Showing 12001 words to 15000 words out of 42022 words
Chapter 5 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt
bayanta
shikuwa Annur tunda ya zube akan kujera bekara mutsiba kai kace bashida rai ba bunda yakeyi sai hucci kamar kumurci
koda hajiya Sareena taji ko ajikinta dan sunfi kusa kuma tasan za arina yanzu abunda ya rage mata ta zuga Annur kar ya rabuda Fateemah har sai ya cimma burinsa akanta duk da tanada aure daga baya su lika mata ciki kinga dule Aliyu ya rabu da ita inma zuciyarsa bata bugaba
Aliyu na kwance Sameer ya shigo da wasu abokan Aliyu suka fara yimishi Allah sanya alkari shi ya dauka auran Fateemah da wani suka zo yimishi murna saida suka huce Sameer ya kalesa yace "angon Fateemah yaudai Allah yayi kalon mamaki Aliyu yayi mishi yace kana nufin dani aka daura auren Deedee" dariya Sameer yayi yace "gaskiya na tayaka murna Abba ya iya bazata dama ni akayiwa haka" cikin faduwar gaba yamike yafice da ya Sadeeq yayi karo yarike hannunsa yace "kai kadai ne zaka fadamun gaskiya yaudawa aka daura auren Fateemah?" murmushi yayi yace "na tayaka murna Aliyu dakai aka daura auren Fateemah" sakin hannunsa yayi cikin farin ciki ya...........!
by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πποΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)π*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
βπ·βπ·
*BAΖIN GIDA*
βπ·βπ·
storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
*PAGE* 19-20
.........................πCup 'din hannunta ne ya subuce gaba 'daya maga nin ya zube a kasa hakan ta farune dalilin tsawar da taji a bayanta juyowa tayi jikinta na kerma tana kalon Aliyu ta ya tsareta da ido cikin lion voice 'dinsa yace "uwar me kikeyi a nan ba kike waiwaye kuma da alamun rashin gaskiya a tattare da ke" jikinta na rawa tace "walahi yaya ba komai" murmushi ta kaici yayi ya kali inda cup din ya fashe ya kaleta yace "hmm da zaki daina wa halar da kanki akan shan wannan shirmen dan ba abunda zanyi da macen da ta zubarda mutuncinta a titi" ido Deedee ta runtse maganarsa tana mata ciwo a rai amma bata ce komaiba sai kai da ta sunkuyar tana zubda hawaye baki ya tabe yace "banaso ganinki ki bacemun daga nan" saurin kebeshi tayi tabar kitcen din yabita da harara ya sa mofa ya goge gurin da maganin ya zube dan bayaso yaga guri da dauda ya dauke fa shashshen cup 'din ya hada tea 'din da yazo sha ya bar kitcen 'din
Fateemah 'dakin Ammi tayi jikinta na rawa
Ammi na ganinta a rude tasan akwai wanda yayi wata tsawa ko wani abun kalonta takeyi da tausayawa amma ba tayi magana
zama Deedee tayi har lokacin jikinta rawa yakeyi tashi Ammi tayi ta zauna a kusa da ita ta dafata kalon Ammi tayi hawaye na zuba daga idon ta tace "Ammi Annur ya cuceni asa har yanzu muta nan gidan nan suna zargina walahi walahi walahi Ammi ban taba aikata zina amma meyasa mutane suka kasa fa himtata" nunfashi Ammi a sauke tace "kiyi hakuri duk daren ba dadewa gaskiya zatayi halinta shikuma Ibrahim daya dora miki jakar tsaba yasaki cikin damuwa Allah sai ya sashi a wanda yafi naki kiyi hakuri kijira lokaci" kai ta gyada kice da gamsuwa ta kwanta akan ammi tana sauke a jiyar zuciya
har cikin ran Aliyu beji dadin a bunda yayiwa Fateemah ba ko banza yanzu matarsa ce kuma masoyiyarsa amma ya zaiyi in ba haka yayiba bazatayi na damar abunda ta aikata ba "to in batayiba fa?" wata zuciyar ta jefo mishi tabbayar kai ya girgiza yana cewa "kai da idona fa na ganta a kan wani kato taya za'ayi ace sharrine" shigowar Usman ce ta katse mishi tinanin da yakeyi
zama Usman yayi yana dariya yace "angon Fateemah me yake damun kane" hara rarsa Aliyu yayi yace "walahi zan fasa maka baki yanzu nan" ido Usman ya zaro yace "oh dan kayi aure shine zaka fasawa yayanka baki to nima nakusa shiga daka ciki" mugun kalo Aliyu ya jefa mishi yace "uban wa yace maka ka isa aure da zakayi" rike haba Usman yayi yace "kana kanina kayi aure saini na kasayi sabuda ban isaba" baki Aliyu ya tabe yana kuna tv yace "dan ka girmeni ai baka kaini lafiya ba" dariya Usman yayi yace "ahaka kakeda lafiyar kana da mata take kwana a wani gurin ba dakin kaba inda nine da saita dawo dakina da kwana ko mu tare a satinnan" baki Aliyu ya tabe ya cigaba da kalonsa batare da yace komaiba
washe gari sai yamma Annur ya dawo gida yana shiga parlour su ya tadda hajja tazo da fara'arsa karasa ya zauna ko gaisuwa babu yace "hajja manyan kasa tunda na ganki na san akwai news me zafi" baki ta tabe take "wato baka maida uwarka da ubanka a bakin komaiba jiya suka ringa kiranka kaki 'dagawa kai ga tantiri ko" dariya yayi yace "hajja kenan jiya akwai abunda ya rikeni a kwana agidan abokina" "hmm kodai karuwa ba" dariya yayi yace "ai hajja yanzu karuwai basa ciniki ka tseda budurwa guda daya wace batasan komaiba kafara nuna mata meye rayuwa sannan ka maida ita 'yar hannu yadda bazataji tana sha'awar kowaba saikai ko fita zakayi wata 'kasar ba ruwanka ka tafi da abarka kiga ba ruwanka da daukan cututtuka a jikin ka ruwai" rike haba hajja tayi tace "yaran yanxu Allah ya shiryaku" dariya yayi yana kalon hajiya da ke harararsa yace "ai kinsan yanzu duniya ta cigaba yara su suke sarrafa iyayensu dan haka sace zuciyar budurwa da kudi ba wani abu bane" fulow hajiya ta cilo mishi tace "kasan ka iya sace zuciyar 'yan mata ka kasa sace ta Fateemah" kai ya girgiza cike da takaici yace "so nayi saina rabata da wannan Aliyu n kafin na sace zuciyarta amma sai wannan Abban yamun shigar sauri ya aura mishi ita" baki hajja ta tabe tace "to an yanka ta tashi Fateema batasha wannan maganin nan ba dan haka dulene nazo asamu wata afutar" cikin mamaki Annur yace "wayace miki batasha ba?" "hmm da tasha da tuni maganin yafara aiki kuma naje gun malamin yace batasha ba kuma harda taimakon aljanun jikinta da wannan Aliyu sune sukayi sanadin taki shan maganin" huci Annur ya fara yana cewa "sai nayi a jalin Aliyu a kan Fateemah wata rana" hajjace tace "in ma huka zakasa ka yanka ta ba ruwan wani yanzu malamin yace saida muyi anfani da kwakwalwar mu muhada tugu da kanmu muraba auren in ba hakaba aljanunta baza su bari a cutar da itaba" sai yanzu hajiya ta sako musu baki tace "yanzu hajja ke zaki fadi me ya dace muyi" murmushi tayi tace ku matso kuji
matsowa sukayi ta fara yi musu rada a kunne can suka saki shewa tare harda tafawa kafin Annur yace "gaskiya hajja kanki naja kiga ba wanda zai zargemu kuma ba me cewa ba haka bane" "hakane hajja Allah ya ja kwana" "ameen nifa akan yarana da jikokina ba abunda bazanyiba" dariya suka saka suka rungumeta suna dariya
wunin yau cir Deedee bata fito ba dan tana tsoro ta hadi da Aliyu ko mommy duk da mommy bata mata komai ko maganar banza amma bata sakar mata fuska shiyasa bata san haduwarsu garama Hafsat ta ware sun cigaba da harkarsu
yau monday kuma ranar zuwa islamiyya ce 3:00pm Hafsat ta shirya ta fito ta biya 'dakin Ammi tace Fateemah ta shirya da yake Ammi ta tafi gidan hajiyarsu su gaisa ita kuma Deedee tama manta tanada wani aure bare ta tanbayi izinin koda mommy ne dan haka ta shirya suka tafi makaranta
Aliyu tunda la'asar yake zaune a parlour amma har 5:38pm bega giftawar kowa ba dan haka ya fara kwalawa Hafsat kira amma shiru
Isham dake shigowa yanzu yace "aikuwa yaya Hafsat ta tafi makaranta na gansu ita da Deedee" " *Deedee* Aliyu ya furta a hankali" ba abunda gabansa yakeyi sai faduwa ga kishi da yake taso mishi amma be nuna ba ace "owk" yacigaba da abunda yakeyi
6:08pm suka shigo parlour suna hira harda dariya 4eyes Aliyu da Fateemah sukayi take gaban Fateema ya fadi ganin irin kalonda Aliyu ke jifan ta dashi jikin tane ya fara rawa tazo zata huce shi rai a hade yace "duk kuzo nan" gabansu na faduwa suka zo gabansa suka zauna ya kali Hafsat yace "uban wa yace ki dauki matar aure ki fita da ita batare da izinin mijinta ba in ita batasan darajar auren taba kema bakisan darajar aurenba?" juyawa yayi ya kali Fateemah yace "da izinin ubanwa kika fita ko abokin zinar takine ya baki izini?" gaba dayansu rasa me kwakwkwaran mutsi akayi sa kuka da Fateemah ta fara sabuda jin ciwon abunda Aliyu ke fada mata tsawa ya duka musu yace "bada ku nakeba" amma shiro sun kasa magana fusata yayi dan bayaso yayi magana a ki kulashi dan haka ya danko Fateema dake kusa dashi ya...........
by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πποΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)π*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
βπ·βπ·
*BAΖIN GIDA*
βπ·βπ·
storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
*PAGE* 21-22
.......................πYayi da nufin dukanta ya jawota da 'karfi ita kuma jikinta ba kwari gaba daya ta tafi luuuuu tafada jikinsa ajiyar zuciya ya sauke yasa hannu ya tureta yana harararta yace "tashi kibar nan tun ban karya kiba" mikewa tayi jikinta a matukar sanyaye tabar gurin nannayan nunfashi ya sauke ya kali Hafsat yace "indai ta 'kara fita bada izininaba to ki tabbata kezan hukunta" kai ta gyada mishi cikeda tsoro "tashi ki bani guri" ya fada yana kumawa ya kwanta itama Hafsat mikewa tayi tabar parlour shikuwa ido ya rufe kamar me bacci shidai yasan harga Allah yana son Fateemah amma besan meyasa duk lokacin da ya tuna yadda ya tadda su da Annur jiyake kamar yasa huka ya yankasu dukansu kuma yau yaso ya 'dan samata amma ta tashi ta fado jikinsa ta kashe mishi jiki ganin bazai iya jure zamanta a gurinba yasa ya salameta kawai amma watara zata 'kara yimasa laifi saiya fanshe harda na yau
Deedee na shiga 'daki suka hada ido da Ammi ganin kalon tuhumar da Ammi take mata yasa ta dauke nata idon taje ta canza kaya ta dawo ta zauna kuma haryanzu taki yadda su hada ido da Ammi
muryar Ammi taji tana cewa "sannu alhudahuda sai akace dan anbarki a gidanku ba'a kaiki gidan mijinki ba kiringa fita sakaka ko to tunda abun naki ba tunani a ciki zan samu yaya nace mishi mungama shirinmu kitare wannan sat......!" maganar tace ta makale saka makon riko kafarta da Deedee tayi da 'karfi tana kuka tace "plz Ammi kiyi hakuri walahi bazan 'karaba indan kuka bawa yaya Aliyu ni kasheni zaiyi dan Allah kiyi hakuri kinji" kukane yaci 'karfinta ta ha'de hannu wata alamun ro'ko
dagota Ammi tayi ta rungumeta tana bubbuga bayanta idonta cike da kwalar tausayin 'yar tata da gowa Deedee tayi tace "kin hakura ko Ammita" kai Ammi ta gyada mata kwai dan bazata iya maganaba kar ta fahimci halin da take ciki
murmushi Deedee tayi tace "shiyasa nake 'kaunarki Ammina" murmushi itama Ammi tayi
Deedee ta maida kanta kan cinyar Ammi ta kwanta tana bata labarin 'yan makarantar su
yau tunda Annur ya fita bedawoba har dare ko wayoyinsa aka kira akashe ga yau sukayi dashi zai kawo musu wanda zasuyi aikin dasu hajja sai masifa takeyi ita kuwa hajiya Sareena kasa magana ma tayi sabuda 'bacin rai
suna bedroom dukansu Zakiyya ta shigo 'dakin ta zauna kusa da hajiya tace "gaskiya yaya Annur bashida hankali yasan yau mukayi dashi zai kawo wanda zasuyi mana aiki akan Aliyu amma ya fita gashi har lokaci ya kure wata kila sai gobema zai dawo" hajja na huci tace "rabuda dan durin uwa sai kace ba dan shi muke wannan wahalar ba so yake in uban nasu ya gina musu gida suka tare yasan ya zaiyi da ita kuma tariga lokacin tazama raguwar wani" kwafa hajiya tayi ta 'kara dauko waya ta kirashi amma har yanzu wayar a rufe mikewa tayi tace "kinga hajja kirabu da Annur tunda munyi niyar abunmu karmu fasa yanxu akwai wani a kasan unguwarmu sunasa Gago to nasan shi zai iya yimana aikin mu kuma a ganina abari sai ranar da ta tare sai ayi aiki kinga mutane zasu fi yadda ko" kai hajja ta gyada tace "gaskiya ne hakanma yayi bari na tashi na tafi har ace nice uwar zuwa gidan 'da" dariya hajiya tayi tace "to wani ya haifa miki saidai kice ita 'dayar sirikar taki zata ringa jin haushi" baki hajja ta tabe tace "ubanwa zaije gurin wannan lusarar batada aiki sai Allah yace Annabi yace jaka kawai" dariya suka sheke da ita harda tafawa
Annur kuwa yana can gurin baby Nafee ita ta kirashi sun tafi Abuja bikin wata 'kawarta sai sunyi 5days zasu dawo shiyasa tasa ya kashe wayarsa kuma bai mata musuba
Aliyu sai da yayi salar magrib ya shiga 'dakin mommy tana ganin sa ta saki murmushi cikin mamaki ya 'karasa cikin 'dakin dan rabonsa da yaga murmushinta tunkan ya rauri Fateemah gaidata yayi ta amsa cike da fara'a kansa a kasa ba tare da ya dagoba yace "dama naje mu gaisa da Abba naga baya nan shine nashigo parlour kuma sai bacci ya daukeni" murmushi tayi tace "na ganka kana bacci bayan ka gama firgitamu 'diyata ko" "wace 'diyar taki kuma?" harararsa tayi tace "wace 'diya gareni in ba Hafsat ba sun dawo daga islamiyya ta shigo tana ta hurihuri na tanbayeta tace kaine" sosa kai yayi yace "mommy yaranki basa jin magana walahi" dariya tayi tace "hakane sai hakuri jiya Abbanku yamun maganar tarewarka da Fateemah yace intanbayeka in kagama shirinku ranar juma'a sai ku tare" kai ya sunkuyar yace "da kin fada mishi ya 'daga tarewar tunda ba sauri akeyiba nid.......!" hannu mommy ta 'daga mishi tace "bana son shashanci tunda an riga an daura auren ai gaggawa kuma ta kare dan haka zancenma a daga be tasoba" kai ya girgiza tamike yayiwa mommy salama habar dakin
a 'dakinsa ya yada zango ya zauna ya dafe kansa ya rasa me yakeji aransa farin ciki ko bakin ciki ajiyar zuciya ya sauke nan da 4days za'a bashi Deedeensa amma ba abunda yaje ji ko yake tunani sai Annur
wata dabarace ta fado mishi to mezai hana kawai ran Juma'ar ya huce da ita zariya kinga can yayiwa Annur nisan da zai ringa ganin Deedee mikewa yayi yashiga toilet yayi wanka ya dauro lalwala yazo yayi salar isha da shafa'i da hutiri sannan yada key 'din mutarsa ya fice daga gidan
Ammi tasan da tarewa Fateema amma batayi gangancin fada mataba sabuda tasan damuwa zata 'dorawa kanta gara tabari sai ranar in yaso tayi na huni daya ta hakura
washe gari Aliyu yaje yasamu Abba da maganar shifa zariya zai tafi da Fateemah kuma Abba be hanaba cewa yayi ai yanxu Fateemah a 'kar 'kashinsa take sa yadda yaso zaiyi da ita dan haka bamai hanashi tafiya da matarsa
Annur anacan duniya tayi mishi dadi anata tsinkar fire shida babyNafee dan mantawa yayi da gida ma gaba 'da yamma yana nan yana tama in yadawo bazai jira sai su hajja sunyi wa Deedee shariba kawai saceta zaiyi kowa ya huta kawai ya gaji da tufkar da yakeyi tana warwarewa yaci ai washin in yakoma rai Asabar to lahadi zai saceta dan ya gama tsara yadda zaiyi ya sacetan
Deedee na kwance a bedroom 'dinsu Hafsat ta shigo ta zauna kusa da ita tace "wai ke Deedee kinsan meyake faruwa ma kuwa" mikewa zaune tayi tace "bansani ba sai kin fada" "hmm lalai yarinya ansha dake to bari kiji ran Juma'a yaya Aliyu zai huce dake zariya" cikin tashin hankali take kalonta tace "kifadamun gaskiya banason irin wannan wasa" "kisan Allah da gaske nake mommy naji tana maganar itada ya Faruq" cikin tashin hankali da ba duwar gaba Deedee ta mike ta fice da gudu bin bayanta Hafsat tayi itama da gudu
Deedee na fita tazo kofar parlour sukayi karo da *Aliyu* jin tayi karo da mutum yasa ta daburce ta kankamesa shikuma ganin tafara jefashi wani hali ga sai yawo yake ajikinsa ya doka mata wata razananniyar tsawa wadda hatta Hafsat dake ta howa saida taci burki Deedee ji saukar muryar shi a kunnanta kuma ta tabbatar da shi ta kankame take zuciyarta ta tsinke kankace kwabo tayi baya luuuuuu a sume....................
by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πποΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)π*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
βπ·βπ·
*BAΖIN GIDA*
βπ·βπ·
storry and writting
by