Header Ads
Showing 36001 words to 38049 words out of 38049 words

Chapter 13 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

418

Ads at the middle of Article

nufa sai ta baza ƙamshin ta take wuce wa.


Misalin ƙarfe 2:pm aka ɗaura auren Suhaima Mukhtar da Hamid Minister Hamza akan sadaki naira dubu ɗari, layin gidan taf ya cika da mutane sosai daga abokan Mahaifin Hamid da na Abba da nasa shi kansa angon, Sani da Na'im ma sun gaiyato abokansu haka zalika su Uncle Sulaiman ma ba'a barsu a baya ba duk wasu abokan kasuwancinsu sai da suka gaiyato su ɗaurin aure, Inna Laure ma ba'a barta a baya ba itama duk yan ƙauyensu sai da ta gaiyato su har da 'yan matan gidansu duk ta haɗo kansu aka kawo su a mota...


Kasancewar Suhaima ba ta da Ƙawaye daga ita sai Aminatu da Suhaila sai kuma friends na school da suka zo mata kowa sanye da anko, tana zaune ya kira ya ce an ɗaura aure ai kuwa ta fashe da kuka, shi kenan za ta bar su Umma ta koma wani guri...


Bayan La'asar aka tafi gurin dinner party; sosai Hal ɗin ya cika sai ga amarya da anko sun shigo, haka aka rakosu har mazaunin su suka zauna aka soma gabatar da abin da ya tara su.
Shuru Suhaima ta yi ta na kallon gefe da gefe can ta hango Sayyid da su Iman zaune a kan kujera suna ɗago mata hannu, wani sanyi ya ratsa ta ta musu alamar da su zo sai suka kalli Sayyid ya jinjina musu kai suka tashi..
Suna isowa ta rungume su suna tayata murna, Hamid ya dubi Suhaima ya ce.
"Sweetheart waɗannan beautiful baby's ɗin fa? Ban taɓa ganinsu ba."
Murmishi ta yi ta nuna masa inda Sayyid yake ta ce.
"Kaga mahaifinsu can sun zo tayamu murna ne."
Kallon inda Sayyid yake Hamid ya yi; saurin juyo wa ya yi ya kalli Suhaima ya ce.
"To ai kama yake dani baban yaran."
Ƴar dariya ta yi ta ce.
"Ranar da muka fara haɗuwa shiyasa na firgita na ɗauka shine."
"Ikon Allah! Ai kuwa zan so ki haɗani da shi mu gaisa.
To Suhaima ta ce su Iman na gefenta a zaune; haka aka dinga shagali sai gaf da magriba aka tashi..


Washegari aka yi walima bayan sallar Isha'i aka kai amarya gidan iyayen ango dake J R.A. Bayan an yi mata nasiha, da murna dangin Hamid suka amshi Suhaima suka mata nasiha suma sannan aka kaita gidanta dake bayan gidan...


Bayan an gama sayan baki ango ya raka amarya ya dawo ya kulle ko'ina sannan ya shigo ɗakin da take lulluɓe da mayafi sai zuba ƙamshi take, wani irin sanyin daɗi ya ziyarci zuciyarsa sakamakon yin arba da hannuwanta wanda suka sha lalle gwanin birgewa.
Lumshe idanu ya yi jin shi yake yafi kowa sa'a da Allah ya mallaka masa Suhaima a matsayin mata, ƙarasowa ya yi kan gadon ya buɗe fuskar tata ya furta.
"Tsaki ya tabbata ga Allah da ya yi wannan halittar."
Murmishi ta yi; ya kamo fuskarta ya yi kissing ɗin ta a kumatu, wani irin yanayi suka ji a tare kowa ya lumshe idanu.
Zuwa can ya umarce ta ta yo alwala, ba ta musa ba ta shige toilet shi ma ya nufi nasa ɗakin.
Wanka ta ta yi ta canja kaya zuwa wasu riga da wando na bacci masu mugun kyau ta ɗaura hijabi ta zauna tana jiran zuwansa, ba ta jima ba sai gashi ya iso ya yi gaba ya tayar da iƙama suka gabatar da nafila su..




Bayan sun gama ya gabatar mata da gasasshiyar kaza, da kansa ya ciyar da ita ta ci ta ƙoshi ta na kan ciyarsa ya goge mata baki sannan shi ma ya ci, bayan ya gama ya ɗauke ta ya kaita toilet suka yo brush suka fito, kwantar da ita ya yi shi ma ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya mata masauki a kan ƙirjinsa.
Tsuru Suhaima ta yi jikinta ya ɗauki rawa, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana rada mata magana a kunne har ya samu ta nutsu, blanket yaja musu ganin yadda take ja baya ya matse a jikinta ta sa masa kuka, kamar bai san ta na yi dan ya manta a ina yake...


Washegari da kansa yake mata wanka da ruwan dumi ta na masa mita shi kuma yana lallaɓa ta, da ƙyar ta bari ya shirya ta ya kwantar da ita ya fita. Tea ya haɗo mata mai kauri ya shiga ɗakinsa ya fito da magani a hannunsa ya dawo.
"Sweetheart tashi ki sha tea da magani."
Ya yi maganar yana ɗago da ita, kuka tasa masa ta ce.
"Ni ka sakeni mugu kawai."
Danne dariyarsa ya yi ya lallaɓa ta tashi ya bata tea ɗin tasha ya bata magani, bayan ta shanye ya kwantar ya ita shima ya kwanta ya lallaɓa ta tana mita har bacci ya yi gaba da ita...


Haka suka ci gaba da amarcinsu, Suhaima na ta yi wa Hamid taɓara shi kuma yana biye mata, ji yake kamar ya mayar da ita ciki saboda so da ƙauna.


Tuni yan biki sun koma gida Aminatu ta ce ita fa taga gari ba inda za ta je haka suka barta; Inna Laure ma ta koma ƙauye haka ma yan Kaduna har Suhaila duk sun koma gida...


Rayuwar Suhaima da Hamid ba'a cewa komai soyayya suke zuba wa madarar, wata irin kakkarfar soyayya ce ke ta guda a tsakaninsu ko wajan aiki ya tafi suna maƙale a waya har ya dawo...


BAYAN WATA UKU




Yau ta tashi ba lafiya cikin damuwa Hamid ya kira Family Doctor ɗinsu ya zo ya duba ta nan ya gano ciki a jikinta na wata biyu, murna a wajan wannan masoyan ba'a magana. Bayan sun gama murna Hamid ya tafi raka Doctor waje sai ga su Ayan sun iso.


"Assalam alaikum Mama!.
Suka faɗa a tare; Suhaima ta kalledu da sauri ta miƙe ta rungume su ta ce.
"Kai gaskiya wannan rana ta yau ta musamman ce a gareni;tun da naji kun yi sallama jikina ya bani kun musulunta."
"Kwarai ma kuwa Mama mum musulunta shi ne Baba ya ce mu zo mu miki albishi.
Ayan ya faɗa yana murmishi, itama faɗa musu tayi tana da ciki suka tayata murna suan tsaka da hira sai ga Hamid ya shigo gidan.
Da mamaki yake kallon su Ayan ya ce.
"Beautiful yaushe kuka zo ban ga shigowar ku ba?"
Iman ta matso kusa da shi ta gaishe shi ya amsa yana ɗago da ita ya zaunar.
Suhaima ta gyara zama ta faɗa amsa cewa su Iman fa ba mutane bane, ta bashi labarin duk abin da ya faru da ita saboda yanzu Hamid ya zama komai nata ba za ta iya ɓoye masa komai nata ba..
Shuru ya yi yana jin gabansa na faɗu wa, wai tare suke da aljannu kuma wanda Suhaimarsa ta haifa. Jin bai ce komai ba idanun Suhaima ya cika da ƙwalla dama wannan ranar take tsoro,ba ta son faɗa masa wannan sirrin da in yaji ƙila ma ya ce zai rabu da ita. Kallon shi ta yi ta ce.
"Ba ka ce komai ba Sweetheart."
Kallon ta ya yi bai ce da ita komai ba, hakan yasa ta fashe da kuka ta rungume su Ayan ta ce.
"Nasan dama in kaji wannan sirrin ba lalle ka yarda ka zauna dani ba, shi ya sa ma naƙi sanar da kai sai yanzu da suke zuwa yasa naga ya dace na faɗa ma a matsayinka na mijina uban abin da zan haifa nan gaba."


Da sauri Hamid ya dawo inda take yasa hannu ya goge mata hawayen ya ce.
"Haba Sweetheart kina tunanin dan wata jarabawa ta faru dake in kika faɗa min zan gujeki ne? Ai ko a gaske kika haifesu ba zan taɓa gudunki ba har abada, ina sonki saboda Allah ba dan wani abu ba su kuma ina murna da musuluntar da suka yi da babansu, za muso suke ziyartarmu in so samu ne ma kullum."
Haɗa su ya yi ya rungume Suhaima ta dinga masa godiya, su kansu su Iman sun ji daɗi matuƙa.
Ranar a nan suka wuni sai dare suka yi wa su Suhaima sallama suka wuce...


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin Suhaima na ƙara girma sosai take samun kulawa ta ko'ina...


Yau Suhaima ta tashi da nakuda hankalin Hamid a tashe ya kaita Asibiti, sai kusan Azuhar ta haifi ɗanta namiji kyakyawa mai kama da ita, sosai aka sha murna zuwa dare aka sallame su suka nufi gida..


Kula ta musamman ake bai wa Suhaima da Babynta Hamid kuwa duk wani abokinsa sai da ya faɗa masa an masa haihuwa.


Ranar suna yaro ya ci sunan Sayyid wannan abu ba ƙaramin faranta ran Suhaima ya yi ba, su Iman kuwa suna manne da Baby Sayyid cike da farinciki an yi wa babansu takwara. Haka aka yi suna aka watse Suhaima da babynta ta tafi zaman wanka.

Sosai Sayyid ke girma yana ƙara wayo; watan ta biyu a gidansu sannan aka mayar da ita gidanta ranar taga soyayya kala-kala.. Sayyid na da wata biyar Suhaila ta haifi ƴar ta mace daɗi ya mamaye Suhaima. Tun ranar kwana biyar ta haɗa kayanta ta tasa Hamid gaba ta dinga masa kuka sai ya kaita Kaduna, ba dan ya so ba ya tarkata su ya kaita ya dawo cike da kewar matarsa sa yaronsa...


Bayan an gama hidimar suna Na'im ya ce shi fa Aminatu yake so, wannan abu ya yi wa su Umma daɗi Abba da abokansa suka je nema masa aurenta, ba ɓata lokaci suka basu auren Aminatu. Sai bayan sun dawo Sani ya ce shi ma fa yaga wata a cikin dangin Suhaima mai suna Karimatu yana so. Abba dan murna har sai da ya yi sujjada bayan kwana biyu suka kuma komawa suka nema masa auren Karimatu aka basu, gabaɗaya wata biyu aka sa bikin..
Suhaima ta ji daɗi ganin dangin har biyu za su zo kusa da ita, tun ana saura sati ta haɗa kaya ta goya Sayyid suka tafi Ethiopia wajan biki...


Sai da aka ģama biki da bayan kwana biyu kana Hamid yaje ya dawo da ita shi ma sai da ya mata zuwan bazata ta gansa..


Haka dai rayuwa ke ta tafiya wataran daɗi wataran akasin hakan..


BAYAN SHEKARA GOMA.


A gajiye ta shigo palon ta yada zango akan kujera, yara hudu suka biyu uku maza ɗaya mace suna faɗin.
"Oyoyo Mommy.
Murmushi ta yi duk suka haye kanta ta ce.
"Ku tashi mana Mimi ina yayanku yake ne har Daddyn naku ban ji motsin sa ba..
Kafin Mimi ta bayar da amsa sai busa taji an fito daga bayan labule aka soma faɗin.
"Happy birthday to you! Happy birthday to you.


Hamid ya iso ta rungume shi tana dariya, ta ce.
"Thank you so much my love."
Murmushi ya yi suka rabu aka kawo cake suak yanka ta fara ba wa Hamid kana Sayyid sai sauran yaran. Bayan an gama Hamid ya miƙa mata gift ta amsa tana dariya, tana buɗe wa taga wata ce sabuwa dal cikin farinciki ta rungume shi tana amsa godiya...


Bayan an gama komai yaran suka wuce dakinsu, juyo wa ta yi ta kalle shi ta ce.
"Ni fa na manta yau ne birthday na."
Zai yi magana suka ji ana kwankwasa ƙofa, suak bada izini.


Ayan ne da Iman suka shiga ciki shigar da kamala hannuwansu riƙe da ledodi, da murna suka tare su bayan sun gaisa suka miƙa wa Suhaima ledar Ayan ya ce.
"Murnar ƙarin shekara Mama Allah ya ƙara lafiya da kwanciyar hankali."
Amsa ta yi tana murmishi ta ga sarka ce mai kyau, ɗayar ledar kuma takalmi da jaka ne har da hijabai guda uku da material shi ma biyu.
Cikin tsananin farin ciki ta rungume su tana musu godiya.
Nan suke sanar mata babansu zai yi aure, sosai ta yi murna ta ce su gaishe shi shi ma Hamid ya ce su gaishe sa Sayyid suak amsa da to sannan suka fice..


Ɗaukan ta ya yi cak ta waro idanu ta ce.
"Kai ba ka tunanin yaran nan su fito su ganmu a haka?"


"Ni ba ruwana da su muje na miki wanka ki huta sai mu bi lafiyar gado.
Dariya ta yi ta maƙale shi suka shige ɗaki....






TAMMAT BI HAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NA *(A MAƘABARTA NE)* Allah ya yafe min kuskuren dana rubuta ya bani ladan abin da yake daidai..
Mu haɗu da ku a littafin FA'IMA bayan salla in sha Allah ni ce taku har kullum da koyaushe *Maman Nusaiba.*

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads