Showing 18001 words to 21000 words out of 38049 words
Chapter 7 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
kar wanda ya ji."
Wani sanyi naji jin ta yarda da maganar na ce.
"Yawwa ķe ma ko kaɗan karki faɗa mata sannan zan miki albishir mai daɗi. "
Da sauri ta dubeni ta ce.
"Umma kamar wanne?"
"Zan sake haifo muku wani ɗan'uwan ko mace."
Da sauri ta rungume ni ta na dariya ta ce.
"Da gaske Umma za ki sake haihuwa." Jinjina mata kai na yi alamar tabbatar wa sai ta mike ta wuce ta na kiran Suhaima dan ta mata albishir zan musu sabon baby.. Abbanku ya ji daɗin wayon da na yi wa Suhaila duk da lokacin ta na shekara 12 ne ita kuma Suhaima shekara 8 ba ta cika ba ma...
Bayan wasu watanni na haifi baby boy, murna sosai muka yi sai ɗaukan sa Suhaila take in ta gaji ta miƙa wa Suhaima shi ; washegari sai ga Inna Laure ta iso..
Ranar suna yaro ya ci sunan Na'im naji daɗi dan ni na zaɓa da kaina aka sa masa sunan; haka aka yi suna aka watse ni kuma Abbanku ya ce ba inda zan je na yi zamana, ba dan na so ba na zauna..
Haka rayuwarmu ta ci gaba da tafiya har duk kuka girma Suhaila ta na gama JSS3 ɗan yayata wadda da mamanta da mamana uwa ɗaya uba ɗaya suke, ya ce shi fa son ta yake a musu aure sai ta ci gaba da karatu. Da farko Abbanku ya ce a'a dan lokacin shekaru ta 18 ne, amma su Baba suka ce ai ba komai a mata kawai. Ba'a wani daɗe ba aka musu aure ta cigaba da karatun ta a can Kaduna...
"Wannan shi ne asalin abin da ya faru; ko da kika fara mugayen mafarkai a tunaninmu ciwon ki ne zai dawo wanda tun kina ƙarama kika yi sa, to shi ne yasa hankalinmu ya tashi matuƙa dan kar a goma gidan jiya..."
Idanun Suhaima ya yi jajur saboda kukan da take, tashin hankalin da take ciki ya wuce gaban kwatance ta yi kalli Umma ta ce.
"Umma ko da ace iyayena suna raye ba zan taɓa son su ba kamar yadda nake son ku, kune komai nawa ban san kowa ba sai ku dan haka kune iyayena tun da ke kika shayar dani kika reneni , dan haka kece mahaifiyata Umma."
Ta faɗa ta na faɗawa jikin Umma; rungume ta Umma ta yi ta dinga bubbuga bayanta ta ce.
" Suhaima ke Ƴata ce ki daina kukan kin ji." Ta faɗa ta na shafa bayanta idanun ta suka kai kan zoben dake yatsar ta, da sauri ta ce.
"Wannan zoben fa?"
Ɗago wa ta yi ta ce.
"Wannan zoben wani tsoho ya bar ta nan dai ta faɗi yadda suka yi da tsohon, ta ƙara da cewa.
"Umma ina so ku kaini Ghana tabbas maganar Aryan haka take A MAƘABARTA NE lamarin ya fara. Dan haka ina so naje wannan maƙabartar dan na gano komai da ya shafi iyayena."
Inna Laure ta ɗaura hannu biyu a kai ta ce.
"Na shiga uku Suhaima su waye kuma Aryan?"
Kai tsaye ta ce mata.
"Inna 'ya'yana ne su, kuma zan so mu sake haɗu wa kafin ku kaini Ghana."
Kwalalo idanu waje suka yi Na'im ya ce.
" 'ya'yanki kuma to kamar ya ya?"
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/9 21:48] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣9️⃣
" 'Ya'yanki kuma to kamar ya ya? "Ya faɗa cike da al'ajabin Suhaima.
Ajiyar zuciya ta sauke ba ta kuma ce musu komai ba ta yi shuru kanta a ƙasa; wani irin zafi zuciyarta ke mata ga tunanuka barkatai, wanda suke neman tarwatsa mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta..
Inna Laure ta matso kusa da ita, ɗago da fuskarta ta yi cike da alhinin ganin ƴar tata a cikin wannan halin; a sanyaye ta ce.
" Ƴar Innarta!" Kuka ne ya ci ƙarfin ta sai ta faɗa jikin Inna Laure ta fashe da sabon kuka; jikinta ya ɗauki ɓari tamkar mazari, Inna Laure ta dinga bubbuga bayanta cikin son kwantar mata da hankali ta ce.
"Suhaima kada ki ce mini kukan rashi iyaye ne kike? Mu ne iyayenki har gaban abada ki daina kukan kin ji. Ko da a ce waɗanda suka haifeki sun fito ba za mu bari su raba mu da ke ba; ki yi haƙuri don Allah ki daina maganar zuwa Ghana nan hankalina tashi yake, tashi ki daina kukan kar ki sake tunanin komai tun da ki na da Allah ki na da mu. "Ta faɗa cike da damuwa; ita kanta hankalinta a mugun tashe yake ba ta taɓa tunanin Suhaima ba ɗiyar ƙanenta ba ce, ko da a mafarki ne ta ga haka ba za taɓa ba wa mafarkin muhimmanci ba, amma gashi dai yau sirrin ɓoye ya fito fili..
Tsagaita kukan ta yi ta soma magana cikin raunatacciyar murya.
"Innata ya zan yi? Yanzu su Umma ba su suka haifeni ba kenan? Su iyayen nawa a ina suke? Kuma me ya sa suka jefar dani a lokacin da na zo duniya? Me na musu Innata? Wallahi ko da na gansu ba zan taɓa yafe musu wulaƙanta ni da suka yi ba; indai da son ransu suka jefar dani to ba na son ganinsu ko a mafarkina su yi zaman su a inda suke, ni ma zan zauna da waɗanda suke so na da ƙauna ta..
Na tabbata wannan tsohon ya san inda iyayena suke; gashi kuma ban san ta ina za mu sake haɗu wa ba, Inna ina jin zuciyata na tafasa, ji nake kamar ana zuba mata zuwan zafi tafasashe."
Kuka sosai take ta na sunbatu Inna Laure na rarrashin ta; su Umma kuwa kasa magana suka yi kowa tausayin halin da take ciki yake yi, ganin sun kasa shayo kanta Na'im ya miƙe daga inda yake ya iso gaban Inna Laure cikin kwantar da murya ya soma mata magana.
"Anty Suhaima ki yi haƙuri mana; ko wani bawa fa da kalar tashi ƙaddarar ke taki a haka ta zo, ki gode wa Allah da ba a mugun hannu kika tashi ba; sannan ki ƙara gode wa Allah da ya sa kika faɗo a hannun musulmai ba kiristoci ba. Tashi kinji in sha Allah komai zai wuce. "Ya faɗa yana miƙa mata hannunsa."
Tsayar da kukan ta yi Inna Laure ta tashe ta daga jikinta; kallon Na'im ta yi ya mata alama da ta zo garishi, hannunta ta sa a cikin nashi ya kama ta ta tashi ya miƙar da ita. Su ko su Umma suna kallon su, da ƙyar ta tsaya a kan ƙafafuwanta jikinta na rawa, ganin haka yasa Na'im haɗa ta da jikinsa ta kwanta kanta a kafaɗarsa. Kasancewar ya fita jiki da tsayi sai ta koma kamar ita ce Ƙanwar shi ne yayan; ɗakinsa suka nufa su Inna Laure suka raka su da idanu har suka wuce....
Inna Laure ta jinjina kai cikin damuwa ta dubi Abba.
"Wallahi Mukhtar ba ka kyauta min ba, ai na ɗauka sirrinka sirrina ne amma sai ka ɓoye mini wannan."
Ƙara sunkuyar da kansa Abba ya yi ya ce.
"Yi haƙuri Yaya Laure Baba ya ce kar na sanar muku ke da Abdallah; shi ya sa ma ban sanar da ke komai ba game da Suhaima."
"Ba komai ya wuce ni yanzu Suhaima nake tausaya wa, yanzu hankalinta kacokan ya karkata zuwa ga asalin iyayenta, ba mu san taya aka jefar da ita ba, ko kuma sato ta aka yi Allah amsanin gaibu."
Ta ƙarashe maganar ta na sa haɓar zaninta ta goge hawaye; ta ci gaba da magana.
"Yanzu dai mu samu a hana ta zuwa Ghana nan, ba kowa ta sani ba kuma ƙila ma iyayen nata ba a nan suke ba; mu samu a shayo kanta a mantar da ita damuwar da take ciki ina son ta sosai yarinyar nan, akwai hankali ga nutsuwa."
Suhaila ta miƙe jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinta suka bita da kallo, tattauna wa suka yi sosai a kan lamarin sannan su Umma suka fita a dakin aka bar Inna Laure zaune ta rafka tagumi.
Ko da suka shiga ɗakin zuwa lokacin jikin Suhaima ya ɗauki zafi; a dame ya ja ta suka zauna a bakin gado ya ce.
"Anty Suhaima don Allah ki yi haƙuri komai zai wuce; bana son ganin ki cikin damuwa duk bana jin daɗi."
Ɗago wa ta yi ta dube shi hawaye na bin kuncinta ta ce.
"To Na'im me zan yi? Da ina tunanin mafarkan da nake ne damuwata; ashe ma ni tsintacciya ce iyayena suka jefar da ni, yanzu a ina zan gansu?"
Kuka take sosai har da shiɗe wa take, ganin haka ya gyara zama ya janyota ya shigar da ita jikinsa; da sauri ta maƙale shi ta ci gaba da kukan ta na sunbatu..
"Na'im rayuwata ba ta amfani in dai ni ba jinin gidan nan ba ce, wa ya sani iyayena ko a wata duniyar suke; ko ma na gansu na tsane su tsana mai tsanani tun da suma suka tsaneni sai n...
Ba ta ƙarasa ba ya yi saurin rufe mata baki da hannunsa jin ta na neman yin saɓo;
"Ki daina magana Anty kin ji jikinki har zazzaɓi ya rufe ki, kar ki kuma cewa kin tsani iyayenki ko ba ki son ganinsu; yanzu ba ki da tabbacin ta ya ya suka rabu da ke, dan haka karki yanke hukunci a kansu. "Ya faɗa yana ɗago da ita.."
Ba ta yarda sun haɗa idanu ba ta kuma koma wa ta kwanta; shi kuwa Na'im wani irin tausayin yayar tasa yake ji na ratsa masa ko'ina na jikinsa, shi kansa yana son sanin iyayenta da dalilin rabuwa da ita a lokacin da take buƙatar su..
Matsa wa ya yi kan gadon ganin ta na rawar sanyi ya lulluɓa mata bargo shi kuma ya jingina da jikin gadon; ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya yi amma sam taƙi yarda sai kawai ya haƙura ya zuba mata idanu cike da tausayin ta; addu'a ya dinga tofa mata a ta na lumshe idanunta, daga ƙarshe wani wahalallan bacci ya yi awon gaba da ita. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya lallaɓa ya raba ta da jikinsa ya maye mata gurbinsa da pilo, da sauri ta rungume pilon ya ƙara rufa mata bargon har kanta sannan ya fita a ɗakin...
Kafin Yamma ta yi tuni jikin Suhaima ya yi tsanani; ko idanunta ba ta iya buɗe wa lokaci ɗaya ƙafafuwanta suka lauye ta kasa tafiya da su. Hankalin su Umma ya tashi suka dinga yi mata addu'a ta na ƙyarma ta na fisge-fisge, zuwa can ta daina yi duk suka zuba mata idanu; wasa-wasa har bayan Isha'i Suhaima ba ta farka ba, Inna Laure ta ɗauko wani magani a cikin leda ta dubi Umma ta ce.
"Bintu kawo garwashi a mata turaren iska kar abin ya ƙara gaba."
Umma dai ba ta iya cewa komai ba ta je ta hura gawashi ya kunnu ta sako a kaskon turaren wuta ta kawo; amsa ta yi ta buɗe ledar ta dauko garin maganin ta afka a ciki...
Cikin minti ɗaya hayaƙin ya gauraye ɗakin ta kuma fito da 'ya'yan habbatussauda shi ma ta afka a kan garwashin ta na cewa.
"In sha Allah za ta samu sauƙi wannan 'ya'yan habbatussauda ɗin zai ba ta kariya in sha Allah."
Tari Suhaima ta dinga yi ta na juya kanta jikinta na rawa, a firgice ta tashi zaune idanunta a lumshe za ta sauko daga kan gadon; Na'im dake kusa da ita ya ruƙo ta da sauri ganin ta na ƙoƙarin kwace jikinta.
"Ku sakeni na tafi.
Suka tsinkayo muryar Suhaima; da sauri ya kuma matse ta ta na fisge wa ya shiga karanto mata Ayatul kursuyu a cikin kunne, hakan yasa ta dinga mimmiƙe wa ta na wani irin kururuwa.
Sai da ta yi lakwas sannan dukkansu suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ganin ta samu bacci; mayar da ita ya yi ya kwantar ya ƙara tofa mata addu'o'i sannan ya rufe mata jikinta.
Inna Laure ta zauna ta na ta na faɗin" Allah ya ba ki lafiya."
Sai wuraren ƙarfe 11: am na dare suka bar ɗakin aka bar ta tare da Inna Laure; shi kuma Na'im ya shiga ɗakinta ya kwanta a kan kujera.
Bacci take amma yatsina fuska take ta na juya kai; Inna Laure ta tsaya a kanta ta na mata addu'a har ta daina juye-juyen sannan ita ma ta kwanta a ƙasa...
"Mama! Mama!
Buɗe idanunta ta yi a hankali ta na kallon ɗakin; can ta hango su a ƙofar ɗaki suna kallon ta. Kamar an cire mata ƙaya haka ta ji ta miƙe ta isa bakin ƙofar ta tsaya ta na kallon su idanunta cike da hawaye ta ce.
"Ayan sun ce ba su ba ne asalin iyayena; ko kuna da masaniya a kan asalin iyayena?
"Ta faɗa ta na rufe bakinta da hannu gudun kar kukan ta ya tashi Inna Laure." Iman ta matso kusa da fuskarta ta kai hannu ta share mata hawayen ta ce.
"Mama ki daina kuka Baba ya ce yana sonki; yanzu mun zo mu tafi dake ne dan ki ga Baba, ya ce yana son yin magana dake."
Baki buɗe Suhaima ke kallon Iman za ta yi magana Ayan ya ce da ita.
"Mama ki zo mu tafi wajan Baba."
Murya ƙasa-ƙasa ta ce.
"To idan Inna ta tashi ba ta ganni ba damuwa za ta shiga; ba za mu daɗe ba ko?"
"Za mu daɗe Mama; wannan kuma ba matsala ba ne. "Ayan ya kuma faɗa tare da buɗa hannunsa wani haske ya fito ya nufi gadon; yana isa sai ga mace sak Suhaima kwance da irin kayan da yake jikinta...
Kwalalo idanu Suhaima ta yi tsananin al'ajabi yasa za ta kurma ihu Iman dake daf da fuskarta ta rufe mata baki; da kansu suka buɗe ƙofar ta yadda Inna Laure ba za taji ba suka yi wa Suhaima nuni da ta fita a ɗakin..
Kallon wadda aka aje a kan gado take a matsayin ita; ganin ta na ɓata musu lokaci suka ɗauke ta suka ɓace daga ɗakin...
A bakin ƙofar gida suka bayyana; waro idanu Suhaima ta yi ganin ta a waje ta ce.
"To ina za mu je wai?"
Ayan ne ya ba ta amsa
"Wajan Baba za mu je mana."
Ya faɗa kai tsaye yana yin gaba; kama hannunta Iman ta yi suka wuce.
Tafiya suka dinga yi har suka bar unguwar; ita dai da idanu take kallon ikon Allah amma ta kasa magana tamkar raƙumi da akala haka take bin su. Hannunta suka kama su duka suka ɓace; kawai ganinsu ta yi a cikin daji fili ne tantawarai bishiyoyi 'yan tsuraru ne, tsoro ya kama ta ta na ƙyarma ta ji sun zaunar da ita...
Ayan ne ya matso daf da ita ya soma magana.
"Mama kin san su waye ahalinki?"
Da sauri Suhaima ta girgiza kai cikin zaƙuwa da son sanin iyayenta; murmishi Ayan ya yi sannan ya soma magana.
"Mama ba kin taɓa haɗu wa da wani tsoho ba?"
Nan ma gyaɗa kai ta yi kamar wata ƙadangaruwa; shi kuma ya ci gaba da magana.
"To wannan shi ne Kakan ki; kin taɓa ganin wasu mata da miji?"
A tsorace ta ce. "E Ayan na gansu amma ƙila wannan muguwar ta kashe su."
Girgiza mata kai ya yi ya ce. "To ai dama sun da mutu tun da daɗe wa."
Zaro idanu ta yi ta na kallon Ayan baki na rawa ta ce. "Sun mutu fa ka ce? To amma me ya sa nake ganinsu?"
"Saboda su ɗin suna son ki ne; kuma Janu ce ta shanye jininsu ta kashe su su duka ukun "Iman ta faɗa ta na dafa kafaɗar Suhaima. Cikin rashin fahimta ta ce.
"To amma su me suka mata ta kashe su?"
"Sun sadaukar da rayuwarsu a kanki, sun fanshi ranki da tasu rayuwar. Wannan mata da mijin sune iyayenki na asali "Ayan ya faɗa yana riƙe hannayenta."
Miƙe wa ta yi a kiɗime suka mayar da ita ta zauna, cikin tashin hankali ta ce.
"Kenan su ne iyayena?"
"Kwarai kuwa su ne iyayenki, kuma ni na kashe su yau kema zan kashe ki tare da wannan hatsabiban yaran.
Muryar Aljana Janu ta ɗakin dodon kunnensu; a zabure Suhaima ta kalli su Iman da suka miƙe tsaye suna fuskantar Aljana Janu.
Wata mahaukaciyar dariya Janu ta yi hannunta riƙe da sarƙa, wurga wa Suhaima ta yi Ayan ya tare sarƙar ta sauka a kansa; wani irin ƙara Ayan ya yi Iman ta kurma ihu mai tada hankali wanda dajin gabaɗaya ya amsa.
"A a Ayan!"
Ta faɗa da ƙarfi hakan yasa hankalin Suhaima mugun tashi ganin Ayan ya koma haske kala biyu; Gefe ɗaya fari ɗaya baƙi, ita kam Aljana Janu dariya ta dinga yi ta miƙa dogon hannunta ta ɗamko Iman. Wani irin zafi ya ziyarci ta ba shiri ta sake ta ta faɗo kan Ayan; hankalin Iman a mugun tashe ta murza zoben hannun ta hasken na isa kan Ayan ganin bakin hasken na ƙoƙarin mamaye farin hasken.
"Dama ai na faɗa muku karo da Janu ba abu ba ne mai sauƙi; ku har kun isa ku ja da sarauniya wadda ta kashe aljanu bila adadin ballantana wannan ƴar'adam ɗin? To kun shiga komar Janu ni bana jin tausayin kowa ba ni da imani, duk wanda ya karya mini alƙawari to gabaɗaya sai na ga bayansa daga shi har ahalinsa. Matsa ki bani guri na ɗauki mallakina."
Ta ƙarashe maganar ta na zaro idanunta marassa ƙyan gani.. Kuka Suhaima take ganin bala'i ido da ido a gabanta; yau ga ta a tsakiyar aljannu ana artabo a tsakaninsu, Iman kuwa tuni ta fusata ta taƙarkare ta kurma ihu idanunta suka koma yellow ta dubi Aljana Janu ta ce.
"Kin yi ƙarya ki ce za ki taɓa mana mahaifiyarmu ki kwana lafiya; ke kin sani mu ba kanwar lasa ba ne tun da kin kara damu a kan Mama kin kasa cin galaba, shi ne