Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 38049 words

Chapter 11 - A MAKABARTA NE By Sarat Alkasum (Maman Nusy).txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jul 2024

416

Ads at the middle of Article

ma ta yi magana Sayyid ya musu bayanin komai ya basu umarni da su mayar da ita gida. Ba dan Iman ta so ba suka ɓace a gurin...
Wani irin huci Sayyid ya dinga yi yana zagaya ɗakin, sosai yake jin ciwon rabuwa da Ummun sa amma ba yadda zai yi tun da farin cikinta yake so...


A ɗakin Suhaima suka bayyana; wadda suka kawo a matsayin Suhaima suka tasa ta miƙe daga zaman da ta yi.
Kanta a ƙasa ta ce.
"Shugaba ai nasha ba za ku zo yanzu ba."
Ayan ya ɗaure fuska ya ce.
"Ina fatan dai ba ki bada ƙofar da aka gane ba Mama ba?"
"E ban bada ba; yanzu ma na ce zan yi wanka ne na shigo dan haka ita sai ta shiga wankan mu mu wuce."
Murmishi Suhaima ta yi ganin mai tsananin kama da ita sak ba wata maraba, miƙa mata towel ɗin ta yi ta kalle su ta ce.
"Yaran Mama sai wata rana in na shirya za mu tafi ku kaini garin su Mamana."
Iman ji take kamar ta zauna a wajan Suhaima amma ba haki, rungume su ta yi suka ɗauki lokaci sannan suka rabu, jin muryar Inna Laure suka yi saurin mata sallama suka ɓace...


Shigo wa Inna Laure ta yi ta na riƙe da kwanon abinci ta harari Suhaima ta ce.
"Kenan dama dan kar ki ci abincin nan shi ya sa kika ce wanka za ki yi? Kwana biyun nan duk bakya cin abinci ko wani abin kuma yake damun ki?"
Murmishi Suhaima ta yi ta ce.
"Kai Innata babu wani abu da yake damuna kawai dai na ƙoshi ne, yanzu na shige wanka in na fito zan ƙara ci."

"Oho dai ke kika sani, idan na dawo ban ga kin ci abincin nan ba za ki sani ne."
Ta na gama faɗin haka ta aje abincin ta wuce...


Bayan ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa wadda ta amshi jikinta; tururuwa masu ƙamshi ta feshe jikinta da shi sannan ta fito zuwa palo..
A palon ta same su su duka har ma da Sani ya zo gidan, suna haɗa idanu ya ce.
"To ci ba kama kenan, ya jikin naki?"
Harara ta masa ta amsa masa ta na turo baki gaba.
"Kai fa ka cika takura Yaya Sani, shi ya sa bana son ka zo gidan nan Wallahi."
Dariya ya yi ta zauna aka ci gaba da hira, sosai suka ga fara'a kan fuskarta saɓanin kwana biyu zuwa uku da ta dinga daure fuska ta na kunshe kai a ɗaki...


Tun da Suhaima ta dawo ta kasa nutsuwa, sam ba ta son ta sanar da su Umma wannan labarin amma kuma ya ta iya? Dole ta faɗa musu dan su san ta tafiyar tata ko za a samu wanda zai mata rakiya..


Yau suna hira ta gyara zama ta basu labarin duk abin da yake faru da ita, da tarihin asalin ta da na mahaifiyarta babu abin da ta ɓoye musu har auren ta da Sayyid da rabuwar da ya yi da ita da yaran suka haifa kaf ta haɗa ta musu bayanin komai...


Inna Laure ta kwalalo idanu waje ta na kallon Suhaima ai kuwa Suhaila ta kwashe da dariya...
"Ƴar Innarta aradun Allah kin yiƙoƙari da ba ki mutu ba; Haba inda ni ce tuni zawo zan dinga yi har mala'ika ya iso gareni."
Inna Laure ke maganar ta na zare idanu ta kara da cewa.
"Alkur'anin Allah yau ba zan kwana a ɗakinki ba, na je ina bacci sai dai na ji ni a sama ina yawo."
Dariya suka yi Suhaila har da riƙe ciki haka dai suka gama hirar . Sai da za'a tashi Abba ya ce mata duka gabaɗaya za su tafi amma a jirgi ta faɗa wa Sayyid ko su Ayan ya bisu a jirgi, to ta faɗa ta na fatan su amince da wannan buƙatar..


Ta na kwanciya Inna Laure ta zo ta kwashe kayan baccin ta da gudu ta bar ɗakin, Suhaima ta dinga dariya.. Ba ta jima ba sai ga Ayan ya zo ya sheda mata ya ji maganar da suke ɗazu kuma Babansu ya amince su tafi a jirgin..


Cikin kwana biyu Abba ya samo musu ticket ɗin jirgin da zai je Ethiopia..


Washegari suna zaune sai ga Iyan da Iman da Sayyid cikin shigar ta alfarma, basu canja kama ba a yadda Suhaima ta sansu a halittun mutane a haka suka zo dan su faranta mata rai, ai ko Suhaima ta ji daɗi sosai..
Suna isa airport jirginsu na isowa ɓata lokaci suka shiga ya ɗaga zuwa Ethiopia.....


Sai wuraren ƙarfe 2 suka sauka a Ethiopia, daga nan Sayyid ya yi gaba ya ce su biyo shi ba muso suka bisa baya..
Su Inna Laure an yi tsit ko tari ta ji riƙe kayanta take ba wanda ta yarda ya kalle tsakanin Ayan da Iman har Sayyid ɗin ma, wani mugun tsoro take ji wai yau ita ce tare da aljanu suke tafiya? Kuma gasu nan kamar mutane sak, sai yau ta ƙara tabbatarwa da maganar da ake cewa aljani babu irin suffar da ba zai fito ba in yaga dama...


Suna yin nisa Sayyid ya ce kowa ya rufe idanunsa; cikin Inna Laure ya bada ƙuuuuu! Ta yi saurin dafe cikin ta damƙi hannun Abba ta maƙale a bayansa, wai in ko tashi sama za su yi to fa ita tana jikin ɗan'uwanta..


A wani gari suka bayyana bakin wata ƙofar gida, izini Sayyid ya basu ya ce su buɗe idanunsu, ba muso suka buɗe. Suhaima ta ƙagara ta ga dangin mahafiyarta sai kuka take ƙasa-ƙasa.


Wani mutum ya fito daga gidan mai tsananin kama da Suhaima yana ganin Sayyid ya yi murmishi ya iso tare da cewa.
"A'a Malam kaine? Sannun ku da zuwa."
Inna Laure tana rakube a bayan Abba a hankali ta ce.
"Tab da kaina waye da ba ka bashi hannu ba."
Sarai Sayyid ya jita ya miƙa wa mutumin hannu ya ce.
"Dama na faɗa muku zan dawo to gani dai na kawo muku ƴar Zaira har gida."
Ya yi maganar yana nuna Suhaima dake tsaye tana goge hawaye. Waro idanu mutumin ya yi yana faɗin.
"Ikon Allah sak Zaira ɗin mu,zo nan yarinya kuma ku biyoni muje ciki."
Ya yi maganar cikin tsananin farin ciki; Suhaima ta iso gabansa ya rungume ta yana faɗin kamr an tsaga kara da Zaira, hannunta ya kama suka sa kai cikin gidan yaan kwaɗawa 'yan gidan kira.."








_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/18 20:14] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_










Daga Alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_








SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:


*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*


*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*


بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣3️⃣




Gabaɗaya mutanen gidan duk suka fito jin yadda yake kiran kowa da sunansa; wata tsohuwa ta iso ta na gyara mayafin kanta ta ce.
"Kai ko Sulaiman ya kake kwarara mana k...
Maganar tata ce ta maƙale sakamakon arbar da ta yi da Suhaima dake tsaye ta na kallon masu kamanni da ita sak, jiki na rawa ta nuna Suhaima da hannu har ta iso gaban Suhaima sai ta fashe da kuka.
"Zaira ashe zan sake ganin ki a rayuwata? Allah sarki! Ina kika shiga duk tsayin shekarun nan Zaira?"
Sosai Suhaima ke kuka jin yadda ake kiran sunan Mahafiyarta; abu ɗaya yake matuƙar saka ta damuwa a wannan gaɓar ,idan ta tuna iyayenta sun mutu ba tare da sun musulunta ba, shi ya sa take yi wa Sayyid da yaransu fatan Ubangiji yasa musu imani a zuciyarsu su ƙarbi kalmar shahada kafin mutuwa ta riske su..


Kamo hannun tsohuwar Suahaima ta yi ta ce.
"Kaka ba ita ba ce ƴarta ce ni."
Tsayar kukan nata ta yi ta ƙura wa Suhaima idanu ta na nazarin maganarta; sai da ta gama ƙare mata kallo ta gane wannan fuskar shekarunta ba su kai na Zaira ɗin ta ba, Jinjina kai ta yi ta ce.
"Ku zo mu shiga ciki ."
Ta yi maganar ta na jan Suhaima; sauran 'yan gidan kowa baki buɗe yake kallon Suhaima, ita kuwa jinta take kamar an cire mata wani nauyi da ya danne mata zuciya, duk da Su Umma sun zame mata bango majingina amma taji sanyin daɗi da taga masu kama da ita. Sau tari takan yi shuru ta dinga hasaso kamannin familyn gidansu; amma duk sai taga basa kama da juna ita kaɗai ta fita zakka a cikinsu, wani lokacin har Umma take tambaya shin ita me yasa ba ta kama da kowa a kaf familynsu. Idan ta faɗi haka Umma wayo take mata ta kawar da maganar ta kawo wata sai ta manta, amma yau dai gashi ta ga masu kama da ita sak wasu suna mugun kama wasu kuma kamar daidai misali, wasu kuma ta yanayin halitta ne suke kama da juna..


Cikin palon tsohuwar suka shiga dukkansu har 'yan gidan; Suna zama wanda ya shigo da su ya yi wa wata kyakyawar budurwa wadda take mugun kama da Suhaima magana da yarensu ta miƙe ta nufi wata hanya da saurin ta, ita kuwa Suhaima ƙurawa dangin nata idanu ta yi hawaye na bin kuncinta farinciki sosai take ta na aiyana a ranta ina ma ace mamanta na raye ta kwanta a jikinta ta ji ɗumin jikinta kamar yadda kowacce 'ya take ji .
Ji ta yi ana goge mata hawayen dake kwaranya akan kyakyawar fuskarta; ta juyo sai ta ga Ayan ne yana girgiza mata kai, murmishi ta yi ta tsayar da kukan sai ga wannan budurwar tare da yara biyu sun shigo musu da nau'ikan abinci kala-kala sun dire musu a gabansu..
Sayyid ya miƙe tsaye yana kallon su ya ce.
"Bari za mu fita waje ni da yaran nan idan kun gama za mu dawo."
Da mamaki suka kalle shi tsohuwa ta ce.
"Haba dai ɗan nan ai ka zauna ku ci abinci; ya za ka ɗauke yara ku fita waje bayan kun zo a gajiye?"
Murmishi ya yi kawai, wani irin azabbaben son ummunsa ke masa yawo a cikin zuciyarsa har baya so ya daina kallon ta, amma kuma ba yadda ya iya dan ya riga da ya sadaukar da komai dan farin cikinta. Ranar da yasa su Ayan suka dawo da ita gida da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa , yana jin in dai babu Ummu a kusa da shi to fa ya zama ba shi da amfani.
Fita kawai ya yi su Iman suka bi bayansa da sauri,Suhaima na ganin haka ta tashi ta bi bayansu duk yan falon suka bisu da kallon mamaki..
Tsohuwa ta kasa daure wa ta ce.
"Sulaiman wannan ko shi ne mijin na jikar tawa?"
Ta yi maganar ta na miƙe ƙafafuwanta dan ta ji daɗin zama.
"A'a Ummi wannan ba mijin jikar ki bane; ya taɓa zuwa gidan nan muka haɗu da shi nan yake sanar dani Zaira na da ɗiya zai kawo mana ita mu ganta, amma dai ban sani ba ko soyayya suke a tsakaninsu saboda yadda yake kallon ita ƴar tamu."

Inna Laure ta gyaɗa cikin raɗa-raɗa ta ce.
"Hmm ku dai a bar kaza cikin gashinta kar a fige ta labarin ya canja salo, da kun san waye wannan zankaɗeɗan mutumin da wannan yaran; da tuni kun suma aljannu ƙarara gasu nan kamar mutane mu dai Allah ya kaimu gida lafiya."
Na'im na jinta ya girgiza kai yana murmishi; tsohuwa ta ce.
"Allah sarki amma ko Allah ya masa albarka. "


Ko da ta fita ba ta gansu ba a harabar gidan hakan ya tabbatar mata ƙila sun koma gida ne.


"Ummu!..


Taji ya kira sunanta daga bayanta; juyo wa ta yi fuskarta a dame suka haɗa idanu sai ya bata tausayi, sosai ta hango soyayyar ta a cikin idanunsa a sanyaye ta ce.
"Sayyid me ya sa ka fito wai? Kuma ina yaran suke ne?"
Murmishi ya sakar mata sannan ya ce.
"Kin san dai mu bama cin abincin ku ko? Shi yasa muka fito kar ace sai mun ci."
Jinjina kai ta yi ta juya ta hango wata bishiyar Mangwaro dake harabar gidan ta kuma dawo da kallon ta kansa ta ce.
"Ni ma na ƙoshi muje can mu zauna kafin su gama cin abincin."
"A'a ba za ayi haka ba Ummu ki koma ki ci abinci da kun gama zan shigo har su Ayan ɗin.
Kamar za ta masa kuka ta narke fuska, ji take ina ma ace Sayyid ɗin nata a matsayin jinsin ta ya fito da tafi kowa dacen miji kamilalle. Sai dai kash shi ɗin ba jinsin ta ba ne dole kuma ta rabu da shi, inda take ƙara jin tausayin shi in ta tuna yadda ya sha gwagwarmaya duk dan saboda son da yake mata ya bata kariya, ta na jin ƙaunar sa sai dai kuma shi ɗin ba mutum ba ne ballantana in bai ce yana sonta ba ita ta tunkare shi ta ce ina sonka wane, kukan zuci take ta na addu'ar Allah ya ba ta managarcin miji ko da kuwa wanda bai kai Sayyid ɗinta ba ya zama yana da nutsuwar Sayyid.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Kar fa ka tafi!"
Ta yi maganar ta na goge hawayen da ba ta san dalilin zuwansu ba, ji kawai take babu lalle ta samu wanda zai mata zallar madarar so da ƙauna kamar Sayyid, in kuwa ta same shi to tabbas ita ɗin mai sa'a ce a duniya, ballantana ma da wahala ta samu mai son ta kamar shi ɗin, shi ya fara sonta fiye da komai nasa, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya nuna mata zallar so..


"Yi haƙuri Ummu kin ji! za ki samu wanda ya fini komai ma, za ki samu Ummana.
Jinjina masa kai ta yi sannan ta juya ta koma ciki ya bita da kallo , sai da yaga shigewar ta ciki sannan ya isa inuwa ya samu kan wata kujera ya zauna...


Ta na shiga ta same su duk sun yi shuru suna sauraron Tsohuwa da take musu godiya cikin kukan ta; a kusa da tsohuwar ta zauna ta na murmishi ta ce.
"Kaka kukan me kike bayan Allah ya haɗa fuskokinmu kafin mutuwa?"
"Kaiya ƴar nan ba dole na yi kuka ba; wannan mutanen arzikin masu zuciyar salihai nake yi wa addu'a da suka riƙe ki amana tamkar su suka haifeki, ina ƙara muku godiya Allah ya faranta muku duniya da lahira."
Amin Suhaima ta ce ta na kallon su Umma da fuskokinsu yake ɗauke da murmishi, wani sanyi ta ji ya ratsa sassan jikinta yau dai gata ga masu kama da ita, ba iya mutum ɗaya ba duk kusan mutanen gidan suna kamanni da juna, murmishi ta yi ta tashi zaune ta dubi wadda suke tsananin kama ta ce.
"Ya sunan ki?"
Kallon ta yarinyar ta yi alamun ba ta san mai take cewa ba; Sulaiman ne ya yi ƴar dariya ya ce.
"Suhaima Aminatu ba ta san Hausa ba, mu ne dai da yake muna fita zuwa Nigeria mun koyi Hausa sosai ba kamar su ba da ko gaisuwa basu sani ba da Hausa."
Dariya Suhaima ta yi tsohuwa ta miƙe ta soma magana da yarensu,, gani kawai suka yi duk mutanen palon sun bar gurin itama ta juya za ta fice Suhaima ta kamo hannunta ta ce.
"Kaka ina za ki je to?"
"So nake ku ci abinci tukun sai mu dawo."


Ok Suhaima ta ce sannan ta sake mata hannu ta wuce.
"Anty yau dai kin ga masu kama dake ko?"
Na'im ya faɗa yana murmishi.
"Wallahi kuwa kaga wacce tafi kama dani amma dai ba ta jin Hausa, ko Uncle zai bamu ita sai mu tafi da ita ta koyi Hausa?"
"To ni ina na sani ki bari in sun dawo ki tambaye. Shi kawai."

Abincin suka ci sai yaba girkin suke; ita kuwa Suhaima farinciki ya hana ta ci abincin yadda ya kamata, da an jima sai ta ce.
"Iko sai Allah! Ga dai masu kama dani."
Dariya suke mata in ta faɗa har suka gama sannan 'yan gidan suka dawo aka ci gaba da hira, cikin hirar da suke ne Suhaima da take yin tambaya ta matso kusan Sulaiman ta ce.
"Uncle a baya mamana ce a wajan su Kaka, ku lokacin kuna ina? Sannan a da su Kaka ba musulmai ba ne ina son sanin bayan kun bar mamana a wannan yankin me ya faru daku har lokacin da kuka musulunta?"
Tsohuwa ta goge ƙwallar da ta zubo mata ta ɗaga kai ta kalli suma.
"Lokacin da za mu tashi daga wannan yankin mun nemi gidan Zaira mun rasa, ƙarshe muka tafo ni da mijina muka bar ta a can. Dama tun farko akwai su Sulaiman lokacin da aka yi wani faɗa ne aka tayar da bom muka rabu da su, sai bayan mun dawo yankin namu muka samu an samu canji sosai wani mai kuɗi ya gyara mana garin nan a gidansa muka samu Sulaiman da Abubakar. Mun sha murna da ganin juna sannan mun basu labarin Ƙanwar su an mata aure amma mun rasa gidansu, sun sha kuka nan dai aka gyara mana gidanmu muka koma su kuma suka ci gaba da karatu. Kullum kukan rashin ƴarmu nake, wata rana dai muka yi ɓaki a gidan nan ashe su musulmai ne, a hankali suke nuna mana kyakyawar alaƙa irin ta musulmai har muka ji imanin shiga wannan addini mai ni'ima da nutsuwar zuciya; ba ɓata lokaci muka karɓi kalmar shahada. Wannan shi ne abin da ya faru, yanzu kuma alhamdu Lillahi komai ya wuce sai tarihi."


Umma ta ce.
"Allah sarki dama rayuwa haka take wata rana sai labari."


Haka dai suka ci gaba da hira inda Umma ta ce gobe za su koma, Tsohuwa ta ce to abar musu Suhaima ta yi musu ko wata biyu ne su kara sanin juna. Ba dan Umma ta so ba ta ce to sannan suka tashi..


Sayyid dake zaune yana jiran su gama hirar sai jin muryar Suhaima ya yi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads