Showing 24001 words to 27000 words out of 38049 words
Chapter 9 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
ta ce.
"Ni kuma? E to tun da naka ne ai ni ma sun zama nawa?"
"Ba irin haka nake nufi ba Ummu; ina nufin ke matata ce. "Ya faɗa cike da tabbatar mata maganar tasa.
Tamkar wata zautacciya haka take kallon Sayyid; murmishi ta yi ta ce.
"Sayyid yaushe kuma muka fara wasa da kai? Ni fa rabona da na ganka an fi shekara goma lokacin fa tun muna yara ni da kai, amma sai ka ce wai ni matarka ce a wa ya ɗaura mana auren ne?"
Jinjina kai ya yi yasan dama za a rina; kamu hannayenta ya yi cikin nuna so da ƙaunar da yake mata ya ce.
"Kwarai kuwa ni mijinki ne Kakan ki ya bani ke tun ranar da kika zo duniya." Wani irin sarawa kan ta ya yi ta yi saurin runtse ido; wannan wacce irin kalma ce haka? Ita ɗin ce aka aurar tun tana jaririya anya ma da gaske Sayyid ɗinta yake? To in ko haka ne kenan yasan inda za ta ga ahalinta. Saurin buɗe ido ta yi ta ce.
"To ka sanar dani a ina ahalin iyayena suke? Sannan taya ka aureni ban sani ba ina buƙatar jin haka Sayyid ka daure ka fitar dani daga cikin duhun da nake ciki."
Sai da ya kamo hannunta ya murza a hankali sannan ya ce da ita.
"Ni ba bil'adama bane kamar ke."
Ƙuuuuu! Cikin Suhaima ya bada ta zaro idanu bakinta na rawa ta ce.
"B..Ban gane ba? Kai ɗin ne ba mutum ba?"
"Sosai ma ni ba bil'adama ba ne; kuma nasan kin san yaran nan suma ba bil'adama ba ne kamar ke, dukkanmu aljanu ne ba mutane ba kuma nine mijinki uban 'ya'yanki gasu nan Iman da Ayan." Luuu! Ta yi baya za ta faɗi ya taro ta ta dawo ta zauna; a ruɗe take kallon su nan da nan ta tuna su Umma, yanzu shi kenan dama dan su kawo ta yankin aljanu ne suka ɗauke ta? Shi kenan ba za ta sake ganin su Umma ba?
Saurin dafe kai ta yi ta ce.
"To amma taya ka zauna da kakana har ya ɗaura ma aure dani?"
Gyara zama ya yi ya ce. "Kada ki tsorata dani Ummu; ki kwantar da hankalinki ba wanda zai sake cutar min da ke. Zan mayar dake gida bayan na ba ki labarin rayuwarki da kuma yadda aka yi aka mallaka wa Janu ke, ina so ki nutsu da kyau kiji wannan labarin."
Cikin zaƙuwa ta ce. "To."
"A can baya wasu shekaru da suka shuɗe; akwai wani gagarumin Boka mai suna Kata wanda yake a ƙasar Ghana a yankin Yamma. Boka Kata ya kasance yana aiki kamar yankan wuƙa, hakan yasa mutane bila'adadin suke ziyartar shi a kodayaushe, yana da alaƙa da aljannu kala-kala akwai mugaye, akwai masu saukin kai, akwai baƙaƙen aljannu. Akwai sheɗanun aljannu, akwai masu haɗa soyayya tsakanin mace da namiji. Ni na kasance ɗaya daga cikin wanda yake haɗa so koda kuwa namijin baya so sai na sa ya so budurwar, ko in macen ce ba ta so sai na cusa mata son saurayin nata dole ta so shi kamar ta cinyeshi..
Janu tana ɗaya daga cikin sheɗanun aljanu, duk wani aiki na kisa ita ce nakasa mutum, makanta, gurgunta,kurumta,hauka, sa mutum ya shiga duniya, sa mutum ya zama ɗan iska, mayar da mutanen kirki abin tausayi, waɗannan kaɗan daga cikin aikin Janu kenan..
Muna nan tare da Boka Kata sai kawai naga wata mace a cikin jeji ta na gudu; a wannan lokacin na sauko na tambayeta lafiya take gudu? Sai ta ce dani.
"Abin bauta ya taimake ka ana so a kasheni ne zan shiga duniya."
Jin haka sai ce da ita.
"To zan taimake ki idan za ki bini inda nake."
Ba ta musa min ba sai ta bini muka tashi gidan Boka Kata; koda muka je lokacin ya tashi daga aikin ganin ɓaki na gabatar masa da ita, ganin nine na kawo ta bai musa ba ya bata masauki...
Haka yake kyautata mata ni kuma ganin Boka Kata ya samu abokiyar rayuwa sai na yi amfani da tsafina na haddasa a tsakaninsu; gari na waye wa yaje ya faɗa mata yana sonta amma shi dai Boka ne zata iya aurensa? A lokacin murmishi ta yi ta ce masa ita ma ai suna bauta wa wani gunki ne dake cikin wani teku, a dokar garin nasu idan har baku haihu da saurayinka ba kafin aure; to ba sai ace ba ka haihuwa daga ranar an sadaukar wa da sarkin garin kai, shi zai yi yadda yake so da kai, ko ya dinga amfani da kai har ƙarshen wayuwarka,
Ko kuma ya mayar da kai baiwa. Ita kuma a garin nasu ta samu wannan matsalar; sun kai shekara suna tare da saurayinta amma ba ta samu ciki ba, dan haka aka miƙa wa sarki ita ya ce sai dai ta zama baiwarsa. Ita kuma taga ba za iya ba sai ta sulale cikin dare ta wata hanya dake cikin dakin da aka kaita ta gudu, har zuwa safiya ta na tafiya sai suka dinga binta ƙarshe dai ta samu ta tsira ta yo nan..
Ko da Boka Kata yaji labarin rayuwar wannan yarinya sai ya cika da mamaki; amma kuma sai ya aje gefe ya tambayi sunanta, ta ce da shi sunan ta Dudu.. A ranar mu muka ɗaura aurensu aka yi shagali da dare muma muka tafi yankin mu.. Haka suka ci gaba da rayuwa har ta samu ciki, Boka Kata ya cika da murna ganin shi ma zai samu wanda zai gaje shi; Suna ta rainon cikin, lokacin da ta kusa haihuwa sai ya kirani ya ce na duba mu gani me za a haifa masa..
Tsafi na aiwatar nan na gano Namiji ne a cikin matar tasa, ya kamu da murna jin abin da yake so ne. Wata rana sai ta haifi ɗanta namiji mai kama da ita; aka sha shagali ranar Janu ta yi wata tafiyar ba ta nan aka yi haihuwar amma na sanar mata komai .
Boka ya sa wa ɗansa suna Damisa; wannan suna nima ya birgeni sosai har ita uwar yaron.. Haka ya dinga girma har ya zama cikakken saurayi; tun daga shi ba su sake haihuwa ba, yana fita farauta sai dare yake dawo ba. Da taimakon mu ya zama mai ƙarfin gaske amma sai dai shi baya son yin aikin Bokanci, idan Boka Kata na nuna masa yadda ake aikin Bokanci da kiran aljannu sai ya nuna baya so sài ya shiga jeji ya yi farauta..
Ana haka wata rana ina zaune cikin jejin da yake farauta sai na gansa da wata yarinya dauke da kwano a hannunta suna hira, sun jima suna hira inda take faɗa masa su a yankin Ethiopia suke garinsu yana da nisa ba mutane sosai a can inda suke, shi ya sa ma suka yo nan dajin na wajan Ghana suka zauna suna ci gaba da kiwon dabbobinsu, ina jinsu suka gama hira shima ya bata labarin shi sannan ya raka ta har kusa inda suak yada zango sannan ya dawo gida..
Wasa-wasa suka kalla soyayya nima na ƙara musu da ƙarfin son juna; a kwana a tashi Damisa ya ce ai shi fa ya ga wata yarinya yana so a aura masa ita...
Sosai Boka Kata da Dudu suka cika murna jin ya yi maganar aure; bayan ya tafi ya kiramu ya faɗa yaronsa ya ga wata yana so a bincika daga ina ta zo.. Ni na faɗa masa labarin da ta ba wa Damisa, Boka Kata ya ce sai Janu ta dawo sai aje anemo masa auren ta. Haka kuwa aka yi sai da Janu ta dawo Boka ya sanar da ita, da farko ta so kar ayi auren sai Boka Kata ya tambaye ko da matsala ta ce babu. Amma dai yarinyar in ta gano uban mijin da za ta aura Boka ne za ta sa su gudu ita da Damisa; a lokacin da take bayanin na gane ƙarya take sai kawai na ce ta barsa ya yi auren, ba dan ta so ba ta bari Boka Kata da shi da Dudu da Damisa da ni da Janu da sauran tawaga muka tafi inda suka yada zango..
Muna zuwa muka nemi auren yarinya, sai Mahaifiyar yarinyar taƙi amincewa har sai da muka sa ta da ƙarfin tsafi ta amince da auren, nan ne aka faɗa mana sunanta Zaira, bamu dawo ba sai da aka daura auren aka bamu ita muka dawo gida...
Tare suke zuwa farauta Zaira da Damisa, muna zamansu lafiya shi da ita..
Lokacin da ta gane uban mijinta Bokanci yake sai ta ce gaskiya mijinta ba zai yi Bokanci ba, Janu taji haushi sosai jin kalaman Zaira amma ta rabu da ita; haka ta dinga cusa wa Damisa kin yin Bokanci wato gadan babansa. Cikin ƙanƙanin lokaci Zaira ta samu ciki suna ta murna...
Cikin nata girma kuma ba daina fita farauta a tare ba.
Aikin Boka Kata ya soma ja baya babu mai zuwa neman a masa wani abu, a lokacin ne kuma na yi wata tafiya zuwa gurin dangina dake can wata nahiya; ya kira su Janu ya ce musu ya aka yi hakan take faruwa ne yanzu ba masu zuwa.
Janu ta dube shi ta ce.
"Matsawar ka na son aikin ka ya dawo yadda yake; to sai an zubar da jinin bil'adama."
Jin haka sai Boka ya kamu da farin ciki ya ce da ita.
"Ai samo bil'adama ba wahala zai yi ba ko yau zan kawo miki ku sha jini ku ci gaba da aiki."
Janu ta ce.
"Jinin wani naka muke so ba na kowa ba; ka sadaukar min da jinin ɗanka ko matarka ko cikin dake jikin matar ɗan ka, in yaso da mun sha jinin sai ta samu wani cikin."
Jin haka sai Boka ya shiga tashin hankali dan yana mugun son abin da yake cikin Zaira ; dukkansu baya son daya daga cikinsu asha jininsa, ita kuwa Janu dariyar mugunta ta yi ta yi tafiyar ta ta na jadadda masa indai bai yi sadaukarwar nan ba to tabbas zai rasa komai..
Kullum haka za ta zo ta yi ta masa maganar sadaukarwar, shi kuwa Boka ya kasa sanar da ahalinsa wannan al'amarin.. Ganin yana ɓata mata lokaci Janu ta haɗa kai da wasu aljanu suka kwashe duk dukiyar Boka, riga basu bar masa ba duk suka kwashe, Boka na zuwa ya ga an kwashe komai cikin mamaki ya kira Janu ya tambaye ta me yake faruwa da shi ne.
Buɗar bakinta sai ta ce ai masu buƙatar shan jini ne suka kwashe kayan ita kuma ba yanda za ta yi da su, hankalin Boka ya kuma tashi sosai..
A takaice dai Boka ya koma bashi da komai, shi kansa Damisa da Zaira idan suka fita basa kawo komai hakan yasa Boka ya nemi da Janu ya ce ya sadaukar da cikin jikin Zaira a dawo masa da jin daɗinsa, dama abin da take nema kenan ta ji daɗi sai ta ce suje indai zai yo alƙawarin sadaukarwar, sannan a kawo mata wasu mutane kamar uku ta sha jininsu, inyaso Zaira ta haihu sai a bata jariri ta sha jinin ,idan ya yi haka zai fi da yin suna a faɗin duniya duk wani ɗan iska da masu mulki za su san da shi kuma suke zuwa suna neman taimako gurinsa. Jin jawabin Janu sai Boka ya cika da murna, ya tura Aljannu da yake aika in haka ta taso su kamo mutane biyu; daret ya kaisa wata maƙabarta a nan tasa ya yi alƙawarin bayar da jinin abin da yake cikin Zaira, suka ɗaura wani ɓakin ƙyanle a jikin wani dutse suka rufe sannan suka dai. Aljannun da ya tura ba muso suka shiga duniya suka samu mutane biyu matafiya suka kawo su. Ita kaɗai ta shanye jinin mutane ukun kafin wani lokaci tuni ta dinga karkato da hankalin mutane kan Boka; nan da nan jin daɗin sa ya dawo....
Shi Boka abin da bai sani ba; Janu ta haɗa kai da wani ɓakin aljani wanda yawanci A MAƘABARTA yake zama, ta na zuwa tana karo sirrikan cutar da mutane da aljannu.
Ana tsaka da wannan halin na dawo daga tafiyar da nayi, nan Boka yake faɗa min abin da suka yi da Janu. Sam na kasa yarda da wannan tsarin na Janu na ce masa kada ya kuskura ko da Zaira ta haihu a sadaukar da abin da ta haifa, to dama shima ba dan ya so ba ya bada sai ya ce taya zai kare abin da yake cikin Zaira ya tsira ko zai bata wani mutum ɗin a madadin abin da yake cikin Zaira?
E na ce masa na ce zan same ta mu yi magana duk da ba wani shiri miki da ita ba saboda zalincin da take yi; nan yake sanar dani indai aka haifi mace ya yi alƙawarin zai aura min ita saboda yadda bake kyautata masa, naji matuƙar daɗi dan tuni na gano mace za a haifa sai ya miƙo min ɓakin zare; ya ce daga an haifi mace in sa mata wannan aure ni da ita an gama.
Muna gama magana naje na same ta na sanar da ita komai..
Cikin ɓacin rai ta ce ba za ta taɓa yarda a canza mata ba dole jaririn da aka haifa za a bata , in kuma ba haka ba to za ta kunno masifa kala-kala wanda ni kaina ba zan iya dakatar da ita ba, faɗa muka yi sosai ta ita a kan jaririn cikin Zaira wanda su basu san me ake ciki ba..
Tun daga ranar Janu take gadin Zaira ta kuma sa ana bin ta duk inda za su je da Damisa, ni ma ina ta bibiyarsu dan sosai naji ina son abun da yake cikin nata.. ..
Ranar Zaira ta tashi da nakuda, Janu na samun labari ta yi wa Boka kiran gaggawa ya zo. Bayan ya iso ta ce da shi ga Zaira ce za ta haihu dan haka ya zo suje inda za ta ƙaro masa ƙarfin tsafinsa, sanin ina biye da Zaira yasa Boka ya bi Janu suka wuce cikin Maƙabartar da suka yi alƙawari..
Cikin mamaki yake kallon ta ganin ta kawo sa maƙabarta; dariya ta dinga masa ta na nuna sa sai ga ɓakin aljani ya fito suka haɗu tare suna ta yi wa Boka dariya abin da ya firgita shi kenan, ganin abin nasu ba na ƙare wa bane ya ce da ita.
"Me za mu yi a nan da kika kawoni? Ko nan ɗin ne inda za a ƙara mini ƙarfin tsafin nawa?"
Tsayar da dariyar ta yi ta soma bashi amsa.
"Boka kenan wai daka ɗauka da gaske tsafin ka za a ƙara wa ƙarfi? To ka yi kuskure dan yau karshen ka ya zo, ɓakin aljani ya faɗa min indai ina son burina ya cika to lalle sai na kashe ka zan samu cikar burina; kuma gashi na kawo ka nan..
"A MAƘABARTA NE ka min alƙawarin jinin jaririn ciki Zaira; sannan kuma A MAƘABARTA NE zan kashe ka na sha jininka na cinye naman jikinka, A MAƘABARTA NE lamarin ya fara dan haka dole A MAƘABARTA NE zan karɓi wannan mulki da nake nema shekaru ɗaruruwa. Ka ɗauka da wai ina tare da kai zan na yi ta ma aiki? To ba ka isa ba ina so ne dama ka cika lokacin da zan kawo ka nan shi ya sa nake tare da kai."
Tun da ta soma magana Boka ya tsora ta sai yanzu ya yi da-na-sanin biyo ta da ya yi, kafin ma ya yi magana ta tsira masa takobi nan take ya mutu suka shanye jininsa ita da ɓakin aljani.. Bayan sun gama ta nufo gidan Boka dan ta kashe su...
Ina tare da Zaira da Damisa da kuma Dudu matar Boka labari ya sameni. Sai dai kash kafin na yi wani yunƙuri sai ga Janu ta baiyana a nan, a lokacin kuma Zaira ta haifi ƴar mace wato ke kenan.
Zabura Suhaima ta yi jikin na mugun rawa ta ce."
"Sa..Sayyid!"
Janyota ya yi jikinsa ya rungume ta tsam yana bubbuga bayanta, a nutse ya ce.
"Ki nutsu na ƙarasa miki labarin."
Tsayar da kukan ta yi; hakan yasa ya ci gaba da magana.
"Faɗa sosai muka yi akan sai ta dauke ki ni kuma na hana ta, hakan yasa muka dinga yaƙi a tsakanin tawaga ta da tata tawagar. Hankalin Damisa ya tashi jin yadda ɗakin yake girgiza, hakan yasa suka fito da sauri Zaira na rungume da Jaririyarta suka bar gidan; tafiya suka dinga yi har suka iso wani gari suka tsaya a bakin gari..
Bayan na ci nasarar jikata Janu na bi bayan su Damisa na same su, nan na sanar da su komai suka tada hankalinsu na nuna musu zan kare ku. Mun shiga cikin Ghana da su Janu ta cin mana ta zo da baƙaƙen aljanu masu yawa.
In taƙaice miki dai a nan suka kashe Iyayenki ni ma sun so su kasheni na samu nasarar dauke ki muka ɓace. Sai da na tsire musu na iso jikin wata bishiya na aje ki da jinin haihuwar ki a jikin ki, ganin wasu mata da miji suna tafiya sai na sa motarsu ta tsaya na saki kuka, nan suka ɗauke ki kafin su tafi na sa ɗiga miki wani farin abu wanda zai kare Janu ba za ta gano inda kike ba, ɓakin zaren nan na sa miki daga lokacin kika zama matata, sai da naga tafiyarsu sannan na tafi...
Ita ko Janu can maƙabarta ta kai su Damisa suka yi ta cin naman su, sannan duka binne ƙasusuwansu A MAƘABARTAR. Amma duk da haka ta taso ruhinsu har kakanki ta soma amfani da su tana cutar da mutane...
Ni kuma jinyar kaina na yi har na tsayin shekaru biyar, kuma har zuwa lokacin Janu ba ta gano inda kike ba, idan ina son ganinki sai na bari zuwa dare