tashin hankali ta ce. "Baba ka yi magana mana. Ba kai ba ne na gani jiya cikin mafarkina? Ko kaima so take ta kashe ka kamar yadda take son ta kasheni ban mata komai ba? Baba shin ka na da alaƙa da ita ne? Ko turo ka ta yi ka kai mata ni?"
Ta jero masa tambayoyi a jere kamar wata ƴar jarida tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta.
Shi kuwa tsoho ya yi shuru sai ma soke sandarsa ya yi ya riƙe ta yana daga zaune ya sunkuyar da kai har ta gama maganar bai ɗago ba, Suhaima ta kuma faɗin.
"Baba ba ka ce komai ba."
Ta yi maganar a sanyaye zuciyarta na ce mata ta gudu shi ma cutar da ita zai yi, wani ɓangaren na zuciyarta na hana ta guduwar.. Ɗago kai ya yi ya dube ta kamar ba zai ce komai ba zuwa lokacin jikin Suhaima rawa yake ganin yadda idanunsa suke wani irin haske, har ta yanke shawarar tafiya ta tsinkayo muryarsa kamar daga sama yana magana..
"Ni ba cutar da ke zan yi ba, halisa ma na zo ne na ba ki haƙuri a kan abin da na aika miki tun kafin ki zo duniya."
Baki sake Suhaima ke kallon tsohon to dama ya san ni wace ce kenan? To in ko haka ne bari na masa tambaya ko zan samu mafita daga wajansa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama shawara da zuciyarta ta ce.
"Baba to ni kuwa mai ka aikata a gareni da har kake neman yafiya ta? Da alama dai ka san wannan muguwar ko?"
"Kwarai kuwa na san ta sosai ma, mun yi zamani da ita lokaci mai tsayi da ya shuɗe. Da ban yi mu'amala da ita ba yanzu da ki na cikin kwanciyar hankali, amma sai dai na kasa wannan tunanin gashi yanzu ke da kika rage ta na son ɗauke ki ta sha jininki..
Baki Suhaima ta bude ta na jin wani hargitsatsen labari mai cike da ɗaure kai da rashin sanin bakin zaren; jin ta ƙage da durƙushen ta gyara ta zauna ta ce.
"To in kuwa haka ne Baba bani labari ka na da wata alaƙa da ni ne?"
Murmushi tsoho ya yi ya ce.
"Kwarai kuwa yarinya ni kuwa nake da alaƙa da ke, ki bari ba yanzu ba zan ba ki labarin rayuwarki. Zan warware miki zare da abawa idan na sake dawowa, idan kuma ban dawo ba zan turo wani a madadina."
Yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye da ƙyar, su Suhaima har da miƙe wa ta riƙe masa sandar ya tsaya da kyau sannan ta ce.
"Baba to amma me ya sa ba za ka faɗa mini yanzu ba? Wallahi ina cikin damuwa da tashin hankali, Abba da Umma sun ƙi faɗa mini abin da suke ɓoye wa."
"Za mu yi magana wani lokacin.
Kafin ta ɗago ta ga ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa a wajan ba; rushewa ta yi da kuka ta sunkuya ta ɗauki zoben da ya yada ta na kallo, zoben fara ce sol sai sheki take.. Kamar wadda ake yi wa magana a kunne ta yi shuru, zuwa can kuma ta yi saurin saka zoben a yatsarta ta hagu sannan ta miki jiki ba ƙwari; goge hawaye ta yi ta juya ta fice zuwa inda take son zuwa...
Ta na isa wajan mai masar ta miƙa dubu ɗaya ta ce.
"Maman Yusuf ki bani Masa ta ɗari uku, ko kuwa ma bani ta dubun kawai." .
Baki a washe Maman Yusuf ta amsa ta zuba mata a cikin leda, sai da ta miƙa mata suka haɗa idanu Maman Yusuf ta waro idanu cikin zallar mamaki ta ce.
"Suhaima kece kuwa? Me ya faru dake haka na ga kin rame sosai?"
Murmushin yaƙe ta yi ta ce.
"Bani da lafiya ne shi ya sa."
Fatan samun lafiya ta mata ita kuma ta wuce gida.
Koda ta iso bakin get ɗin gidansu tsayawa ta yi ta saisaita nutsuwarta sannan ta buɗe ta shiga; Inna Laure na zaune ta kafe ɗaurin ɗan kwali a gaban goshi ta na kaɗa kai sai ga Suhaima ta
Shigo.
"Yawwa ƴar albarka ɗiyar Innarta maza kawo mini masar nan rabona da abinci tun jiya, kwana na yi ina kukan takaicin rashin faɗa mini mutuwar Abdallah. Yanzu in ban da rashin mutumci irin ubanku taya za ayi mutuwa amma sam ya kasa sanar dani, wannan ai rashin sanin darajar 'yan'uwantaka ne."
Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka har da sauke ɗankwalin daga kanta ta rufe fuska da shi; Shuru duk suka yi Suhaima ta iso gabanta a sanyaye ta ce.
"Innata ki yi haƙuri Abba ya kira wayarki ba ta shiga ƙarshe ma a kashe ake ce masa, shi ya sa ba kiji a kan lokaci."
"Allah sarki Audu kwanaki ya kirani ashe hirar ƙarshe ce muka yi da shi, ba komai Suhaima na yafe wa Mukhtar ba dan halinsa ba. Yanzu bari na tafi gidan na marigayi akwai masu zuwa gaisuwa za su zo daga garinmu..
Murmushin yaƙe ta yi ta shiga kitchen ta ɗauko mata kwano ta zuba mata; sauko wa ta yi daga kan kujera ta zauna ta yi bismillah ta soma cin abincin, ganin Suhaima ta yi tagumi yasa ta yatsar da cin abincin ta zuba mata idanu ta ce.
"Ƴata lafiyarki kuwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Innata da sauƙi dai zazzaɓi na yi na kwana ɗaya shi ya sa."
"Subhanallah! Bari muje mu dawo mu zauna za mu yi magana Allah ya ba ki lafiya.. Amin ta ce ta koma kan kujera ta kwanta tare da lumshe idanu; tunanin mafita ta shiga yi amma sam ta kasa gano inda lamarin nan zai tsaya mata cikin daɗin rai, jariran nan suka faɗo mata a rai ta buɗe idanunta ta sauke su a kan Inna Laure dake cin wainar ta na goge hawaye. Dariya abin yaso ya ba ta ganin ta na cin abinci ta na kuka, sake rufe ido ta yi ta na jiran Innar tata ta gama su tafi dama su kaɗai suka rage su Suhaila sun wuce tun ɗazu...
Bayan Inna Laure ta gama suka wuce zuwa gidan Abdallah, koda suka shiga Inna Laure guri ta samu ta zauna ta na goge hawaye mutanen da suka santa suna mata gaisuwa ta na amsa musu tare da musu godiya....
Yau aka yi sadakar bakwai, kuma har yau Inna Laure ba ta samu sun zauna da Suhaima ta faɗa mata damuwarta ba.
Misalin ƙarfe goma da dare, zaune take ta rafka tagumi kwanciya take son yi amma tsoro da fargaba sun hana ta kwanciya. Wutar dakin ce ta ɗauke, shuru ta yi ta ƙasa motsawa daga kan gadon sai ji ta yi an tsikara mata wani abu kamar allura a gefen cikinta; da sauri ta dafe gurin ta juyo, babu abin da ta gani ta shafa wajan ta jan bargo ta rufa jikinta na rawa.
Garam! Ta ji an banko ƙofar ɗakin da ƙarfi, kin buɗe ido ta yi sai ma ƙara ƙanƙame jikinta da ta yi; surutai ta dinga ji cikin kunnuwanta ba shiri ta miƙe zaune ta na zaro idanu.
"Mama! Mama!
Ta ji muryarsu ta kawo wa kunnenta ziyara; saurin juyo wa ta yi gefen da taji muryar tasu ai kuwa ta gansa a samar ɗakin suna mata murmushi, itama murmushin ta musu suka yo ƙasa-ƙasa zuwa kan gadon ta miƙa hannu ta taro su sai taji nauyi sosai. Waro idanu ta yi ganinsu a siffar yara 'yan shekara shida, kasa daure wa ta yi ta ce.
"Ya aka yi naga kun koma masu girma?"
Macen da take haƙarƙarinta ta ce.
"To ai mun girma ne, kuma za mu iya zuwa miki a duk yadda muke so mu zo; sai dai Baba ya ce muke zuwa a suffar mutane dan kar ki tsorata da yawa."
Jinjina kai ta yi ita dai mamakin yaran nan take da suke kiranta da Mama , ga shi har maganar Baba suke mata wanda ba ta san shi ko wani kala ba