Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 42022 words

Chapter 3 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ki fito ina waje ki amsa" "a jiyar zuciya ta sauke tace gaskiya dare yayi saidai zuwa da safe" "oh kinada matsala Fateema bafa zama zakiyiba kina amsa zaki dawo kuma gobe samako zamuyi nida Daddy kuma ba lale mudawo a wan-nan mouth d'in ba" "owk bari na fito yanzu" tana gama fad'in haka ta katse wayar ta kali Ammi da ita ta kurawa ido tace "Ammi bari na amshi litafina gurin zakiya" "dare yayi kibari sai gobe" "haba Ammi 9 fa yanxu dare baigama yiba" "shikenan karki dade kuma ki kula da kanki" "to Ammi na" tana gama fad'in haka tamike tafice dama da hijab d'inta ajikinta








tana fita bakowa a waje harzata koma taji ya k'ara kiranta d'agawa tayi tace "banganka ba" "oh sorry Deedee na mantane na tafi room d'ina amma ki shigo ki amsa" "a'a nidai kafito" "haba Fateema cinyeki zanyi" yayi maganar cikin fushi jikinta ne yayi sanyi duk da basani dakin tayiba ta nufi b'an garen mazan gidan








kiranta yayi ya fad'a mata d'aki gabanta na fad'uwa ta nufi bedroom d'in ba abunda take tunani ilah idan ta had'u da ALIYU tace dashi me
knocking tayi ya bata izinin shigowa shiga tayi amma baya nan sai motsi da taji a toilet gaba d'aya jikinta rawa yakeyi sabuda tsoro






shi kuma Annur a toilet wayar Aliyu ya kira saida kiran ya yanke ya k'ara kira takusa yankewa ya d'aga batare da yace komai ba
murya Annur ya make yace "nine wanda nake kiranka kayiwa Allah karka kashe abu daya zan fad'a maka" jin Aliyu yayi shiru yasa ya cigaba da magana "na d'ade ina cemaka kanwarka Fateema tana bin mazan banza kaki yarda to yau in kanaso ka tabbatar ka shiga d'akin d'an uwanka Annur ka gani" yana gama fad'in haka ya yanke kiran yayi dariya san-nan ya cire komai bajikinsa ya dauro tawul a k'ugunsa ya fito








tunda ya kashe kiran ALIYU yake rike da phone d'inshi a hannu sa zuciyarsa nawani irin bugawa da kamar ya share saiyaga in yayi hakan ba mafita bace dan bazai iya bacci ba cikin tashin hankali ya nufi bedroom d'in Annur








Annur na fitowa sukayi 4eyes da Fateema saurin juyawa tayi ta runtse ido jikinta na wata iriyar rawa murmushi yayi yace "ga book d'in naki" kasa juyuwa tayi ya k'araso gabanta ya janyo hannunta da karfi ta fad'o jikinsa suka zube akan bed dai-dai time d'in da Aliyi ya shigo room d'in ganin halinda suke ga Fateema dayafi kyauna da kishi arayuwarsa akan wani kato akwance har jikinta narawa sabuda jaraba ai atake ya yanke jiki ya fad'i a gurin
Annur na ganin ya fad'i yai saurin sakin Deedee




ita kuma tai saurin mikewa daga kan sa bai bari taga Aliyu ba yai sauri yace "sorry fateema walahi bada niya nayiba" kai kawa ta gyada masa har yanxu jikinta rawa yakeyi book d'in yamiko mata tayi hanyar fita da sauri saidai me karo tacida mutum a sume akasa ido ta zaro da larfi ya furta "yaya *ALIYU* "............!






*PAGE* 13-14






.....................πŸ“–Ko kalon inda suke beyiba ya huce ya dauko phone 'dinshi ya bar gidan
kwace hannunta Deedee tayi tana kuka tace "me nayi maka kake neman kassara rayuwata kafa damin abunda nayi maka plz ba dan niba" murmushi yayi yace "laifi 1 kikamun soyayya da abunda nafi tsana a rayuwata wato Aliyu bayan kinsan irin mugun son da nake miki" wani mugun kalo ta watsa mishi tace "walahi walahi walahi dana aureka gara na mutu banyi aureba kuma abunda kamun kaje keda Allah" tana gama fa 'din haka ta juya zatabar gurin yai 'kara ruko hannunta yace "da kin daina wa halar da kanki dan saura 'kiris na malake ki in kinga ban aureki ba bana nunfashi" yana gama fadin haka ya saketa yabar gurin ciki ta huce tana kuka me tsuma zuciya






Annur yana shiga part 'dinsu ya samu hajiya a bedroom ko salama babu ya fa 'da room 'din kalon shi tayi tace "my son meya faro naga ranka a 'bace" kusa da ita ya xauna yace "hajiya na gaji da gafara sa banga 'kaho ba har yanxu banji inda aka kwana akan aurena da Deedee ba" ajiyar xuciya ta sauke tace "kwantar da hanka linka my son Daddyn ku nake jira ya dawo kuma yau xai dawo na riga na sanar mishi da komai yana dawowa xaije ya tada hankalin yayansa dan haka kadaina sa damuwa a ranka" murmushi yayi yamike batare da yace komai ba ya fice daga room 'din






da dare Daddy yana dawo wa hajiya ta tashi hankalin shi sai yaje ya samu Alhaji da zancan bikin Annur da Deedee
ko hutawa beyiba tasa yamike yanufi dakin yayan nashi






Alhaji Nura na xaune a parlour sa ya cin fruits Daddy ya shiga ko Salama babu kalon mamaki Abba yake binsa dashi xama Daddy yayi ya dau Apple 1 ya fara ci saida yagama yadau banana itama yacinye yakai hannu xai dau wani abun Abba ya rike hannu ya harareshi yace "amma baka da ta ido Suleman ka shigomin ba salama san-nan kaxo kafara cimun fruits ko"






hannun shi ya xame ya kali Adda yace "ba wan-nane ya kawoni ba nazo inji ina aka kwana akan lalatamun 'da da 'yar gurinku tayi" kalon mamaki Abba yayi mishi yace "dama mace tana iya lalata namiji?" "au bakada labari to inma baka sani ba kasani mata da yawa sun lalata maxa koma ga misali akan 'yar gurinka Fateemah" murmushi ta kaci Abba yayi ya kaleshi yace "to yanzu diyya xamu biyaka" hararar Abba yayi yace "ai dama dule ka anbaci dayya dan anci an tada kai da gadanmu" kai kawai Abba ya girgixa yace "bana so dugon bayani bacci nakeji kafa 'di nawa kake so kawai dan nasan rashin kudine yasaka yin wan-nan wautar" dariya sosai Daddy yayi yace "Nura a yanxu kudi ba damuwata bane abunda nake so shine tunda har sunriga sun yi masha'arsu to kawai a hadasu aure kowa ya huta"






wani irin mugun kalo Abba yayi mishi yace "walahi ko Fateemah ko tarasa mijin aure baxan aura mata lalatace irin Ibrahim ba" dariya Daddy yayi yace "in banda abunka to ai itama lalataciyar ce ita da take kai kanta har 'dakin shi ai tafishi laifi"






mikewa Abba yayi yace "kaga Suleman inda abunyi tashi ka fita" mikewa Daddy yayi ya kali Abba ido cikin ido yace "kuskure mafi girma da xaka tafka a rayuwarka shine hana Annur auran Fateemah koma ko ka aurar da Fateemah gawani walahi bata tsiraba da fatan ka fahimci abunda nake nufi" yana gama fa 'din haka ya juya yafice abunsa
ba abunda gaban Abba yake sai fa duwa komawa yayi ya xauna cikin tashin hankali yasan halin 'kaninshi Suleman sarai bashida hankali akan yaransa yayi nisa cikin tunani mommy ta shigo dakin ga ninshi a cikin wani hali yasa ta 'karasa tana tanbayar lafiya da kamar yayi shiru sai yatuna abukin kuka shi ake fadawa mutuwa cikin nutsuwa ya zayyane mata yadda sukayi da Alhaji Suleman






baki ta tabe tace "to yanxu meye abun damuwa aciki yariyar nan kowa yasan 'yar iskace irin Annur to me xai hana ahadasu auran tunda dama lalatace sai lalat.......!" daga mata hannu Abba yayi cikin fushi yace "tashi ki fita banasan ganinki" cikin dana sanin abunda ta fada tace "Allah ya huci zuciyarka" "Maryam kifita tun raina be 'kara bacci ba" tashi tayi jikinta a sanyaye tana me ladamar abunda ta aikata
tashi Abba yayi ya shige bedroom dan ya kwanta






washe gari takama Tharsday Abba yana zaune a parlour sa yana saka da war wara *ALIYU* ya shigo da salama amsawa Abba yayi ya shigo yasamu guri nesa da Abba ya gaida shi amsawa Abba yayi yace "dama ina nemanka" kai akasa Aliyu yace "gani Abba" "dama bawani abu bane gobe friday za'ayi daurin auren wani yaron abokina kuma nayi alkawarin daukan nauyin komai shine kuma abun yaxomun banida kudi ko xaka rantamun ko 30k ne"




"haba Abba saika rokeni" ciro rafar 'yan 50 yayi guda 2 yamikawa Abba daya Abba ya dauka yace "abiya sadaki da wan-nan ita kuma dayar kaje kasuwa ko ka aika ataho da goro da alewa ko ya kace" murmushi Aliyu yayi yace "hakan ma yayi Allah ya sanya alkari" "ameen ameen dama maganar kenan tashi kaje Allah yayi maka albarka" mikewa Aliyu yayi yanacewa "ameen Abba nagode" da haka yafice daga dakin mikewa Abba yayi ya dauko phone 'dinshi yara kira da mutane yana sanar mishi gobe akwai daurin auren da xa'ayi a gidansa (tofa ko auranwa xa a daura Allah masani)






Annur ne yaje yasamu Daddy da xancen ya sukayi da Abba murmushi Daddy yayi yace "kwantar da hankalinka Annur Fateemah dai taxama taka" wani irin ihu Annur yayi ya rungume Daddy yanacewa "gaskiya Daddy nagode sosai" yai wani fari da ido yace "harna hangoni ina hutawa da Deedee yarinya da gani xatayi ruw.....!" saurin rufe bakinsa yayi dan yakusa ka tubara kar Daddy yasan ba abunda ya shiga tsakaninshi da Deedee






murmushi Daddy yayi yace "Fadi da ihu zaka huta yaro" dariya Annur yayi ya mike yana rawa yafice dan yasan inya xauna xa'a iyayin katubara








Fateemah ce kwance akan ciyar Ammi suna ta hirarsu irinta 'ya da uwa kalo daya zakayiwa Deedee kaga ramar da tayi lokaci kadan duk ta xabge




kalon Ammi tayi tace "walahi Ammi ni duniyar nan ta ishene komai bayamun dadi" murmushi Ammi tayi tace "idai xakisa tunani arai nexai hana baxaki ji duniya ta ishekiba" mikewa tayi daga kwancen da take tace "walahi Ammi daga jiya xuwa yau gabana sai faduwa yakeyi abun harya fara bani tsoro" kanta Ammi ta shafa tace "addu'a xaki ringayi xaki samu salama" kai ta 'daga ta koma ta kwanta suka cigaba da hirarsu






Usman na xaune a dakinsa yanata boga game a phone 'dinshi Aliyu ya shiga da Salama ya fada kan bed yasaki ajiyar xuciya kalonsa Usman yayi yace "lafiya kake kuwa" kai ya kawar yace "lafiya" baki Usman ya tabe yace "bakada adalci Aliyu har yanxu fa Isham bedawo ba da kaine nasan baxa ka zauna a zariya na tsayin kwanakin nan ba" dagowa yayi yace "na mantane kirashi kace ko begama ba ya taho gida" murmushi Usman yayi ya kashe game 'din ya kira Isham yana dauka yace "kayi murna yaro Aliyu yace kataho gida" daga can Isham yace "da gaske koda wasa" "kai walahi da gaske nake, ashe da rabun za asha bikin dakai gobe" "kaidai bari yanxu xan tahoma" yana gama fadin haka ya kashe wayar








kalon Aliyu yayi yaga ya tsareshi da ido yace "malam lafiya kar ka cinyeni" harararsa ALIYU yayi yace "auren wa xa'a daura gobe" dariya Usman yayi sosai yace "lalai yaro yarone, yanxu ka yarda ina gaba da kai ko tunda har aka sanar dani za ayibiki amma kai ba a fada makaba" cikin 'kusawa da magana ALIYU yace "ni kawai ka fadamun aurenwa xa a daura" murmushi Usman yayi yace "to ba auren kowa za'a daura gobe ba sai.................!"










ba amun comment yadda nake so dan haka nima xan rage typing ko natafi hutun 2mouth








by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πŸ“•πŸ–ŠοΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)πŸ–Œ*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/


☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷


storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 11-12




..............πŸ“–Ruko hannunsa yaji anyi cinke da mamaki ya juya yaga ya Faruq ne cin fushi ya Faruq yace "kai Aliyu wan-nan yane irin wautace yazaka daketa me tayi maka" Aliyu na huci ya kali ya Faruq ya girgiza kai kawai yabar parlour cikeda ta kaici
kalon Deedee ya Faruq yayi dataketa faman kuka yace "kiyi hakuri Fateema kinsan halin Aliyu sai a hankali amma baya abu saida dalili me kikayi mishi" kai kawai ta iya girgiza mishi tabar gurin tana cigaba da kuka room 'din Ammi ta huce ta fa 'da kan bed ta fashe da kuka me tsuma zuciya
tana kukan Ammi tashigo ta ganta amma batayi gigin rarrashinta dan abunda yafi kuka ya halarta Deedee tayi








zaunawa Ammi tayi kusada ita tana saurarun kukan nata jin bazata iya jurewa ba itama kukan zatayi ta tashi ta fice daga 'dakin ranta a dagule
cikin kuka Deedee take fa 'din "Allah ya isa tsakani na dakai Annur ka cuceni ka rabani da me sona so na gaskiya ka 'batamin suna acikin family mu bazan rama abuda kayimun ba amma zankai kararka gurin meduka shiyasan yadda zaiyi dakai" haka ta ringa sunbatu har bacci barawo ya saceta






fita daga gidan Aliyu yayi ba zame ko inaba zai gurin abukinsa Muzali
shi Aliyu duk wan-nan yawace-yawacen da samari sukeyi bayayi daga gida sai office saidai in zariya zashi dan sunda reshe acan










Muzali na ganinshi cike da fara'a ya tarbeshi yanacewa "yau agari ko dai 'batan kai kayine inmaida ka gida" harararsa Aliyu yayi ya nemi guri ya zauna
kalon shi Muzali yayi yace "amma dai bakada lafiya ko Aliyu" "me ka gani" Aliyu yayi maganar cikin fushi
dariya Muzali yayi yace "maida hukar Aliyu bawani abu bane gani nayi duk karame gaka bakada wani kuzari walahi" ajiyar zuciya Aliyu yayi yace "to uban sa ido banida lafiya amma yanzu naji sauki" "habawa nifa ince karame sosai, nikuwa Aliyu ina Deedee ne.2days bataje islamiyya ba" baki Aliyu ya tabe yace "itama batada lafiya" dariya sosai Muzali yayi yace "kai yaran yanzu Allah ya shiryeku sabuda soyayya tamuku dadi in 'daya zaiyi ciwo sai 'daya yayi hmmm duniya taimuku dadi" tsaki Aliyu yaja yace "malam ka takuramun walahi kamun shiru kona tashi natafi" cikin mamaki Muzali yake kalonsa yasan koya kayiwa Aliyu maganar Deedee tofa in baka ganin fara'arsa zaka gani amma yau duk ya 'bata rai lalai akwai lauje cikin na 'di zaiyi binkice meya ha 'dasu yar suke ciwo tare
da wan-nan tunani ya mike ya fice yabar Aliyu da har yafara bacci








washe gari aka salamu Annur daga husbitel dan yaji saki sosai
yana xaune a parlour Hajiya ba abunda yakeyi sai murmushi kalonsa hajiya tayi tace "hmmm meya farune kaketa zuba fara'a haka" dariya yayi yace "gaskiya ni mugune yanxu fa ko Deedee xata ha 'diyi Qur'ani dan ran tsuwa ba me yarda da ita" "to wa zai yarda da ita ankamata dumu-dumu, yanxu ba wan-nan ba hajja takawo layun nan kuma na bawa Zakiyya ta bunne su" saurin kalonta Annur yayi yace "Zakiyya fa hajiya kinsan yarinyar nan da shirme da kinsani bari kikayi muka dawo" "in bari mudawo kuma kasan da zafi-xafi akan daki 'karfe kuma na mata kashedi sosai" dariya Annur yayi yace "yanzu abu 'daya ya rage kicewa daddy yaje yace sai anbani auran Deedee tunda ita ta lalatani" dariya hajiya tayi tace "ai ba sai ka fa 'daba wan-nan azaune take in sunki yarda mu 'dau mataki daya dace" ihun murna Annur ya saki yace "kaini angon Fateema naji dadi na" tashi hajiya tayi tana dariya tabar parlour
duk abuda suke fa 'da Zakiyya najinsu ta tabe baki tace "hajiya duk da ke kika haifeni amma baxan bari ki cutarmin da abunda nake so ba dan haka ma na kona layun da kika bani na bunne in Deedee zaku kashe ko a kaina zantayakuma dan tanaso abunda nafiso a rayuwata amma in Aliyu zaku ta 'da zan iya karku gaba 'daya" ita ka 'dai taketa zancen zuci








bayan sati 1
Aliyu ya warke sosai haka Deedee da Annur kuma duk a cikin satin ba wanda yaga 'dan uwansa a cikinsu
abun duniya yayiwa Aliyu yawa yana so yasa Fateema a idonsa ko ya samu sassauci a cikin zuciyarsa amma abu ya gagara




itama agurin Deedee hakan take so take taga Aliyu tamai bayani ko ta samu sassauci amma ina tarasa inda zata ganshi batada aiki kulum sai kuka tun Hafsat na tan bayarta harta gaji ta zuba mata ido abunda yafi damunta ma yanxu inta gaida mommy ciki-ciki take amsa mata sa 'banin daddy da inta gaidashi zai amsa yaitayi mata nasiha ba wadda take jin dadinsa a gidan sai Amminta kowa ya daina ganin girmanta a zatunta koda abunda ake zargi da gaske ta aikata batayi zatun za ajuya mata baya hakaba mu samman Aliyu ya bata mamaki






shikuwa Annur nema yake ya ha 'du da ita ko zai kara kula wani abun a kara yadda da abuda ake zargi shiyasa yake fakonsu sai yaga Deedee da Aliyu tare zai kara hada wani fadan amma yana tsuron Aliyu ya 'kara jibgarsa








Deedee taxo fita kamar a mafarki saitaga Aliyu ya xaune a parlour jikinta a sanyaye ga tsuro da ya mamayeta ta durkusa a gabansa tana hawaye tace "walahi ya Aliyu abunda kake zargi ba gaskiya bane" mugun kalo ya watsa mata yace "ko kowa be yarda ba ni bazanki yarda ba sabuda da idona na ganki ko idona zai gane mun karyane" kai ta girgiza ta Bude baki tayi da niyar yin magana ya d'aga mata hannu yana jifanta da mugun kalo yace "bakida abunda xaki fadamun nariga nasan irin abubun da kike aikatawa a bayan fage ahaka kamar ta kirki nan kuwa 2 face ce ke"






kwalar da ta cika mata idoh ta share murya na rawa tace "walahi ya *ALIYU* ba abunda ka ke tunani bane nifa......" hannu yakara daga mata tareda wurga mata harara ya fice daga parlour ranshi a b'ace






agurin ta durkushe tasaki kuka me sauti a dunaya ba abunda ta tsana irin mutum ya ringa xarginta musamman da babban laifi irin xina






itace xata aikata wannan babban laifin da ranta da lafiyarta tana cikin haiyacinta
tana cikin kukanne Hafsat ta shigo ta tadda ita ahaka kara sowa tayi da sauri ta d'a gota ta maida ita kan kujera ta fara

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads