Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 42022 words

Chapter 8 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

zauna a 'kasa ya gaida ita tana kalonsa ta amsa tare da cewa "meyake damunka karame haka Aliyu?" kai ya dukar yana sosa kai yace "kaina ke ciwo Mommy" "Allah ya sauwake amma sai ka rage tunani kar hawan jini ya kamaka" "ameen Mommy amma hawan jini fa kikace?" "eh mana hawan jini dan wannan ciwon kan naka 'kila shine nifa da san rainane a raba auren nan kawai kowa ya huta" da sauri ya kaleta ta hurga mishi harara tace "ko ban isaba" kai ya girgiza yace "kinfi hakama amma kiyi hakuri" baki ta tabe tace "basan Fateemah ne banayiba asalima da nafi kowa san a hada auranku amma halinta duk ya sauya ina tsoron yaranka su aita abunda tayi" rintse ido Aliyu yayi yanaji kamar soyayen mai Mommy ke watsa mishi amma ba yadda zaiyi da ita






mikewa yayi dan bazai iya daukan zantukan taba yace "bari naje na amso magani insha" "to sai ka dawo Allah ya sauwake" "ameen" yace tare da fice daga 'dakin






yana fita ji ya ci karo da mutum kalon gurin yayi yaga Deedee ce har tana fa'duwa kasa tea 'din dake hannuta ya zube yarasa meyasa duk lokacin da sukayi karo saitakai 'kasaba ko bata da kwarine iho






hannu yasa ya dagota yana 'karewa fuskar ta data kunbura kalo
kanta a kasa murya na rawa tace "inakwana" batare da ya saketa ba ya amsa yace "bagya kula sai kin jiwa kanki ciwo ko?" fuska ta marairai ce xatai magana ya rufe bakinta tare da kamo hannunta yace "gara da muka hadu kinga sai ki rakani na amso magani tunda duk akankine nake ciwo" batayi mashi musuba kuma bai kokari kwace kanta ba tabishi tunda dama bata rabo da hijab a jikinta










suna fita ya bude mata mota tashiga gaba ya 'bude ya shiga yaja motar ya fice daga gidan
Zakiyya dake bakin windo tayi dariya ta dauki phone 'dinta ta kara a kune tace "gashi nan zasu fito tare wannan bana son asamu matsala...............!"








by
*ZAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πŸ“•πŸ–ŠοΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)πŸ–Œ*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/


☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷


storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 31-32




.......................πŸ“–Ja dabaya Annur ya farayi Aliyu na binsa jikinsa har rawa yake idonshi kamar yai aman huta binsa yake har yakai jikin bango za goce Aliyu ya danki huyansa ya shakesa kakarin mutuwa yafarayi sabuda ya shaku iya shakuwa gashi ya kasa kwatar kansa idonsa ne yafara kafewa Aliyu ya makashi da kasa yara takashi ya dukanshi da iya karfinsa ihu nema agaji Annur yake amma bame jinsa






rasa irin gukan da Aliyu zai masa ma yayi ko ta ina duka yake kaimai har saida yaga baya nunfashi ya rabu dashi ya dauko igiya ya daureshi ya jashi har waje yasa shi a but ya rife shi dawowa yayi ya dako Deedee da har yanzu ba ta farkoba ya sauya mata wata rigar wacan ta yage yasa ta a mutarsa ya hau yaja sai gidansu






yana 'karasa sawa gidan ya fito da Annur ya jawoshi har parlour hajiya Sareena yayi sa'a suna zaune gaba 'daya
ko salama beyiba ya jawo Annur har tsakiyar parlour






mikewa Daddy da hajiya sukayi suna kalon ikon Allah
kalonsu Aliyu yayi yace "indan kunason danku yaci gaba da nunfashi a duniya ku rabashi da iyalina kuma yanxuma bazan rabu dashi ba sai na dau mataki" yana gama fa'din haka ya 'kara jan Annur ya fice






ihu hajiya Sareena ta kurma "nashiga 3 Allah ka tsinewa shegen yaron nan da yakeson ganin bayan 'dana nashiga 3 shege tsinane dan......!" (baxa kuji xagin nan abakina ba) saikuma ta fantsamu ta biyo bayan Aliyu






shi kuwa lokacin har yakai parlour Abba
Abba na ganinshi ya mike cikin tashin hankali yace "meye haka Aliyu baka da hankali dubi yadda ka jawoshi ba kaya ajikinshi kome yayi maka ai baxaka yi mishi wannan to zarcin ba"
saida Aliyu ya bugashi da jikin kujera yana huci ya zauna akasa lokacin ne hajiya ta fantsamo tashigo tana ihu tana tsinewa Aliyu






Abba ne ya ringa bata hakuri amma ta cika gidan da ihu
aikuwa kamar jira 'yan gidan suke suka fan tsamo suji meke farowa kowa yaga halin da Annur yake ciki sa jikinshi yayi sanyi






kan kace kwabo kowa na gidan ya halara a parlour Abba harda Ammi da mommy
Abba ne ya mike ya dako riga yasa Sameer yasawa Annur da har yanxu baya nunfashi
sannan ya kali Aliyu da kanshi ke 'kasa jikinshi sai rawa yakeyi nunfashi Abba ya sauke yai gyaran murya parlour yayi tsittttt sai kukan hajiya Sareena kakeji






kalon Aliyu Abba yayi yace "bansan haryanzu kai yaro bane sai yau bansan cewa bakada tunani ba sai yau sabuda rashin hankali shine zaka yiwa 'dan uwanka wannan dukan abun haushi ma ka toho dashi tsirara haba Aliyu meyake damunka haka" ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya dago idonsa abun mamaki hawaye yakeyi muryarsa na rawa yace "kayi hakuri Abba ba da gangan na taho dashi haka ba dan bansan ida kayansa sukeba nima haka na ganshi" mikewa yayi ya fice






mota yaje ya dako Deedee kamar jaririya ya shiga ciki parlour da ita
salatai suka dauka agaban Abba ya direta ya dago ya kali Abba murya na rawa yake "gata nan yadda na tadda ita Ibrahim yana niyar ketamata hadi Allah yasa na dawo gidan na tadda harta suma kuma yadda na ganshi ba kaya haka na 'dako shi"






salati mutan gurin suka 'kara dauka wasu na kukan bakin ciki
Hafsat na kuka ta 'karaso ta dago Fateemah kan cinyarta ta fara kiran sunanta
mikewa tayi da gudu ta dauko ruwa ta watsa mata a fuska
ajiyar zuciya Deedee tayi bata bude idoba sai kuka da ta fara tana cewa "inalilahi wa'ina ilaihirraji'un plz Annur kara bu dani kar kamun haka duk sharin da kamun be isheka ba sai ka biyoni gidan mijina zaka ci zarafina haba dan Allah kawane irin mutune" jijigata Hafsat ta farayi tana kuka ganin duk a firgice take "ki bude idonki Deedee ba abunda zai sameki"








idonta ta bude suka sauka ana Aliyu da shima ita yake kalo mikewa tayi ta fada jikinsa tasaki kuka tana cewa "ina katafi kabar wannan azalimun xaici mutuncina" rungumeta yayi shima yana hawaye








Hafsat ce tace "kiyi hakuri ki daina kuka komai yazo 'karshe insha Allah" maganar Hafsat da taji yasata saurin juyowa ta kaleta sai lokacin ta kula da muta nen parlour a kunya ce tabar jikin Aliyu ta koma gefe ta dukar da kai jitake mar kasa ta tsage ta shige ciki






Abba ne ya kamo hannunta yace "Fateemah kidai na kuka kinji tunda Allah ya tsare ki saiki gode mishi" kaita gyada tana cigaba da kuka mara sauti








hajiya Sareena ce ta mike tana masifa tace "sabuda ba a sona da 'ya'yana shine iya taku 'yar kuka sani har kuka taima ka mata ta farko ninawa 'dan yamutu ko" mikewa Abba yayi ya bata hakuri yace da Usman da Sameer su kamashi suka kaishi mota Abba da Daddy suka bi bayansu suka tafi husbitel dashi






mommy mikewa tayi ta fice tabar parlour Ammi tabi bayanta itakuwa hajiya ta dade da ficewa
haka suka riga ficewa kowa da abunda yake cewa har suka fice suka bar Aliyu da Deedee da Hafsat
Aliyu ne ya mike yali Hafsat yace "tashi ki rakata 'dakin Ammi tayi wanka taci abinci" "to" ta mike ta kama Deedee suka fice daga parlour








bedroom 'din Ammi ta kaita ta zaunar da ita gefan bed ta kali Ammi da takebin Fateemah da kalo tace "Ammi yaya Aliyu yace abata abinci taci tunda safe bataci komai ba" kai kawai Ammi ta iya 'dagawa Hafsat ta fice daga 'dakin






Ammice ta mike ta dawo kusa da Deedee ta zauna tana kalonta tace "ba abunda yamikidai ko?" kai Fateemah ta gyada tana hawaye "alhadullah tashi kije kiyi wanka kici abinci" "to Ammi" ta mike tashige bathroom Ammi ta bita da kalon tausayi tanawa Allah godiya daya tsare mata 'diyar tata






Aliyu 'dakin Usman yaje ya kwanta yana jin zuciyarshi na zafi waya ya zaro yafara kiran Isham bugu 2 Isham ya dauka "hello yaya" "kana ina yanxu" "ina 'dakina" "okey kaje ka siyowa Fateemah magani yanxu ka kaimata" "to yaya" daga haka ya katse wayar






ajiye wayar yayi ya rufe ido kamar me bacci wayarshi ce ta fara ruri ya duba yaga Usaman ne da kamar zai share sai ya dauka Usman ne yace "Aliyu ansamu matsa Allah ya.................!








by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πŸ“•πŸ–ŠοΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)πŸ–Œ*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/


☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷


storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 37-38






.........................πŸ“–A toilet ya direta ya hada mata ruwan yafara kokarin cire mata rigar jikinta rike hannushi tayi ya kaleta yaga kuka take sha'be-sha'be dariya ta bashi daga cewa zai mata wanka take wannan kukan mazewa yayi ya mike ya fice daga toilet 'din saida ya fita yace "kiyi ki gama wankan kizo kici abunci" yakoma kan bed ya kwanta yana jiranta






itakuwa tanajin ya fa'di haka tai saurin tashi ta kule bathroom 'din tana sauke nunfashi ta da'de a toilet 'din sannan tayi wankan ta maida kayan data cire ta fito
karo taci da Aliyu a kan bed a kwance tazata bacci yakeyi ta bu'de werdorop ta dauko jalabiya baka tanofi toilet zata janxa taji anjawota ta fa'da kan shi
rungumeta yayi ajikinsa ido tarufe gabanta nafa'dowa mikewa yayi da ita ajikinshi yace "meyasa kika maida kayannan jikinki bayan kinsan sunyi datti" ya fadi haka yana amshe jalabiyar hannunta






yasa hannu yayi kasa da zip 'din rigarta ido ta zaro cike da tsoro tace "plz ka bari zan sa da kaina" shareta yayi ya zare rigar daga jikinta yayi jifa da ita 'kankameshi tayi cike kunya
shikuwa Aliyu ajiyar zuciya yaringa saukewa yanajin tsigar jikinsa tana tashi






hannu yasa yana fanfareta daga jinkinsa amma yakasa dan ta 'kan'kameshi sosai kan bed 'din yakoma ya zauna yana kalon yadda ya 'boye kanta a 'kirjinsa ajiyar zuciya ya sauke yace "kisakeni indai baso kike ki cinye niba" kuka tasa tace "to kabani rigata nasa" murmushi yayi yace "dan na amshi rigarki shine kike neman ki cinyeni" shiro tayi bata 'kara maganaba jin tayi shirune yasa ya bale brez 'dinta ya zareta kuka Deedee ta fashe dashi sosai






shiru yayi yana jin zuciyarshi kamar zata fa'do dan bugawar da takeyi
rigar hannushi ya ajiye yasa hannu ya 'banbare nata yarabata da jikinsa ido tarintse tana 'kara sautin kukanta






ido Aliyu ya kura mata duk tabi ta ru'de tana kuka sosai rigar ya dako ya xira mata ya dako hula yasa mata
muryarsa narawa yace "tashi muje kici abinci" bata bu'de idoba haka bata daina kukan datake ba janyeta daga jikinsa yayi yamike yana kokarin saita kanshi da jikinsa dake ta rawa ya kamo hannuta ya fito parlour suka zauna a parlour ya kira Hafsat yace ta kawo musu abunci
ta kawo musu ya ibo a spoon ya kawo bakinta ta kau da kai tana sharar kwala






fuska ya ha'de yace "me akayi miki kike kuka kodan makiyinki ya ta'baki?" kasa tayi da kanta batace komai ba
ya 'kara kawo spoon 'din bakinta ta 'kara kauda kai cikin fushi ya daka mata tsawa yace "ni zan baki abu kika kar'ba inda wani katon ne xaki iya binshi har 'dakinsa kikai kanki ko" amsar abincin tayi tace "zan iya ci da kaina" harararta yayi yamike yafice daga 'dakin






baki ta ta'be dan dama duk atakure take tafara cin abuncin saida taci ta 'koshi ta mike ta koma 'dakin Ammi tayi salah bayan ta idar tamike ta koma kan Ammi ta kwanta Ammi ce tace "ni 'dagani 'yar mesan jiki" ajiyar zuciya Deedee tayi tace "kinsan meya faru Ammi ta?" "a'a meya faru" ajiyar zuciya Deedee ta sauke ta bata labarin duk abunda ya faru






"inalilahi wa'ina ilaihirraju'un" abunda Ammi ta ringa maimaitawa daga 'karshe tace "Alhadulilah Allah ya dubemu yaga zuciyarmu ya fitar dake daga sharrin wannan mutanan, Allah ya 'kara karemun ke damu gaba 'daya" "ameen Ammina" haka suka cigaba da hira da jimamin abunda ke damunsu






shikuma Aliyu yana fita dakinsa yanufa wanka yayi da salah sannan ya kwanta dan dare yayi
duk yadda yaso yai bacci da huri dan gobe yanada inda zashi da huri amma yakasa ba abunda yake tunawa sai dazo juyi kawai yakeyi yanajin yanayin jikinshi na sauyawa mikewa zaune yayi yana tunani mafita cikin ransa yace "mexai hana gobe kashirya kukoma zariya da matarka?" kai ya girgixa yace "wannan ba mafita bace dan ba lalai Abba yabari ya 'kara komawa zariya da Fateemah ba amma tunda baza a barshiba shi zai ringa janta ajiki har ta saki jikinta taringa kwana agunsa" kumawa yayi ya kwanta ya dauko phone 'dinsa yafara kiranta






cikin bacci Fateemah taji wayarta na 'kara a 'dan tsorace ta tashi takaci agogo taga 12:42am sannan ta kali wayar taga Aliyu ne gabanta ne yayi wata irin faduwa ta dauka ta kara akune hadi dayin salama






amsawa yayi murya a shake yace "bacci kikeyi" "eh" tafa'da murya a sanyaye "yanxu har kika iya bacci bakinsa halinda mijinki yake cikiba sabuda baki damu dashiba ko?" shiru tayi batace komaiba yayi murmushi yace "to nakasa bacci kixo ki rungumeni ko ki goyani har sainayi bacci sannan kiyi" ido Deedee ta zaro aranta tace "gowo kuma" "yes gowo kobaxaki yibane" fuska tarife kamar yana kalonta dan ta dauka azuci tayi maganar






"inajiranki karki 'batamun lukaci inkuma bazakizo ba ki fadamun" shiru tayi batace 'kalaba har ya katse kiran
komawa tayi ta kwanta ta cigaba da baccinta
Aliyu jin shirun tayi yawa ya 'kara kiranta amma har kiran ya yanke bata daukaba 'kara kira yayi ta dauka tace "plz kabarni nayi bacci na ni tsoro nakeji bazan iya fitowaba" "owk bari..........!" kafin ya 'karasa maganar ta yanke kiran cikin fushi ya 'kara kira amma saiyaji wayar a kashe le'be ya ciza ya girgixa kai ya mike yasa jala biya ya fito yanufi part 'dinsu




a kule yake dayake yada key 'din yasa ya bu'de shiru kowa ya kwanta ga duhu sai phone disa ya kuna ya haska yanufi 'dakin su Fateemah
bacci sukeyi itada Hafsat hankali kwance
Fateemah ce a farko sannan Hafsat a 'karshe gaban bed 'din ya 'karasa ya dauketa a hankali dan karta farka yana san'da yafito ya kule part 'din tana hannusa ya 'karasa bedroom 'dinsa yana ajiyeta akan bed 'dinsa kamar wadda akatasa ta bu 'de ido






mikewa tayi amatukar tsorace saida tasa hannu ta murxa idonta waiko mafarki take amma taga ashe da gaskene mikewa zatayi Aliyu ya daka mata tsawa fuskar nan a murtike yace "idan kika motsa daga nan saina sa'bamiki dan naga sokike kisa nayi abunda banyi niyya ba" hawaye tafarayi tace "karifamun asiri kamai dani kar wani yagani annan" cikin fa'da yace "to meye in wani ya ganki ba 'dakin mijinki kika zoba ko dawanda zaimiki katanga tsaka ninki dani" kaita girgixa tace "duk da haka nidai ka maidani tsoro nake kar wani ya gani" murmushi yayi yace "owk tunda 'dakin kwartanki ne nan zaki iya tashi ki koma da kanki" ido ta zaro tace "um um tsoro nakeji gaskiya kazo ka mardani" kwanci yayi akan bed 'din ita kuma tai saurin zabura ta tashi ya ta'be baki yace "waya tsayar dake ki tafi mana kuma karki sake na 'bude idona naganki inba hakaba saina miki abunda bakiyi tsammani ba" yana gama fa'din haka ya gyara kwanciya ya rufe idonsa








cikin kuka Fateemah tace "indai tsoro nakeji ka taimaka ka zo karakani tunda aidama kai ka daukoni" idonshi a lumshe yace "indai ni zan maidake to saikinyi abunda yasa na dakoki" tanaji ya fa'di haka ta 'kara sa sabon kuka ta zame ta zauna ta kifa kai a tsakankanin cin yoyinta tana cigaba da kuka me sauti








duk shiga da fitar da Aliyu yayi da dako Fateemah akan idon Abba yayi dan yana jin 'karar bu 'de kofa ya leko yaga Aliyu ne har zai fito yaji meyaxo yi a darannan sai wata zuciyar tace ya tsaya yaga iya gudun ruwansa








aikuwa sai gashi ya fito da Fateemah yadakota kamar wata baby doll cike da mamaki ya taso Mommy yace tazo taga ikon Allah tana ganin shigewar Aliyu da Deedee a hannushi ta saki baki kafin tayi 'karfin halin cewa "lalai Aliyu bashida kunya tun be tafasaba zai kone" dariya Abba yayi yace "Aliyu fa ba yaro bane kuma ko yarone yau yanuna miki shi namijine yana bu 'katar abokiyar rayuwa shiyasa nake cemiki kibar nunawa yaron nan bakiso auranshi da Fateemah zai ringa jin haushinki tunda yana son matarsa" "hakane amma kowafa yasan yarinyar nan ga abunda tayi" "duk da haka ai ba tabbatarwa kikayiba shi dayake mijinta yafiki sannin gaskiyar abun" cikin damuwa Mommy tace "duk abunda sukeyi akan ido nane idai ba a cikin kwana 2 da sukayi a zariya Aliyu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads