Showing 15001 words to 18000 words out of 38049 words
Chapter 6 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣8️⃣
A ruɗe na kalli doctor na ce.
"Ta rasu?"
Na faɗa muryata na rawa dan ni a tunanina jaririyar da muka tsinta ce ta rasu.
"E hajiya ta rasu sài haƙuri ga dai ɗayar jaririyar. "Ta faɗa tare miƙo mini ita; ganin tawa ce ta rasu na fashe da kuka saboda na ƙwallafa rai akan abin da yake cikina tun kafin ya zo duniya, haƙuri ta dinga bani ta ɗauke jaririyar na ce ta miƙa wa mijina yana waje. Sosai naji mutuwar jaririyata amma kuma da na tuna akwai wata sai naji damuwata ta ragu sosai nan bacci ya ɗauke ni..
Doctor na fita da jaririyar a lokacin Maman Aruf ta zo tare da Suhaila da Aruf; ta na isowa Suhaila ta dage ita za a bai wa jaririyar, ganin haka yasa Abbanku ya ce ta zauna a mata. Jiki na rawa ta zauna sai washe baki take aka runguma mata jaririyar; bayan ta bata ne nan take sanar da su cewa ɗayar jaririyar ta rasu nan fa Maman Aruf ta kalli Doctor cike da rashin fahimta ta ce.
"Kamar ya ya ɗayar ta rasu? Dama biyu ta haifa ne?"
Ta faɗa fuskarta ɗauke da mamaki ƙarara; Abbanku ne ya ce Allah ya jiƙan ta su je a bashi ita a mata sutura, jagora ta masa zuwa inda ake aje gawawwaki.. Bayan na farka ne aka bar su Maman Aruf suka shigo ɗakin, zuwa lokacin ina zaune suka sameni, da sauri Suhaila ta iso inda nake bakinta yaƙi rufuwa ta soma rattaɓo mini bayani.
"Umma sister na mai kyau ce sosai; Umma a goya min ita zan ke zuwa wasa da ita tare da su Aruf."
Murmushi kawai na mata ban iya ce mata komai ba, kallon Maman Aruf na yi ganin yadda take kallona sai na gane ƙarin bayani take son na mata; a sanyaye ta ce da ni.
"Maman Suhaila dama 'yan biyu kika haifa ne?"
Kallon Abbanku na yi sai ya mini alama da kar na ce mata a'a, kallon ta na yi ina murmishi na ce.
"E biyu ne ai bayan na zo aka haifi ɗayar, ita wadda na haifa a gida ta rasu sai wannan ɗin."
Jinjina kai ta yi sai kuma ta saki murmushi ta na faɗin.
"Ai dama na sha faɗa miki wannan cikin naki yara biyu a ciki, amma kika kasa yarda yanzu dai gashi maganata ta tabbata kin haifo biyun."
Murmushi na yi muna haka sai ga Doctor ta iso ta bamu sallama shi kuma Abbanku ya tafi ya biya kuɗin magani ya dawo muka tarkata muka dawo gida...
Ko da muka zo gida na ɗage sai mun koma Nigeria amma ya ce sam ba za mu tafi ba; ranar har kuka na yi amma ya yi burus dani sai kira ya yi ya sanar da su haihuwar, su kansu sun so ya dawo dani gida amma ya ce gaskiya a barni zai kula dani ba sai an ɗauke ni ba daga gurinsa. Inna Laure na jin labarin ta kira ta zazzagi Abbanku ta ce ya dawo da ni amma ya ce Sam ba zai zo ba sai dai su su zo suna zai biya kuɗin jirgi; kasancewar yanzu Allah ya buɗa masa har da shagon atamfofi garesa.
Bayan kwana biyu muka ya kira iyayensa da nawa iyayen muka musu bayanin komai da ya faru, ni kan tsoro naji kar su ƙi amincewa; amma abin mamaki a cikinsu ba wanda ya ce wani abu sai ma sa mana albarka suka yi sannan suka ce wannan ya zama sirri tsakanin mu shida ɗin nan. Naji daɗi sosai ganin sun fahimce mu muka musu godiya...
Tun da muka tsinci Suhaima nake ta ganin abubuwan mamaki, yarinyar ba ta yin rigima ko yunwa take ji ba ta kuka. Ranar kwananta huɗu da haihuwa ina toilet na ji kukan ta na fito da sauri, turus na tsaya ganin Suhaila ta na kiciniyar ɗaukan ta, ganin fa da gaske ɗaukan nata za ta yi na ƙaraso na hana ta ta ɗauke ta. Sai da na rungume ta na zauna ina shayar da ita kawai naga hannunta na hagu an ɗaura mata wani ɓakin zare mai kyau, sosai abin ya bani mamaki na kama hannun ina juya zaren, sai kuma na ga ya mini kyau sosai na bar mata shi...
Washegari sai ga Inna Laure da Maman Sani da Ƙanwata da mamana har yan'uwan mamana, sai Abdallah da ƙanena Salim; na sha murna sosai kamar zan goya su, Inna Laure na zama ta ɗauke Suhaima ta rungume ta na kallon jaririyar har idanunta suka kai kan ɓakin zaren nan, cikin murmishi ta ce.
"A su Bintu ba a manta da gargajiya ba kin ga ta sa wa jaririyar nan ɓakin zare."
Murmushi kawai na yi ina kallon su suma suna ta cewa ai kuwa ya yi wa jaririyar kyau, haka muka wuni Maman Aruf ta musu girki mai rai da lafiya sai sa mata albarka suke...
Ranar suna jaririya ta ci sunan Inna Laure sai na ce ake kiran ta da Suhaima; ranar Inna Laure ta sha kukan farinciki ganin Abbanku ya mata takwara ni kaina Abbanku ya birgeni da ya sa mata sunan Inna Laure... Sai bayan suna da kwana biyu suka tafi da ƙyar aka rabani da jikin mamana ina kuka sai na bisu, sai da na ga shigarsu mota na koma ciki na ɗauki Suhaima na zauna..
Su Suhaila abin na ya samu ko school ta je sai ta ce da 'yan ajinsu.
"Ni ma ina da sister."
Aruf ya tayata faɗa kaf 'yan ajin ba wanda bai san sunan Suhaima a bakin Suhaila ba, kodayaushe maganar Suhaima ɗin ta take an kusa saka ta makaranta za suke tafiya tare..
Haka muka ci gaba da rainon yaranmu Suhaima na daɗa wayo, sosai nake mamakin yarinyar idan na tafi Islamiya na kaita gidan su Maman Aruf har na dawo ba ta kuka, wani ƙarin abin mamakin ma idan dare ya yi haka kawai zan ga fuskar Suhaima na haske ta na ta wasa cikin tsakiyar dare; sosai nake ganin abubuwan al'ajabi a gurin yarinyar..
Haka dai take girma abin ta har ta yi shekaru biyar sannan aka sa ta a makaranta; ranar zuwan ta na farko ana tashi aka neme ta aka rasa a makarantar.. Suhaila ta dawo gida ta na kuka ta ce mini wai an rasa Suhaima, hankalina ya yi mugun tashi na kira Abbanku na sanar da shi wai Suhaima ta ɓata; nan da nan muka tafi makarantar tasu. Ko da muka isa nan suke sheda mana cewa suma neman ta suke kaf makarantar an zagaye basu ganta ba; hankalina ya kuma tashi na dinga kuka Abbanku na rarrashina muka tafi police station muka bada pictures ɗin ta, ranar dai haka muka dinga bayar da cigiyar ta a gidajen radio.. Yamma ta yi lis muna hanyar dawowa daidai get ɗin wata maƙabarta na hangi wani abu kamar mutum zaune; na yi saurin ƙara kallon gurin ai kuwa na ga Suhaima zaune ta na ta wasa a gurin, bakina na rawa na ce.
"Abban Suhaila ka ga Suhaima can a get MAƘABARTA."
Da sauri ya kalli inda nake nuna masa ya ganta muka paka na fito har ina haɗa wa da gudu na isa bakin get ɗin maƙabartar, ina isa na kamo ta ban tsaya yin komai ba na rungume ta na miƙe da sauri na isa motar muka wuce.
A hanya nake kalle ta na ce.
"Suhaima me ya sa kika fito daga makaranta? Kuma wa ya kawo ki bakin maƙabarta kika zauna kina wasa?"
Dariya ta yi ta kalle ni ta ce.
"Umma wata Anty ce ta ɗauko ni daga School ɗin ai, shi ne ta kawoni nan ta ce na zauna za ku zo ku ɗauke ni. Kuma har da abinci ta saya mini mai ɗaki ta kaini wajan wasa sannan ta kawo ni nan ta shiga cikin gidanta ta barni a waje.."
Kwalalo ido na yi ina kallon Suhaima shi kansa Abbanku a lokacin saboda al'ajabi har so ya yi ya bigi wata mota garin kallon Suhaima, a kiɗime na ce.
"Gidanta kuma Suhaima? To nan ai ba gidanta ba ne MAƘABARTA ce inda ake binne mutum idan ya mutu, ita Antyn naki ce ta ce miki nan ne gidanta?"
Gyara kwanciyar ta ta yi a jikina ta ce.
"E haka ta ce har ma da mijinta Umma, ta ce nan ne gidanta ni ma na shiga ciki."
Tsananin al'ajabi yasa na ce.
"Ke! A MAƘABARTAR NE kika zauna?"
"E."
Kawai ta faɗa ta koma ta kwanta ta na lumshe idanunta sai sauke ajiyar zuciya take...
Ko da muka zo gida sai juya kalaman Suhaima nake, hankalina ya kasa kwanciya da maganarta, Abbanku ya watsar da magana ya ce kawai magana ce irin ta yara ba komai ba; amma kuma ni hankalina ya kasa kwanciya, ganin bani da mafita sai kawai na dinga mata addu'a ƙarshe ma na hana ta zuwa School ɗin...
Tun da na hana Suhaima zuwa School ni ma na daina zuwa Islamiya a satin; haka kawai naji hankalina ya kasa kwanciya da lamarin yarinyar.
Ashe dai ba'a rabu da bukar ba an haifi habu, sai na bar Suhaima a ɗaki amma da an jima sai dai naji ta buɗe ƙofar palo ta shigo, idan na tambaye ta ya aka yi ta fito sai kawai ta ce wasa suke da ƙawayen ta.
Washegarin ranar data fara fita cikin dare muka nemi Suhaima muka rasa; babu inda ba mu duba ba a cikin gidan amma sam bamu ganta ba hakan ya ƙara sa zuciyata bugawa, waje Abbanku ya fita ya tambayi Maigadi ko ya ga Suhaima; sai ya ce bai ganta ba gaskiya.. Ganin ba ita ba dalilin ta sai muka fita bakin get muna ta duba wa amma sam bamu ganta ba, gefen layin gidanmu muka dinga bi da mota muna nemen ta ko Allah zai sa mu ganta. Abin mamaki sai ga Suhaima a get ɗin maƙabartar da muka tsinto ta ta yi zaune ta na surutu, da sauri muka tsaya Abbanku ya fita ya iso gareta yana mata magana.
"Suhaima me ya sa kika zo nan cikin daren nan?"
Buɗar bakinta sai cewa ta yi.
"Abba wasa muke ni da ƙawayena, kuma dama na ce musu zan tafi gida yanzu ina jin bacci."
Cike da tsoron lamarin yarinyar ya dinga duba wa ko zai ga wani ɗan'adam a gurin amma ba kowa, hannunta ya kama ya ce.
"To tashi mu tafi gida."
Da ƙyar ta yarda suka tafo daga get ɗin maƙabartar, ko da ta zo shiga sai cewa take.
"Sai gobe zan sake dawowa mu yi wani wasan, zan kawo muku kayan wasa."
Ni kan tuni jikina ya ɗauki rawa saboda tsoro gani nake kamar ba Suhaima ɗina ba ce an canja mini ita; ta na shigo wa motar ta faɗa kaina ta na dariya da yi shuru ban ce mata komai ba dan tsoro ma take bani .
Muna zuwa gida na mata wanka na tofe ta da addu'a sosai ranar a tsakiya muka saka ta muka yi bacci da ita. Washegari Suhaila ta dage sai sun koma makaranta ba dan na so ba na shirya su muka je na kaisu; Maigadin makarantar na yi wa magana kamar zan yi kuka saboda fargaba.
"Don Allah Baba kar ka bari Suhaima ta fita daga School ɗin nan, idan ba ni na zo ɗaukan ta ba kar ka bari ta fito ka taimakeni Baba."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Babu matsala yarinya zan kula da ita in sha Allah."
Godiya na masa na wuce gida ina ta zullimi. Tun kafin lokacin tashi ya yi aka kira Abbanku daga School ɗin ku, nan suke sanar masa ya yi maza ya zo Suhaima ba lafiya har suma take; hankali a tashe ya kira ni ya faɗa mini ya zo muka wuce. Muna isowa muka samu an kewaye ta ita da Suhaila da Aruf suna ta kuka; ni kaina da na ga halin da Suhaima take ciki sai da hankalina ya tashi matuƙa har ban san lokacin da na ture mutane ba na iso gaban su Suhaila. Wasu irin ƙuraje ne suka feso mata a jiki kamar ƙurajen da in ana zafi yake fito wa mutane, sai dai jikinta ya yi mugun zafi kanta kuma sanyi kamar an saka shi a freezer. Haka muka nufi Asibiti da ita ta na mimmiƙe wa a jikina; taimakon gaggawa suka ba ta ta samu ta yi bacci sannan doctor ya kira mu ciki.. ce mana ya yi kawai wasu ƙuraje ne suka feso mata masu saka zafin zazzaɓi har ma su shanye ruwan jikin mutum, ƙarshe ma har da jini; magani ya rubuta mana muka saya kwanan mu uku ta samu sauƙi..
Bayan sati ɗaya ya kuma dawo mata muka koma Asibiti aka kuma bamu gado, mun fi sati biyu muna Asibiti kafin ta samu sauƙi muka dawo gida; muna dawowa na takura wa Abbanku na ce sai mun dawo gida gara ayi mata maganin gargajiya, bai musa ba ya nemi a masa transfer zuwa Nigeria ga halin da ƴarsa take ciki. Da ƙyar da sidin goshi suka yarda dan sun ce su gaskiya aikinsa mai kyau ne in ma kuɗi yake buƙata zasu linka masa akan wanda suke biyan sa, shi kuma ya ce musu a'a kawai dai zai koma Kasar su ne sannan suka masa transfer. Yana faɗa mini na miƙe na haɗa kaf kayanmu a cikin akwatuna na shiga na yi wa Maman Aruf sallama, har da kuka na rabuwa da juna dan mun shaƙu ba kaɗan ba. Haka na tubure na ce ranar za mu tafi a lokacin an yi la'asar, ticket ya nema mana na jirgin dare sai ma muka ci sa'a akwai na ƙarfe shida ba ɓata lokaci muka wuce zuwa airport...
A Kano muka sauka daret muka wuce gidanmu, sai bayan mun huta ne na kira Maman Sani na sanar da ita mun dawo gida; sai gata sun zo ita da yaranta uku Sani da Maryam da Ma'ida... Bayan kwana biyu muka tafi Kaduna muka zaga dangi kowa sai murna yake idan yaji an ce an yi wa Abbanku transfer ya dawo Kano da aiki; sati muka yi sannan muka tafi ƙauyen su Inna Laure. Kamar ta goya mu ,Suhaima kuwa dama ba ta yardar kowa ya taɓa ta ta na lafe a jikina, amma abin mamaki muna zuwa ta bar jikina ta koma gurin Inna Laure ta goye ta duk da ta girma amma haka ta goya ta.. Ranar Abbanku ya koma ni kuma sai da muka yi kwana uku sannan muka soma shirin dawowa, ai kuwa Suhaima ta ce ba ta san maganar a raba ta da Innarta ba ; kasancewar magani muke nema sai na keɓe da Inna Laure na faɗa mata ga abin da yake faruwa da Suhaima, amma zan barta a nan a nema mata maganin gargajiya ko Allah zai sa a dace.. Inna Laure har kuka ta yi na barta muka dawo gida ni da Suhaila.
Ranar Monday aka mayar da Suhaila School amma kullum mita take yaushe Suhaima za ta dawo, sai na ce mata sai zuwa sati za a kawo ta...
Alhamdu Lillah da taimakon Allah da taimakon surukin Inna Laure Malam Habu; Suhaima ta samu lafiya watan ta uku a can ana mata rubutu ta na sha ana shafa mata rass Allah da ikonsa ya ba ta lafiya.. Haka aka dawo da ita naji farin ciki ganin yadda ta yi sharr abin ta, Suhaila kam jan ta ta yi aka kaisu gidan Abdallah sai murna take.
Tun da aka kawo Suhaima ba ta taɓa fita ba ko ta yi wani abu makamancin wanda ta dinga yi a Ghana; amma duk da haka Inna Laure sai ta bada magani an kawo mata har da rubutu, sosai suka shaƙu da an musu hutu ita ta ce ƙauye za ta tafi, ita kuma Suhaila sai ta ce ba ta zuwa ƙauye ta wuce Kaduna gidan Ƙanwata..
Wata rana muna hira ni da Abbanku na ce da shi.
"Yanzu dai Alhamdu Lillah Abban Suhaila komai yana tafiya lafiya, amma ba ka tunanin wannan abin da yake faruwa da Suhaima ko yana da gami da alhalin ta? Ni fa ina jin tsoron kar wata rana asirin mu ya tonu gashi ba wanda muka sanar wa da maganar nan sai iyayenmu kawai suka sani."
Kallona ya yi shi ma ya cè.
"Gaskiya da dai abin na bani tsoro, ballantana ita a cikin jinin haihuwar ta dan rashin imani irin na mutane aka jefar da ita, ko mai ta yi wa wanda ya mata haka? Kawai ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alkhairi tun da an yi wa tufkar hanci."
Na gamsu na bayanin sa na na ce.
"Haka ne ni fa ina tunanin aljannu ne ta kwaso A MAƘABARTAR nan, amma dai tun da Allah ya raba ta da su Alhamdu Lillah za mu ce."
"Umma waye ba shi da lafiyar?"
Da sauri muka juyo jin muryar Suhaila a bakin ƙofa; sosai na tsorata na dube ta na ce.
"Me kika ji muna cewa?"
Fuska a dame ta ce.
"Umma na ji kun ce wai Suhaima ta na ciwo to ba ku so ta sani ne?"
Ajiyar zuciya na sauke jin ba ta fahimci komai ba sai kawai na ce mata ta iso ciki, zaunar da ita na yi na soma tsara mata magana ta yadda za ta yarda da maganar.
"Suhaila 'yar'uwarki wani ciwo ne take mu kuma ba ma son ta sani?"
"Wani ciwo kenan? "Ta faɗa ta na zaro idanu.
"Yawwa kin san ciwon zuciya ko?"
Gyaɗa mini kai ta yi na ci gaba da magana.
"To shi ne take ɗauke da shi tun kuna ƙanana, to shi ne bama so ta sani dan kar ta saka kanta cikin damuwa; idan har ta sani ba za ta yi farinciki ba kuma ƙarshe ma zuciyarta ta buga ta mutu."
Dafe ƙirji Suhaila ta yi ta ce.
"A'a Umma kar a faɗa mata ku ɓoye ya zama sirri daga ni sai ku