Showing 12001 words to 15000 words out of 38049 words
Chapter 5 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt
ne; ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Ranar da kuka zo kun ce za ku faɗa mini matsalata , to yanzu ina jiranku ku bani amsa me kuka gano game da mafarkin da nake da wannan muguwar kun ga jiya ma har yankar jikina da dinga yi ta na shan jinina, ta na gaf da kasheni sai ga wani ya zo ya ceceni amma ban san shi ko waye ba dan yaƙi yin magana ballantana na ga fuskarsa."
"Mama kamar yadda Janu ta faɗa an mallaka mata ke ta sha jininki ta yi yadda take so da ke; idan ta so za ta iya sarrafa zuciyarki take amfani dake ta na cutar da mutane dan dama halinta kenan. Yanzu haka ta na nan ta na son taga bayanki abin da yasa ma ba ta samu damar yin hakan ba muna lalata wasu abubuwan da take yi ne a kanki, amma ba dan haka ba da tun shekarun baya za ta yi abin da takeso da ke.."
Kallon rashin fahimta Suhaima ke yi wa yaran, tsoro, mamaki, al'ajabi, tashin hankali, duk sun tattaru sun kawo mata ziyara a lokaci ɗaya ta numfasa ta ce.
"To waye ya mallaka mata ni?"
Kallon kallo yaran suka dinga yi wa juna ganin haka yasa idanun Suhaima kawo ruwa ta soma magana.
"Kun yi shuru ba ku ce dani komai ba, waye ya mallaka mata ni kuma meye haɗina da wanda ya mallaka mata ni?"
"Mama indai har kina so ki san hakan to ki fara tambayar su Abba su faɗa miki abin da suke ɓoye miki, idan sun faɗa miki mu kuma zamu ƙara binciko miki komai. A halin yanzu dai muma ba mu san waye wanda ya sadaukar da jininki ga aljana Janu ba; Baba ya sani amma yaƙi faɗa mana."
Namijin ya faɗa yana kallon Suhaima da jikinta ya yi sanyi; Tsayar da hawayen ta yi ta ce.
"To ya zan yi ? Umma da Abba sun kasa faɗa mini abin da suka ɓoye taya zan gano bakin zaren matsala ta ne?"
Ta faɗa ta na kallon su; Hayewa jikinta suka yi suna goge mata hawayen ita kam Suhaima ba shiri ta kallesu jin yaran sun yi nauyi, hannu ta kai ta rungume su ta soma magana.
"Har yanzu ba ku faɗa mini sunanku ba, idan har da gaske ni mamanku ce to ki faɗa mini sunayenku."
"Sunanmu Ayan da Iman Mama kuma ke mamanmu ce.
Macen ta faɗa ta na kallon Suhaima; murmishi ta yi ta daga baki za ta yi magana taji ana buga ƙofar, zaro idanu ta yi ta ce. "Kun ga ana buga ƙofa ku tafi sai mun sake haɗuwa."
Ayan ya ce.
"Ba sai mun tafi ba Baba ya ce mu jima ya bamu lokaci mai yawa." Ita dai Suhaima shuru ta yi ta na kallon ƙofar, buɗe ƙofar ta yi ta shiga da sallama ta na cewa.
"Ke ƴar nan yanzu kina jina ina buga ƙofa amma kin kasa tashi ki buɗe mini?"
Kallon su Ayan dake lafe a jikinta ta yi, ta ce. "Inna na gaji ne kasa tashi na yi amma dai a nan za ki kwana ko?"
"Kwarai ma kuwa ina so mu tattauna ne naga duk kin rame sosai, wani lokacin ma sai ki yi tagumi me ke damunki ne?"
Ba ta ɓoye mata komai ba ta faɗa mata duk abin da yake faruwa da ita, sai dai itama ba ta ce mata ta yi mafarkin an kashe Uncle ɗinta ba. Riƙe baki Inna Laure ta yi ta na gyaɗa kai ta ce. "Ikon Allah yo ke kuwa Suhaima me ya haɗaki da mafarkin aljannu?"
"Mama ki tambayeta abin da Abba suka ɓoye.
Taji muryar Ayan na magana; jinjina kai ta yi ta ce.
"Inna wai kin san wani sirri ne da su Abba suka ɓoye mini?" Da mamaki Inna Laure ta dube ta ce. "Wani irin sirri kuma Suhaima? Dama akwai abin da suka ɓoye miki wanda kike son sani ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"E Inna akwai dai abin da basa so na sani."
To ki yi haƙuri gobe ni zan tasa shi Mukhtar ɗin gaba sai ya faɗa miki abin da kike son sani, ni
ba na son ganinki a cikin damuwa kwanta ki huta gobe za ki sani."
Baya ta yi ta kwanta su Ayan na manne a ƙirjinta suna jin su.
Sai da suka ga ta soma jin bacci suka ɓace daga jikinta...
Aljana Janu ce zaune a maƙabarta ta tasa Suhaima a gaba fuskarsa har fitar da wani hasken wuta take saboda ɓacin rai, a fusace ta miƙe tayo kan ta sai dai ta na zuwa gef da ita aka yi sama da ita aka watso ta gefe. Cike da mamaki take kallon Suhaima taga ba kowa a tare da ita, idanunta ne ya sauka a kan zoben dake yatsar Subaima sai haske take, manya-manyan idanunta baƙaƙe ta zaro ta ce.
"Ke! Wa ya ba ki wannan zoben?"
Ita kuwa tuni ta firgice sakamakon arba da idanun aljana Janu da ta yi, zata sake yi mata magana wata ƙatuwar macijiya ta ɗauketa ta yi sama da ita...
Futsarin da ya matse ta ne ya farkar da ita, da sauri ta kalli zoben dake tsayarta ta na mamaki yadda zoben ya ba ta kariya; miƙe wa ta yi ta shige toilet jin ana kiran salla...
Takwas duk Inna Laure ta kira su Abba ɗakin Suhaima shi da Umma suka shigo tare da Na'im da Suhaila. Kallon Abba ta yi ta ce.
"Mukhtar ka saurareni da kyau."
Sunkuyar da kai Abba ya yi ya ce. "To Yaya Laure ina jin ki."
"Ina so ku faɗa wa yarinyar nan abin da kuka ɓoye mata wanda ni kaina ban san da wannan sirrin ba.."
Dam! Ƙirji Umma da Abba da Suhaila ya buga,, ya kalli Inna Laure ya ga ba wasa nan ya ƙara tabbatarwa kansa yau dai abin da ya ɗauki shekaru yana ɓoye wa sai ya faɗa, sirrin da ya ɗauki shekaru yana ɓoye wa saboda farin cikin Suhaima amma yau gashi ta haɗa shi da wadda ba zai iya mata wayo ta bar maganar ba.
Gyara zama ya yi ya ce.
"Ki gafarceni Yaya Laure da ban sanar da ke wannan maganar ba."
"Ina jinka maza ka faɗa mini.
"Yaya Laure Suhaima ba mu bane asalin iyayenta, m.. bai ƙarasa ba Suhaima ta ƙwalla ƙara sai gata a gaban Abba ta damƙi ƙafarsa cikin tsananin tashin hankali ta ce..
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/7 14:32] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣7️⃣
Cikin tsananin tashin hankali ta ce.
"Ab..Abb.. Abba don Allah ka ce dani mafarki nake kamar yadda nake yi kodayaushe."
Tamkar wata zautacciya ta juyo ga Inna Laure data saki baki ta na kallon Abba da ya sadda kai ƙasa, faɗa wa jikinta ta yi sai yanzu taji wani irin kuka ya zo mata ta soma yi wa Inna Laure magana.
"Innata kin gani dan na ce sai na san abin da suka hana na sani, shi ne Abba ya faɗi wannan mummunar kalmar wadda ko a mafarki naji ta ba zan sake komawa bacci ba. Innata don Allah ki ce masa na haƙura da jin maganar ba zan sake tambayar su ba har numfashi ya ƙare , Inna ki yi magana mana."
Ta ƙarashe maganar da ƙyar ta jan numfashi. Kafin Inna Laure ta ɗaga hannu tuni ta saki jiki a jikinta alamar suma ta yi; hankali a tashe Inna Laure ta soma jijjiga Suhaima amma shuru kake ji babu alamar motsi, ɗago da idanunta ta yi wanda ya yi jajur saboda tashin hankali ta dubi su Umma da ko ƙwaƙƙwaran motsi sun kasa yi, baki na rawa ta ce.
"Na..Na'imu kawo ruwa don Allah kar su kashe mini 'yata."
Jiki ba ƙwari ya miƙe ya nufi freezer ɗin ɗakin ya buɗe ya fito da ruwan ya kawo mata har ya fara ƙanƙara; shi kansa ya shiga ruɗu, tashin hankalin da yake ciki ji yake kamar shi ne aka ce ba ɗan Abba ba ne, tunanuka sun masa dirar mikiya masu cike da tambayoyi kala-kala. Indai har ba Abba ba ne mahaifin Suhaimar sa to waye ya haife ta? Sannan me ya sa suka yada ta? Anya kuwa Abba gaskiya yake faɗa musu?"
Na'im ya faɗa a cikin ransa bai san maganar ta fito fili ba sai jin muryar Inna Laure ya yi ta na amshe zancen nasa.
"To ka dai tambayar mana shi Na'imu wannan ai masifa ce mai rawani, kai yanzu Mukhtar so kake ƴar taka ta mutu ko? To Wallahi sai na yi ƙaran ka Hisba sai sun bi mata haƙƙinta na sumar da ita da ka yi, wannan ai makasar ta kake nema. Ka faɗi abin da yarinya take son sani wanda ya danganci mafarkinta ba wai ka tsoratar da yarinya ba da wannan ɓakar kalmar, bani da mutumci Mukhtar ka sani Wallahi zan ci kwalarka na zazzabga maka mari, shin za ka yi magana ne ko sai na yi maka dakan tsakwara ne?"
Ta faɗa tana fashewa da kuka, ita kanta hankalinta a mugun tashe yake da maganar ta Abba, taya ma zai ce wai basu bane asalin iyayen ƴarta Suhaima wadda duk yaransa tafi son ta fiye da su Na'im..
A sanyaye Abba ya ɗago ya kalli Inna Laure da take kuka wiwi ta na shafa fuskar Suhaima wadda sai a lokacin ne numfashi ya dawo, amma sam ta kasa buɗe idanu.
"Yaya Laure babu abin da muke ɓoye wa Suhaima illa wannan sirrin, tabbas Suhaima ba mu muka haife ta ba hasalima ba a ƙasar nan muka tsinci Suhaima ba."
Zabura Suhaima ta yi jin kalmar Abba take tamkar ana zuba mata ruwan wuta a ko wata kafa ta jikinta, kallon Abba ta yi zuciyarta na mugun bugawa ta ce.
"Abba!" Ta faɗa da wata iriyar murya wadda duk wanda yaji yasan mai maganar ya kai ƙarshe a tashin hankali; Suhaila ta dubi Umma ta ce.
"Umma wai da gaske ne maganar da Abba yake magana a kaina? Don Allah ku fitar damu cikin duhu kar zuciyata a buga, taya za ku ce wai ba ku bane iyayen Suhaima dani aka je asibiti lokacin da za a haife ta kuma aka fito da ita ni na fara rungume Suhaima a lokacin, amma yanzu ku fito da wannan maganar wani lefi ta aika a gareku kuke son hawan jini ya kama ta lokaci guda?"
Umma ta goge hawaye ta dubi Inna Laure ganin Abba ba zai iya magana ba ta ce.
"Suhaima ki tashi ki ji sirrin da muke ɓoye miki wanda bama son ko a mafarki kiji, an ce ranar wanka ba'a ɓoyan cibi dan haka yau ni zan sanar dake komai."
Saurin tashi Suhaima ta yi jiki na rawa ta tabbata dai ba su suka haife ta ba kenan?
"Waiyo Allah rayuwata to su waye iyayena Umma?"
Ta faɗa jikinta na rawa har sai da Inna Laure ta riƙe ta ganin ta na neman faɗuwa.
Gyara zama Umma ta yi ta soma magana hawaye na sauko wa daga cikin idanunta. .
Shekaru ashirin da bakwai da suka wuce, ni da mijina mun yi auren soyayya; asalin mu 'yan garin Kaduna ne iyayenmu suna Hayin rigasa. Mijina su uku ne a wajan iyayensu Inna Laure sai Abbanku sai Abdallah. Suna da haɗin kai sosai ita Inna Laure kasancewar dangin babanta suka riƙe ta ba a Kaduna ta zauna ba a can Katsina take a wani ƙauye, a nan aka mata aure shi ya sa ba sosai take zuwa Kaduna ba dan ba ta saba da iyayenta ba; ba ta taɓa haihuwa ba amma ba ta damu ba ko kaɗan ni kuma ina jin tausayinta sosai a lokacin ina amarya. Wata na goma da aure na samu ciki ranar an sha murna a dangin mijina da ma nawa dangin, cikina na isa haihuwa na haifi mace kyakyawa mai kama da mahaifinta. Ranar suna yarinya ta ci sunan surukata wato Saudat muke kiranta da Suhaila; haka muka ci gaba da kulawa da ita a lokacin Abbanku ya gama karatu yana koyar da yan jami'a dan aikin da yake so bai samu ba sai ya amshi koyarwa. Ya karanci ɓangaren computer ne, to da bai samu aikin ba sai ya nemi na koyarwar; sai da Suhaila ta yi shekara da haihuwa sannan ya samu aiki a nan Kano.
Tun da muka zo Kano ban san kowa ba ni kaɗai nake zama sai sannu a hankali na sama da maƙotana; ana haka Abbanku aka tura shi ƙaro karatu a ƙasar Ghana. Ranar na yi murna ganin yadda hanyar samu take zuwan mana a lokacin kuma na yaye Suhaila Inna Laure ta zo ta ɗauke ta suka tafi ƙauye sai bayan wata ta dawo da ita. Muna ta shirin tafiya Ghana Abdallah ya kira Abbanku ya ce matarsa ta haifi ɗa namji, ai kuwa mun sha murna sosai kasancewar saura kwana goma mu tafi sai muka shirya ana saura kwana biyu suna muka tafi wajan suna. Washegarin suna na tafi gidanmu na musu sallama, sun so na bar musu Suhaila amma na ce babanta ba zai bari ba suka haƙura muka dawo; da Yamma lis muka shirya 'yan'uwa suka mana fatan alkhairi sannan muka dawo cikin kewar dangi.
Lokaci na cika muka shirya tsaf zuwa muka wuce Ghana cikin farinciki musamman ma ni nafi Abbanku murnar zuwa gari; muna sauka aka zo aka ɗauke mu aka kaimu wani gida, wanda ya kaimu yake sanar da mu anan za mu zauna muka masa godiya ya tafi..
Washegari Abbanku ya fita zuwa wajan aiki, ranar sai dare ya dawo da har na tashi hankalina ganin ƙarfe takwas ta yi bai zo ba hankali a tashe nake tambayar sa.
"Abban Suhaila lafiya dai tun safe sai yanzu ka dawo?"
Sai ya ce dani.
"Aiyuka ne suka min yawa sosai shi ya sa, yanzun ma ba dan na gama na dawo sai gobe."
Jin abin da faɗa sai hankalina ya kwanta..
Haka muka ci gaba da rayuwarmu a Ghana Suhaila ta yi wayo sosai wani lokacin yaran maƙotan mu suke zuwa su tafi da ita, sai zuwa Yamma suke dawo da ita; anan garin Abbanku ya sakani Islamiyar Unguwar da ake zuwa bayan La'asar...
Haka muke rayuwa a ƙasar; har muka kai shekara biyu a ƙasar Ghana, Suhaila a lokacin ta na da shekaru huɗu amma har lokacin ban sake samun ciki ba.. Haka na takurawa kaina akan rashin sake haihuwa na matsa muka tafi Asibiti; ko da muka je aka mana gwaji aka tabbatar mana da lafiyarmu ƙalau kawai dai haihuwar ce ba ta zo ba..
Addu'a na dinga yi ina roƙon Allah ya bani haihuwa dan kullum Suhaila sai ta dinga cewa.
"Umma ki haifa min sister ni ma irin na su Aruf, a gidansu su uku ne ni ma so nake mu zama uku."
Idan ta faɗi haka sai dai na ce mata to kawai na rabu da ita..
Sai da na ƙara wata shekarar biyu sannan na samu ciki; ranar na sha murna sosai daga ni har Abbanku, ko Maman Aruf ban ɓoye mata samun cikin ba; ita ma ta tayamu murna, a lokacin ita ce Ƙawata kuma maƙociyata ta na da kirki sosai kullum Suhaila na gidanta. Haka muka ci gaba da rainon cikin har ya kai watan haihuwa. Wata ranar Lahadi cikin dare ƙarfe 4:30pm ciwo Gadan-gadan ya zo gashi ranar bai kwana gida ba; ƙoƙarin ɗaukan wayata na yi dan na kira shi amma na kasa motsa wa . Ƙarfe biyar daidai na yi na haihu ni kaɗai a cikin ɗaki a kan carpet; ko da jaririyar ta faɗo ba ta yi kuka ko kaɗan ba abin da yasa hankalina mugun tashi.
Rarrafa wa na yi na janyo wayata jikina na rawa dan babu kuzari a jikina; na danna wa Maman Aruf kira sai da ta kusa tsinke wa ta ɗauka cikin mamagin bacci ta ce.
"Hello Maman Suhaila lafiya dai?"
A wahalce na ce mata.
"Na haihu please ki zo."
Ba shiri ta miƙe ta ce gata nan zuwa ta kashe kiran; ta na shigo wa ɗakin sai ga Abbanku ya dawo, a rikice ya kwashe ni da jaririyar Maman Aruf ta ce za ta gyara gurin in ta gama za ta biyo mu a baya.. Muna cikin tafiya mun kusa isa Asibiti motar ta tsaya, hankali tashe ya fito dan ya ga meye matsalar; sai ya ga faci ne tayar gaba duka biyun suka yi, ɗayar tayar ma ta tsage ta na ƙoƙarin fashe wa.
Kamar daga sama naji kukan jaririya ya daki dodon kunnuwana, saurin kallon tawa jaririyar na yi naga ba ita ba ce sai na sauke glass ɗin motar ina waige; can jikin bishiyar bakin hanya na hango jaririyar a cikin zani sai ɗaɗɗaga ƙafafu take. Sake waro idanuna na yi naga dai mutum ne ba idanuna ba ne, juyo wa na yi na dubi Abbanku na ce.
"Abban Suhaila ka ga jariri a jikin bishiyar can yana kuka."
Da sauri ya kalli inda na kalla ya ga abin da nake faɗa masa, wajan ya nufa bakinsa ɗauke da addu'a ya ɗauko jaririyar jinin da aka haife ta a jikinta ko bushewa bai yi ba an dai yanke cibiyar; ya bani ita na ɗaura ta a ɗayar cinyata ya shiga muka wuce Asibitin.. Muna isa aka shiga duba lafiyarmu Doctor na cewa me ya sa na bari na haihu a gida, sai na ce mata.
"Maigidan ne baya nan shi ya sa."
Allura aka mini har da ƙarin ruwa, suma yaran aka zo duba su nan ake sheda mana cewar ɗaya daga cikin jariran sun rasu, a ruɗe na kalli doctor na ce.
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/8 16:15] Ummu Amjad: _*🧟♀️🧟♀️A MAƘABARTA NE 🧟♀️🧟♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin