Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 38049 words

Chapter 3 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

408

Ads at the middle of Article

suka bayyana a kan fuskarta, jiki ba ƙwari ta miƙe tsaye a lokacin Abba ya bar ɗakin sai Na'im da yake tsaye yana kallon yayar tasa cike da tausayawa. Fita suka yi tare da rufo mata ƙofar, Suhaima ta yi shuru surar mata da mijin data gani sun tsaya mata a rai sai tambayar kanta take.
"To su kuma wannan su wane ne? Sannan me ya sa suke tambayata na gane su?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta na shaƙar numfashi ta lumshe idanunta zuciyata ta cunkushe komai ya tsaya mata cak, nemen mafita kawai take ta na son ta gano maƙasudin haɗin ta da maƙabartar da take gani, da kuma aljana Janu me ta aika mata duk ta hana ta sukoni a rayuwarta..
Juyi ta yi da koma gefe sai ta ji ta rungumi wani abu , da sauri ta buɗe idanunta ta yi arba da jariran nan kwance gabanta sun ƙura mata idanu wannan karon suffarsu da dama-dama irin ta mutane ce.. Da hanzari ta janye jikinta ta na tashi zaune ta zuro ƙafafunta za ta sauka ta ga ɗayar gaf da ƙafarta ta na shafa mata ƙafar, Wani irin sautin murdawa cikinta ya bada ƙuuuuu! Ji ta yi kamar ta yi zawo a jikinta da sauri ta janye ƙafar ta haɗe ta da ƴar'uwarta ta na haki..
"Kada ki ji komai yau ba za mu ba ki wahala ba, mun zo ne mu tayaki hira ya ke Mama. "
Jaririyar ta faɗa ta na dawowa kan gadon ta ɗane kan cinyar Suhaima ta kwanta luf kamar wacce za a shaya nono; ganin haka shi ma ɗayan ya kwanta a ɗayar cinyarta suka dinga kallon ta suna murmishi.. Suhaima ko motsi kasa yi ta yi ganin sun haye mata cinya ta sume daga zaunen da take, macen ta dubi ɗan'uwan nata ta ce.
macen ta dubi ɗan'uwan nata ta ce.
"Kai Mama fa ta suma."


"To tashe ta mu yi sauri mu koma. Ya ba ta amsa yana zama; Gefe ta kalla sai ga ruwa daga samar kan Suhaima yana zuba kan fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe idanunta ta ga sun yi mata cirko-cirko duk sun yi fuskar tausayi suna kallon ta.
"Ku wai su waye?
Ta tambayesu jiki na ɓari tsoro ya cika mata ciki ganin jarirai na magana .
Macen ta matso ta kwanta a jikinta ta lumshe ido Suhaima ta kwalalo idanu waje kafin ta motsa shi ma ɗayan ya kwanta a jikinta, macen ta ɗago daidai fuskar Suhaima ta ce.
"Mama Baba na gaisheki."
Baki da hanci Suhaima ta saki ta na nanata sunan Mama a zuciyarta, wai kuma Baba na gaisheta ta yi ta maza ta ce.
"Waye kuma Baba? "Ta faɗa cikin nuna mamaki da al'ajabin wannan jarirai.
"A MAƘABARTA yake shi ma ya ce mu zo mu gaisheki. "Cewar namijin yana kallon ƴar'uwarsa; sake kashe ta suka yi da mamaki ta yi kim ta na tunanin to waye shi Baban da suke cewa ya ce su gaishe ta? Sannan ma meye haɗin ta da su da suke zuwar mata bayan wannan muguwar aljanar?
"Mama ki daina tunani dayawa za mu taimakeki, muna son mu rabaki da Janu kar ta kashe mana ke, amma dole sai mun shiga mun karanci tunaninki da komai naki sai mu faɗi daga inda matsalar take. "Namiji ya faɗa yana gyara kwanciyar shi a kan ƙirjinta...
Jin abin da ya faɗa ba tunanin komai ta ce.
"Na yarda ku bincike tarihin rayuwata in dai hakan zai sa wannan muguwar ta rabu da ni na zauna lafiya, sannan ku ba ku faɗa mini su waye ku?" Murmishi suka yi a tare suka ce.
"Ba buƙata yanzu ki ji su waye mu har sai mun yi miki abin da ya kawo mu daga baya za mu faɗa miki, Baba ne yasa mu taimake ki ya ce ya bamu dama mu yi komai dan mu rabaki da Janu." Jinjina musu kai ta yi ji ta yi ba ta jin tsoron yaran ta sakar musu murmishi, ganin haka yasa macen ta ce. "Rufe idanunki Mama."
Ba muso ta rufe idanun su kuma a tare suka sa 'yan yatsunsu ɗai-ɗaya a gefen kanta suka danna, shuru Suhaima ta yi jin wani abu ya ɗan soke ta kamar haki. Basu fi sakan ashirin ba suka ce ta buɗe idonta, buɗewa ta yi ta na kallonsu za ta yi magana suka rigata cewa. "Mun tafi lokacin mu ya ƙare kar Janu ta gane muna bibiyar ta." Kai kawai ta ɗaga musu a gaban idanunta suka ɓace ta ɗan ji tsoro sai dai ba sosai ba, lumshe idanu ta yi sai yanzu ta tuna da addu'a ta shiga karanto Ayatul kursuyu har bacci ya ɗauke ta...


Washe gari Suhaima ta tashi da zazzaɓi amma hakan ta daure suka tafi gidan Uncle ɗin ta.
Koda suka je kasa yi wa kowa magana ta yi ba e ba a'a, duk abin da take Umma na ankare da ita har aka yi sallar Azuhar ba ta saki jikinta ba; jin zazzaɓin na ƙara ƙarfi yasa Suhaima ta kalli Mommy ta ce. "Mommy zan kwanta."
A sanyaye Mommy ta ce.
"Shiga ɗakin part ɗin Sani akwai ɗaki ɗaya sai ki kwanta a can nan mutane ne." Jinjina kai ta yi ta miƙe da ƙyar ta nufi hanyar da za ta sada ta da part ɗin Sani; a hankali take tafiyar kanta na sara mata ta kai hannu ta dafe goshinta ta shige part ɗin.
Ɗakin ta shiga ta kwanta a kan gadon ta lumshe idanu. Ta na rufe idanu ta bacci ya ɗauke ta; kamar jira ake ta rufe idanun sai ga ta a kan hanya ta na ta buga sauri .
Da gudu ta miƙe wata hanya ta yanka cikin dajin ta ci gaba da gudu ta na waiwayen bayanta, turus ta ja ta tsaya ganin ta a gaban get ɗin maƙabartar da take yi wa gudu a baya. Jiki na rawa ta kuma falfalawa da gudu tamkar motar da ta sha mai, sai da ta yi nisa sosai ta ji ba ta jin hucin abin da yake binta ta sunkuya ta na haki a wahalce; dan ba ƙaramin gudu ta ci ba.
Ɗago kai ta yi da nufi ta ci gaba da gudu ta kuma yin arba da maƙabartar a gabanta get ɗin ma a buɗe wayam, kwalalo ido waje ta yi ta na yin baya ganin yadda ƙaburburan suke motsi kamar wani abu zai fito daga ciki; tamkar wadda aka dasa a wajan ta kasa motsa ƙafarta sai kallon cikin maƙabartar take cike da firgici. Wani kalar ɓakin hayaƙi ne ya dinga fitowa daga cikin ƙaburburan yana haɗuwa waje ɗaya, Suhaima ta kasa guduwa ta na son ta motsa amma gam an riƙe ƙafar tayi-tayi ta kasa ɗaga ƙafar; hayaƙin na taruwa ya nufo ta gadan-gadan ta ƙwalla ƙara ta na jiran zuwan wannan annoba ta iso gareta dan ta saddakar yau dai kashe ta za su yi.
Kamar daga sama ta ji ana faɗin.
"Suhaima! Ki matsa sauri."
Da sauri ta yi ƙoƙarin daga ƙafar tata ai kuwa ta ji ta ɗago, a 380 ta fankaya da gudu wannan hayaƙin na bin ta, ji ta yi an ɗauke ta an cilla ta gefe ta faɗi timm Kamar ba ta ji ciwo ba ta miƙe tsaye sai ta ga wani farin haske na tunkaro ta.
Baya ta soma ja ta ji an yi magana da ƙarfi.
"Ki tsaya!"
Aka faɗa ta ja birki ta tsaya numfashinta na sama da kasa, kamar an ce ta kalli gefen ta ga wannan ramin mai macizai a bayanta; da sauri ta yo baya hasken ya ƙaraso gareta ta na kallonsa , jariran suka bayyana ta musu kallon mamaki ta ce.
"Kuma kenan kuna son ku kasheni?"
"A a Mama za mu ceceki dai sannan mun gano miki maƙasudin matsalar dake tsakanin ki da Aljana Janu "Suka faɗa a tare."
Baki na rawa ta ce.
"Ku taimaka ku faɗa mini kun ji."
Macen ta ɗaga baki za ta yi magana Suhaima ta ji ana bubbuga pilon da ta kwanta a kai;
A zabure ta tashi ta na zare idanu kanta ya yi mata mugun nauyi Kamar an daura mata ƙaton dutse a cikin kan haka take ji, da ƙyar ɗago ta kalli wanda ya katse mata bacci da maganar da take son ji wadda za ta kawo mata mafita; ganin Na'im ne haushi ya kama ta ta ja tsaki ta ce.
"Dalla can malam ka wani tasheni ina bacci."
Shi ma Na'im harara ya aiko mata ya ce.
"Ƴar rainin hankali yo dan na taimakeki ma shi ne kike ja mini tsaki Kamar wata tsaka, to ki tashi har an yi la'asar kina baccin asara kasa kawai, ke bakya gajiya da bacci ne."
"Tsuwww! To matsa ka bani guri ko in bangaje ka na wuce futsararre kawai ina yayarka amma kake ce mini Ƴar ranin hankali dan ka ɗaukeni kamar wata ƴarka ko? Wallahi sai na haɗa ka da Abba ya mana tsakani ɗan'iska kawai."
Banza ya mata ya juya ya wuce bai ce mata komai ba...


Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta nufi gurin su Umma ta gabatar da Sallah. Tun kafin ta ƙarasa yin salatin Annabi (s.a.w) jikinta ya ɗauki rawa ta maƙure a jikin bango ta na kallon 'yan ɗakin, Umma data shigo yanzu ta kai kallon ta kan Suhaima ta ga idanun na lumshewa da buɗewa; da sauri ta ƙaraso gareta ta ɗago da ita ta na kiran sunan ta.
"Suhaima me ya sameki? Zazzaɓi kike ji?"
Umma ta faɗa a rikice ganin ɓakin idanunta suna sama sai farin kawai. 'Yan ɗakin hankalinsu ya yo kan su wata mata ta ce .
"To ku kaita Asibiti mana dan da alama ta na jin jiki sosai." To Umma ta ce ta soma ƙoƙarin tayar da ita amma ta kasa saboda ta saki jiki, wasu daga cikin matan suka taimaka mata suka ɗauke ta aka firo da ita sharaf-sharaf kamar gawa.
Waya Umma ta buga wa Abba sai ta ji Na'im ya ɗauka, kafin ya yi magana murya na rawa ta ce.
"Ka turo Na'im ya kaimu Asibiti Suhaima ba ta da lafiya."
Da sauri Na'im ya miƙe tsaye ya amsa mata da to ai shi ne ma ba Abban ba sannan ya kashe kiran ya yo inda suke; suna fitowa yana isowa ya buɗe motar suka saka ta zuwa lokacin jikin Suhaima ya yi tsanani sosai zufa sai tsatstsafo mata take a goshinta,. Suna shiga aka buɗe musu ƙofar suka bar gidan....












_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/2 21:43] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_














Daga Alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_






SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*


بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣5️⃣




Cikin ikon Allah suka isa Asibitin Murtala, Na'im da kansa ya ɗauketa da sauri ya nufi ciki yana kwaɗawa Nurse kira, yana isowa ciki suka amshe ta suka nufi emergency room da ita.
Umma ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake wajan ta na goge hawayen tausayin Suhaima;
Safa da marwa Na'im ya dinga yi ganin abin ba na tsayuwa ba ne ya iso kusa da Umma ya durƙusa a gabanta ya ce.
"Haba Umma ba fa mutuwa ta yi ba."
Ɗago kai Umma ta yi a sanyaye ta ce.
"Ina jin tsoron Suhaima ta gano abin da muka ɓoye mata bana son rabuwa da ita Na'im. Ka na ji abin da take cewa wai za ta shiga duniya indai ta gano mun ɓoye mata wani abu."
Cike da rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa yake kallon ta, wato kenan akwai abin da suke ɓoye mata to mene ne shi abin da suka ɓoye mata? In ko haka ne shi ma zai so na ji wannan ɓoyayyen sirrin da suke rufewa. Tashi ya yi ya dawo kan kujera ya fuskanci Umma ya ce.
"Umma kenan mafarkin Suhaima take ba ƙarya ba ne? Me ya sa kuka ƙi faɗa mata abin da kuke ɓoye wa? Ko shi sirrin naku ba me daɗin ji ba ne?"
Ya jero mata tambayoyin da yasa Umma ɗago wa da sauri; sai yanzu ta tuna da saɓutar bakin da ta yi, share fuskarta ta yi ta ce.
"No ba wani sirri ba ne wanda zai gagara faɗi, kasan dai Suhaima da saka damuwa a rai musamman ma mafarkan nan da take yi. Tsoron da nake ji idan ta gano aljannun da take gani a mafarki gaske ne za ta fi haka shiga tashin hankali, abin da ba na fata ya faru shi zai faru shi ya sa na damu."
Shuru Na'im ya yi yana nazarin kalamanta, ita kuwa Umma kawar da kanta gefe ta yi dan kar ya kuma jefo mata wata tambayar..
A can ciki kuwa gwaji suka shiga mata nan take suka ga ba ta da jini ya zo matakin ƙarshe, ruwan jikinta ma ya ƙare, ruwan suka ɗaura mata suka mata allurorin da za su taimaka mata kafin asa mata jinin. Ɗaya daga cikin Nurse ɗin ce ta juya ta bar ɗakin da sauri Doctor na mata bayani ta ɗauki wata takarda ta wuce; a tsaye ta gansu ganin ta yasa suka yo wajanta suna tambayar ya mai jik? Kallonsu ta yi sannan ta soma musu bayani.
"Hajiya muna buƙatar jini da gaggawa ba ta da jini kwata-kwata, ku samo wanda za a ɗiba a jikinsa ko kuma ku saya in aka wuce minti 20 ba'a sa mata to gaskiya komai zai iya faruwa."
"Doctor muje a gwada nawa idan ya zo daidai da nata sai a sa mata, idan kuma bai zo ba za mu saya kawai."
Cewar Na'im yana matso wa kusa da Nurse ɗin; nuna masa inda zai shiga a gwada ta yi ta na jadadda masa ya hanzarta ya amsa da to sannan ya wuce, Umma kuwa komawa ta yi gwajab ta zauna ta rafka tagumi ta na ƙara jin tausayin Suhaima...


Cikin ikon Allah aka gwada jinin Na'im ya zo daidai da na Suhaima, ba ɓata lokaci suka ɗibi leda biyu; wata Nurse aka miƙa wa ta amsa ta wuce da sauri.. Sai da Na'im ya jima a zaune sannan ya tashi ya nufo inda ya bar Umma; da sauri tare sa ta na faɗin.
"Ya ya Na'im an dace kuwa?"
Jinjina mata kai ya yi hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna; shi ma zaman ya yi sai ga Suhaila ta shigo mayafi a hannu ta na rusar kuka ta zauna a ƙasa hannunta a bisa kanta ta soma magana.
"Kin gani ko Umma? Dama sai da na ce kar ku faɗi maganar da za ta tarwatsa mata zuciya amma shi ne kuka sanar da ita? Yanzu a wani hali take ciki Umma?"
Na'im ya yi shuru gabaɗaya duk sun kulle masa kai, yana tambaya a cikin zuciyarsa; wai wani abu ne wanda ake tsoron faɗa wa Suhaima wanda shi ma a iya tunaninsa bai sani ba?
Girgiza kai ya yi ya dubi Suhaila wacce har yanzu ba ta daina kuka ba ya ce.
"Malama ki mana shuru kin shigo mayafi a hannu kamar rainon 'yanmata, kuma meye ba ku so ku faɗa wa Anty Suhaima? Ni fa kun ɗaure mini kai da yawa ki fahimtar dani Umma."
Mayafin ta ɗauka ta yafa ta lulluɓe jikinta sannan ta kalli Umma da ta ƙura mata idanu ta ce.
"Umma ki yi wa wannan ɗan rainin hankalin magana ni ta ƴar'uwata nake yanzu bani da lokacin yin faɗa da shi, in ban da ma ka rainani ni yayarta ce ta biyu amma so kake ƙarfi da yaji kai ka koma babba dan ka ga ka girma ka fimu tsayi ko? To ka fita idona karka sake tambayata."
Ta ƙarashe ta na tsuke bakinta dan kar ma ya sake faɗa mata magana..
Kwafa ya ja dan ya lura basa son shi da Suhaima su san abin da suke ɓoye musu, ita kuwa Umma lokacin da Suhaila na magana kaɗan ya rage ta rufe mata baki jin ta na neman kira musu ruwa; itama kanta Suhaila gane za ta yi katobara ya sa ta rufe Na'im da faɗa ta ci sa'a kuma bai ce komai ba...


Sai gaf da Magariba likitocin suka fito daga pɗakin su uku biyu mata ɗaya namiji suna biye da shi a baya, suna ganinsu namijin ya tsaya a gurin su Umma ya ce.
"Ku biyoni Office."
Na'im ya bi bayansa su kuma suka zauna zaman jiransa; bayan sun zauna Doctor ya shiga masa bayani dalla-dalla..
"Babu wata matsala mai yawa kawai dai ta firgita ne ko na ce ta ga abin da ya firgitar da ita, hakan ya haddasa mata bugawar zuciya da zazzaɓi mai zafi sosai har ruwa da jinin jikinta suka ƙare. Amma Alhamdu Lillah abun ya zo da sauƙi zan rubuta maka magunguna sai take sha in sha Allah za ta warware, amma fa kuke kulawa da ita sosai kar ta kuma firgita da taimakon Allah numfashinta ya daidaita."
"To in sha Allahu Doctor hakan ba za ta sake faruwa ba, na gode sosai."
Cewar Na'im yana miƙa hannu suka sallama sannan ya kuma cewa.
"Za mu iya ganinta?"
"E amma sai gobe in sha Allah za mu sallame ku.. Miƙe wa ya yi ya fita zuciyarsa na wasi-wasin lamarin gidan nasu.
Bayan ya dawo ya faɗa musu yadda suka yi da Doctor suka mata fatan samun lafiya, Abba ya kira suka ce bacci take sannan suka shiga ciki. Kwance suka ganta kamar gawa hannu ɗaya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads