Showing 39001 words to 42000 words out of 42022 words
Chapter 14 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt
Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷
storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
*PAGE* 55-56
..........................📖Ta da jikin bango ta fara dukan cikin ta baji ba gani
da azama hajja ta 'karaso ta fara janye hajiya amma hajiya tayi cili da ita tana huci ta 'kara cafko Zakiyya
ta cigaba da jibgarta
cikin tashin hankali hajja ta mike ta fita da gudu tana kururuwa neman agaji 'yan gidane suka fito akazo ana janye hajiya aka janye Zakiyya da tuni ta suma sai jini dayake ta zuba daga 'kasanta
cikin masifa hajiya ta 'kara yo kan Zakiyya Mommy da tashigo yanxu ta tareta amma ta tureta hajja ce tasa hannu ta dauketa da marika 2 masu kyau tana huci tace "wai Sareena bakida da hankaline kasheta zaki da ita da 'dan cikinta" "CIKI" mutanan dakin suka fa'da cikin al ajabi
"eh ciki gareta shine take so ta kasheta da 'dan cikin nata" "inalilahi wa'ina'ilaihirraji'un" mutanan parlour suka dau salati
cikin jimami Mommy tace "mu dai keta a kaita Hospital kar wani abu yasameta da 'dan cikin nata" da sauri aka kinkimi Zakiyya akai waje da ita
ita kuwa hajiya kuka tasa tana cewa "Allah ya isa tsakanina dake hajja kin cuce ni kin falasa asirin da naketa gudu ya faru kinsa makiya zasu ringa yimun dariya har muna fuka Maryam ta fara cewa akaita asibiti a ceto 'dan cikinta sabuda ta haifi 'dan shege ayi dariya"
ba wadda yabi ta kanta bare a kulata suka fice daga part 'din masu dariya sunayi masu jamami nayi
Ammi Mommy ta kira ta sanar da ita abunda ke faruwa tace suzo su tafi Hospital 'din tare ba musu Ammi ta shiya suka tafi Mommy ta kira Abba tace "ya aiko musu da ku'din ko za'a bu 'kaci wani abu" "to" Abba yace ya tura Usman ya kai musu ku'din
tunda aka kai Zakiyya Hospital ake akanta har magrip saida wani babban likita yazo sannan aka samu tadawo hayacinta amma an kilaceta ba ayarda kowa yaje gurin taba sai su likitocin
da dare Abba yazo yasa mi Dr dan jin abunda a ke bu 'kata
Dr yace anbiya komai amma zasu rike Zakiyya har sai Allah ya sauketa lafiya sannan su salameta amma zasu ringa bari ko mutum 2 ne suringa suwa du bayan 5days su ganta
cikin alhini Abba yaiwa Dr godiya ya dauki su Mommy suka huce gida kowa Zuciyarshi ba da'di
Aliyu na kwance a parlour yanata kalo a TV kiran Usman ya shigo wayar da kamar bazai daukaba sai kuma ya dauka ya kara akune
"hellow" "inajinka malam meya faru" tsaki Usman yaja yace "mtssss da'dina nakai ba'a kiranka ayi hirar zumunci saika 'batawa mutum rai" 'dan tsaki Aliyu yaja yace "inajinka" kai kawai Usman ya girgiza sannan ya sanar da Aliyu abunda ke faruwa a GIDAN nasu
cikin tsananin damuwa Aliyu yace "kai lamarin GIDAN mu yana bani tsoro yanxu 'yar Zakiyya hartasan tasa ayi kisan kai kuma yanxu gashi wai harciki kace tana dashi yarinyarda ko isa auran batayiba hartasan tai ciki" "hmm Aliyu kenan yanzu ko 'dan 13years zai iya abunda Zakiyya tayi kuma da kake cewa bata isa aure ba bata girmi Deedee ba" "mtsss naji yanxu yajikin nata" "da sauki za'ace amma sun hana a ganta wai saita haihu zasu bada ita"
ido Aliyu ya rintse ya girgixa kai yace "Allah ya bata lafiya" dai dai lokacin Deedee ta 'karaso parlour ta zauna kusa dashi tana kalonshi shima ita yake kalo "ameen" Usman yace sukayi salama ya kashe wayar
a hankali Deedee yace "waye bashida lafiya" hannuta ya kamo yana murmushi yace "ba abuda ya shafeki bane" "okey yaushe zaka kaini naga Mommy" fuska ya yamutse yace "duka duka yaushe Mommy ta kawo min ke da zakice zaki gida" fuska ta marairaice tace "plx ko da darene ka kaini na kwana"
ido ya zaro yace "kwana fa kikace hmm lalai zaki jima bakijeba yarinya" hannunta ta 'kace ta mike za ta bar gurin ya 'kara riko hannunta yana dariya yace "ki zauna na fa'da miki wace bata da lafiya" xama tayi tana kalonshi ya mike zaune yayi ya dawo da ita kan ciyarshi yace "Zakiyya ce bata da lafiya" cikin damuwa tace "ayyah meya sameta" ajiyar zuciya yayi yace "hajiyarsu ce tamata dukan kawo wuka sabuda taji tanada ciki" "what cikifa kace" Fateemah ta fa'da a tsorace
rugumeta Aliyu yayi ajikishi dan ganin yadda jikinta ya dauki rawa
cikin rarrashi yace "ki mutsu malama" cikin kuka tace "cikifa kace 'yar uwata tanadashi kuma bayan nasan bata da aure" iska ya furzar yace "nasan 'yar uwarki ce amma ai ba 'yan uwan takan suke damuba sun ware kansu suna san ganin bayanmu yarinyar da tasa a kasheki kikewa kuka"
"duk da haka ko ba 'yar uwa ta bace ai 'yar uwatace musulma dule na shiga damu idan naji wani abu ya sameta" "hakane amma ki nutsu kinji" ciki gaba tayi da kukan da take dan haka Aliyu ya ha'de bakinsu guri 'daya yana kissing 'dinta
saida yaji ta fara sauke nunfashi da sauri da sauri sannan ya zame bakinshi yana kalonta da sexy eyes 'dinshi lumshe ido tayi tana kokarin mikewa daga jikinsa sakita yayi ta mike ta shige badroom 'dinta da gudu harda sa key dariya yayi sosai dan yasan kunyace take damun Fateemah shi har mamaki yake dama har yanxu akwai masu kunya irinta Fateemah
mikewa yayi ya shige nashi 'dakin yayi wanka sannan ya bu'de 'dakin Deedee ya shiga dan duk tsanani baya bari su raba gurin kwanciya
yana shiga ya tadda har tayi bacci
shima kwanciyar yayi ya jawota jikinshi har bacci ya daukeshi
washe gari tuda sassafe hajiya Sareena ta fito taketa hauka a gidan wai an saida mata da 'yarta
ba wadda ya fito ya kulata ita ka'dai take haukarta da taga baza'a kulataba tayi part 'din su Mommy ta shiga da gudu tana kuru ruwa
Abba ne ya fito yana bata baki tayi hakuri amma taki
wayarshice ta fara ruri ya dauka ya kara akune yana cewa "barka da asuba Dr" banji me nacikin wayar yaceba sai jinai Abba yace "okey gamu nan zuwa yanxu" ya ajiye wayar yana kalon hajiya yace "Dr Sageer ne yakira yanxu wai Zakiyya tana nemanmu" cikin tashin hankali hajiya tace "nashiga 3 meya sameta" Mommy da tafito yanxu tace "koma meya sameta ai kece sila"
gaba Abba yayi suka bi bayanshi suka tafi Hospital
office 'din Dr suka huce ya taso suka duguma zuwa room 'din da Zakiyya take
a kwance suka tadda ita idonta a bu'de sunazubda kwala
sannu suka fara jera mata ta amsa da gyar kafin tace "Mommy ina Fateemah?" cikin tausayawa Mommy tace "tana gidan mijinta" sautin kukanta Zakiyya ta 'kara tace "nasan bazan jima a duniya ba amma dan Allah Mommy ki neman min yafiyarta dan namata lafi ba ka'dan ba" nan ta kwashe duk tugun da sukayi da hajiya da hajja da Annur ta sanar da su ta 'kara dacewa "kiwa Allah Mommy ki nemar min yafiyar Fateemah dan nasan ba lalai musake ha'duwa da itaba" Mommy na hawaye tace "Allah zai baki lafiya Zakiyya kuma zan sanar da Fateemah sakonki" "na gode sosai Mommy" da ga nan kuma tafara tari harda aman jini da sauri Mommy taje ta kira Dr yazo yace su bashi guri suna fita hajiya Sareena ta kwala 'kara ta zube a gurin sumamiya......................
by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷
storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
*PAGE* 59-60
..........................📖Rungume Deedee ya manna mata kiss a kumatu yace "Allah yasaka miki da gidan aljannah my wife" hawaye ne suka zubo mata ta share ta sakar mishi murmushi ya shima murmushin yayi ya kali Dr yace "dole nabaka tukuci Dr sabuda wannan abun farin cikin da ka sanar dani" keycar ya dauko daga alji hunshi ya mika mishi yace "gashi nan na malaka maka mutar dana zo da ita halak malak"
cike da farin ciki Dr ya amsa yana yiwa Aliyu godiya
phone Aliyu ya zaro ya kira Sameer yace ya kawo mishi mota yanxu yana Hospitel
ba a 'dau time ba saiga Sameer 'din ya 'karaso ya de besu Dr nata godiya ya kaisu gida
tofa aiki yasamu maza Aliyu daina fita yayi sai kula da matarshi da babynsu
shi yakeyin komai nagidan baya bari ko tsinke Deedee ta dauke
kwanci tashi ba huya har bikin su Hafsat da Zakiyya da tasamu 'dan me gadin gidansu zata aura Abba yaso hanawa tace taji ta gani
ya matso anata shirye shirye duk da Deedee nason xuwa ayi komai da ita amma Aliyu ya hanna wai kar taje ta ringa wahar mishi da babynshi
sai ran kamu tasa mishi kuka sha'be sha'be shine ya yarda ta shirya ya kaita da yace sai ran daurin aure
anyi kamu lafiya an tashi lafiya amare ansha kyau haka ma Deedee abun ba'a magana tayi kyau sosai abunka da me ciki kuma ba tsufa yayi ba
duk wannan shagalin da akeyi Hajiya Sareenah tana kwance rai a hannun Allah Dr gajiya yayi ya sala mota aka dawo da ita gida kashi a kwance fitsari a kwance Abba ne ya samo me kula da ita ana biyanta duk munth
washe gari aka daura aure masha Allah anyi taro sosai kuma da dare za'ayi dinner da ga nan a huce da amare gidansu
da daddare kowa yanata shirin tafiya gun Dinner hakama Deedee tasha kwaliyarta masha Allah tayi kyau abunta
tana zaune tana daurin dan kwali kiran Aliyu ya shigo wayarta
dauka tayi ta kara a kune tayi salama
"kin gama shirn ki fito mutafi" fuska ta ya mutse tace "ayyah ya Aliyu nifa da su Mommy zantafi" "mtsss zaki fito ko nai tafiya ta kuma natafi walahi baza kijeba" ido ta zaro sannin halin Aliyu yasa ta mike tana turo baki tace "ganinan" kashe wayar yayi ta dauko veil 'dinta ta fito
gun da yai parking ta 'karasa ta bu'de gaban mutar tashiga kalonshi tayi tace "nidai da ka barni na tafi da Mommy ta" kawai da kai yayi yace "ki fita amma karnaga 'kafarki a gun Dinner" fuska ta shagwa'be tace "muje to" kalonta yayi ya ta'be baki yace "ko kyau bakiyiba" kalon kanta tayi fuska a marairaice tace "da gaske kake" dariyarshi ya 'boye yace "na ta'ba yimiki irin wannan wasan, musaman wannani jan bakin da kikasa yayi bau"
hannu tasa ta fara goge jan bakin kamar zatayi kuka
shikuwa Aliyu dariya yayi dan yana sani yaimata haka dan yana kishin aganta a haka
mutar ya kuna yana cewa "har daurin kankima beyi kyauba" cirewa tayi ta 'kara canza wani wadda har yafi wacan yi mata kyau
suna zuwa gurin ya parka ya juyo yana kalon ta cikin da ya 'dan fito ba 'karamin kyau ya 'kara mata ba yayi ajiyar zuciya yana kalon yadda samari suke shiga gurin
ajiyar zuciya ya sauke yace "kai zan barki kishiga gurin nan kuwa kali yadda maza suke shigowa"
kawar da kai tayi tace "haba ya Aliyu ka barni naje ai goge kwaliyar" kura wa fuskarta ido yayi yace "ga kwaliyar ina gani gaskiya saikin wanketa zaki shiga ciki"
haka ba yadda ta iya ta wanke fuskar sannan ya barta ta shiga guri
a gurin ma zama ga gararta yayi sabuda Aliyu ya hanata sakewa wai ita kadai yaga ana kalo a gurin da ya gaji ma sata yayi agaba saida suka tafi gida ko tashi ba ayiba
haka akayi taro aka watse lafiya
after 7 munth
cikin Deedee ya tsufa sosai har Mommy tasata a gaba ta tafi da ita duk da Aliyu baisoba amma haka ya hakura ya koma can ya tare
yau ma tana zaune a 'dakin Ammi tana karatu alkur'ani tana ka ranta suratul Maryam Aliyu ya shigo 'dakin saida takai aya sannan ta rufe alkur'anin tana kalon Aliyu
shima ita ya kala yana cewa "me yake damunki kika rame haka" ajiyar zuciya ta sauke tace "tun jiya da dare narata da bayana sukemun ciwo daure kawai nakeyi" "kuma bakiyi magana atafi Hospital ba" lebenta ta cije ta dafe mararta
saurin ru'kota yai yana tan bayarta lafiya ganin ta kasa magana yasa ya fara kwalawa Ammi kira
da sauri Ammi tashigo tana tabayar lafiya ganin halinda Deedee take yasa ta 'karaso tace Aliyu ya fito da mota sutafi Hospital da sauri yayi hanyar fita amma kan ya kai kofa yaji kukan baby
cike da mamaki ya juyo yana kalon ikon Allah
Ammi ce tace "kaje ka kira Mommy ka fito da motar muje a duba su kaji" "toh Ammi" yace ya fita da saurinshi
saida aka gyarata tsaf da baby boy 'din data haifa me kama da Aliyu sukaje Hospital 'din aka duba su akaga lafiya lau suke suka dawo gida
kan kace me gidan ya cika da 'yan barka harda Hafsat wadda cikinta ya fara fitowa ita kuma zakiyya tana katsina gidan mijinta ita cikin gareta
haka aka ringa sha ani da shagali har ran sunah
yaro yaci sunan Abba suna kiranshi da Aryan ansha shagali Aliyu yayi bajinta sosai anci ansha abun gwanin sha'awa
tunda Deedee ta haihu ko bacci Aliyu bayayi sai da Aryan a kusa dashi darana ma da gyar yake badashi sai yaga Mommy ta 'bata rai tukun
har yanxu jikin Hajiya Sareenah abun ba a magana dan yanzu takoma kamar karmami abun abun tausayi
Hajja kuwa tunda taji an daure Daddy kulu cikin kuka take ko abunci bata iya ci idan ka ganta yanxu duk ta lalace ga ba abunci idan Abba ya kawo matama bata ci saidai ta tafi bara ta samo abunda zata ci
yauma tashirya da ya gulalan kayanta ta fito bakin titi tana bara an tsada mutoci ta tafi sa saurinta wai tariga ta kusa da ita xuwa gurin wata 'katuwar mota shi kuma me wata 'yar kurkura ya taho ba burki yaxo yayi ahon gaba da ita haka mutane akasa salati shikuma me motar yagudu haka aka ibeta aka kaita Hospital aka amsheta da akayi emagency da ita
su Abba suna jin labari suka garzaya Hospitel 'din
nan sukaga halin da hajja take ciki Dr yai musu bayanin saidai a yanke mata 'kafafunta duka 2 kuma kwakwalwarta ta tabu tasamu ta 'bin hankali
haka Abba ya biya kudi aka mata aiki
2week tayi a Hospital 'din aka salameta hauka tubu ran hajja takeyi
8days da salamo hajja daga Hospital Allah yaiwa hajiya sareenah rasuwa wadda ta rasu da sunan Fateemah a bakinta
haka aka shiryata aka kaita ma kwancinta
Zakiyya tasha kuka har kuda ta farayi sabuda tashin hankali haka aka dauketa duk da cikin be isa haihu waba saida aka mata aiki aka ciri baby boy akasaci a kwalba
haka rayuwa taringa juyawa yau fari gobe baki
kuma kulum ciwon hajja gaba yakeyi abun ba a cewa komai saidai addu'a
Aryan yayi wayo sosai kulum Aliyu yana tare dashi haryafi yarda da shi akan Deedee yayi wayo sosai
Hafsat ta haihu tasamu baby girl itama Yaseera matar Usman ta haihu ta samu Sabeer
Aryan nada 2years Deedee ta kuma haihu tasamu Maryam me sunan Mommy suna cemata Afrah
after 3 years
Deedee ta 'kara haihuwa ta sa sunan Ammi suna kiranta Mubeenah
itama Hafsat ta haifi Hanan
ita kuwa Zakiyya 'dan da haifama mutuwa yayi amma yanxu tsohon ciki gareta
yau wa adin su Annur ya cika a gidan maza aka fito dasu
inalilahi kawai na iya furtawa sabuda ganin hadda su Annur suka koma kai kace a 'kar 'kashin kasa suka shekara 5
Daddy a gidan yari yayi rauni a hannunshi ciwon yaita cinshi ba akaishi an duba ba har hannun ya fara wari ya ru'be saida akaga haka aka kashi Hospital su kuma suka ce saida a yanke mishi tsin tsiyar hannushi akuwa aka yanke saida dungulmi
yau gida kamar biki akeyi anata shirin tar bar su Daddy lokacin da aka kayosu saida Daddy yayi kuka ganin irin tarbar da Abba yasa akayi mishi bayan sunyi wanka sun shirya aka zubo su abinci kala kala abunka adade ba'a ha duba haka suka ringa cin abunci kamar hauka bayan sun gama sun nutsu aka sanar dasu rasuwar hajiya nanfa duk parlour ya dau kuka mutawar ta dawo sabu bayan angama koke kokene Annur haje har gaban Deedee yana kuka ya roketa ga fara yace alhakinta ne yake bibiyarsu
ita ma kukan take tace ta yafe musu Allah ya yafe musu gaba 'daya nan aka ringa hafar junah kowa ya yafewa 'dan uwanshi aka ha'de kai *BAƘIN GIDA* ya kuma *FARIN* *GIDA*
ALHADULILAH
Duka duka anan nakawo 'karshen wannan novel me suna *BAƘIN GIDA* abunda na rubuta wadda ba daidai ba Allah ya yafe min ameen
wadda na 'batawa ina neman gafararshi
Allah yasa sakon da nake so isarwa yaje gareku ameen
nice taku har kulum
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
marubu ciyar
*DR* *AMEENAH*
*KANWAR* *MATATA*
*AURAN* *JAREEMEE*
*BAƘIN GIDA*
ina wa masoyya na fatan alkari wata kila ba lalai