Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 38049 words

Chapter 12 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

417

Ads at the middle of Article

ta na cewa, ita fa ba za ta iya wata tare da su Umma a kusa da ita ba kawai dai za ta yi sati ɗaya. Murmishi ya yi sai ya iso cikin palon ya ce shi zai koma gobe zai dawo su tafi da su Umma, Sulaiman ya ce a'a ya yi haƙuri kawai zuwa goben sai su tafi tare ya daure. Ba dan ya so ba ya amsa da to...


Washegari su Umma suka bar Suhaima a cikin danginta cike da kewarta, ita kuwa har da kuka ta janyo su Iman ta rungume su a hankali ta ce da su.
"Yaran Mama fatan za kuke ziyartata ba za kuke barina da kewa ba?"
Gyaɗa mata kai suka yi Iman ta ce.
"Mama za muke zuwa kullum muna hira dake, ki sani kodayaushe muna a tare dake da kin ji ki na son ganinmu to za ki ganmu. "
Murmishi ta yi ta ce.
"To shi kenan ku gaishe da babanku sai kun zo."
Ta yi maganar ta na sakin su suka wuce suna ɗaga mata hannu. Tun da suka fara magana Sayyid na jinsu, jin ta ce su gaishe shi sai ya yi murmishi ya tsaya su kuma suka wuce dan yana son mata sallama..


Kallon shi ta yi ta na murmishi ta ce.
"Sayyid to sai wani lokacin ina godiya da kulawar ka a gareni ina ma fatan samun mace mai hali irin naka."
Ta yi maganar muryarta na rawa; jin ta na shirin masa kuka ya ce.
" A'a Ummu kada ki yi kuka; kin san abin da nafi shiga damuwa to shi ne naji kina kuka ki shiga ciki da zarar ki na son ganina za ki ganni ina tare dake Ummu."
Goge hawayen da ya zubo mata ta yi ta na murmishi ta ce.
"Wai kai ma kana da zuciya kamar bil'adama."
Dariya maganar ta ba shi sai ya yi murmishi ya ce.


"Ummu kenan! Kamar yadda kuke jin zafi da raɗaɗi idan kun rabu da abin da kuke so; to haka muma muke ji fiye ma daku, muna da zuciya kamar yadda mutane suke da ita, muna jin sha'awar abubuwan da duk wani bil'adama yake ji, kawai mu mun fiku ƙarfi ne sannan halittarmu ba ɗaya ba ce da ku, amma muna jin duk abin da kuke ji ko ma in ce fiye da ku mutane.
Ina jin ba daɗi da baki kasance jinsi na ba, amma kuma ba komai hakan ba zan iya goge ƙaunar da nake miki ba, ina sonki sosai Ummu musamman lokacin da kika haifa min su Ayan. A lokacin naji kin gama yi mini komai a rayuwa; kin bani yaran da nake ta son samu duk da ke a zahiri ba ganinsu kike ba sannan ba ki ɗauki cikinsu a fili ba."
Murmishi kawai Suhaima ta yi in taji ya ce wai ta haifa masa su Ayan jin abin take ban-bara-kwai wai ita ce ta haifi yara biyu tun ba yau ba.
"To sai wani lokacin.
Taji sautin muryarsa yana mata sallama; hannu kawai ta ɗaga masa dan a wannan gaɓar ba za ta iya ce masa komai ba, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya magana mai daɗi komai nasa irin na mutane yake mata kamar shi ba wata halittar ba ce..

Ciki ta koma cike da tunanin maganganun Sayyid har bacci ya ɗauke ta...


Sai dà Suhaima ta yi wata ɗaya sannan ta birkice ta ce kawai ita su Umma take son gani su mayar da ita.. Washegari sai kawai ganin Sayyid ta yi ya bayyana a ɗakinta ya ce ta haɗa kayanta ta fita ƙofar gida yana jiran ta ya mayar da ita gida; sake da baki take kallon sa duk da ba tsoro ya ba ta ba amma ya zo mata zuwan bazata, sai da ya ɓace ta janyo akwatinta ta fito ta na gyara zaman hijabinta ta ce Sayyid na waje yana jiran ta. Da mamaki Sulaiman ya dube ta ya ce.
"Kai yarinyar nan! Yanzu yana waje ba ki sanar damu ba ya shigo ciki ko da ruwa ne ya sha sai ki barsa a waje."
Murmushi Suhaima ta yi a ranta ta na cewa da kun san waye Sayyid ɗina da ba sai kun wahalar da kanku ba.


Tsaraba ba kaɗan ba suka haɗa mata a nan ta dage sai an ba ta Aminatu sun tafi da ita; ita ko Aminatu sai murna take da aka ce mata za ta je Nigeria da Suhaima, da gudu ta ɗauko kayanta ko wanka ba ta yi ba ta ce su tafi. Dariya duk suka mata tsohuwa ta ce su tafi dan ta ga inda Suhaima take zama, haka dai suka fito har gurin Sayyid ya gaisa da yan gidan sannan suka wuce zuwa bakin hanya...


Mota ya tara suka shiga zuwa cikin birni daret airport suka nufa, ita dai Aminatu sai kalle-kalle take yau dai gata a birni. Jirgin su ya sauka suka shiga ciki.
Sayyid ya so kawai ya kai Suhaima gida cikin daƙiƙu kaɗan, amma ganin Aminatu sai ya haƙura suka zauna a jirgin..




Jirgin su na sauka suka samu Na'im ya zo ɗaukan su ya yi tsaye yana jiran zuwansu. Bai gansu ba su kuma sun gansa Suhaima ta saki Jakar hannunta ta nufi Na'im cikin jin dadin ganinsa.. Bai ankara ba sai taji an faɗo kansa ya juyo da sauri sai ya ga Suhaima ce, dariya ya yi ya ce.
" Anty sannu da zuwa ku zo muje."


Sayyid ya musu sallama ya fice suma suka nufi gida..
Suna zuwa aka dinga murnar zuwansu sosai Umma ta ji daɗin ganin Suhaima, da har ta shiga damuwa ganin sun ce ta zauna da su ta ɗauka amshe abarsu za su yi, sai gashi ta dawo har da ƙari ma suka mata na Aminatu...


Cikin sauri ta shirya saboda ta yi latti; da sauri ta fito ta ɗauki tea a tsaye ta dinga sha ta na cusa bredi hannu baka hannu gwarya ta dinga yi har ta cinye ta wuce da sauri. Na'im ta samu a mota tare da Aminatu ta ce.
"To fa! Yau kuma Aminatu za ka ɗauka ku shiga gari ko?"
Dariya ya yi ya ce.
"Kai Anty to ai so nake ta zama ƴar gari makarantar koyon Hausa zan saka ta."
Murmishi kawai Suhaima ta yi suka wuce zuwa school...


Bayan an tashi ta fito ta na tafiya a hankali saboda muguwar gajiyar da ta yi, dan yau sun sha darasi sosai.


"Am Suhaima!.


Ta ji an kira sunan ta cikin wata kalar murya mai daɗin sauraro; ta yi saurin juyo wa suka haɗa idanu ta ja da baya ta na zare idanu..








TAKU HAR KULLUM MAMAN NUSAIBA.
[3/21 00:33] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_










Daga Alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_








SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*


بسم الله الرحمن الرحيم


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚




1️⃣4️⃣


Da mamaki yake kallon ta ganin yadda ta tsora daga yin arba da shi; riƙe baki ya yi ya soma magana cike da mamaki.


"Suhaima!
Ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi; yadda ta zaro masa fararen idanunta ba ƙaramin tafiya da imaninsa ta yi ba.
Baki na rawa ta ce.
"Sa...Sayyiddd!
Taja sunan cikin rikicewa haɗin da zallar tsoro bisa kan fuskarta, jikinta duk ya ɗauki rawa sai ta ƙura masa idanu ta na binsa da kallon ƙurulla. Shi kam harde hannayensa a ƙirji ya yi yana mamakin jin ta kirasa da Sayyid, to waye ma wani Sayyid da take haɗa sa da shi?
Ya tambayi kansa yana ciza lips ɗinsa na ƙasa.
"Waye kuma Sayyid Suhaima?
Ya yi maganar yana waro nasa idanun. Jin abin da ya faɗa sai taji ta ɗan samu nutsuwa, sosai ta dinga mamaki ganin mai kama da suffar da Sayyid ke bayyana a gareta, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma ba shi haƙuri.
"Yi haƙuri Malam; ka yi min kama da wani ne da na sani shi ya sa kaji na kira ka da haka."
Ƙayataccan murmishi ya sakar mata sannan ya gyara tsayuwarsa cikin nutsuwa ya ce.
"Am dama ina son mu yi wata magana ne; tun wancan satin nake ta neman inda zan ganki amma kuma Allah bai nufa ba, idan ba damuwa ban takura miki ba muje na kaiki gida."
Sunkuyar kanta ta yi ta na wasa da gefen hijabinta, ji ta yi jikinta ya mutu murus har bakinta hakan yasa ta kasa ce masa komai.
Ganin haka yasa shi ƙara yin magana.
"Please Madam."
Ya yi maganar yana yin gaba; ita kuwa ji kawai ta yi ta na binsa a baya har gurin motar.
Suna zuwa ya buɗe mata gaba; a sanyaye ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, haka kawai taga ya cika mata idanu ya mugun yi mata kwarjini. Ba ta san lokacin da ya tayar da motar ba sai da taji suna tafiya; nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ya kalle ta tare da yin murmishi ya soma koro mata jawabi.
"Am Suhaima tun ranar da na fara zuwa School ɗin nan na dinga jin matata na cikin wannan school ɗin; sai kuma gashi a hankali Allah ya haɗa mu can kwanaki muka bigi juna ni da ke, har kika fasa min waya kina ta bani haƙuri."
Ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya kuma faɗar.
"Ina zamu bi ne Gimbiya?"
Tun da ya fara maganar ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, yau dai gashi ta samu mai kama da Sayyid kuma ya furta mata kalmar so, lumshe udanu ta yi ta na tunano yadda Sayyid ke faɗa mataza ta samu wanda ma ya fishi komai; sai dai ta na da wahala a samu wanda yake mata son so kamar Sayyid ba ta gansa ba, kuma ba ma za ayi sa ba a cikin maza. Ajiyar zuciya ta sauke har yanzu zuciyarta ta ƙasa goge soyayyar Sayyid duk da shi ba mutum bane amma har ƙasan ranta take jinsa, saboda ya taimaka mata tun kafin ta zo duniya yake ɗawainiya da ita har ta zo ta zama mutum bai gajiya ba, kuskure ɗaya ya aikata a gareta; shi ne auren ta da ya yi har ta haifa masa jinsinsa wanda haramun ne aljani ya auri mutum. Wannan lefin ta kuma yafe masa shi saboda alkhairansa ya yi yawa a cikin rayuwarta, dan haka ba ta ganinsa a matsayin mugu dan ya aure ta wanda kakanta ne ya bada auren nata dan ta rayu a doron ƙasa ya yi haka.
Ɗago kai ta yi ta dube sa a kunyace ta masa kwatancan gidansu, daga haka kasa cewa komai ta yi har suka iso.

Hannu ta kai za ta buɗe ƙofar ya yi saurin kulle wa ta kalle shi da sauri, tamkar wani ya yaro ƙarami ya shagwaɓe fuska ya ce.
"Please give me phone number sai mu ƙarasa maganar a waya, naga alama kunyata kike ji."
Rufe fuska ta yi ta na murmishi ta miƙa masa hannu ya bata wayarsa ta sa masa sannan ta masa godiya ta fita a motar. Sai da ya ga ta shige cikin gida sannan ya juya kan motarsa ya koma inda ya fito...


Ta na isa gida wanka ta fara yi ta ci abinci har zuwa lokacin Na'im da Aminatu basu dawo ba, ta na gama yin komai ta haye kan gado ta janyo waya ta shiga WhatsApp.
Wata baƙuwar number ta ci karo da ita wadda bata Nigeria ba ce, da mamaki ta shiga cikin number ta tarar da voice yafi goma ta soma ɗaga wa, muryar Uncle Sulaiman taji yana ce mata sun yi kewarta ga Tsohuwa za ta mata magana...
Wani farinciki ne ya mamaye zuciyarta ta dinga ɗaga saƙon ɗaya bayan ɗaya ta na mayar musu da amsa, bayan ta gama ta fita a number ta yi saving sai ta kuma ganin wata number an mata magana; da mamakin ta ta shiga ta ga an rubuta saƙo kamar haka.
"Ummuna Uncle ɗin ki ya amshi number ki za ki ga ya yo miki magana, sannan ka su Iman nan za su kawo miki ziyara."

Sake da baki Suhaima take ƙara karanta saƙon, tunani ta dinga yi to dama aljannu suna yin social media ne? Kenan yanzu sai ka iya yin friend da aljani ba ka sani ba a social media?
Murna ta yi ganin ya kuma turo mata da wani saƙon.


"Ummu kenan! Wai kina mamaki ne dan na miki magana a WhatsApp? To ki daina mamakin hakan dan duk abin da mutane suke muna shiga cikinsu mu yi mu'amala da su basu san me me mutane bane; muma muna yin social media ɗin nan za ki iya ɗaura abota da aljani ba ki sani ba Ummu, da haka wasu ke shiga jikin bil'adama in macuta ne su dinga cutar da mutum ayi ta zuwa Asibiti amma a ƙasa warke wa...


Dariya Suhaima ta yi bayan ta gama karanta saƙon, wani abu ta tuna ta yi saurin danne voice ta soma masa magana.


"Tab Wallahi Sayyid abin ya bani al'ajabi, a da in aka ce aljannu na yin social media sai nake ɗaukar abin a wasa; sai gashi na ga zahiri a wajan ka. Yawwa wai ni ko dama ina so na maka wata tambaya akan Uncle ɗina; shi wai me ya yi wa Janu ne ta kashe shi?"
Ta na ƙarasa faɗar haka ta saki, tana cikin number taga ya ɗaga sai dai bai dawo mata amsa ba, sai can ya ce da ita ga su Iman nan za su zo mata da amsar. .Da murna ta amsa da to sannan ta sauka sai ga kira ya shigo, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta yi shuru ba ta ce uffan ba.


"Assalam alaikum Girmbiyata ina fatan kin shiga gida lafiya dai ko?"


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce masa.
"Alhamdu Lillah fatan kaima haka ka isa lafiya."
Murmishi mai sauti ya yi sannan ya ci gaba da magana.
"Ni sanana Hamid dan cikin garin nan ne ni, har iyayena maganar gaskiya Suhaima ni ba da wasa na zo ba, ina so ki bani dama na gabatar da kaina a wajan su Baba sannan na turo da iyayena. Sunan Mahafina Alhaji Hamza na san ma za ki sanshi a garin nan ba ɓoyayye bane a kaf garin nan.."
Waro idanu ta yi ta ce.
"Minister kake nufi fa!
"Kwarai shi dai.
Ya ba ta amsa yana murmishi; jinjina kai ta yi kamar yana ganin ta ya yi ta roƙo ta bashi dama ya zo ta ce ba damuwa ya zo kawai.
Sun jima suna hira sannan hira daga bisani suka yi sallama...


Washegari bayan sallar Isha'i Suhaima na zaune ta ba duba takardu ta ji saukar wani abu, da sauri ta juyo sai ta yi arba da su Iman.
Da sauri suka zo a tare suka rungume ta suna murnar ganin ta, ɗago da su ta yi ta ce.
" A'a haka kuka koma?To ina Babanku yake?"
Da sauri Iman ta ce.
"Mama Baba ya ce yana gaishe da ke, sannan ya ce mu faɗa miki amsar tambayar ki."
Gyara zama ta yi ta ce.
"Ina ji Iman faɗa mini."


"Abin da yasa Janu ta kashe Uncle Abdallah shi ne; wata rana ta zo ɗaukan ki sai ta samu ke da shi kuna zaune a palo, ta so shiga jikin ki shi kuma a lokacin ya kunna karatun littafin ku à TV ya ƙure volume, hakan yasa jikin Janu ya soma ƙone wa da ƙyar ta gudu ta bar gurin. To shi ne bayan ta yi jinyar kanta ta yi alƙawarin sai ta kashe shi har ke ɗin ba, to bayan ta kashe shi aka soma bincike a kan kisan ,ko kwana biyu ba'a yi ba ta sa duk kowa ya manta maganar kess ɗin aka manta da taya ma ya mutu.
Wannan shi ne abin da yasa ta kashe shi."


Goge hawaye ta yi ta ce.
"Allah sarki Uncle; ta sanadina ya rasa ransa Allah ya maka rahama.
Ta yi maganar ta na kallon Ayan da ya yi kikam kamar wani gunki, da mamaki ta ce.
"Yarona lafiya yau duk naga ba ka yin fara'a?"


Murmishi ya yi ya ce.
"Mama ina Inna Laure take ne? So nake na ɗan tsorata ta."
Itama dariyar ta yi ta ce.
"A'a Ayan kar ka tsora min Innata kasa ta sheka kwananta bai ƙare ba."
Murmishi ya yi suka ci gaba da hira anan yake faɗa musu haɗuwar ta da Hamid sak Babansu a suffarsa ta mutane, dukkansu suka ce ta amince kawai tun da yana sonta, bata musa ba ta amsa da to sannan suka tafi...




Cikin kwanaki kaɗan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Suhaima da Hamid, hakan yasa ya faɗa wa mahaifinsa su zo nema masa auren ta, ko da suke zo Abba sai da ya kira Uncle Sulaiman dan dama tuni ya faɗa masa zuwan nasu, ta waya aka yi magana da shi ya ce ai ko mai Abba ya zartar aksn Suhaima to ba za su ce komai ba, dan haka komai yana garesa. Sosai Abba ya ji daɗi matuƙa da wannan karar da ahalin Suhaima suka masa ya ce ya bai wa Hamid auren Suhaima, hakan ya yi wa mai girma Minister daɗi aka sa biki wata ɗaya suka dawo gida da labari mai daɗi...


Ranar Hamid da Suhaima kusan kwana suka yi suna hira farinciki ya hana su yin bacci a wannan ranar..


Lokaci yana ta tafiya biki na matsowa, aba saura sati ɗaya ɓakin sai ga su Uncle Sulaiman da dukkanin familynsu gabaɗaya babba da yaro ba wanda aka bari kowa ya zo, waɗanda ba su taɓa zuwa Nigeria ba suka matsa Aminatu sai ta kaisu sun ga gari, Na'im ya ɗauke su ya dinga jigila da su idan suka fita sai kusan Magariba suke dawowa gida, sosai suka ji daɗin Ƙasar..
Amarya ta sha lalle ɓaki da ja ta sha gyara sosai duk inda ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads